← Book details Me Zanyi Da Ita Part Complete 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 25

Sashe 22

Me Zanyi Da Ita Part Complete 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Shi kuwa sauri kawai yake ya isa part d’insu ya fitar da shatu kafin friends d’inss suzo su same ta. Yana bud’e d’akin mamaki ya kamashi ganinta tana barcinta peacefully ya zata zai zo ya sameta tana kuka. Gashinta a baje a saman pillow. Ya tsaya yana kallonta kafin ya daddage ya d’aka mata duka. Da sauri ta tashi da addu’ar farkawa daga barci a bakinta kamar yarda mommah ta koya mata. Ta tsaya tana kallonsa ranta a ‘bace. Tsaki yayi “da halla mi’ke ki fice Min a d’aki kafin wani yazo ya ganki kin wani baje min a bed kina barci salon ki saka min virus,saura kuma Idan kin shiga ki gayawa mommah ni na hanaki zuwa wallahi sai na miki rashin mutunci dama tana tambayrki kice barci ne ya kwasheki kuma kanki Na ciwo shi yasa ba kije ba.” ta’be baki tayi kafin tayi magana ya ja hannunta cikin mita yake cewa “wuce muje na lura so kike sarakan maganar nan su ganki anan to ta Allah ba taki.....” sak yayi yana kallon abokansa da suke zaune a parlourn idanunsu a kansa a zuciyarsa yayi tsaki yace mayu kawai ya juya d’akinsa ya rufe gam da key. Dariya suka tuntsire da ita Ali da Abdul suka bi bayansa don tsokana sai dai suna zuwa suka tarar ya rufe bedroom d’in gam.Ali ya tuntsire da dariya “Bar magulmaci dama wa zai ce baya son wannan zu’ke’kiyar da gaba ma ba’a son kyan da za tayi ba.

Shi kuwa Imran dama ya san idan ya bar ‘kofa a bud’e yaga ta kansa don haka ya rufe. ‘Ko’karin cire kayan sa yake yana cire babbar rigar zai d’aura akan gado idonsa yayi masa kyakykyawan gamo da sauri ya ware ido yana kallon stain d’in da yake gadon sa da d’an ‘karfi yace “what?”lallai ma yarinyar nan ta gama raina ni ‘bata gurin nan tayi haka Allah yaso wani bai shigo ya gani ba, balle a zata disvirgining d’inta yayi.ya dafa kan sa zuciyarsa na tashi “wallahi yau shatu kin gama dani ina zan kai wannan kayan ‘kazantar ko masu aiki na bawa fassarar da zasu yi min kenan kai ya Allah wace irin yarinya ce wannan?” Tsaki ya sake ja ya fara ‘ko’karin yaye dubet d’in da bed cover d’in ya d’aga can dole yaje toilet ko idonsa ne ya rufe ya wanke ga shi bashi da hand gloves.iya gurin ya kama yana runtse idonsa, bud’e toilet d’in ke da wuya ya sake yin wani gamon da sauri yayi cilli da bed sheet d’in cikin sink amai na taso masa wannan wace irin ‘kazama ce yanzu kuma ita aka aura masa? Wallahi ba zai iya wannan ‘kazantar ba, idonsa a runtse yay flurshing toilet d’in yana yi yana ja
Mata Allah ya isa kamar wani ya sa shi. Ya saka harpic, yana sakin ajiyar zuciya a zatonsa ya gama amma ina juyawar sa ke da wuya ya ga undies d’inta zube a ‘kasa da sauri ya ja baya,kamar ba zai yi ba sai kuma yayi tsaki ba dolena nayi ba duk wanda na kira kamar na tarawa kaina jama’a ne kowa kuma da fassarar da zai yi masa.idanunsa a runtse shima undies d’in ya d’auke shi ya saka a toilet bin kafin da safe ya kira ta wallahi sai ta wanke masa toilet tsaf duk dama gobe zai bar gidan sai ta ci kanta ita kad’ai, da kyar ya wanke bed sheet d’in kawai don baya son yin wani cikin friends d’insa by mistake ya shiga ya gani wallahi da shima barin sa zai yi ta zo ta wanke to yana gudun ‘bacin rana kada ayi zaton wani abu yayi da ita shi kuwa Allah kada ya nuna masa wannan ranar da wani ido zai kalli jama’a bayan tarin cika bakin da yayi akan cewa MAI ZAI YI DA ITA. Yana gama wankewa ya cilla shi cikin washing machine sai sannan zuciyarsa ta dinga tashi ai kuwa ba ji ba gani ya dinga kwara amai sai da ya gama aman yayi brush yana gamawa ya fice da sauri murya a cunkushe yace wallahi ban yafe ba banza ‘kazama.😂 ya gyara gadonsa tsaf ya bad’e bedroom da turaren wuta da room freshner. Sannan ya fice parlour baya tunanin zai iya wanka a toilet d’in wallahi dole key ya d’auka a daren gwara yaje gidansa yayi wanka. Yana had’e rai ya fito, ai kuwa suna ganinsa Ali da shegantaka ya taso”wai ya aka yi ne yalla’bai mai amarya tazo yi part d’inka ko dai har ka fara sonta ne?”harara ya zabga masa “matseni in gaya maka” Abdul yace “ai abin bai kai na matsewa ba in dai wannan ne ai baya ‘buya abinda zamu gani ‘kunshe a mahaifarta muzo mu sha suna.” “Mtsww God forbid wallahi sai kace irin ku ai ni tunda nace muku ba abinda zanyi da yarinyar nan to kuwa zaku sha mamaki ba ku san waye Imran ba.” Dariya su kayi sosai suna kallo ya fice Ali yace “mhmn a dai juri zuwa rafi yalla’bai wata rana tulun zai fashe” Abdul ta tuntsire da dariya yace “d’an iska ranar mayar da martani ba.” Yana jin su murmushi kawai yayi ko don tanadin iskanci da suka yi masa ai ba zai kusanci yarinyar nan ba haka zai saketa wallahi da zarar shirinsa ya kammala. (To kowane shiri ne wannan mhmmn wani abin sai d’an gidan manga)

Ita kuwa tana bedroom d’inta bayan tayi wanka Night gown a jikinta da cup d’in tea a hannunta tana sipping a hankali so take ciwon marar da yake d’an damunta ya lafa mata. Hafsa ta shigo d’akin idanunta a kanta ta zauna a gefen gadon “wai ina kika shiga ne? Ban ganki wajen dinner ba?” Hafsa ta fad’a tana shafa kanta.
Murmushi shatu ta saki a karo na farko taji tana son rufa masa asiri saboda sam bata son haushinsa da mommah take ji tace “wallahi period pain ya hanani fita d’azu fa kamar na mutu dole kuwa nayi kwanciyata side d’in su Ya Imran.” Hafsa ta girgiza kai “ashe da gaske yake wallahi na zata ‘karya yake har na had’a shi da mommah sai kije ki wanke sa a wajen mommah don wallahi ta kunnu da yawa cewa take zai zo ya sameta don ma Hajiya mama tana hanata tace ba huruminta bane da tuni ta kira shi ta sulle shi sai kije ki wankeshi.” Shatu ta mi’ke ta tafi wajen mommah. Tsaf ta wanke shi kuwa mommah ta jata jikinta “oh am sorry daughter to da kika yi zamanki a can hope ba abinda yayi miki kuma kin sha magani?” Daga kai tayi tana kwanciya a cinyar mommah da take feeling d’inta kamar Innaji she really love mommahnta to the extent.

Da safe Dahda ya shiga wajen hajja gaishe ta da kyar take amsa gaisuwar. Sister’s d’insa ma duk suka gaisheshi anan yake sanar da Hajja tariyar shatu ita ma kamar yarda kawu sa’idu ya tsara sati mai zuwa Hajja ta ta’be baki”To ni yanzu ina ruwa na nayi magana kaje ka yayata ni a bakin duniya ai ba abinda zance maka manga aje Allah yayi albarka gobe-gobe ma zamu tattara komatsanmu muyi gaba ba kuma zamu sake dawowa ba kamar yarda ka bu’kata kuma ina son ka jini da kyau dama ka samu fili ka siya ka fara yi min gini anan kano duk san da na tashi zuwa na dinga zuwa can na sauka na san mallakina ne. Shashasha ana yi maka gata baka san gata ake maka ba duk an mallakeka da
Surkullen fulani.” Murya can ‘kasa Dahda yake amsa mata “Insha Allah Hajja za’a Gina,amma tafiyar da kun bari wani satin idan shatun ta tare.” Hameedah mai son ganin ‘kwaf ta gaban Hajiya ta saka baki “eeh Hajiya mu bar shi wani satin idan ta tare sai mu tafi cab amma za’a ga ‘kwailar amarya ai ni na zata ba yanzu zata tareba. Dahda ya zabga mata harara don sam basa shiri da hameedah baya son halayenta gaba d’aya.ya mi’ke yana yiwa Hajiya godiya bayan ya ajiye mata ma’kudan kud’i da niyyar yi mata toshiyar baki. Bakin Hajja kam yana mutuwa tsaf saboda kud’i.nan ta shiga jera masa albarka. Yana fita hameedah ta shige part din zainab ta bata labarin tariyar. Hankalin zainab ya tashi don basu kawo tariyar nan kusa ba sun zata sai ‘yar su ta riga ta mallake gida tukunna sai ga sabon labari ya bayyana a zuciyarta tace ashe kuwa sai na tashi tsaye kafin kwa’bata tayi ruwa.

Tsaf yayi wankansa ya shirya cikin shigarsa ta musamma farin filtex d’insa da hula damanga takalmi bartozzi ya d’ora agogon rolex d’insa a damtsen hannunsa kana ganinsa kamar ka sureshi ka sace. Sai zabga ‘kamshin turarensa da yake mix yake different colours ‘kamshinsa daban yake.
Direct part d’in mommah ya nufa cikin tafiyar izza kamar Kuma ‘kasaita kamar yarda ya saba yi kullum. So yake yaje ya dam’ki ‘yar gidan mommah ta wanke masa toilet duk da yasa an wanke amma sai ya wahalar da ita.
Chapter 22 · 0% Book details