← Book details Matar Damisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 57

Sashe 18

Matar Damisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bin bayan ta yayi da kallo yana wani tunani sai dai bae tsaya yin wani dogon tunanin ba ya tashi ya nufi toilet
Domin yasan halin Mom d'insa yanzu sai tace zata tafi kuma ba isasshen lafiya gareta ba...

After 1 hour
Mom tana zaune a gaban dinning table tana jiran fitowar Junaid amma shuru har yanzu.
Har ta gaji ga yunwa sai dai bazata iya cin komai ba batare da Junaid yaci ba....

sai jin takun sa tayi yana sau'kowa daga stairs a hankali kamar bazai taka 'kasi ba...
Girman Kai, Isa, gadara, jiji da kai, kwalisa, iya wash duk sun tabbata akan Junaid!

Mom kawai binsa take da kallo itama kanta yayi mata kyau sosai..
yau wankan black janpa akayi
riga yazo masa iya cinyarsa baije gwiwa ba yasha hannun leaps, ga takalmi shima black cover shoe, ya gyara suman kayinsa ya kwanta luf² sai she'ki yake har zuwa sajen sa zuwa short gemun daya bari sunyi ba'ki qirin sai sheqin da suke, hasken fatan sa ya 'kara bayyana, ga wani siririn glass da ya d'ora akan dara ² idanuwansa gwanin burgewa, kayan nan sun kama jikinsa sosai!!
Yana takowa a hankali but hankalinsa yana kan agogon hannunsa da yake d'aurawa....

A haka ya nufi dinning a nutse ya zauna yana fad'in "gud morning my Mom.."

'Dan hararar sa tayi bata kula shi ba ta maida hankalinta kan kular da take zuba musu ferfesun kayan ciki a plate, ta had'a musu tea mai kauri da cake, sai kuma ta 6angare guda roll eggs ne with bread, sai kuma apple da banana da pineapple, watermelon, sweet melon, pawpaws and other things duk an yanyanka su a cikin dinner set.....

Cikin nutsuwa sukayi breakfast
Junaid ne ya fara cire hannu ya goge bakinsa da taisho sannan ya d'auki phone d'insa da key d'in motar sa,
Ya nufi hanyar da zai sadashi da waje yana fad'in "Mom ki daina fushi dani, sai na dawo."

Kayataccen murmushi tasau sannan tace "a dawo lafiya my son"

A harabar gidan ya nufa, ya shiga motar sa
Ya karya kwana a hankali sannan ya mi'ki hanyar get already kafin ya Isa mai gadi ya bud'e masa, a d'ari ya bar gidan kamar walkiya ko bayan motar ba'a gani...

Mommy tana zaune kamar wacce aka aikowa sakon mutuwa,
Ita a duk sanda Junaid zai fita tana tararradi da fargaba domin ba wani cikakken mai hankali bane, ciwon sa zai iya zuwa mishi a kowani lokaci,
Kuma tsoronta kar ya hallaka mutanen dake waje.....

****

Junaid can Headquarter ya nufa wajen aikin su dake cikin Abuja,
Bayan ya gaggaisa da abokansa da kuma oganninsa direct office d'insa ya wuce domin gudanar da wasu ayyuka...

Duk da an dakatar dashi daga gurin aiki sakamakon cutar sa hakan baisa ya daina zuwa jifa ² ba,
Ba korar sa akayi ba andai bashi hutu ne duk wasu ayyukan yana yinsu a gida......

Around 6pm yabar h-quarter ya nufi hanyar hospital, kafin kace Mae Junaid ya Isa domin shi baya tafiya da mota a hankali....

____________ da sallama a bakin sa ya shiga cikin room d'in da Ayush take,

Dr. Hasheem ne zaune a bakin gadon da Ayush take tana zaune itama yana bata abinci a baki
yana fad'in "idan baki samu kinci abinci ba taya zaki samu karfin jiki, kinga allurar tana nan zanyi miki idan baki ci ba...."
kamar wata Yarinya haka yake bi da ita akan taci abinci.

Shugowar Junaid ne yasa hankalinsu ya koma kansa!
Tsayawa yayi yana kallon ikon Allah, jikinsa ne ya soma za'kami, wani irin yawu ya had'iya kamar wanda ya had'iyi dutsi, 'kololuwar ba'kin ciki ne ya ziyarci zuciyarsa....

Da sauri Junaid ya nufi gurin da Dr. yake ya cakumi gaban rigar sa ya mi'kar dashi yana fad'in
"Dr. Hasheem what did you means about her? meye matsalarka da ita, ko akwai ala'ka ne a tsakanin ku?..."

Dr. ri'ke hannun Junaid yayi ya zamar da hannun daga kwalar daya ri'ke masa
Shima yana fad'in "captain Junaid kenam Kai meye na tada jijiyoyin wuya akan ta bayan ita ba komai bace a gurinka."
Ya karasa maganar yana masa kallon tuhuma....

Murmushin takaici Junaid yayi sannan yace "she's my life"

Junaid bai tsaya jiran abunda Dr. zaice ba ya finciko hannun Ayush wacce tana zaune ta zuba musu eyes ita bata San akan Mae suke wannan sambatun ba,
Sai ji tayi an jawota.
zai fita da ita Doctor Hasheem shima ya ri'ke d'aya hannun Ayush yana cewa "Ina kuma zaka kaita ai bamu sallameta ba"

"This's our hospital bana bukatar sallamar ku..."
Junaid ne yayi maganar yana faman jan Ayush
Shima Doctor ya dage akan baza'a fita da ita ba yana ta janta ciki shima,
Haka suka sakata a tsakiya!
wannan yana jan ta tanan wancan yana janta ta can.

"wayyo Allah zaku cire mun hannu Ku sakeni, taimako jama'a, menayi muku ne haka....."
Kuka ta fara rerawa.

Janaid fa ran maza ya 6aci wani irin wulli yayi da Ayush gefe Wanda shima Dr. bai san lokacin da ta zame masa a hannu ba,

Wani irin sha'ka Junaid yakai wa Dr. ya Kama wuyansa sosai ya d'aga shi sama da hannu d'aya,
Idonsa ne ya koma blue like tiger eyes,
Ransa ba karamin 6aci yayi ba kuma hakan yakan haifo da matsala irin haka...

Dr. ri'ke hannun Junaid yayi yana so ya 'kwaci kansa amma ya kasa,
Numfashin sa ne yake fita sama ²

Ganin haka yasa Ayush ta fice da gudun gaske ko waiwayowa bayan ta batayi, gaba d'aya ta gama tsorita!

Da gudun gaske tazo ta wuce security masu tsaron get d'in asibiti,
Suna tambayanta meya faru amma ko tsaya sauraronsu batayi ba, ita dai ta kanta takeyi, gani take kamar yana biyota a baya, hakan yasa ta 'Kara bawa gudun nata wuta,
Ita kanta bata san Ina ta nufa ba.......

Security ganin Ayush ta fita da gudu yasa suka shiga ciki domin ganin abunda ke faruwa....

(am nace ba na tausaya maka Doctor tinda ka shiga hannun tiger, bayan kasan halin sa mezesa kayi jayayya dashi? wato Kai lovayya ko 🤣🤣 )..

*MASHA* *ALLAH*
🙏🙏🙏

*ASMEETAH* *CE* ✍️✍️✍️

*FREE* *BOOK*

🐅 *MATAR* *DAMUSA* 🐅
(the wife of tiger)

*MALLAKIN*
*ASMEETAH* ✍️✍️

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________

https://www.facebook.com/103637491942644/

💫💫 *{{N W A}}* 💫💫

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم

*BOOK* *ONE*
*PAGE* 45 to 46⬅️

_________ Tsabar karfin da Junaid yake da haka ya ri'ke wuyan Doctor ya d'aga sama sai sawayensa da suke lilo, Dr. ya kasa ceton kansa daga hannun Junaid!
Ga idanuwa sun koma kamar na dodo,
Cikin fushi Junaid ya doka Dr. a tiles d'in d'akin yana gurnani kamar kuntaccen kura,
Gaba d'aya ya fita hayyacinsa,
sai da Dr. ya sume a wajen!
hakan ma bai isheshi ba ya 'kara d'ago da Dr ya sake buga shi da 'kasi, haka ya rin'ka buga shi a 'kasan tiles duk kayinsa ya faffashe sai jinin dake ta tsiyaya ya malale 'kasin tiles gaba d'aya...

haka Junaid yake kukan kura yana bubbuga Doctor,
(wayyo! Allah ya ji'kanka Doctor 🥹)..

Jin kururuwar ihun da Junaid keyi ne ya jawo hankulan mutanen asibiti zuwa d'akin da suke, haka security ma suma d'akin suka nufa da gudu.....

Ganin halin da Junaid ke ciki yasa mutanen da suka zo gurin tsorita,
Juyowa yayi a fusace yana kallon su da wad'annan idanunsa masu ban tsoro,
Nurses kam sun kai biyar wad'anda suka fad'i sumammu ganin eyes d'in Junaid
Sauran kuwa guduwa sukaita yi hatta mazan likitoci suma kowa ta kansa yake
Har marasa lafiyan ganin yanda aketa gudu suma gudun suka fara yi ba tareda sanin maike faruwa ba...

Security ne kawai suka tsaya suna so su kama Junaid
Wani irin kallo yake binsu dashi, wani irin sufaa yayi ya yo Kansu habaaa suma sukace qafa mai naci ban baki ba, da gudun gaske sukabar asibitin suma, sai wani daga cikin security shikam baije ko inaba ya baje a 'kasi shima ya zama sumamme...

Haka yake bin mutane da gudu, duk yanda yaga mutum sai ya yo kansa
Ya hau bakin titi ya na bin mutane da gudu, kowa ya ganshi kuwa zai gudu....

Haka aka turo wasu ma'aikata qarfafa masu aiki a gidan zoom!
Ma'aikata sun kai goma wad'anda suka riqe shi.
Shi kuwa ba abunda yake inba kukan damusa ba,
Idan damusan sa ya motsa masa yana shan wahala sosai, a yanzun ma shi kad'ai yasan irin rad'ad'in da yake ji!
Da 'karfin gaske suka sashi a motor sai babban gidan zoom wanda ake kaiwa namomin daji nan,
Daga nan sun yanke hukuncin gidan zoom na kasar Australia zasu kaishi domin shima dabba ne mai hatsari barinsa anam zai haifar da matsala! A cewar su oganni masu kula da dabbobin namun daji......

Duk halin da ake ciki kuwa Mommy bata sani ba.

Shi kuma Doctor Hasheem emergency room aka shiga dashi akwai kwararrun likitoci a cikin asibitin har da turawa wadanda aka d'auko daga kasar waje...
Oxygen aka sanya masa domin akwai sauran bugun zuciyarsa sai dai numfashin ne ya tsaya cak.
Likitoci sun kai biyar akan Doctor Hasheem, ga yana bu'katar d'inki a kayinsa saboda kayin ya fashe sosai
Inka ganshi kamar wanda trailer tabi ta kanshi ko ina yaji ciwo a jikinsa har da karaya a hannuwansa biyu....

Duk halin da ake ciki ba'a kira Mommy an sanar mata ba.

*****
Junaid kuwa an d'add'aure shi da kaca hannu da 'kafa an jefa shi cikin zoom, kukan damusan da yakeyi ne yasa duk namun dajin dake gurin suma suka fara kuka kowa da kalar kukansa,

Ogan gurin ne yazo da shocking a hannunsa bud'e get d'in da Junaid yake ciki yayi ya jona mishi shocking a jikin sa, daga nan Junaid bai 'kara motsi ba ya kwanta a gurin wajen ko siminti babu sai 'kasa amma haka bawan Allah nan yake kwance jikinsa sai 6ari yake yana kakkarwa da karfin gaske shockin yabi jikinsa, jinin jikinsa ne yaketa hargutsuwa....
Ya salam
(Ayi musu uziri basu san koshi wanene bane shiyasa, amma captain d'in sojoji akayiwa haka 😨😨)....
Chapter 18 · 0% Book details