← Book details Matar Damisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 57

Sashe 22

Matar Damisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ɓingel nasan kin tsaneni a cikin zuciyarki, sakamakon labarin da mahaifiyarki ta baki akaina, wanda hakan ba gaskiya bane,
Mahaifiyarki bata san komai a kaina ba, ni ba mungu bane, ni ba azzalumi bane, ni kaina nasan dalilin daya sa nake wahalar da Junaid wanda sirri ne a gareni, zaki san wannan sirrin amma ba yanzu ba akwai lokaci!
Ɓingel ki daina ɗaukar kanki cewa ke bakida ƴanci,
Ke ƴa ce kamar kowa ni mahaifinki ne, kuma ta hanyar Aure aka sameki, amma sai dai mahaifiyar ki bata san da hakan ba,
Ni na sanar miki ne domin ki sakawa ranki nutsuwa, ki kwantar da hankalin ki a matsayinki na ƴer masarauta gimbiya *MAYUSHERT* asalin sunanki kenam!!!
Sannan mahaifiyarki tana nan da ranta bata mutu ba, akwai lokacin da zakii ganta ba yanzu ba...
Kece AYANAR JUNAID hakan yasa damusa na baya iya motsi idan kina tare da Junaid domin duk wani motsin sa yana a tattare da Junaid,
Rashin motsawarsa kuma illa ne hakan yasa banaso kina kusantar shi saboda damusa yana cutuwa motsinsa kuma zaisa Junaid cutuwa,
Makaryar wannan tsafin kuma yana tattare da ke, hakan bazai yuba saboda zaki iya cutuwa, kuma zan iya rasa duk wani ƙarfin ikona...."

Ajiyar zuciya yajaa yana kallon ɓingel ɗinsa wacce itama kallon mahaifin natan take..

Leɓenta ne yake motsi da ƙer ta iya cewa "meye abun dake jikina na makaryin tsafin?.."

Dariya yayi short har sai da dimple ɗinsa ya lotsa yace "bazan sanar miki ba ɓingel, saboda nasan idan soyayya tayi nisa zaki iya cutar da ni,
Amma inaso ki sani cewa bazaku taɓa yin Aure ba a tsakaninku ke da Junaid,
Har sai an karya wannan tsafin jikinsa, idan kuma ba haka ba
*DAMUSA* *BAZAI* *AURI* *GIMBIYA* *MAYUSHERT* *BA*...

Kafin ta furta wani abu ya kuma katseta da cewa "ga wannan duk wani ƙundin tarihi na yana ciki, kada ki bari wani ya gani"
Wani ƙatoton littafi ne ya miƙa mata a bayan littafin an zana masarauta.....
Ya kuma cewa "duk wanda ya ɗauki littafin nan bazai taɓa buɗe shi ba, sai wanda yake da alaƙa da masarautar kamar ke...
Na barki lafiya Ɓingel.."

Juyawa yayi yahau saman dokin sa,
Ayush kuwa tana riƙe da takobi da kuma littafin da aka bata
Baki na rawa tace "shin menene sunanka?"

Murmushi yayi sannan yace " *SARKI* *RAAMAD*..

Ya kamata ki rage tsoro domin ke jinin Jarumi ne....
Sannan ni ba Boka bane sai dai na kasance ni matsafi ne, kuma ni musulmi ne! kada kuyi mun mummunan fassara..."

Yana kaiwa nan yayi tafiyarsa.
Ita kuwa Hasken daya kawota shine ya kuma ɗaukar ta....
Sai tsintar kanta tayi a cikin toilet ga ruwan shower yanata zuba..
Jikinta ta duba taga jallabiyan Junaid aka maido mata dashi, ga kuma hannunta riƙe da littafin tarihin mahaifinta da kuma takobin da ya bata...

Bata ankara ba taji ance "Yushert wai mekike a toilet haka since."
Muryar Junaid ta jiyo yana magana..
Wanda tin ɗazu shigowar sa room ɗin bai ganta ba sai zubar ruwa yake ji,
A tunaninsa wanka take sake yi, bai yi tunanin babu kowa a ciki ba...

Rasa yanda zatayi da abubuwan da suke hannunta ta yi, da sauri ta buɗe drower cikin toilet ta a jiye su a ciki sannan ta rufe..
Ta kashe ruwan dake zuba sannan ta fito,
Zuba mata eyes yayi yace "daman ba wanka kike yi ba tin ɗazun? to me kikayi kenan?"

kiɗimewa tayi ta soma ƙinƙina tana faɗin "daman daman da daman nayi ne"
Kallon ta yake cike da mamaki yace "kinyi mai?"
Gaba ɗaya ta rasa mai zata ce, sai kawai zuba masa ido tayi...

Tashi yayi daga zaunen ya nufi toilet ya buɗe ya gama dube-dubensa
Yakai idonsa kan drower yasa hannu zai buɗe da gudu Ayush tayo kansa tana faɗin "na wanke toilet ne kar ka ɓata shi," ta kuma riƙe hannunsa wanda yakai zai buɗe gurin ma'ajiyin ta.

"Mtsw kuma shine ina tambayarki kika yi shuru?.."
Sunkuyar da kanta tayi ƙasa ta kasa ɗagowa,
Jan hannunta yayi suka fita daga cikin toilet,
Kai tsaye haurawa saman bed ɗinsa yayi
Ya kwanta tare da janyo mayafi ya rufe jikinsa
Tsayawa tayi Ayush, yace "ke bazaki kwanta bane?"

Murya ciki-ciki tace "ni bazan iya kwanciya a tareda kai ba"
"For what?"
Ya tambaya a takaice.
"Saboda bazan iya juran yanayin da zan shiga ba!"
"Ban ganeba? What do you means?"
Yayi tambayar yana kallon fuskar ta.
Sunkuyar da kai tayi ta kasa cewa komai...

Tashi yayi daga kan gadon
Yace "toh kwanta na bar miki gadon tinda bakyason kwanciya da ni"
Ɗaukar pillow yayi yaje saman sofar ɗakin ya kwanta...
Itama bin kan gadon tayi ta mimmiƙe tareda rufe kanta da mayafi..

Maganganun mahaifinta ne suka soma dawo mata kwakwalwar ta,
Tayi matuƙar yin farin cikin jin abu biyu daga gare shi
Mahaifiyarta tana raye, da kuma ita ba ta hanyar fasiƙanci aka sameta ba,
Wannan abun yayi mata daɗi a ranta
Bugu da ƙari kuma taga mahaifinta face to face tinda aka haifeta bata taɓa ganinsa ba.....

A ranar da farin ciki ta kwana.......!

*MASHA* *ALLAH*
yaaa Allah kamar yanda ka bani damar rubuta littafi na Allah ka bani ikon kammalawa 🙏🙏

*ASMEETAH* *CE* ✍
️✍️✍️

*FREE* *BOOK*

🐅 *MATAR* *DAMUSA* 🐅
(the wife of tiger)

*MALLAKIN*
*ASMEETAH* ✍️✍️

wannan page ɗin naki ne Aunty Fateemah shugabar ƙungiya 🥰😘..

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________

https://www.facebook.com/103637491942644/

💫💫 *{{N W A}}* 💫💫

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم

*BOOK* *ONE*
*PAGE* ➡️53 & 54⬅️

______________ washe gari Mommy tana zaune akan kujerar ɗakin da aka kwantar da Dr. Hasheem,
sai gani tayi ya miƙe zaune yana faɗin "Allah ku ceceni daga hannun wannan mungun mutumin, wayyo zai kashe ni". yana ta waige-² idonsa ne suka sauƙa akan mommy wacce ta riƙe shi tana cewa "Dr ka kwantar da hankalin ka babu abunda zai sameka, insha Allahu zaka samu sauƙi."
Sama-² yake jan numfashin sa gaba ɗaya ya rasa sukuninsa, duk jikinsa sai ciwo yake!

Kansa ya sha bandeji ga hannayensa waɗanda suma suka sha ƙarfuna, ya samu karaya sosai.
A yanzu ba mutumin daya tsana a rayuwarsa inba Junaid ba
Yana maganar zuci "wai ni Junaid zai rufe ido yamun wannan aika-²? insha Allahu zan ɗau fansa bazai ci bulus ba, nima zan nuna masa nii ba kawwan lasa bane, nima inada gata..."

Yayi tagumi sai hawayen dake tsiyaya daga idanuwansa,
Mom ce ta dafa kafaɗarsa tace "Dr Hasheem kayi hakuri dan Allah, nasan Junaid ya aikata babban kuskure, amma inaso ka sani cewa yayi maka hakane ba tareda saninsa ba, baya cikin hayyacinsa kaima kasan da hakan, ka kuma san halin abokin nakan, nima a hankali nake binsa saboda abu kaɗan ne yake ɓata masa rai...."
Hmmm! Jan zuciya tayi sai hawayen daya zubo saman fuskar ta, zuciyar ta ne yake mata raɗaɗi ta rasa yanda zatayi ta magance matsalar Junaid...

Shuru Dr yayi baice komai ba, shi kaɗai yasan kalar raɗaɗin da yake ji shima..

*****

Asuban farko Ayush ta farka daga bacci tana miƙa tashi tayi tanason shiga toilet domin ɗaurowa alwala sai da ta kunna light ɗin ɗakin before ta shige cikin toilet tama manta da Junaid acikin ɗakin,
Har saida ta tsuguna kafin ta tuno ashe dai tana period, turɓune fuska tayi tana faɗin "kashh! na manta" ta nufi hanyar fita kenam ta tuno da ajiyar datayi cikin drower, da sauri ta nufi gurin ta buɗe ciki, ajiyar zuciya tayi ta dafe saman ƙirjinta,
Ɗaukar su tayi ta fice daga toilet
Tana fita kuwa idonta suka sauƙa akan Junaid gaban ta ne yayi wani irin bugawa sauran kaɗan tasau littafin a ƙasi, hannunta ne yahau ɓari!
Shi kuwa yana kwance sai shan baccinsa yake cikin nutsuwa.

Da sauri ta tusa littafin da takobin ƙarƙashin gado.
Ta taso tana tafowa gurin da Junaid yake a kwance saman sofa, durƙusawa tayi tana fuskantarsa idonta akan sa tana ji yanda yake jan numfashi a hankali idonsa a rufe ba ƙaramin kyau yayi mata ba,
Ta kai idonta kan maroon lips ɗinsa gashi ɗan ƙarami
tana matuƙar jin sha'awarsa amma shi ko kaɗan baya wannan tunanin a ransa
Ji take kamar ta rungumeshi tsabar tsananin so da ƙauna,

Red lips ɗinta take matso dashi saitin nasa tana ƙoƙarin manna masa kiss
Jin yanda numfashin su yake gaurayuwa yasa Junaid buɗe eyes ɗinsa daiden lokacin ta ɗan zura tongue ɗinta cikin bakinsa,
Ita kuwa kasa control kanta tayi yasa har ta aikata hakan ba tare da saninta ba,
Cikin sa'a kuwa ta kamo harshensa ta fara masa tsotsar lollipop tana lumshe ido.

(To fah Ayush ta tafi sararin samaniya 🫢,
Yooo lips ɗin Junaid ne jan hankali gareshi 🙈🙈🙈 )..

Shi kuwa kamar wanda aka ɗauke masa wuta, ido ya lumshe yana jin duk tsotsar da take masa amma ya kasa dakatar da ita,
Shi ko kaɗan baya wani jin feeling sai zaƙin harshenta da yake ji, harshenta kamar zuma.

A hankali yake motsa tongue ɗinsa yana juya shi a cikin nata
Wani irin salo yake bada wa hakan ya ƙara jefa ta cikin duniyar taurari,
Bata san lokacin data haura saman sa ba ta rungume shi sosai,
Hot kiss suka shiga aikawa juna, a cikin tana nishi ciki-² har ya fito fili, duk abunda take kuwa yana jinta!
Amma duk da hakan bai sa yaji sha'awa ba sai dai nutsuwar da yake samu a tattare da ita,

Ganin bata da niyar barinsa yasa ya tallafo kanta ya raba bakin ta da nasa,
Yana faɗin "it's okay, kin samu nutsuwa koh?.."
Chapter 22 · 0% Book details