← Book details Mijin Kwaila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 14 OF 14

Chapter 17.

Mijin Kwaila Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Cikin abinda baishige mintuna goma ba dr.ru'kayya tagama had'a kayan aikinta tare da kwararrun likitoci sundu'kufa akan zahra don gano ko tasamu matsalane a brain d'inta,
Abinda suka binciko shine yad'anso daga hankalin dr.ru'kayyan bawai matsalar zata shafi lafiyar zahra dun-dun-din bane,saidai hakan zai iya haifar da barazana ga lafiyar kwakwalwarta amma kuma muddin tana samun kula akwai tendencies na zata iya warkewa cikin kankanin lokaci.
Dukkan wani abu daya kamata likitocin suyima zahra sungama cikin ikon Allah kan natane kawai yasamu matsala ayanayin nasu binciken zata iya farkawa akowanne lokaci so abu d'aya dai dasuke ganin mafitane gareta shine idan tafarka tafara kallon abu mafi soyuwa agareta,wanda akowanne lokaci takeson kallo.
Saikuma abu na 'karshe wanda takalla bawai kallo na razanarwa ba,watakila tahakanne zaisa ta'iya tunano abunda yafaru abaya,kenan bazata samu matsalar tunani ba.
Wannan kenan....
Isha'q kam dukkan bincikensu baikaisu ga gano ainahin inane zahra ta kurd'a ba,hakan yasaka shi kifa kanshi ajikin kujera zuciyarshi kamar zata tsage kirjinshi tafito don tashin hankali da damuwa,
Soyakeyi hawaye sufito daga idanunshi watakila zaisamu sassaucin tashin hankalin dayake ciki.
Abinda yafi daga hankalinshi baishige yanda zaisake rasa zahra akaro na biyu a rayuwarshi ba.
Yakira wayar mummy yafi a 'kirga tana ringing sai dai babu amsa,sosai suka shigarda report wa police don binciko zahra.
Acan gidansu zahran ma hankalin duka atashe yake,kusan kowa zakaga babu natsuwa a tattare dashi,duk shirmen zahra a irin wannan halin datake ciki yakamata kowanne mai imani da hankali ya tausayamata.
Abba kam da aminanshi basu samu zamaba,bazama sukayi neman amarya zahra dafatan komai zaizamo cikin sauki da salama.
Sai wajen uku na yammacine motar dr.ru'kayya tayi fakin cikin harabar katon gidan nasu maicike da jama'a yan biki,dayawa sunamata sannu dazuwa dakuma tambayar maijiki takan amsa kawai sai dai babu natsuwa ko d'igo a tattare da ita.
Dakin dady tanufa da telephone din dake kan dan teburin tsakiyar dakin tasamu damar lalabo lambar dady wanda harzuwa lokacin yana fama da ba'ki,
Ganin kiran matarshi yasakashi kebewa gefe guda yana amsa sallamar datakeyi,
Cikin damuwa dr.ru'kayya takecewa dashi"abban hanan kana inane?"
Yabata amsa"inatare da ba'ki ince dai lafiya?"
Tad'anyi kokarin kauda damuwar dake tattare da'ita tace"kalalaboman number isha'q yanzu inason magana dashi ne".
Dady yad'anyi jimm saikuma yace"akwai matsalane mummyn hanan,kidai bari in karaso gidan,don aurenma da har mahaifin yarinyar yace afashi kawai."
Itama abinda takeson sanar dasu din kenan tawatso mashi tambayar"anfasa kokuwa ya'ake ciki?"
"and'aura mana,mezaisa afasa".
Cikin raunanniyar murya tace"abban hanan matsala babba nahangowa isha'q,yanzu haka amaryar tana asibitina a kwance tasamu accident yuwuwar samun lafiyar kwakwalwarta shine abu mafi wahala,bana zato ko tsammanin cikin kankanin lokaci zata zama normal koda miliyan nawa aka barnatar don lafiyarta din,shikenan zamu zubama isha'q idanuwa yazama sakarai akan macene?inada tabbacin akwai zahra ko babu zahra isha'q dole zai iya rayuwa"
Tad'anyi jim tanason jin abinda maigidan nata zaiic Jin baitankaba yabata damar cigaba da maganarta"nikawai atawa shawarar a d'age bikinnan harzuwa lokacin da zahra zata samu lafiya,inyaso sai ayi auren shikuma isha'q yasakama zuciyarshi dangana tunda dama aurene kawai na jeka nayika bawani abu zai tsinta jikin yarinyar ba."
Dady ya katseta dacewar"to naji naki batun idan shawarace ko umarni duka ina tayaki jimamin rashin samun karbuwarsu don yanzu haka anrigaya da andaure aure tsakanin zahra da isha'q,sannan koda cikin mafarki banzaci bakinki zai iyafurta wannan maganar ba,mutanen dasuka yimaki hallacci saboda batashi sukayi aurar da yarinyar suba,ganin kima da mutunci dakuma halinda isha'q ka'iya fad'awa yasaka suka aminta da aurar mana da ita amma kisani idan za'akai zahra turu 'karewar hauka tofa bazamu dage dai-dai da second daya na biki ba.
Tunda har da lafiyarta iyayenta suka bashi ita,yakumace yaji yagani to lallai madamar ta warware zata tare d'akinta inyaso yayi jinyarta sannan banason nakuma jin bakinki akan maganar matsalar da isha'q zai shiga,idan yaro yadauki gatari rikemashi kota akeyi."
Bai saurari mai zatace ba yadatse wayar,
Tafi minti uku tana kallon kan telephone dib dake hannunta kamar shine yake mata maganar,tagyad'a kai ita sam dady bai fahimci manufarta ba,idan soyayya ce bazai nunamata kaunar zahra ba amma abu daya dabazata dauka ba shine fadawar danta cikin wahala haka kawa.
Tana niyyar fitowa daga d'akin dr.aysherh tana kutso kai atare suka kalli juna,aysherh tafara magana"nadad'e ina sauraron shigowarki ga baqi sunata zuwa sai akace kina dakin dady bayan naga fitarshi tun dazu,ince dai lafiya?"
Tayi tambayar idanunta sunakan dr.rukayya,
Sauke ajiyar zuciya rukayya tayi dacewa"matsalar isha'q bansan har tsawon lokacin da zata dauka kafin warwarewar taba,"
Aysherh tace"sanar dani komai qawata,abokin kuka ba'a boyemashi mutuwa."
"Hakane"
Dr.ru'kayya tafad'a lokaci guda tana warwarema aminiyar tata zare da abawa.
Wani mugun farin cikine ya ziyarci zuciyar asherh saitake ganin lokaci yayi dazata cilla kibiyarta wajen farauto ma tilon d'iyarta aneesa zuciyar isha'q wanda aneesan tayi matukar macewa akan kaunarshi.
Cikin kwarewa da hila dr.aysherh ta langwa'be kai dacewa"ayya gaskiya na tausayama zahra,sai dai kokusa isha'q yafi tsayamun araina yanda baligin mutum kamar isha'q zai tsaya a rayuwar kila wa kala don natabbatar matsalar zahra matsalace da take daukar lokaci kafin warakarta kobayaga haka abinda zaifi tayar da hankalina yanda kamalin mutum kamar isha'q wannan matsalar ka'iya kaishi ga aikata sabo na zina donshi ma lafiyayyene kamar kowa yanada feelings akan mace.sai dai na tabbatar matsalar zahra bazata ruguje komai ba Allah yabata lafiya ".
Shiru dr.ru'kayya tayi tana juya maganar aminiyar tata cikin kwanyarta,for how isha'q zai tsaya zaman jiran lafiyar zahra bayan jiran girmanta?
Anya tayi nazari wajen amincewa da zahra yarinyar da kwakwaran wayo baigama zama ajikin ta ba? Mafita daya dazata nemawa isha'q take tunani amma wacece mafitar,tadaisan ko hauka take bazata taba iya tunkarar iyayen zahra da maganar su rike zahra harsai tasamu lafiya ba,kuma shi kanshi isha'q din bazai lamunci rayuwa babu zahra ba.
Kenan menene mafita?
Mafita...mafita..abinda take nanatawa kenan tana kirga tsawon shekarun da kamilin yaro irin isha'q zai dauka na jiran gaibu,don zahra gaibu ce ayanzu adai wannan halin datake ciki.
Tafara matsar yatsun hannunta tana jeranta awanni zuwa sekonni kwana zuwa sati kai matsalar isha'q abin iyaye suyi nazari ce gaskiya.
Jin andafata yasata tunawa dacewar akwai kawarta dr.aysher tana kallonta suka sakarma juna murmushi lokacin da dr.ayshe take cewa"mafita akwai mafita,mafitar d'ayace amma wahalarta yafi ace kizagaye garin kaduna akafa,mafita itace auree".
"aure?"
Dr.ru'kayya ta tambaya fuskarta akwai alamun mamakin jin maganar kawar tata,
"of course,aure zaki karama isha'q shine hanya mafi sauki dazata bashi dama dakuma ikon kula da kanshi dama ita zahran gaba daya".
"nooo,ican't aysher"
Cewar dr ru'kayya"haryaushe xan'iya kallon idanun mahaifan zahra inmasu wannan butulcin?"
Aysherh tadage kafad'a"bazaki iyaba muddin bakya kaunar farin cikin danki isha'q......
turkashi!!!nayi nan...


*real mum meenat*��
Copied By
YAYA HAYAT
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
Cool novel, makeup and kitchen2⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen3⃣)


WHATSAPP NO:
+2349030159301
Chapter 14 · 0% Book details