← Book details Matar Damisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 57

Sashe 36

Matar Damisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Doctor Hasheem yana kallon cikin idanuwan ta yace "becouse i love you, I love you Ayushert, ke rayuwata ce sannan kuma mafarki na, ki cika mun burina na Auren ki dan Allah my Ayushert..."
Ajiyar zuciya Ayush tayi sannan tace "bai kamata ace munyi maganar soyayya a nan ba, saboda majinyaci ne a gaban mu..

"No Ayushert idan kika amince da soyayyata ni kin gama mun komai, inaso Junaid ya zame mun shaida duk da nasan baya cikin hayyacinsa, please my Ayush..."

yana murza mata lallausar hannayenta yana ƙara matsowa daff da ita,
a tunaninsa zata dakatar da shi sai kuma yaga akasin haka, farin ciki ne ya fara wanzuwa a zuciyarsa, hakan ya bashi daman rugumarta jikinsa yana faɗin "sorry my Ayush, keɗin farin ciki nane"
Itama kwantar da kanta tayi akan kafaɗarsa tana zubda hawaye ta kasa cewa komai,
ita dai hankalin ta yana kan Junaid, Doctor ne ya ɗago ta suna fuskantar juna, bakinsa yake shirin kaiwa nata saitin bakin, ganin lokaci guda Junaid ya buɗe idonsa, da sauri Ayush ta kawar da fuskarta ta nufi gurinsa tana faɗin Yaya Junaid ka tashi ne Alhamdulillah, ta zauna daf dashi tana shafar suman kansa...

shi kuwa Junaid yayi shuru baya iya cewa komai, sai binta da ido yake yi, ita kuwa hawayen farin ciki take zubar wa tana wasa da sajen fuskarsa da hannunta,

Doctor Hasheem kuwa zuba mata ido yayi, shi dai takaicinsa Ayush tafi nuna damuwa akan Junaid sosai ma..

ganin ransa yana shirin ɓaci yasa yayi saurin fice wa daga cikin room ɗin...

( ta wani ɓangare Ayush ta magance matsala Junaid a rashin sani, domin tinda Ayush ta taɓa shi, shikenam jaririn Aljani ya bar jikin Junaid sai dai an toshe masa bakin magana, bazai iya aikata komai ba...))

suna cikin wannan halin Ayush taga bai kulata ba, ta ɗago da kanta tana kallonsa tace "Yaya Junaid kayi shuru kayi mun magana mana ko zanji sanyi a raina, insha Allahu zaka samu sauƙi.."
tana kaiwa ƙarshen maganar ta saiga Mommy ta shugo da sauri tana faɗin "Ayush na karɓi takardar sallama, Junaid maganin gida yake buƙata bana hospital ba.."
cikin rashin fahimta Ayush take kallon Mommy tace "meya samu Yaya Junaid ɗin har sai an nemi maganin gida..?"

Mommy ce tayo kan Junaid tana faɗin "kukan luɗa yake yi amma yanzu kuma naga baya cewa komai,"
ta dudduba shi naga jijiyoyin kwakwalwarsa basa motsi, kallonsa tayi cike da mamaki tace "Junaid meyake damunka ne haka?"
shi kuwa still idanuwansa suna kan Ayush ko ƙibta idon baya yi,
wasu likitoci ne suka shugo da keken guragu na asibity yanda zasu ɗora Junaid akai,

Ayush ganin yanda aka ɗauki Junaid aka ɗora shi akan keken yasa ta faɗin "wai meyake faruwa ne da Yayana Junaid, Mommy inadai ba gurguncewa yayi ba, dan Allah Mommy ki sanar mun mana..!

Mommy ce ta zauna ta sanar da Ayush abunda ya faru har zuwa wannan lokacin...
Ayush ba abunda take sai kuka, idon nan ya yi jawur tsabar kuka har kayinta ya soma ciwo....

Da haka aka fitar da Junaid har harabar asibitin suna tura shi, sannan suka saka shi a cikin mota, Ayush ce ta zagayo ta ɗayan ɓangaren ta shugo,
Junaid ta kwantar a saman cinyarta, Mommy kuma ta zauna a gaban motar,
Doctor Hasheem ne ya shugo cikin motar yana draving ɗinsu yana kallon Ayush ta cikin madubin motar....

isar su gidan sukayi horn da ƙarfi,
Mommy tana faɗin "bansani ba ko Baba mai gadi ya dawo.." kafin ta rufe baki sukaji an buɗe gate, direct miƙar hanyar da zai sada su da harabar gidan suka nufa,
bayan Baba mai gadi ya rufe gate yana gudu ya biyo motarsu Doctor, cikin ƙanƙanin lokaci ya iso gare su yana faɗin "Hajiya ashe Junaidu ne ba lafiya..?"
tsayawa Mommy tayi tana kallonsa tace "Baba ina kaje? ka barmun gate a buɗe, sannan meya samu yarana?.."

Baba mai gadi murya na rawa yake cewa "wallahi Hajiya bansan meya faru dasu ba, nidai abunda na sani shine ina zaune akan dadduma na sai najiyo ƙaran ihu daga cikin gidan, wallahi tsoro ne yasa na gudu, nayi tunanin Damusan sa ne ya motsa shiyasa..."

Ajiyar zuciya Mommy tasau tana kallon Baba mai gadi tace "Baba kaifa namiji ne, bayan Junaid kai kaɗai ne namiji kuma baza kaso wani abun cutarwa ya cutar dasu ba, dan Allah Baba a kiyaye dokar aiki..."

Baba jiki na ɓari ya amsa da "toh shikenam hakan bazai sake faruwa ba"
tace "Allah yasa"
ta shige cikin falo tana kara waya a kunnenta, tareda faɗin "Assalamu Alaikum Malam ya gajiya, dan Allah ina nemanka ne a gidana akwai babban matsala.."
sun gama waya ta katse kiran,
Upstairs ta haura yanda Doctor Hasheem ya kai Junaid wato ɗakinsa tare da Ayush, itama zuwa tayi ta samesu har an kwantar da Junaid akan gadonsa, daga nan Doctor ya yi wa Momy sallama yayi tafiyarsa domin bazai iya juran ganin Ayush tana manne da Junaid, hakan ba ƙaramin ɓata masa rai yake ba....

After 1 hour
Sai ga Malam har yayi parking motarsa a harabar gidan, sannan ya nufi cikin falo kai tsaye,
jin tsayar da motor yasa Mommy sauƙowa downstairs tana ƙiran malam tare da cewa "Dan Allah Mallam kazo ka duba mun jikin Junaid abu yayi tsanani ko tashi baya iya yi balle magana.."
Mallam da sauri ya haura upstair yana faɗin "subhanallah meya faru haka?"
Mommy fashewa tayi da kuka itama tabi bayan Malam, ɗakin Junaid suka shiga gaba ɗayansu, da sallama a bakin malam ya shiga tareda jera wasu add'o'i, yana shiga kuwa idonsa ya sauƙa akan Ayush a razane malam ya tsaya cak yana faɗin "Ayshert..."
itama Ayush tashi tayi tsaye ta zaro ido waje tace "Baba Malam..." lokaci guda tasau murmushi a saman fuskarta,
Mommy ce ta katse su da cewa "ha'aa daman kunsan juna ne?"

Malam ne ya dubi Mommy sannan yace "ai wannan....." Ayush tayi saurin katse shi da cewa "am am daman maƙwabcin mu ne, shi yayi magani a mahaifiyata har Allah yayi mata rasuwa, bamuda kowa shi ya temake mu, daga baya muka tashi a unguwar da yake.."
Ayush ta ƙarisa maganar tana girgiza wa malam kayi.

shima biye mata yayi da cewa "eh hakane.." yana kuma mamakin yanda ta iya zura ƙarya har haka, a cikin ransa yana faɗin "duk yanda akayi yarinyar nan tana ɓoye musu wani abu a cikin gidan nan, toh ma ya akayi tazo gidan nan bayan mahaifiyar ta Bara'at ta zauna har suka kore ta...." ya ƙarasa maganar zuci yana kallon Ayush wacce tin tinin gumi ya wanke mata fuska, tsoro ne ya bayyana akan fuskarta yau ta haɗu da wanda yasan labarinsu da mahaifiyarta kuma yanada alaƙa da gidan nan,
a cikin ranta kuwa cewa tayi "wayyo Allah na, asiri na ya kusan tonuwa idan har suka san cewa ni ɗiyar Bara'at ce shikenam kasheni Yaya Junaid zaiyi..." itama ta ƙarasa maganar tana zubda hawaye..

shima kansa malam ya fahimci Ayush tana cikin damuwa kuma zai temaka mata, yanada wannan niyar a ransa..
nufar gurin da Junaid yake kwance yayi, sannan ya zauna a bakin gado ya riƙe hannunsa sosai tareda rufe idonsa yana karanta wasu abubuwa,
cikin ƙanƙanin lokaci ya buɗe idonsa yana kallon fuskar Junaid, ga hawaye yanda yake gangaro masa daga cikin ƙayar idanunsa,
sannan ya juyo ya kalli Ayush ya karkaɗa kayi tareda yin murmushi, ya buɗe cikin jakar daya zo da ita ya ɗauko turare mai ruwa anyi rubutu ta larabci a jikin turaren,
yace "Hmmm! Aljanu aka turo masa, wanda zasu hanashi yin komai,"
Mommy tace "to malam daga farko kukan jariri yake yi yanzu kuma ya daina" malam yace "waɗannan ƙananun aljanu ne kuma suna matuƙar jin shakkar wata yarinya ce mai ƙarfin iko, wanda raɓarsa tayi ne yasa suka gudu, yanzu wani Aljani ne a jikinsa wanda bansan dalilin zamansa a jikinsa ba, amma yanzu zamuji abunda zai ce.
Wannan turaren ne malam ya watsa a saman fuskar Junaid,
nan take fuskarsa ta koma yellow ya kanne idonsa sosai!

Malam yana fuskantar Junaid yace "inason sanin meya kawo ka jikin bawan Allah nan..?"

Junaid ne ya buɗe baki kamar shine mai maganar, wata ƙatuwar murya ne yake magana kamar
"NI SUNANA ALJANI ƘUDDUS, AN TURO NI NE DOMIN NAZO NA KASHE JUNAID DAGA MASARAUTAR RAAMUD, TAUSAYINSA DA NAKE JI NE YASA BAN KASHE SHI BA, SHINE NA RAƁI JIKINSA, BAZAN TAƁA BARIN JIKIN JUNAID BA SAI AN CIRE ZOBEN DISH DAKE JIKIN CIBIYAR ƳAR SARKI RAAMUD..."

daga nan Aljanin yayi shuru,
kallon Ayush malam yayi sannan yayi murmushi,
yace wa Mommy "kindai ji abunda yace, amma insha Allahu zai samu lafiya...."

Mommy ce tayo kan Junaid tana kuka,
shi kuwa ganin haka yasa yayi wa Ayush magana yace "inaso zanyi magana dake Ayush, ki isoni a cikin motata ina harabar gidan.....

*ASMEETAH NOVEL✍️✍️*

typing📲

🐅 *MATAR* *DAMUSAA*🐅
(the wife of a tiger)

*written* *and* *story* *by*
*Asma'u Muhammad Auwal*

( *ASMEETAH NOVEL* ✍️)

*WhatsApp me 09065443871*

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________

https://www.facebook.com/103637491942644/

💫💫 *{{N W A}}* 💫💫

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم

*BOOK ONE*
🅿️ -------> 77 & 78 <-------

💫💫✨ Ayush tana zaune a cikin motor tare da mutumin da ake kira da Malam Lawan, tana zubda hawaye kai a sunkuye tace "malam wallahi banzo gidan nan don nayi musu leƙen asiri ba, ni da farko ban san su ba, dan Allah ka rufa mun asiri..."

Dariya Malam yayi da farin gemunsa yace "Ayshert kenam! inda ace zan tona miki asiri ai da tun farkon zuwanki gidan nan na tona, saboda har aka kaiki asibiti daga nan Hajia Fateema take riƙe da ke, nasan da alkhairi kika zo gidan nan, sannan zoben dake jikin cibiyarki sanan shine maganin ciwon Junaid,
ki temaka ki ceto Junaid ke kaɗai ce zaki iya magance masa matsalarsa Ayshert, insha Allahu baza ki mutu ba...
Chapter 36 · 0% Book details