← Book details Mijin Kwaila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 13 OF 14

Chapter 14.

Mijin Kwaila Part 1 Complete Hausa Novel · about 14 min read

Zahra ta gwada wasu daga cikin kayan yafi a 'kirga musamman takalman sunyi mata kyau a idanunta harwani canja salon tafiya takeyi wai yanda zata dinga yimasu uwande yanga take gwadawa,
Tun umma na korarta harta gaji ta zura mata idanu.
Mata kuwa har dare basu dena sintiri gidan umma kallon lefe ba.
Kwanci tashi bawuya gamai tsawancin kwana,cikin juyawar lokaci dare yakan wanzu yabada safiya safiya tazama maraice maraice yakoma dare,
Acikin wannan juyin na lokaci Allah yakawo mu ranar da take d'aurin auren zahra.
Abun kamar yaune akafara zancen amma dayake komai baida wuya awajen Allah saigashi lokaci yayi,shiyasa bahaushe yake cewa komai akasama rana tozaizo,hakanne kuwa tabbas!.
Ango isha'q cikin d'anyar shaddar githzener dinkin boda wanda ya masifar fito da tarin baiwar kyau da kwarjinin da Allah yabashi,gefe guda yakwafa hula kalar shaddar jikinshi mayen turarenshi yana aikin fitar da 'kamshin da'akoda yaushe yake manne jikinshi,
Akwai bakin takalmin Gucci akafarshi sai siririn glass dake kuma 'kayatar da kyakyawar fuskar tashi,
Lokacin daya fito cikin gidan ta'ke yake da mata y'an uwa da abokan arziki,gefe guda mummy da tarin 'kawayenta anata hada-hada da abincicika.
Ratsa mutanen yajeyi har yakai inda mummy take,yana zuwa ta bayanta ya rungumeta,turarenshi kadai ya shaidamata isha'q d'inta ne.
Juyo dashi tayi a hankali lokaci guda wasu siraran hawaye suka sauka akan fuskar isha'q dr.ru'kayya tasan me hakan yake nufi don haka tafara shafar sumar kanshi tana zuba mashi addu'ar fatan nasara dakuma dacewa akan auren nashi dayasa gaba.
Taron abokananshi duka suna waje suna jiran fitowar ango fuska kamar wanda akayima kyautar gonar auduga haka bakin isha'q yaki rufuwa,dayawa mutane suna mamakin yanda isha'q ya 'kallafa rai akan mace haka soyayya mai zaifi yakeyima zahra so bana wasaba.
Dady ma yana tare da manyan abokananshi wanda sune zasu amshi auren isha'q,sai dai ya aliyu dabai samu zuwa ba,saboda yanayin aiki dayasha karfinshi.
Gidansu zahra kam shina cike yake da mutane anata girke-girke,zahra kam musamman anty lubnah ta gyareta cikin wata atamfa super atamfar jace mai manyan fulawowi dinki doguwar riga bubu tamatukar daukar zahra, musamman jan abu ga ba'ki.
Basu saka mata relaxer aka ba,saidai sun gyare mata gashinta ya kwanta luf yasauka har akan gadon bayanta,duk yanda taso subarta tayi kwalliyarta sun hanata kwalliya maikyau suka tsara mata wanda tayi matu'kar fito da kyan zahran.
Gidan anty hauwa nan kusa da gidan su zahran nan zahra ta tara 'kawayenta sunfi goma sha biyar..
Umma ce ta'aiko masu da abinci,zokaga yanda su ummilolo aka cakare da kayan sallah bikin babbar aminiya sukutum da guda.
Farko abun kamar abin arzi'ki zahra bata tokali kowa fad'a ba,
Saida lami tazo gidan ana cin abinci ana fira uwande ce tafara cewa"yauwa natuna ke lami bayan gulma da munafurci maiya kawoki gidanaanan bayan kince mun wai mamanku tace ko anyi auren zahra babu inda auren zaije tunda zahra batada hankali"?
Lami datakai lomar shinkafa abaki batasan sanda ta 'kware ba,ta fiddo idanu waje dacewa"kai uwande Allah yatsine uwar mai 'karya yaushe nace maki haka?"
Uwande wadda taci d'ammara tace"kada kimaida karuwa y'ar iska,ranar nan da aka aikeki shagon habu cheese zaki siyo maganin sauro da daddare konayi 'karya"?
Ta'tambayi lami tana fiddo idanuwanta waje,
Lami takasa motsi duka jikinta yad'au rawa.
Zahra kam aituni tacire d'an kwali tayi d'ammara tafara turza 'kafafu 'kasa dacewa"aidama nasan babbar munafukace lami,kuma saikin gayamun gidan ubanda nazama mahaukaciya".
Lami idanu suka kawo ruwa,amma dayake itama badaga bayaba wajen iya masifa tayi tamaza wajen cema zahra"gidan ubanki,kika zama mahaukaciyar kodan kinga nayi shiru,shiru shiru ba tsoro bane gudun maganane."
Aitun kafin takai aya su ummilolo sunfara zuga zahra da ri'ke baki"yanzu ke lami zahran kike zagi?wlh zahra kici ubanta rigima uban wata kashe?"
Aiko zahra jiki har tsuma yakeyi ta bugi 'kirjin lami,itama lamin takuwa dage iyakar karfinta ta mangaje zahra har saida kan zahra yabugi bango tafad'i 'kasa.
D'agowar da zahra zatayi idanunta yasauka akan jamila tana mata dariya,
Aiko koda zahra ta d'auki lami saita sunkuta da 'kasa,tahaye tana bugu iyakar karfinta.
Yara suna sake tura zahra,azabar duka yasaka lami cizon zahra a yatsa,aiko zahra kamar jira takeyi tafara naushin bakin lami iyakar karfinta cikin rashin sa'a hakorin lami ya fita baki yayita jini.
Koda zahra taga lami tari'kr baki tana 'buratin kuka,sapita d'aga lami tace dawa Allah ya had'ata bada jamila ba?.
Kama jamila tayi da kokawa,rigima kica-kica aka yaga rigar zahra,abinda ya'kara fusatata ta ri'ke kitson jamila d'aya iyakar karfinta su ummilolo suna jan jamilan amma saida zahra ta fincikeshi fitt kitson ya fita.
Hakan yasaka jamila fashewa da kuka,ta kwashi kitso tayi gida tana kuka itada lami,
Gidansu jamila gidan yawane gasu masifaffu hakan yasaka sukayo zangi guda saigasu sunyo gidan anty hauwa,zasu bugi zahra.
Ganin hakan yasaka zahra ware iyakar karfinta ta angije jamila wadda ke maida ba'asin yanda akayi,waje tayi aguje yayinda sauran yara suka rufa mata baya...
Dai-dai lokacin da motar su isha'q ta iso kofar gidan,tare da manyan abokananshi,
Gefe guda waliyyan isha'q ne cikin fara qal ta shadda.
Zahra nazuwa batare datasan waye gabanta ba,tasaka iyakar karfinta danufin angije kowaye ya tare mata hanyar shigewa gida.
Idanun isha'q ya sauka akan nata idanun,cik tatsaya takasa motsawa bayan hakin datake ajiyewa.
Sauran yaran harsun iso wajen,sadi'q ya kalli isha'q yana tambayar wacece wannan kuma?"
Baikai ga tankawa ba,zahra tasake kwasa aguje tajuya don ganin hanyar gidan nasu a cunkushe.
Gudu sosai takeyi yayun jamila suna biye da'ita dai-dai zata tsallake titin mandawari cikin tsautsayi da baya wuce ranarshi wata 'katuwar prado ce taxo wucewa sam idanun zahra a rufe suke,jikake 'kuuuuu karar buge mutum da motar tayi kasantuwar itama motar a guje take....
Yayun jamila na ganin haka suka juya aguhe waidon kada ace sune,
Zahra kam babu alamar rai a tattare da ita,
Sai jini dake kwaranya akanta harzuwa bakinta da hancinta,akid'imen matashin dake driving motar yafito cikin tsananin tashin hankali ya sunkucin zahra.....

Kuna tare da maman meenat, Aisha T. Fulani Insha Allah
4 comments 09078902304
[12:03, 24/11/2017] hm: MIJIN 'KWAILA ����‍♀BY MAMAN MEENAT


EDITED :AISHA ABDULLAHI T. FULANI (UMMUN HYDR, FAROUQ)

Wannan shafin naku ne yara manyan gobe Allah ya shirya mana ku baki daya meenat, saleem �� ismaeel, nasir, aliyu hydr zakin fama, my little haneef, umar farauq adon gari, fysal, little angel aisha


Chapter15.


Tsananin tashin hankalin ganin halin da zahran take ciki yasaka saurayin turata kujerar baya yabama motar wuta sosai yana gudu,addu'arshi d'aya kada yarinyar ta mace a hannunshi.
Wata tsadaddiyar private hospital yakaita,wanda anan suka yanki kati,nan likitansu yake muddin sukazo kasar shine yake kula dasu.
Dr.haisam siririn likita fari 'kal dashi yanada sanqo akanshi,
Shine yafito da sauri don already saurayin daya kad'e zahra yakirashi awaya.
Da nosing guda biyu suka taho suna turo gadon da zai d'au zahra,
Yanda jini ke zuba yafi sake d'aga hankalin matashin.
Kasa natsuwa yayi musamman lokacin dayaga anshige da zahra emergency room saiyake ganin kamar bazata tashi ba,
Zagaye asibitin kawai yakeyi yana naushin iska,gami da furzo da zazzafar iska daga bakinshi yatambayi kanshi fiye da sau d'ari how coms hakan ta faru shikam ko kaza baita'ba kadewa ba barantana dan mutum.
Kusan 2hours yakasa natsuwa,saiyake danasanin zuwanshi kasar Nigeria yazo a rashin sa'a lallai.
Ganin dr.haisam yafito da sauri yasaka saurayin nufarshi idanu jajur yake tambayar "doctor yajikinta bana fatan tamutu sanadiyya ta doctor pls"...
Likitan yayi gaba yana bashi amsa"biyoni muje office dina ko?"
Bamusu yabi bayan likitan jikinshi duka a sabule yake,
Akujera mai fuskantar ta likitan ya zauna yana matsar yatsun hannayenshi d'aya bayan d'aya.
Yan rubuce-rubuce likitan yayi kafin yakai dubanshi akan sauran yakira sunanshi a tausashe" Aliyu ahmad(A.A).
Aliyu ya kafeshi da jajayen idanunshi da babu d'igon walwala acikinsu yabama likitan amsa"sunana kenan,likita sanar dani halinda patient dinnan take ciki kasani sarai banason jan time inabama lokacina muhimmanci fiye da komai".
Gyad'a kai likitan yayi dacewa"hakane".
Yasake numfasawa akaro na biyu"A.A bazan 'boye maka halinda yarinyar nan take ciki ba,hakika tana cikin hali na tsaka mai wuya,babbar matsalar kantane yasamu matsala akwai yuwuwar kozata samu kanta lallai zatayi loosing memory nata."
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un,abinda A'A yake maimaitawa kenan,
Saikuma ya marairaice fuska kamar ba A'A da dr.haisam yasani ba,A'a da magana ma ta fatar baki wahala take bashi amma yau shine yake zuba surutu yaga wahala na tunkaro shi.
Cigaba da magana A'a yayi"doctor pls babu wata hanya da yarinyar nan zata zama normal,banason wani abu ya faru da ita ta sanadiyyata.
Natureta da mota kuma ace tayi losing memory what's wrong with me doctor"?
Dafashi dr.yayi dacewa"calm down my friend,wannan matsalar zamu iya solving nata ta hanya mafi sau'ki ammafa sai kabada hadin kai".
Cikin za'kuwa A'a yace"komenene doctor zanyi kokari nidai kada yarinyar mutane ta salwanta dalilina ".
Likitan ya gyad'a kai"d only thing shine a fitar da yarinyar nan waje shine kawai hanyar da nake ganin zamu iya controlin din matsalar tun kafin ta mamaye kwakwalwarta,jinin dake zuba a kanta shine bamaso ya ta'ba kwakwalwa da yawa hakan zai'iya zama sanadiyyarta korasa hankalinta gaba d'aya,
So kadaisan yanayin kasar tamu bawai bamuda kwararrun likitoci bane saidai likitocin dayawansu basuda lokacin patient dinsu."
Aliyu yasauke numfashi,lokaci guda yana cewa"matsalar bazata wuce yanda zan gano ainahin iyayen yarinyar ba,amma zanyi kokarin bada cigiya duk inda ya kamata inyaso sai ayi komai akan idanunsu."
Kallon mamaki dr.haisam yakema A'a kafin yace"abokina wannan matsalar fa bawai matsalace da zamu iya jan time akanta ba,matukar munason rayuqar yarinyar tofa dolene aga yau zuwa gobe ya kasance tana 'kasar cairo don ganawa da kwararruwuce wannan lokacin tamkar rasa yarinyar ne.so d only way inaga kafara processing yanda zakabar kasar da'ita nikuma zanmaka dukkan wani shige da fice daya dace don ganin kasamu manyan likitocin in time."
Mikewa A'a yayi jiki babu lakka,
Aranshi yana raya"kai tsautsayi baya wuce ranarshi,
Dakin da zahra take yashiga tana kwance tayi plat bazaka ta'ba gane kamaninta ba,matukar bakasan taba.
Kanta gaba d'aya ya kumbura fuskarta tayi suntum idanunta duka sunzama kananu saboda kumburin fuskarta impact dai kamaninta gaba daya bakace zahra bace.
A'a jiyayi wani mugun tausayin yarinyar yashigeshi,idan banda taimakon oxygen aibazaka taba yarda zahra tanada raiba,
To ba motsi ba motsawa gatananan kamar gawa haka take.
Dasauri yajuya yafice yabar dakin hankalinshi yakai kololuwar tashi,number mum dinshi yaketa try amma bata shiga sam.
....................................
Isha'q ango anata fama da jama'a amma sam hankalinshi baya tare dashi,saiyake ganin kamar akwai wani abu personal dazai faru.
Yanadai cijewa ne kawai bayason yanunama fans nashi cewar yarinyar data kwasa a guje itace amaryarshi amma a time din jiyake kamar ya bita ya rungume kayanshi yahana koda quda sauka ajikinta.
Duk jama'a sungama hallara liman yafara haramar d'aura aure,lokacin da su ummilolo suka 'karaso wajen a gujesuna kuka da majina sha'be-sha'be,isha'q yafara lura da hakan dasauri yayi wajensu yana tambayar abinda yake faruwa saboda yanda jikinshi yabashi akwai wani mummunan labari dazai riskeshi.
Cikin kuka ummilolo take sanar mashi"wani mai motane ya banke zahra kuma yatafi da i.."
Bata 'karasa ba,isha'q yajuya da saurin gaske ya fad'a motar dasukazo da abokanshi yajata aguje zuciyarshi tana wasiwasin anya zahranshi ce"?
Ganin yanda yafice cikin taron jama'a a kidime shine dalilin dayasaka mutane farga suka fara tambayar abinda ke faruwa.
Itakuwa ummilolo tana mayar da martani cewa zahra ce mai mota yabuge yakuma saceta,
Lokacin da ummilolo take maganar abba yafito daga cikin gida yana sa'ba babbar riga tsayawa yayi cik kamar wanda aka dasa.
Gaba d'aya ma'aikatun kwakwalwarshi sun dakata da aiki na wucin gadi...
Juyawa yayi cikin gida hankali tashe,yana sanarma liman adakata da d'aura aurennan tukunna...
Kuna tare da maman meenat, Aisha T. Fulani Insha ��
4 comments, 09078902304
[12:03, 24/11/2017] hm: MIJIN 'KWAILA ����‍♀


BY MAMAN MEENAT

EDITED :AISHA ABDULLAHI T. FULANI (UMMUN HYDR, FAROUQ) ��


Kuna raina mmn Fysal, mmn Amna ina alfahari daku yn uwana


Chapter16.


Yanayin yanda mutane sukaga abba yashiga gidanne ya d'aga hankalin kowa,umma tana bakin gado a zaune abba ya aika kiranta.
Da sallama tashiga d'akin cikin abinda baishige minti gudaba tagano damuwar dake kan fuskar mijin nata,
Tambayarshi take cikin taushin murya:"abban zahra lafiya kuwa,meyake damunka"?
"bani ruwa tukun"
Cewar abba wanda yake kokarin tu'be malunmalun d'in dake jikinshi,
Ruwan randar abba umman ta mi'kamashi,ya kafa kai sosai yasha ruwan sida yafara karantama umma yarda daduk wata kaddara ta alkairi kota sharri kafin sanar da ita abinda ya faru da zahran.
Umma kam zuface tagama rufeta,tami'ke da sauri tana kai kawo atsakiyar d'akin sai alokacin ta'iya watsama abba tambayar"yanzu zahran tana inane"?
Shima mikewa yayi yana tafiya yana amsa mata"takamaimai banace ga inda take ba,amma zamu bincika asibitoci muga halin datake ciki."
Umma da ilahirin jikinta yagama yin sanyi ta'amsa da "Allah dai yasa abin yazo da sauki".
Ameen"
Abba yace yasakai yafice hankali tashe,
Tuni mutane suke tambayar umma ba'asin dake faruwa kowa yaji halin da'ake ciki saigaka jikinshi yayi sanyi.
Kai tsaye abba yafito waje yasamu kebewa da alhaji saifullahi yana sanar dashi abinda ke faruwa da zahra,abba yaci gaba dafad'in"anawa ganin kawai a dakata da d'aura aurennen harzuwa yanda hali yayi Allah yaga zuciyata banyi niyyar hana isha'q auren zahra ba.amma babu yanda na'iya da kaddara haka Allah ya nufa dole ce zata saka inhana isha'q auren zahra don bazan kaimashi wahala ba."
Ya tsagaita idanuwansa jajur,
Alhaji saifullahi kallon abba yakeyi da matu'kar mamaki akan fuskarshi yace da abban"amma malam adamu kabani mamaki kwarai da gaske,yanzu don *wata jarabta*tasamu zahra har kake tunanin zan'iya hana isha'q zama da ita?
Tokasani koda mungoyi da bayan hana isha'q auren zahra isha'q bazai lamunta ba,shine yaga zahra yaga tamashi a hakanta yake sonta na tabbata isha'q yanama zahra soyayya ta gaskiya yanama zahra *so d'aya tak*son da babu kiyayya koda yaya zahra takoma,zahra ta isha'q ce abadan da'iman don haka matu'kar dai babu wani dalilin personal acikin ranka to kawai a d'aura aurennan inyaso zahra taci gaba da samun kulawa daga maman ta wato *dr.ru'kayya*."
Abba ya gyd'a kai cike da gamsuwa,yana sake godiya ga Allah daya hada zahra da surukai na gari yanakuma fatan Allah ya tashi kafad'un zahra yabata ikon yima iyayen mijinta dama mjin shi kanshi biyayya.
Haka kuwa akayi take aka sanarma liman yakuwa dage ya tamke igiya uku ras tsakanin zahra da isha'q aurekam ya d'auru bisa sadaki mafi karanci don aure yafi albarka da karancin sadaki.
Umma tana cikin gida taji ana shafa fatiha sai lokacin wasu zafafan hawaye suka sauka akan kumatunta,wato dai shi tsautsayi baya wuce ranarshi.
Yanda isha'q ya kid'ime yasaka sadi'q binshi da mota yakara mashi motar yasha gaban isha'q duk suka fiffito daga cikin motar suna rokon isha'q yayi hakuri yabi komai a sannu,
Kasa motsawa yayi kamar wanda ya daskare haka yakejin jikinshi indai ba bayada rabon aure a duniya ba,mezaisa yarasa zahra akaron farko yad'auki dangana awannan karon yakuma sake rsa zahra?anya wannan kaddarar dake watangaliliya da rayuwwarshi kuwa.
Haka kawai yasakejin soyayyar zahra kamar ana ninka mashi ita,tabbas soyayya ba karya bace kuma amana ba wasa bace,
Abokanshi wajen biyar suka rufar mashi da rokon bude motar hakan ysakashi budewar kuwa,yanda yafito saika rantse yasha giyane saboda yanda jiri yake kwasarshi dakyar ya'iya furta"sad'iq zahra tazama tawa kokuwa ayauma nasake rasa zahra?"
Wani irin tausayin isha'q ya tsilga dukkan abokan nashi,
Dafa kafadarshi sadi'q yayi"haryanzu zahra adam ta isha'q ce,banga dalilin dazaisa afasa kulla auren da Allah yanufi saiya wanzu ba,isha'q bana tunanin akaf duniya akwai wanda yafi dacewa da zahra kamar ka.already zahra tana karkashin kulawarka isha'q".
Wata ajiyar zuciya isha'q yasaki,sai lojacin yasamu kwarin gwuiwar shiga motar da su sadiq suke sauran abokan suka shiga motar isha'q sukayi gaba suna sake kwantar da hankalin isha'q din.
.
Duk tarin yawan mutane gidan baihana dr.ru'kayya ficewa dag gidan ba, sakamakon kiran gaugawa data samu daga dr.haisam akan wata yarinya dawani yakad'e wadda take bukatar agajin gaugawa inma da haki sunason saka hannun dr.ru'kayya wajen fitar da yarinyar zuwa kasar cairo.
Jin yanayin matsalar yasaka dr.ru'kayya zura fara kal ta rigarta gami da saka hijabi tafice dasauri tana barma dr.aysha sallahun cigaba dakula da bakinta kafin ta'iso.
Rafiyar mintuna ashirin tasadata da babbar asibitin,dakanta take driving abinda harta mance rabon datayi kenan.
Parking tayi inda aka tanada domin hakan,tafito dasauri dai-dai lokacin da A'a yake mikama dr.haisam hannu don tafiya wajen cukuiniyar visa.
Dakatar dashi dr.ru'kayya tayi,tana tambayar koshine yakad'e yarinyar?
Dr.haisam ya amsa "shine hajiya"
Tayi d'akin da aka kwantar da zahra,tura dakin tayi cike da kwarewa takutsa kai dakin idanunta suka sauka akan zahra wadda take kwance batare datasan waye akanta ba.
Dasauri dr.ru'kayya ta karasa tana dudduba fuskar zahra,lokaci guda ta shaida atamfar jikin zahra wadda itace dakanta tabada d'inki iri d'ayane dana hanan.
Saikuma y'ar siririyar sarkar gold mai kwad'on da'akama designed da harafin Z wato farkon sunan zahra tabbas zahrace to why meyasamu zahra garin yaya hakan ta kasance?
Bata tsaya 'bata lojaci ba,ta fito a hanzarce tana shaidama dr.hisham yarinyarta ce ma ashe,yasha mamakin jin maganar don ayaranta babu wanda bai sani ba.
Sai dai basuda lokacin neman karin bayani ayanzu dasuke cikin hali na tunanin hanyar kubutar da rayuwar zahra daga halaka.
Kusan manyan likitoci hud'u suka nufi d'akin xahra da kayan gwaje2 don dr.ru'kayya tace sufara jaraba tasu sa'ar kafin ayi tunanin fitar da zahra kasar waje......
October 9,


Kuna tare da maman meenat, Aisha T. Fulani Insha Allah ��
4 comments 09078902304
[12:03, 24/11/2017] hm: *MIJIN 'KWAILA*
_jinjina ga masoya lbrn mijin kwaila'gsky bnsan yama zan fasalta matsayinku awajena ba_ =luv yhu guys=��
editing aisha T.fulani.


*by maman meenat*
Chapter 13 · 0% Book details