← Book details Muguwar Suruka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 9

Sashe 7

Muguwar Suruka Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Bayan 'yan kwanaki da faruwar haka Suhaima ta shiga laulayin ciki, Safwan yayi murna sosai amma idan ya tuna da abinda Hajiyar sa tace sai Hankalin sa ya tashi yace wa Suhaima su zubar da cikin tace ita baza ta zubar ba inshi baya so ita tana so, haka ya hak'ura sukai ta kula da cikin Saiham ce ta lura da irin sauyin da ta gani tare da Suhaimah da kuma yadda taga Safwan yana kula da ita yana tarai rayar ta aiko Hankalin ta ya tashi sosai ta tafi take sanar da Momyn ta don ta dai na shiga harkar Hajiya bare ta fad'a mata.
Momyn Saiham ce to kira Hajiya take shaida mata abinda ke faruwa Hankalin ta ya tashi sosai tayi gidan tana zuwa taci sa'a Safwan yana gida tana, shiga parlorn ko sallama batayi ba ta fara masifa tana zagin Suhaimah "dan ubanki zo ki tafi gidan ubanki cikin shege ba a nan gidan ba kije ki nemo uban D'anki amma ba Safwan ba Hankalin Safwan ya tashi sosai yana bawa Hajiya hak'uri "Hajiya dan Allah kiyi hak'uri ki yafe ni wallahi cikin nan nawa ni ba na wani ba.

Ai Hajiya tana jin haka ran ta yak'ara b'aci tace "Wallahi Safwan ka k'ara cewa cikin nan naka ne sai na tsine ma kuma wallahi a gurin nan ina so kasaki yarinyar nan kafin rai na ya b'aci.
Kuka yake kamar k'aramin yaro yana bawa Hajiya hak'uri amma kamar bata san yana yi ba haka yana ji yana gani Hajiya ta bashi takadda ya rubuta mata saki d'aya yana kuka ya mik'a mata ya fice ya bar gidan Hajiya kuwa murna fal cikin ran ta amma duk murna da Hajiya take yi bai kai Saiham ba don ita ji take kamar anyi mata albishir da gidan aljanna don ita dama ta tsani, Suhaima saboda murna bata san lokacin da ta rungume Hajiya ba tana godiya yanzu Safwan ya zama nata ita kad'ai.
[9/2, 2:44 PM]
: .
*MUGUWAR SURUKA*
EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*
_Writing by_ *:-pharteemarh*
_Story by_ *:-bebe'ath (yar gatan hudah)*
_Edited by eloquent editor_ *:-bebe'ath*
~page~
65to70
Mayafi Suhaimah ta d'auka ta tafi gida tana kuka tana shiga Momy ta ganta tana kuka da sauri ta taho ta rik'e ta hankalin ta a tashe ta fara tambayar ta
Suhaimah lpy?
Mai ya faru?

Tana kuka take sanar da Momy abinda ya faru suna zaune sai fa Dadyn ta ya shigo Momy ta fad'a mai abinda ya faru rain shi ya b'aci sosai zai fara magana kenan sai sukaji sallamar Hajiya Bilki tana zuwa ta fara zayyana musu k'aryar da gaskiya ita dama tun da akayi auren nan yarinyar nan yawon ta take tafiya idan tayi mata fad'a tayi mata rashin kunya shiyasa ta zuba mata ido kuma da naga tana yawon ta na hana Safwan ya kusance ta na haramta mai shiga d'akin ta toh kunga yanzu ga abinda ta d'ebo don haka mu cikin nan ba namu bane sai ku nemi maishi.
Kuka sosai take tana fad'in wllh cikin sa ne Dady ne ya bige mata baki tare da fad'in ki rufe min baki kafin ran ki ya b'aci a nan gurin.
Waya ya d'auka ya kira Safwan yace yazo yana neman shi yanzu, yana isowa gidan yaga Hajiya hankalin sa ya tashi da ya tuna da gargad'in da tayi masa.
Dady ne yace Safwan ina tambayar ka ka fad'a min gaskiyar zancen nan kanshi a k'asa yana hawaye yace gaskiya Alhaji ni bansan da cikin nan ba banawa bane, yana gama fad'in haka ya tashi ya fita saboda wani kuka mai k'arfi da ya kwace masa.
Chapter 7 · 0% Book details