← Book details Mijin Kwaila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 7 OF 14

CHAPTER 7.

Mijin Kwaila Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Umma taja tsoki takoma tazauna abinta,
Yayinda zahra ta cillar da jakar islamiyyar dakuma hijabi tafad'a band'aki.
Dr.ru'kayya tasauke numfashi tana kallon su umma kafin tace"wannan kuma 'kanuwar Zahran ce kokuwa.?
Umma ta kalleta da mamaki tace"a'a itace zahran ai."
Wani shegen gumine ya karyoma dr.ru'kayya lokaci guda tafara tsane zufa da handkerchief dake hannunta aranta tana addu'ar tafarka daga rud'adden mafarkin dayayi hajijiya da tunaninta dama kwakwalwarta.
Tad'an saita kanta kad'an kafin tad'ora dafad'in"to agaskiya dolene ku kalleni a matsayin wacce kanta ya zautu,kokuma 'batan kai inba hakaba babu mahaluki mai hankalin dazai dubi karancin shekaru irinna zahra a gari ba 'kauyeba yace ayimata zancen aure."
Tad'an tsagaita tana sauke numfashi kafin tad'ora dafad'in."adukkan zatona dakuma tunanina nayi zaton zahran babbar budurwa ce,amma don kamanni da tawa zahran tabbas suna kamanni nagasken gaske,sai dai kash wannan zahran tayi kankantar dabe kamata ace anyimata aure yanzuba."
Sai lokacin su abba suka fahimci inda tasa gaba,
Abba yami'ke yana cewa"inace dai yaron dakeson zahran shine awaje tsaye ko.?"
Doctor ru'kayya ta'amsa dacewar"shine malam",
Abba yafita kofar gidan,isha'q har lokacin yakafe kofar gidannasu zahra da manyan idanunshi yanason ganin ta'inda kyakyawar fuskar zahra mai kama data black Americans zata 'bullo,sai dai sa'banin zahra saiyaga abba yafito yana sa'ba babbar riga.
Isha'q yayi saurin du'kawa yana gaida abba,
Abba ya'amsa kanshi tsaye yace"kaine isiyaku."?
Isha'q yawaro idanuwansa masu kwarjini da haiba,yace"abba isha'q nake."
Abba yace "afto ai duka dai d'ayane,to inason magana dakai ga mahaifiyarka can cikin gida don haka kashigo ayita a gabanka ta 'kare."
Gaban isha'q yabuga da 'karfi,idanunshi tuni sun canja launi daga farare zuwa green tsigar jikinshi tabada yarrrr,aranshi yana addu'ar kada Allah yasaka yasake rasa zahra akaro na biyu bayan tadawo gareshi.
Kai yama rantse komai rintsi bazaifa rabu da sanyin idaniyarshi ba,aidukkan mai imanin dayasan tarayyarshi da zahra abaya bazaiga laifinshi don lokaci guda ya mayincema little zahra ba.
Abune mafi tsanani agareshi yakice soyayyar da'aka dasa tun zamanin 'kuruciya yanason zahra yana 'kaunarta yanamata *so d'aya tak*son daya rantse babu mi'ki ko algussu acikinshi.
Jikinshi babu 'karfi yabi bayan abba wanda tuni yakai zaure,
Inbayanga addu'ar samun nasara babu abinda isha'q yakeyi acikin zuciyarshi.
Da sallama ya kunna kai cikin gidan,lokacin yayi dai-dai da fitowar zahra daga band'aki,
Idanunta suka sar'ke dana juna lokaci guda duk rashin kunya da fitsarar zahra taji isha'q yamata wani kwarjini wanda ita atata haukar jitayi ya burgeta don zahra akwaita dason y'an gayu,uwa uba tanadason kwalliya duk da cewarta ita ba'kace amma saitafi su anty hafsa zama y'ar gaye.
Tasauke idanunta cikin na isha'q wanda yamace atsaye yana kallon baiwar gashin dake kan zahra,yatunano tashi zahran batada irin wannan gashin,
Ya runtse idanuwa,yana tasbihi ga Allah wanda ya'kagi kamanni tsakanin zahra dakuma little zahra.
Itama dr.ru'kayya mamakin irin gashin zahra takeyi,lokaci guda taji yarinyar tazaunan daram acikin zuciyarta tabbas soyayyar datake yima marigayiya zahra ce zata koma akan wannan zahran,
Kai itama tana ganin kobada aureba yakamata zahra tazama wani 'bangare daga jikinta,she luv xahra moree.
Isha'q yatako kamar wanda kwai ya fashemawa aciki yazauna kusa da mahaifiyarshi yana gaida umma wadda takafe kyakyawan saurayin da idanu tana dad'a tasbihi ga Allah daya tsara halitta mai tattare da baiwar natsuwa irinta isha'q.
Zahra kam bata saurare suba taja jakarta da hijab tajefa d'aki,
Tadawo kitchen tana neman abincinta hankalinta kwance dukkuwa da sarai tagane isha'q,shine mayen kallonta d'innan idanunshi basamata kyan kallo,saitaji gabanta yana fad'uwa idan tana kallonshi.
Dr, ru'kayya ta kalleta a tausashe tace"zonan d'iyata zahra,
Kamar baki,saiga zahra tataka sif-sif zataje inda dr.rukayya take,
Idanunta suka sar'ke dana isha'q akaro na biyu,
Ta murgud'a mashi baki had'i da jefa mashi harara.
Yasakar mata murmushi,
Abinda ya 'kufulata yasaka tacije baki had'i da girgiza kai.
Saida taje kamar zata wuceshi taje wajen doctor ru'kayya tasaka 'kafarta ta take hannun isha'q wanda yadafa 'kasa dashi.
Yajanye hannun da sauri,yana yarfawa.
Ta kwashe da dariya lokacin data ra'ba jikinta dana dr.ru'kayya tace"yaro kaci gaba da kallona kamanta ranar dana 'kala maka sheri sojoji suka kamaka ko.?"
Tafad'a tana cije le'be da fiddo sexy eyes dinta waje.
Isha'q ya girgiza mata kai alamar kada ta fad'a,
Amma saicewa tayi"tomiye kuma naga kanata girgiza kai,hhhh katuna marin da wannan mai 'katon cikin yayi maka ne.?"
Abba ya daka mata tsawa yace "rufe mana baki,waya tambayeki."
Umma ai kunya bata barta zama wajenba,saita tsiri fura wutar dole.
Dr. Ru'kayya tayi tsam tanason tunano ranar da isha'q yadawo yacemata bashida lafiya dataga fuskarshi da kumburi ta tambayeshi yace mata yafad'ine wajen training.
Ta girgiza kai kawai.
Abba yafara magana"to masha allah isha'q kaine ka aiko mahaifiyarka akan kanason inbaka auren zahra."?
Isha'q ya gyad'a kai kanshi yana 'kasa yana wasa da yatsun hannunshi.
Abba yasaki murmushi nasu na manya yace"to isha'q bazan 'boyemaka ba,bakuma don kunada arzi'ki yasaka zan fad'i ra'ayina akanka ba,wlh kallo d'aya namaka naji nasamu natsuwa dakai.sannan akwai alamar kwarjini da wata baiwa da Allah yamaka wadda dukkan mahalukin daya mallaki hankalin kanshi ya kalleka zaigane kai kamilin mutim ne,"
"Hakane"?
Yajuya yana tambayar umma,wadda ta tsugunna bakin adarkin kitchen,
Umma tace"hakane malam".
Dr. Ru'kayya sai murmushi take anyaba mata d'an lelenta.
Abba yad'orabdafad'in"kaikuwa wacce 'jarabta ce takaika za'kulo zahra amatsayin matar dakakeson aure,nafarko zahra dai yarinya ce 'karama nabiyu zahra bawani kwayon da zaya rud'i mutum gareta ba,illa tulin sumar kai wadda harmun gaji da askewa mun barta taji da abarta.sannan bazan 'boyemaku gaskiya ba,zahra batada kunya ka ganta nan,"
Ya nunata da yatsanshi,
Takuwa zumbure baki tana 'kunkuni.
Dr. Rukayya tace"a'ah zahra d'iyata meyasa kike hakane,abban kikema gunaguni."
Zahra tace"nifa badashi nake ba,"
Umma ta 'amshe to anan ciki waye tsarar wasanki dawa kike"
Ta nuna isha'q da yatsa,tana sake turo baki"bashine yaketa kallonaba,kuma wai har yana runtse idonshi d'aya,(kashe ido)
Kunya kamar ta kashe isha'q haka yaji.
Dr.ru'kayya maka mashi mafecin dake hannunta tayi dacewa"tashi maza kabar nan,mara ta idanu kawai."
Yakoyi 'kememe abinshi baiko motsaba.
Abba yad'ora dafad'in"to agaskiyar zance nikam bantashi yima zahra aureba,donkuwa dukkanin yayunta babu wacce na aurar batare da ta samu sakamakon takardar n.c.e ba,don haka idan nace zanyima zahra aure awannan lokacin na zalunceta nakuma shiga hakkinta duk da bawai musuluncine ya hana aurar da yarinya tana shekaru sha biyu ba,hasalima shekara tara musulunci ya yarda ka aurar da yarinyarka,amma yanzu zamani ya canja akwai cutuka da dama da ada bamudasu sai yanzu,sannan zahra bawai wayone ya iaheta ba,bayaga rashin ha'kurinta tanada mugun surutu dakuma su'butar baki.
Amma nayi maka al'kawarin muddin zahra ta girma tace tana sonka zan aura maka ita,wannan shine kawai maganata."
Dr. Rukayya ta kalli isha'q wanda idanunshi suka kad'a sulayi jajur,
Tace "tokaji da kunnuwanka abinda abba yace,saikayi hakurin zahra ta girma kusan shelaru goma nan gaba 'kila."
Hawayen dayake 'kokarin ri'kewa tuni sun 'balle,babu kunya ya ri'ke kafafun abba yana ro'konshi"abba don girman Allah kada ka nisantani da zahra abba,ka tausayamun soyayyata da zahra *had'in Allah*ne,bana nufin cutar da rayuwarta har abada pls abba."
Duk da taurin zuciyar abba saida yaji tausayin isha'q amma kuma donme ze tauye rayuwar zahra.
Umma jitayi bazata iya kallon hawayen isha'q ba,saita shige d'aki abinta.dama ita nata biyayya duk abinda abba yatsara awajenta yagama tsaruwa.
Dr.ru'kayya ta kalli isha'q daya kasa dena fitar da hawaye tace"kajiramu awaje inazuwa."
Yatashi ya fita,yana sake waigen zahra wadda dukkan jikinta yayi sanyi 'kalau tana kallon isha'q badai tagane akan me suke tattaunawa ba.
Dr. Rukayya tasake rusunama abba tace"nagode da kyautar dakayima d'ana amma na ro'keka daka taimaki rayuwarshi,don Allah kada kayi fancakali da lafiyar damuke tarairaya tashi,natabbata isha'q zai rike zahra amana,
Wlh namaka rantsuwa babu wani abu na ga me da auratayya dazai shiga tsakanin isha'q da zahra harsai takai munzalin hakan,
Sannan karatu konan da inane zan tsayama zahra tayishi,inada yarinya bazata shige tsarar zahranba atare zan renesu don dukansu y'ay'a nane."
Ta tsagaita tanason jin amsar da abba zai bata.
Nima natafi break
September 26, 2016 at 10:43pm · Public
[12:03, 24/11/2017] hm: MIJIN 'KWAILA ����‍♀

BY MAMAN MEENAT


EDITED BY AISHA ABDULLAHI (UMMUN FAROUQ)
Chapter 7 · 0% Book details