Chapter 5.
Mijin Kwaila Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Da touch light ya haske mata fuska ta d'ago fuskarta da alamar tsorata don sarai tasan abba bayada wasa.
Da 'karfi yakira sunanta"zahra,mekikeyi anan daga ina kije.?"
Kanta tsaye tace"wasa naje yi",
Abba ya gyad'a kai,"dakyau".
Kawai yafad'a yayi cikin gida abinshi,yayinda zahra ta rufa mashi baya.
Umma tana tsakar gida hankali a tashe abba yashigo zahra nabin bayanshi,
Umma tana ganin sundawo tawuce d'aki abinta ranta a dagule yake.
Bai tanka zahranba ya kutsa dakin da umma take,tahad'a kai da gwuiwa idanunta daf da hawaye.
Abba yadafa kafad'arta dakiran sunanta"amina,kiyi hakuri kifidda damuwar zahra acikin ranki,kisani kowacce rayuwa akwai jarabta mu tamu jarabtar kenan,don haka kima dena zancen wai kiyita dukanta.kitattara kici gaba da addu'a amma ni sam lamarin zahra yadena bani mamaki yakoma bani tsoro."
Umma tasauke numfashi,"to yaya zan'iya cire damuwa abban zahra,damuwa ai ita keyin kanta.ace babu rana ta ubangiji dazata fito takoma ga allah ba'azo ancedani zahra ta'aikata wani abuba.saikace tafi sauran y'ay'ane."
Abba yace"kul dakiyima yarinyar nan baki,mudaici gaba da addu'a,jiyama liman yazo hargida yanamun kashedi wai tajefashi kwata zashi sallar isha'i."
Umma tazaro idanu dafad'in "liman d'in dakanshi,,?
Abba ya gyad'akai"'kwarai kuwa,waisuna wasa anrufe idanunta toyazo 'ketare kwata tazata yarinyace shinefa ta cakumeshi,shikuma wai yana addu'ar zuwa masallaci bazaiyi maganaba.
Nana kokuwa ta sar'ke tajefashi kwata."
Umma duk da 'bacin ran datake ciki saida ta dara,
Data tuna yanda liman yake saka malummalum idan zashi masallaci.
Ta girgiza kai,"Allah ya shirya,"
Abba yace "ameen."
Zahra kam tuni ta kwanta abinta, bata tsaya neman abincin dareba don dama ba ma'abociyar cin abinci dayawa bace.
Barta dai ga 'kwalama wannan fa ogace.
**********
Bayan kwana biyu....
Zaune yake a tsakiyar grass carpet d'in daya gewaye tsakiyar 'katon falon,
Gabanshi laptop ce yana 'kara nazarin banbancin dake tsakanin zahransi da little zahra kamar yanda yasaka mata suna,
Gefe guda 'kanwarshice hanan wacce bazata shige tsaran zahraba,
Doctor ru'kayya ta tako ahankali daga stairs cikin dakakken leshinta mai tsadar gaske,jikinta akoda yaushe yana fitar da siririn kamshin turarenta mai tsada.
'yar kyakyawar fuskarta dabata tsufa tana manne da glass din daje kuma kayatata.
Isha'q da hanan atare suka mi'ke dukansu suna sakarmata murmushi
Tazare wayar dake kunnenta tana sakarma kyawawan yayan nata murmushi,
Ta kalli isha'q dafad'in"yayankane muke maganar yarinyar dakake bani labari,yace kamata yayi mushirya muje muganta ayi komai da lissafi,sannan yakira wayarka tana a kashe."
Isha'q yasaki dariya yace"nakashetane nasaka charge mum".
Yami'ke da sauri yana fad'in"mum kice kawai inshirya yau saigidansu pretty,yawani dun'kule hannuwa da naushin iska,wlh mum saikin ganta she's very beautiful nd younger."
Mum tace "kome kakeso isha'q aibaka ganin muninshi,haka kake tun kana yaro.sa'banin yayanka dayakeda a'kida dakuma ra'ayinshi na santseni."
Ya shafi gefen fuskarshi yana murmushi,"Allah mum tanada kyau,iluv zahra very much mum."
Zaunawa tayi tana canja channel''idan kagama surutunka inajiranka,haka zakaje kana rawar jiki ai yarinyar saita raina class dinka,ya murmusa yana tafiyarshi ta 'kasaita yace"haba mum kada kisa wannan ta'kwalar ta rainani mana."
[9/23, 10:00 PM] mum meenat: Yanuna hanan wadda ta zubama yayan nata idanu tana kallonshi,
Dasauri ta tashi ta la'be bayan mum dafad'in "mum zakije dani".
Doctor ru'kayya tamurmusa tace"kibari dai watarana saikije lokacin kinsamu hutun makaranta,yanzu kam ai zaki takuratane."
(tazata zahra babbace )
Isha'q kam fakaitarta yayi yasaki dariya dafad'in"sai mumcy",
Tana zaune tana kallon wani series yafito cikin hadadd'en yadinshi filtex mai yal'ki ruwan madara,
Kanshi yasha hular zanna bukar baqa,
Kafarshi cikin bakin takalmin daya matu'kar dacewa da shigar tashi.
Handsome and giant,
(abinda na raya kenan.)
Hadadd'en 'kamshin turaren American crew yakasa barin jikinshi,
Still akwai farin glass a idanunshi,
Ita kanta doctor ru'kayya tana alfahari da isha'q matsayin d'anta very handsome guy.
Yanada dukan qualities daya kamata mace taso a tattare dashi,
Dogone irin tsayin hadaddun maza d'innan,yanada fasalin 'karfi da jarumta a tattare dashi don 'kwarae mayen exercise ne.
Yana rud'a makwad'aitan mata da kamfacecen 'kirjinshi dakuma murdadden jikinshi.
Wankan tarwad'ane wato ya d'auko kalar doctor ru'kayya ne,
Sa'banin yayanshi aliyu dayake fari tar yad'auko kalar mahaifinsu.
Isha'q gogaggen matashine wayayye daya samu shedar kammala karatunshi na degree mataki na biyu akan mass communication ma'aikacine da gidan talabijin ta 'kasa wato NTA sosai yake samun sa'konnin yammatan dasuke mutuwar 'kaunarshi musamman don fara'arshi,
Dakuma iya zama da mutane don isha'q bdai iya kyautatawa ba.
'karasowa yayi jikinta ya tallafi fuskarta da hannayenta"am readay my mum"
Yafad'a da shagwa'barshi,memasa kyau.
Tace "i see"
Tami'ke tana gyara zama mayafinta dasaka glass d'inta,
Isha'q ya tsuramata idanu"am proud of you be my mother mumma."
Tashafi fuskarshi itama da murmushi,aranta tana jin zallah farin ciki saboda dawowar walwalar d'anta daya rasa tsawon lokaci.
Tare suka jera gwanin sha'awa suka shige cikin d'aya daga cikin motocin gidan,
Tazauna a mazaunin kusa da driver yayinda isha'q yake driving suka lula gidansu zahra.
Umma tagama gyara d'an matsakaicin gidansu,tana saka turaren wuta tajiyo sallamar doctor ru'kayya,
Taleko da fara'arta tana fad'in "lale marhaba da ba'kin yamma."
Doctor ru'kayya ta murmusa aranta tana yaba wayewar umma.
Ruwan randa mai sanyi umma ta'ajiye gaban doctor ru'kayya,bayan ta shimfid'a mata tabarma.
Dr.rukayya tazauna tana cire gilashin idanunta,likaci guda tana kai ruwan da umma ta'ajiye mata a baki.
Takur'ba kana tace da umma"nasan baki sanniba ko?."
Umma ta gyad'a kai"kwarai kuwa."
Dr. Ru'kayya tasake murmusawa tace a ta'kaice"sunana ru'kayya anas kado malumfashi,ni haifaffiyar malumfashi ce,iyaye da dangi mahaifina y'an canne,sai dai dangin mamana sune mutanen funtu'a, nayi karatun likitana anan Nigeria sai dai nasamu sakamakon zama babbar medical doctor ne a India,inda acanne na'karasa karatun nawa.
Nayi aure anan kaduna da mijina babban d'an kasuwane anan abubakar gumi,awancen lokacin ayanzu yanada manyan kamfanoni a ciki da wajen 'kasar nan.
Inada y'ay'a uku maza biyu sai autata hanan,
Babban sunanshi aliyu yayinda mai binsa shine isha'q,
Daganan haihuwa ta d'aukemun sai daga baya Allah yabani hanan,Aliyu yanzu haka yana 'kasar turkey yana kula da kamfanin mahaifinshi dake jigilar rid'i."
Muje zuwa
September 23, 2017at 10:27pm ·
*by anty y'ar charas*����♀
[12:03, 24/11/2017] hm: MIJIN 'KWAILA ����♀
NEW WORLD NOVELS
BY MAMAN MEENAT
EDITED :AISHA ABDULLAHI T. FULANI (UMMUN HYDR)
Wannan shafin naku ne yn (Madarasatul Tahafeezul Qur' an Funtua, Allah ka qaramana fahimta a
iliminmu)