← Book details Mijin Kwaila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 9 OF 14

Chapter 10.

Mijin Kwaila Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Isha'q yad'an murmusa yana shafar sumar kanshi,
Sadiq yace "Allah am serious abokina,yakamata inga wannan zahran tauraruwar mata.
Isha'q dake mi'kewa tsaye yana tafiya abinshi yana bashi amsar"zaka ganta very soon but not today,"
Hindatu tasakeyin dariya"isha'q bani phone number nata my be mu saba kafin tazo gida,idan dai tanada son jama'a."
Gaba yayi abinshi yana bata amsar"kidaice zaki koyamata gulma da kitififi kawa,"
Duk sukayi waje da sadi'q suna mata dariya.
Ajikin motar isha'q suka tsaya,sadi'q yana tambayar"abokina kamata yayi ashirya komai harkar girma kasan y'ammatannan yanzu suncika saka bidi'a a al'amarin aurensu."
"Banda zahra itakam batada wannan halin,"
Cewar isha'q wanda yabude motar yana kokarin tayarwa,
Sadi'q yabishi da kallon mamaki sam isha'q yawani canja kamar bashi ba,yatuna lokacin wancen auren yanda yaketa rawar jiki kusan koda yause maganar kenan yakeyi,koda yake watakila hakan nada alaka da rasa zahra dayayi akaro na farko yana tsoron rasa wannan zahran akaro na biyu.
Da sallama yashiga falon mummy tana zaune da hisnul muslim a hannunta,ta ajiye littafin bayan ta tsura mashi idanu fuskarta babu walwala,
Kusa da ita yazauna,lokaci guda yana matsa kafafunta"barka da yammaci mummy yau kindawo aaibiti da wuri hope lafiya dai".
Yatambaya dukkan hankalinshi gareta.
Tayi kokarin kauda damuwar dake kan fuskarta dacewa"banmaje asibitin ba yau banajin dadin jikina,nayi handling komai wa dr.aysha nasan zataji da komai "
Isha'q ya gyad'a kai yana kallon zalla damuwar dake fuskarta,
Yajuya ga hanan wacce take buga game hankalinta kwance yace"jeki d'akinki kiyi wasanki inason kadaicewa da mum".
Tamike abinta duka kanta yanaga game,
Yasake duban dr.rukayya akaro nabiyu yace"mum akwai zalla damuwa akan ni'imtacciyar fuskarki mai kwarjini pls mum sanar dani matsalarki i will save it insha Allah."
Kai ta girgiza mashi''banida wata damuwa isha'q kawai ina nazarin yanda zakaji dad'in rayuwar aure da yarinyar da kwata-kwata batasan me kalmar aure take nufiba,ina tunanin yanda zakaci gaba da rayuwar tazuranci alhalin kanada mata,ina nazarin yanda zaka zama *mijin kwaila*kuma mijin dazaiyi zaino,ina hango maka matsalar kada zahra tagirma ta gujeka bayan ta fahimta who you are.isha'q inajiye maka ka rainar ma wani mata".Kalamanta sun d'aga hankalin isha'q wanda idanunshi suka kad'a jajawur yana kallonta cikin idanu yawani koma kalar tausayi,musamman idan katuna duk soyayyar dayakema zahra saboda wata zahrance ba wannan fake zahran ba,
Ya sauke numfashi murya a raunane yace"pls mum don't say that,bana tunanin zahra zata gujeni bana fatan insake rasa zahra bayan tadawo gareni,kamata yayi kiyi courage d'ina akan zahra but kema nasan u feel loved her,nasani zahra tayi kankanta amma wata rana zata girma mum. Bajikin zahrane yake 'kayatar daniba da Zahra ko babu zahra zan iya kame kaina bazanyi abinda nasan addinina da al'adata bazasu soba."
Dr. Ru'kayya ta danyi dumm kafin tami'ke tadawo da littafin addu'o i tace"kaje kayi isthakara isha'q,nakuma saka malam babba yatayamu da rokon Allah akan zabin damuke so.amma nikaina inajin son zahra har cikin zuciyata sai dai halinta nake gudu wanda kowa yake kuka dashi"
Isha'q dake duba littafin yace"komai mai wucewane mum,kada ki kalli wannan ki hango alkairan dake tare da ita ba sharrintaba."
Mum tace hakane Allah yayimaka albarka,
Ameen yace gami da mi'kewa yahaye upstairs abinshi.
***************
Lala..la.la..lah.. ubanka ta tsinke mata azo asai nama sauran 'kashi da y'ar tsoka....muryar zahra data karad'e kaffatanin unguwar ce ke rera wa'kar zagi bayan d'an sabo ya kwasheta da mari,lokacin data jima 'kaninshi wankan gawayi.
Abinda yafaru kuwa shine hamid 'kanin d'an sabo,dayake gidansu dukansu fararene,shine yake tsokanar zahra dacemata wankan baqi asarar ruwa ko yayima kamar baiyiba,zahra dai tasan ko giyar wake tasha hamid yafi 'karfinta don garjejene zahra tarasa hanyar dazatabi tayi ramuwar gayya,hakan yasakata kama 'kanin su d'ansabo mesuna dady taje dashi gidan anty bilki wata makwafciyarsu datake shiri da zahra kamar me,don ita zahra dariya ma take bata.
To shinefa anty bilki tana bacci batasan shigar zahraba,tasamu gawayin da anty bilki take girki dashi tadaka a turmi lu'kwui ta yima dady wanka dashi tas duka jikinshi,bayan anmashi wanka da fararen kaya,
Yaron yafito waje yana kuka karantse aljanine.
Koda d'an sabo ya tambayi ba'asi yaro yace zahra ce,
Hargida d'an sabo yaje yakai kashedi wa umma,umma takama zahra tayimata dukan tsiya.
Dalilin dayasaka tatara duwatsu sunkai cikin fanteka ta tattaro basawanta wato su ummilolo suka dinga yima gidan ruwan duwatsu,zahra itake bada common datace "ajefaa"zakaji duwatsu nasauka bisa kwano kamar aradu.
Ashe d'an sabo yana bayansu shine ya lalla'bo ya cafke zahra ogar tasu,sauram suna ganin haka suka ranta ana kare,sukabar zahra wadda d'an sabo yake kwashewa da lafiyayyun mari har biyu.
Agabanshi tadinga ro'konshi yayi ha'kuri bazata 'karaba,mutane suna bashi hakuri yana sake d'uramata ruwan ashariya.
Aiko yana sakinta tafara antaya mashi style d'in zagi sunfi kala d"ari tun yana girgiza kai saida takai yakasa jurewa,babu irin kiran da umma batayima zahraba amma inaa zaginta dayafi bama d'an sabo haushi shine da'akace bananar
babanshi ta tsinke mata suzo susai nama .
Sai da hawaye suka zubo mashi,musamman dayaga abokananshi sunata kwasar dariya hada masu ri'ke ciki.
'kwafa yayi duk randa yakama zahra kashetane kawai bazaiyiba. .
Zahrama tahad'a mashi plane cewarta aitasan gidan budurwarshi saitaje ta kunyatashi...

Kuna tare da maman meenat, Aisha T. Fulani Insha Allah
[12:03, 24/11/2017] hm: *MIJIN KWAILA*����‍♀


by maman meenat

editing (maman faruq)
Chapter 9 · 0% Book details