← Book details Matar Damisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 57

Sashe 8

Matar Damisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Security gidan kuwa suma da gudun gaske suka shiga cikin d'akin direct d'akin Junaid suka nufa saboda sun san duk wani problem daga d'akin Junaid yake fitowa,
Suna shiga cikin d'akin suka tarar da abun al'ajabi, zaro idanuwa sukayi waje sun firgita da ganin Junaid a haka ga kuma mommy a shanye a 'kasi sumammiya, cikin zafin nama suka nufi gurin da Junaid yake Gadan-gadan sun d'ago hannu zasu jawo Junaid nan sukaji an had'a kayuwansu biyu aka gwara kamar daga sama kuma basuga kowa ba, ba 'karamin buguwa akayi musu ba kwakkwalwarsu ne ya fara juyawa kafin nan kowannen su suka fad'i sumammu, sauran two bodyguard suma ganin hakan yasa suka nufi gurin babu tsoro a fuskarsu zasu sa hannu su finciki Junaid daga jikin gini sukaji an sha'ko wuyansu duk su biyun an d'aga su sama kakaki suka farayi suna ri'ke wuyansu, saiga mai gadi shima ya shugo da gudu cikin d'akin abunda ya ganine yasa shi tsayawa cakk ganin gardawa a sama suna lilo da 'kafafuwansu kuma bai ga abunda ya d'agasu sama ba, nan take yasau fitsari a wando jikinsa ne ya hau 6ari,
Su kuwa sai da numfashin su ya tsaya cak sannan aka wurgar dasu kan mai gadi da yayi sumar tsaye, sai yaraff duk su biyu akan mai gadi shima saida yayi asalin suma jin Manya-manyan gardawa a samansa.

Bayan 1hour Ayush dai tana cikin toilet jin ihun da akayi yasa ta 6oye a gurin, tana tsugune har ta gaji jin babu komai yasa ta bud'e 'kofar toilet tana Le'ke-le'ke cikin sand'a take tafiya har ta sau'ko falo babu kowa,
A hankali take 'kiran sunan "Aunty, Aunty, kina Ina ne" taji shuru ba'a amsa mataba, ta nufi kitchen tana bud'ewa taga wayam ba kowa
Anan fa ta fara rawar jiki tsoro ne ya bayyana akan fuskarta, "innalillahi wa inna'ilaihi raju'u, Allah yasa dai ba 6arayi bane suka shugo gidan, naji ihu kuma yanzu babu kowa"
Tana magana cikin kuka hawaye ne sharaf-sharaf suka fara gangaro mata a saman kunci, ta lalle'ka ko Ina amma bataga Mommy ba, ta duba agogon saman bango 12:30 ne.
Tayi hanyar waje ko zataga security hankalinta zaifi kwanciya,
"May be an kirata ne a asibiti" a cikin ranta take wannan maganar!
Abun mamaki ko dataje waje bata ga kowa ba hatta mai gadin sai haske Dara-dara ta ko Ina,
Wani irin yawu ta had'iya ga gumi kuwa daya fara tsirto mata, kakkarwa ta somayi tana tunanin kar itama a sace ta
Da gudun gaske ta koma cikin d'aki tana maida numfashi,
Ta zauna a saman kujera 1seater dafe kanta tayi ta fara rera kuka
Ita kanta ta rasa shin kukan mai takeyi
Shin na rashin ganin mutanen gidan ne ko kuma kukan tsoro ne, tana cikin wannan halin ta tuno da Junaid! Da sauri ta d'ago kanta idonta sun rine sunyi jaa "Ina yaron gidan, ko shima an sace shi" tana magana tana kallon upstairs d'in d'akin Junaid
Cikin rawar jiki ta mi'ke da sauri tayi hanyar d'akin Junaid tana taka matakala da sauri-sauri kamar zata kife,
Tana zuwa daf da d'akin tasa hannu zata bud'e naushin da Junaid yayi mata ne ya fad'o mata a rai, tsayawa tayi cak cike da fargaba ta fara tunanin "ya za'ayi na shiga d'akin wannan azzalumin d'azu ya naushe ni yanzu kuma ban san wani muguntar zai 'kara mun b, ta juya zata bar gurin ta koma falo sai wani tunanin ya sake fad'o mata shin idan kuma shima ansace shi fa? Inma ba'a sace shi ba ai zai fita ya nemo mutanen gidan!

Knocking ta fara yi taji shuru ko motsi bataji ba ta sake buga 'kofar still ba motsi
Almost 30minute tayi a tsaye tana sa'ke sa'ke a raanta
Daga baya ta yanke shawarar shiga kawai, cikin rashin sa'a tana shiga tayi tuntu6e da mutum a gabanta,
Juyowa tayi ta kalli gurin ganin Mommy a kwance yasa taji fad'uwar gaba,
"Innalillahi was inna'ilaihi raju'un Aunty meya sameki" jijjigata ta somayi taga babu alamar motsi
Juyawar da zatayi taga mutane uku aguri d'aya 2 bodyguard da mai gadi ja da baya tayi cikin firgici da tsoro tana waiwaya gabanta taga still 2 bodyguard kwance ba motsi
Daman bodyguard 4 ne a gidan sai mai gadi

Bakinta ne ya soma kakkarwa ko magana ta kasayi
Ga wani irin guminda yake yarfo mata
Cikin fargaba da tsoro take bin d'akin da kallo
Karaff idonta ya sau'ka akan Junaid dake manne saman bango rai a hannun Allah, 'Kara ta sau tare da toshe bakinta kuka ne yaci ranta yau taga abunda tinda aka haifeta bata ta6a gani ba.

Da gudun gaske ta nufi gurin da Junaid yake, jinin da yake d'idd'iga daga jikinsa duk ya 6ata tiles d'in d'akin,
'Dagowa da kanta tayi ta 'kura wa fuskarsa ido lokaci guda kuwa ta zaro Manya-manyan idanuwanta waje bakinta ne yake motsi kamar maiyin magana, jikinta kuwa rawar sanyi ta soma, cikin firgici ta jaa baya da sauri sai da ta fad'i 'kasi still idonta akan Junaid
Da kyarr ta iya bud'e bakinta cikin kuka ta fara fad'in
"Wayyo Allah nah Umma nah, Kaine ka kashe mun Ummana bazan yafe maka ba, ka sanya ni cikin maraici! Saika tozarta a rayuwa, sai kayi mutuwar wulakanci kamar yanda ka kashe mun mahaifiyata"
Gaba d'aya Ayush idonta ya rufe bata ganin halin da Junaid yake ciki, kamar zautacciya haka take maganganu cikin fitar hayyaci,
Saida ta gama surutanta ta mi'ke da gudu ta fice daga cikin d'akin...

Shi kuwa Junaid duk abubuwan da yake faruwa bai saniba , baya cikin hayyacinsa,
A halin yanzu taimako yake bu'kata
Kuma Ayush ce kawai zata iya wannan taimakon, in har ba itaba ba Wanda zai iya ceton Junaid daga hannun azzaluman Aljanun nan da kuma mahaifinta.

Barin Ayush cikin d'akin falo ta nufa ta kwanta 'kasan carpet tana rera kukanta mai cin rai, a halin yanzu ba mutumin da Ayush ta tsana kamar mutumin da ya kashe mata mahaifiya,
Kuma saita d'au fansar mahaifiyarta akan sa,
Wato JUNAID.........

TO BE CONTINUE INSHA ALLAH.

*ASMEETAH* *CE* ✍️✍️✍️

*FREE* *BOOK*

🐅 *MATAR* *DAMUSA* 🐅
(the wife of tiger)

*MALLAKIN*
*ASMEETAH* ✍️✍️

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________

https://www.facebook.com/103637491942644/

💫💫 *{{N W A}}* 💫💫

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم

*BOOK* *ONE*
*PAGE* ➡️21 to 22
Chapter 8 · 0% Book details