← Book details Mijin Kwaila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 4 OF 14

Chapter 4.

Mijin Kwaila Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Isha'q yaji 'kirjinshi yabada dam,
Amma dayake jarumine saiya fuske gami da janye hannun sadi'q dafad'in "kayi abinda yadameka malam",
Sadi'q yasake kyal'kyalewa da dariya yana fad'in"allah yarinyar ce so funny"
Isha'q yaja tsoki bai tankashi ba,
Sai gab da isha'i zahra tanufo gida,'kirjinta yana bugun uku-uku aranta tana addu'ar "Allah yasaka umma bata tsakar gida,
Talala'bo tana sand'a lokacin datashigo gidan takalma a hannu bayan tafara zuro kanta taga gidan babu kowa.
Tafara tafiya sad'af-sad'af danufin fad'awa d'akinta sai dai batayi auneba taji umma tacafketa caraf ,
Ta waigo fuskarta da alamun tsoro,
Kafin tayi wata magana umma takifa mata mari.
Da tambayar "daga gidan ubanwa kike?"
Zahra idanu suka raina fata,
Tafara ro'kon umma"wayyo ummana kiyi ha'kuri bazan sakeba."
Umma tace"rufemun baki shashashar banza,bazan 'kara d'inkiba datana tasiri dayanzu namance dawata aba wai ita damuwa.meyasa kikeson sakamun hawan jinine zahra,abinda duka y'an uwanki basuyiba."
Umma ta'kare maganar kamar zatayi hawaye.
Zahra dai kuka take tana"allah umma nadena."
Umma bata bartaba saida tayimata ligi-ligi tasaketa,tafara haramar alwalar isha'i.
Zahra ta 'kyalla idanu taga umma tashige d'aki,
Hakan yabata damar sake ficewa gidan da saurin gaske,
Bazata mance kirarin dasukeyima kansuba wai *abuga asaki bata maganin d'an iska sai dai ta'kara taurin fata*.
Azauren su ummilolo tala'be,tana 'kwalama ummilolon kiran,
Hajara kishiyar innar ummilolo tafito tana masifa don tasan zahrace"kewai wacce irin ballagazar yarinyace,halan kekam uwarki bata kwa'ba maki.duka yaushe kuka shigo gidan amma dayake bakida tarbiyya harkin sake fitowa,to oya maza fice anan ummi babu inda zataje."
Shegiyar yarinyar yarinya mai kama da d'inya,ke ba'ka halinki ba'ki.
Zahra ta murgud'a baki dacewa "badai niba."
Inna hajara tace"sai ubanwa"
Zahra cikin rashin tsoro tace "ubanki"
Aiko inna hajara tayo kanta zahra tajuya da niyyar rugawa amma tuni inna hajara ta cafketa.
Mari biyu 'kwarara tayi mata, taci gaba dafad'in"duka iskancin dakikeyi 'kyaleki akayi.wlh kinshigo gonata ubanki zakici."
Zahra dayake ruwa ruwace tuni ta 'barke da kuka tayi waje aguje,
Takuwa koma 'kofar gida ta tara duwatsu tadinga yima gidansu ummilolo ruwan duwatsu,
Duk da haka bakinta bai sassauta da zagin datake d'urama hajaraba.
A tsotsayi d'an hajara yafito zashi kicin d'aukar abinci dutsen ya sauka akanshi jini sosai ya tsinke ganin hakan yasaka hajara kama hannunshi suka nufi gidansu zahra tanata masifa.
Zahra daganan zugar yaranta sukaja,suka la'be lungu ilai kuwa saiga inna hajara tadawo da abbalo ansaka mashi bandage,
Zahra da sauran 'kawayenta sukayi masu ature da 'kasa har cikin bakin hajara da idanuwanta.
Zahra data du'ka tana 'kyalkyala dariya tace"kuma wlh kisake dukana saina kama wannan d'an naki a islamiyya saina fasamai baki."
Inna hajara tace"tsinanniya kije zaki samu dai daike."
Zahra dake wani gantsarewa tace"tsinanniya tana bayan uwarta tanashan nono,"
Sauran yaran suka kwashe da dariya.
'karshe dai inna hajara ganin zasu kunyatata gaban mutane yasakata sulalewa tayi gida,acan tad'ora sabon bala'i tana sauke kwandon zagi akan zahra da iyayenta.
A filin gad'a ma zahra saida suka dambace da yara kusan uku,
Daganan tace ayi zuga atafi jan fad'a.
Suna tafe duk wanda suka gani saisun tsokana,wani ya 'kyalesu wani yabisu a guje amma baya iya kamosu.
Dai dai wani lungu suka hango saurayi da budurwa na tad'i,
Zahra tace "yauwa alhmdlh dama waccen habibar dake fira prefect d'in makarantar muce gata muguwa tayita dukanmu,
Kuzo muje"
Yara suka bita d'uuuu,tana gaba.
Dayake garin akwai hasken nepa dakuma na farin wata,
Habiba na tsaye gefen saurayin nata can gefe wasu samarine data gama yima wula'kanci taga mai mota yazo.
Bata saka hijabiba sai d'an gyale daya tsaya iyakar kafad'unta.
Gefe dasu teburin masu shayine damasu tsire antara majalisa ana cafta.
Zahra tana isa kusa da habiba batayi wata wataba tasaka iyakar 'karfinta ta fincike zanin habiba,
Habiba gashi sam bata saka undey ba.
Saiga 'kafafun habiba tsaye zalo .
Zahra kuwa tace 'kafa menaci ban bakiba.
Takwasa aguje,yayinda saurayin habiban ya rufa masu baya
Tsabar kunya habiba saita du'ke inda take.
Sauran samarin data yan'kwana kuwa har fad'uwa sukeyi suna burgima saboda dariya .
Majalisar masu tea ma dariya suke suna 'karawa.
'karshe habiba d'an gyalen dake kafad'arta ta yafa a kafafunta.
Da rarrafe ta shige gida .
Su zahra sunyi gudun da yakai nisan inaa.sannan suka yarda zanen saurayin ya tsintoshi bayan ya du'ka yanata hakin wahala
Dafad'in "shegun yara saigudu kamar zomaye."
Daga tonon wannan fad'an kowa ya ware gida,
Kanshi tsaye banda zahra dake faman ra'be ra'be.
Tamakure a lungu,
Abba yadawo daga nemanta har yagaji yanufo gida yaci karo da mutum...
Matsalar nepa.
Ayi ha'kuri da wannan
September 22, 2017 at 7:44pm ·


��������

by yar charas��
[12:03, 24/11/2017] hm: *MIJIN 'KWAILA*����‍♀
Chapter 4 · 0% Book details