← Book details Mijin Kwaila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 2 OF 14

chapter 2.

Mijin Kwaila Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Gudu take kamar wacce zata tashi sama,
Ahaka tasha kwanar layinsu da yawa y'an unguwar sunsan halinta don haka suna ganinta suka fara dariya,
Wasu nafad'in "mai hali baya fasa halinsa zahra."
Saida ta kutsa d'an sirdad'en lungunsu kana ta dakata da gudun tana luliya agwalumar abango dafad'in"luliya-luliya danya awakin baba da dad'i."
Sai dai batayi auneba ta hango mai agwaluma a three thirty ya kutso lungun,
Hakan yasakata idasa fad'awa gidan kamar wacce aka cilla da kibiya .
Umma dake tsaye bakin band'aki da buta a hannu, zahra batamasan ta angije ummanba,ta danna d'akinta gami da gar'kama sakata.
Umma tabita da idanu,
Yayinda anty hafsat dake tsaye gefe tabita da tambayar lafiya zah....
Bata 'karasaba sukaga me agwaluma ya fad'o gidan,
Baikobi takansuba yarufama zahra baya zuwa d'akin datake ciki.
Anty hafsa cikin mamaki ta tareshi dafad'in"lafiya malam bakada hankali zaka fad'o cikin gidan matan aure bako sallama.?"
Yayimata kallon banza ranshi yana zafi kafin yace"aiba sallama ta kawoniba,wlh sai anbiyani kud'ina kokuma in karya yarinyarcen,
Yanuna d'akin da zahra take ciki.
Yayinda take lekowa ta window tana mashi gwalo,
Yakuma 'kufula,
Anty hafsat itama hararshi takeyi tana nuna mashi kofa"get out"
Ya kalleta da jan idanunshi"bansan wannan yaren ba."
Anty hafsa itama akwai masifa don haka tamike dafad'a,
"nizakama rashin kunya,wato kashigo gari ka waye haryanzu jahilcin kauye bai sakekaba,idan laifi akamaka kai ataka basirar da wannan cin maganin dakakeyi zaka kwatarma kanka y'ancine,?
Tajuya a fusace ganin yanda yake harararta,yana mata qunquni.
"bari inkira police idan yaso idan kaje bayan kanta zakayi bayanin abinda yashigo dakai gidan matan aure."
Umma tariketa tana fad'in"me yayi zafi hafsat,bansanki da hakaba,
Kifara tambayar abinda zahra tayimashi don bana raba d'aya biyu itace ta tsokanoshi.."
Umma tasake kwantar da murya tana tambayar me agwaluma abinda yafaru,
Idanunshi taf da hawaye, yake bama umma ba'asin yanda komai ya farun.
Umma tagyad'a kai tana fad'in"nasan za'a rina ai,
Nidai zahra bazan maki bakiba sai dai ince allah ya shiryeki,abinda kikeyi amma nagaji nagaji da halinki bari babanki yadawo a tattara amaidake can kauye inyaso kici gaba da halinki a can am.a nikam nagaji."
Tajuya afusace tanufi d'akin da zahra tuni ta danna mashi sakata.
Anty hafsa tazuge jakarta tafiddo da dubu d'aya tamikama mai agwalumar tana hararashi dafad'in"next time kasan yanda zakayi magana da nasama dakai ".
Shima hararta yayi,
Sai dai bai tankaba.
Anty hafsa tadafa kafad'ar umma wadda tazauna zugwui da damuwar da zahra ke sakata akoda yaushe,
Tace"umma pls banason ganin damuwarnan taki,kina sane da lalular dakike fama da ita,
Umma kamata yayi kinama zahra addu'a bawai yawan damuwaba."
Umma tasauke numfashi"toyaya zanyi kinasaje da halin yarinyar nan,khatta da sunan da yaran unguwa suke kiranta dashi wai *zahra'u mala'ikar yara inkin mutu ba ruwan Allah walakiri ya jibgi kayanshi*."
Umma taci gaba"sam idan kinga nasamu naji sa'ida to kuwa zahra tatafi makaranta toyanzu hatta da makarantar abin yaci tura iya shege kullum sabon salo take fiddowa,jiya Monday tafara zuwa makaranta js 1,take amma wai baifi wata biyu da shigartaba yara bakwai ta fasama kai da dutse,dacirema wata yarinya ha'kori,
Principal ta bugeta shine tatara yara bayan antashi makaranta sukayima motar principal ature,da 'kasa har suka fasamata glass din mota.shine fa akazo hargida dakorarta sukayi dakyar babanku yasamu ya mayar da ita suka amsheta ,amna saida yabiya kudin duka asarar dasukayimata kinga ayau har ta dakko wata maganar.
[9/20, 1:16 PM] mum meenat: Anty hafsa ta sauke ajiyar zuciya,
"nidai umma sainake ganin kamar lamarin zahra fa akwai sa hannu wannan abin datakeyi bafa normal abu bane,gaskiya is abnormal ne umma yakamata mutashi tsaye,yarinya saikace ana kad'ata da ruwan hanji sam zahra bata d'auko halayyarmuba."
Umma tace "kema kya fad'a ai,nida ace ba'a gida na haifi zahraba tozan iya rantsewa da Allah anyiman musayar tane batawa bace ba.gata sam bata d'auko kamanni dakuba,hakanan bata dauko halayyarkuba.
Ku shidda na gaifa allah ya dauki ran maza biyun dasuke cikinku sai kumata guda hud'u da allah yabarmun,duk na aurar daku ku ukku akan matakin karatun zamani dana addini dai dai gwargwado bamu tauyekuba,gakunan duka cikin rufin asiri amma zahra sam tazamo zakka acikinku,itabaga karatuba baga natsuwar ba,itakenan kamar tunkiya duk inda ta gifta sai ance kayya."
Umma ta'kare maganarta kamar zata fashe da kuka.
Da'kyar anty hafsa ta shawo kan umma,ta lalla'bi zahra ta bud'e dakin tanufi kitchen tadauko abincinta wanda tuni ya sandare saboda hucewa,
Tazauna kamar wata saliha tanacin abincin anty hafsa namata fad'a akan rashin jinta.
Itadai bata tankaba,
Har lokacin sallar la'asar yayi tatashi tayi wanka akaja wata kwasheshiyar jagira wadda tasamu matsugunni a gefen kunne,
Tad'auko janbaki jajawur ta dafsa bayan ta zagaye bakin nata da tarin ba'kin kwalli.
Tajuya da fuska tanama madubi murmushi tana tsuke d'an matsakaicin bakinta aganinta ba nabiyunta wajen kyau.
Duk da tana cikin 'kunci baihanata ganin kyawon nata ba
Sai dai aranta kullum tanajin haushin meyasa anty hafsa da anty salma kai harma da anty lubna duka suke farare tas,
Amma ita saitayo duhun fata,
Taja tsoki ita d'aya dafad'in"nadaisan dama ummanmu ba sona takeyiba shiyasa ta haifoni ba'ka.
Tasaka uniform na islamiyya check blue dasuka d'au guga sukayi luf dasu,
Tafito har lokacin umma bata dena fushi da itaba,
Takalli umman cikin kukawa tace"umma natafi,"
Umma tace"adawo lafiya sauran yauma akawomun 'kararki kinyi fad'a dawani mutum zaki bani labari."
Ta turo baki gaba,batare da tatankaba,
Umma tayi tsaki dafadin"shashasha kawai shekaru shabiyu amma fitinarki tafi ta masu shekaru ashirin."
Itadai gaba tayi abinta kamar yanda tasaba,
Tafito lungunsu tana gunaguni,charaf idanunta suka sauka akan na ishaq wanda ya sar'ke hannayenshi a kan kirjinshi yakafe kofar lungun nasu da idanu,
Duk da rashin tsoro irinna zahra saida gabanta yafad'i,amma dayake tsiwa gareta saita murgud'a mashi baki dafad'in''kurwa
ta kur namana d'aci,me d'a yaci d'anshi mara d'a yaci 'ko'kon tsuliyarshi."
Ishaq duk da baya jiyo abinda take fad'i shidai komai takecewa ahakan burgeshi tayi,
Yanason d'an murgudennan nata,
Ya numshe idanu daya tuno da zahra gaf da bikinsu yakafeta da idanu tayimashi murgud'e dafad'in "kallonfa,
Alokacin murmushi yasaki yanace da ita"nanda wata biyu saina tsotse bakin murgud'enanna naki."
Alokacin dariya tasaki dacewa"kai yaya ishaq,bakajin kunyata nifa kanwarkace".
Ya runtse idanu,kamar zai fashe da kuka afili yafurta "i really luv yhu zahra,inason koda mace mai sunankine bare kuma mai kammani dake."
Post everyday nsha Allah
September 20, 2017 at 7:31pm ·

��������

by
Anty yar charas ����
[12:03, 24/11/2017] hm: *MIJIN 'KWAILA*����‍♀

*to you maman Aliyu this page is for you*��
Chapter 2 · 0% Book details