Sashe 57
Matar Damisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
wajen yayi tsit ana sauraronta,
hannu tasa ta yaye gyalen kan natan tana kallon Junaid tace "Ban Amince ba, kuma bazan taɓa Auransa ba! dukan mata yake yi, yau ma saida yayi wa wata budurwarsa duka kamar zai kasheta, a haka zan aure shi? to gwara na mutu banyi Aure ba, idan na Aure shi zai iya murɗe mun wuya ya kashe ni, ga ƴanmatan ka nan ka zaɓi ɗaya ka Aura amma banda ni......"
tana kaiwa ƙarshen maganarta ta juya da gudu zata tafi, ta gurmuɗe da takalmin ƙafarta zata faɗo ƙasan floor da aka ɗanyi tudun beni a gurin da sauri Junaid ya cafko kunkuminta ya rungumota jikinsa har idonsa ya cicciko da ƙwalla yana kallon yawan mutanen da suke wajen mata da maza gasu nan, yana rungume da ita jikinsa na kakkarwa tsabar takaici da baƙin ciki tinda yake ba'a taɓa basar dashi a cikin mutane ba sai yau, gaba ɗaya ya rasa ya zaiyi kamar ya nitse cikin ƙasa haka yake jii,
hajijiya ne yake shirin ɗibarsa, ƙafarsa tayi masa nauyi yana shirin faɗuwa da Ayush da yake rungume da ita, abokinsa commander yusuf yasa hannu ya ɓanɓare Ayush a jikinsa ya zaunar dashi yana bubbugar kafaɗarsa alamar rarrashi,
Ayush zame jikinta tayi tana tattara rigarta ta bar wajen kwata-kwata...
idan aka ware Laylah da Rumana da kuma Adity duk wajen ba wanda zuciyarsa bai sosu ba, musamman abokansa tsabar takaici kasa cewa komai sukayi suna zazzaune kamar wanda ruwa ya cinyesu,
Mommy kam haɗa kanta tayi da gwiwowinta bansani ba ko kuka take yi...
Angel itama kamar ta rausa ihu tsabar takaici, domin duk abunda zai taɓa Junaid haka take jinsa a ranta,
babban tashin hankalinta shine ganin hawayensa, tinda take dashi bata taɓa ganin hawayensa ba sai yau...
suna zaune babu wanda ya motsa sai matar nan mai liƙab itace ta tashi da sauri tabi bayan Ayush,
tana shiga parlour kai tsaye upstairs ta wuce saboda taga daga nan aka fito da ita,
tana buɗe ɗakin Ayush ta tarar da ita kwance sai faman rera kuka take,
ta rufe ƙofar sannan ta ambaci sunata "Ayushh.." cikin ɓacin rai ta ƙira sunan..
Ayush ɗagowa tayi da manya-manyan idanuwanta waɗanda sukayi jaa, har yanzu ta kasa gane ko wacece,
matar hannu tasa ta ɗage liƙab ɗinta sama,
a razane Ayush tana kallon matar ta tashi zaune tareda faɗin "Umaa! Uma kece daman kika zo.."
Ayush tashi tayi da gudu ta nufi yanda Uman natan take zata rungumeta, ta riƙo Ayush ta zabga mata mari, tana ɗagowa kuma du ta ƙara zabga mata wani marin ta ɗayan ɓangaren ta saketa ta faɗi ƙasi tana kuka ta riƙe fuskar ta da hannu biyu.......
*ALHAMDULILLAHI ANAN NA KAWO ƘARSHEN LITTAFINA NA ƊAYA..*
*YA ALLAH KAMAR YANDA KA BANI IKON KAMMALA LITTAFINA NA FARKO ALLAH KA BANI IKON GAMA NA BIYUN*