← Book details Matar Damisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 57

Sashe 17

Matar Damisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

seaching yayi daga computer ya rubuta *DAJIN* *MAQARQASHE* Dajin dayafi ko wanne hatsari a duk fad'in duniya...
yana so ya kutsa cikin dajin ta computer amma abu ya gagara Error ! Error !! Error !!! Kawai yake nunowa, koda naƙura baza'a iya shiga ciki ba...

masu tsaron wannan dajin sune manya-manyan ba'ka'ken aljanu masu hatsarin gaske,
ga namun daji masu hatsari na tsafi an bazasu a cikin dajin nan ta ko ina, kafin ka iso gurin bokan nan tafiya ne mai nisan bala'i har sai anyi sati guda ana cikin wannan dajin ba'a isa gurin sarkin ba,
a gaba akwai wani 'katoton rami na gaske, 'kasin ramin wuta ne yake ci koda yaushe yana kan ruruwa, abu na tsafi sai a hankali!
siririyar gadane aka d'ora akan ramin wanda za'a bi kafin ka tsallake, idan kayi kyakykyawan taku kuwa tsabb zaka fad'a cikin wutan...
bayan wannan ramin sai ka had'u da manya-manyan kadoji na bala'i masu jajayen idanuwa (crocodiles)
suma saika tsallake su, sai kuma a gaba 6angaren macije masu kayuwa biyu-uku har da masu kayuwa biyar biyar masu dafin tsiya kana ganinsu kasan na tsafine,
saika tarar da masifu da bala'i a cikin dajin nan kafin kazo 'kofar get na fada wanda masu gadin kofar wayyo ganinsu ma masifa ne, ba 'kananun masifun aljanu bane, ko tsuntsu basa bari ya shigo cikin wannan fadar wanda baka iya hango tsayin get d'in.......
kafin ka wuce harabar fadar sai kayi tafiya mai nisan bala'i hakan ma kana tafiya kana taka garwashi mai 'kunar gaske sai 'kafarka ya gama toyewa kafin ka iso mashigar cikin fada na biyu shi kuma 'kusosi zakaita takawa har ka isa mashigar kofa ta uku, anan kuma zallar taron aljanune manya da 'kananu masu tsoritarwa kowannensu da madubin haske duk ilahirin jikin mutum
shi wannan madubin tsaraicin mutum yake nunawa saboda kar a shugo musu da abun ya'ki, hakan mah tsaro ne.!
Daga nan sai kofar shiga cikin fadar sarkin matsafa, nan ma kafin ka shiga akwai kofar tantancewa sai da shatin hannun wani ba'kin 'katon aljani mummunan gaske kallonsa abun tsoro, wannan idan bil adama ya kalleshi ba abunda zai hana ya tafi lahira tsabar bashida kyan gani, saida shatin hannunsa kafin wannan kofar ta bud'u sai kayataccen fadar sarki ga kujerarsa na alhurma...
gashinan mutum ne dan adam fari tass dashi kyakykywa suman gashin sa akwance har gadon bayan sa kamar mace,
gashi da 'kirar yahudawa, sai wasu tarukucen sar'ko'ki a wuyansa, kujerarsa mai zanen Damusa ne, ga kuma wani 'katoton Damusa a gefen shi yana zaune, (Damusar Junaid ba)
A gaban sarkin wani kayataccen madubi ne mai she'kin bala'i wanda a cikinsa yake ganin duk abunda yake faruwa a cikin gari,
duk waran da yakeson gani haka madubin zai nuna masa, madubin tsafi kenam....

saman jikin bango kuma an manna kalandar photon Ayush an sanya mata hular sarauta a kanta da rigar sarauta irin wedding gown fari sol, ga gashi yala yala a kanta har gadon baya sai she'ki yake...
(Ku lura itace take fitowa a cikin mafarkin Junaid da wannan shigar sarautar 😃)....

Idan kaga sarkin matsafa kaga Ayush a wanda ya lura kenam...

*****
Shi dai Junaid yanata danne dannan computer sa har dare yayi masa a cikin wannan dakin, amma ya kasa gano komai akan sarkin matsafa....

(Nace ba anya kuwa Junaid zaka iya kamo shi kuwa??...)

Toh abun mamaki anam shine taya mahaifiyar Ayush ta shiga wannan dajin ita da kawarta???...

My fans ku gano mana wannan amsar, domin marubuciyar mahh ta kasa....
😅😅😅😅😅

🙏🙏🙏

*ASMEETAH* *CE* ✍️✍️✍️

*FREE* *BOOK*

🐅 *MATAR* *DAMUSA* 🐅
(the wife of tiger)

*MALLAKIN*
*ASMEETAH* ✍️✍️

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________

https://www.facebook.com/103637491942644/

💫💫 *{{N W A}}* 💫💫

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم

*BOOK* *ONE*
*PAGE* ➡️41 to 42⬅️

karfe 12am na dare Junaid yana zaune he didn't fine anything about sarkin tsafi, bacci ne ya fara d'aukarsa a zaune ga kuma laptop a gabansa, kukan kuliya ne ya katsar dashi dasauri ya bud'e eyes d'in sa cike da mamaki yace "Whatt! what this cat are doing here?"

Shi a sanin sa babu kuliya a gidan nan..
kuliyar nan ba'ka 'kirin ga jajayen idanuwa sai kuka taketa mishi tana fuskantarsa, zuciyar Junaid ne ya fara d'ard'ar shima kansa ya tsorita da ganin kuliyar nan...

abun mamaki mai zai gani?
Sai gani yayi kuliyar tana yun'kurin amai
ta amar da wata farar takarda a cikin leda fara,
tana amarwa kuwa ta 6ace 6att! sai sakon data ajiye masa, daman an turota ne ta kawo masa...

"Innalillahi wa inna ilaihi raju'un" abunda Junaid ya furta kenam ganin 6acewar kuliyar...

tashi yayi a hankali ya nufi gurin da takardar take Ya karanci sunan Allah sannan yakai hannu ya d'auki ledar takardar ya yageta
wani rubutu ne a bayan takardar wanda aka rubuta da yaren fulatanci
ganin bai iya yaren ba yasa bai tsaya 6ata lokaci wajen karantawa ba kawai ya bud'e kai tsaye....

"Hahaha! Hahaha!! Hahahahaha!!! Junaidu! Junaidu!! Junaidu!!! Wato kana wasa da rayuwarka ko, kada kace zaka sha wahala wajen nema na, domin abune mai wahalan gaske,
ka zauna a iya matsayinka idan har kana son rayuwarka,
kasan dalilin dayasa na barka a raye? Hahahah saboda kai abun harin shalelen Damusa nane, kuma kaine jigon Damusa na,
Damusa na yana nishad'artuwa ne daga 6angarenka,
kaine lafiyar Damusa na, idan kaga ciwonka ya warke to Damusa ne ya mutu, zan iya juyar da tunaninka a duk sanda na ga dama, zan iya azabtar da kai a duk lokacin dana so,
kasani cewa 6ingel na itace farin cikina, ka kula mun da ita.........

karshen sa'kon kenam!
'Dagowa Junaid yayi sannan ya yayyaga letter yana fad'in "Nayi alkawari saina gama da rayuwarka, saina kamoka da hannayena...

yana huci ransa a matukar 6ace mutane biyu ya tsana a rayuwarsa,
daga wannan sarkin tsafi sai kuma Bara'atu wacce tayi sanadiyar mutuwar mahaifinsa......

"Toh amma wacece 6ingel kuma? aina take?
Itace farin cikin sa!!"
Haka yaketa wannan tunanin a ransa....

baisan 6ingel itace Ayush ba 🤣🤣🤣

Idonsa ne yayi nauyi ga baccin da yaci idonsa ga takaicin wannan hatsabibin bokan,
da haka yaja 'kafa yabar cikin d'akin nan ya rufe shi kamar yanda yake a rufe sai kofar ta shafe kamar ba d'aki a wajen,
toilet ya shiga ya watsa ruwa a kansa sannan ya d'auro alwala ya fito yayi lafulolinsa tareda addu'o'in neman tsari daga ubangiji,
daga nan yabi gadon kwanciyar sa,
already ya cire jallabiyan da yayi sallah da ita, daga shi sai short wando da singlet a jikinsa,
bacci ne yayi awon gaba da shi.....

Kwata-kwata Junaid ya mance da Ayush a gadon asibiti....

*****

Ta 6angaren Ayush kuwa Dr. Hasheem ne a wurinta har cikin daren nan bai koma gida ba, yana tsaron Ayush
yayi mamakin ganin ba wanda yazo duba Ayush tin tafiyar su Junaid, shi kuma bai nemesu ba,

shi yana kan kujera ya kasa yin bacci gani yake kamar za'a sace Ayush ya kasa motsawa ko ina.....

ita kuma tana kwance tanata sharar baccin ta, duk da kafin tayi baccin tayi tunanin su Junaid zasu dawo amma shuru....

MASHA ALLAH.....

kuyi manage da wannan page babu yawa.....

Sai bayan kwana biyu kuma 🙃🙃

*ASMEETAH* *CE* ✍️✍️✍️

*FREE* *BOOK*

🐅 *MATAR* *DAMUSA* 🐅
(the wife of tiger)

*MALLAKIN*
*ASMEETAH* ✍️✍️

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________

https://www.facebook.com/103637491942644/

💫💫 *{{N W A}}* 💫💫

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم

*BOOK* *ONE*
*PAGE* 43 to 44

_____________meyasa kike son shiga cikin rayuwar mu?
Nace miki ki tafi bama bukatar ki, amma kin 'ki to yau zaki tafi kiyamar da bazaki ta6a dawowa ba...... 'Daga wukar hannunsa ya yi zai caka mata!
Wani irin ihu Ayush ta kurma tana juye-²
Dr. Hasheem ne ya riketa yana fad'in
"Lfy kuwa Ayusha? wani irin mafarki ki kayi haka! Subhanallahi"

Tashi tayi tana huci tana waige ² tare da fad'in "wayyo Allah na zai kasheni, zai kashe ni wallahi..... Gumi duk ya wanke mata ilahirin jikinta duk sanyin A.C dake cikin room d'in...

Addu'a Dr. yake tofa mata tare da sanyaya mata zuciya..
"kinga Ayushat ki kwantar da hankalin ki ba abunda zai sameki kinji ko? kwanta ki cigaba da baccin ki"

"a'a inaso zanyi sallah ne, kafin lokacin sallar asuba ya gabato"
a cewar Ayush.
Allah sarki bawan Allah shi kuwa ko rintsawa baiyi ba duk yana zaman gadin Ayush!

*****
Washe gari da safe around 10:00
Mom ce tazo d'akin Junaid tana ta knocking ganin shuru baizo ya bud'e ba yasa ta tura d'akin ya bud'u tana fad'in "My son baka tashi bane har yanzu "

Shi kuwa yana kwance ya baje sai sharar baccinsa yake hankali kwance tin dawowarsa daga sallar asuba.

"Junaid wakeup mana, na gama had'a breakfast since, nasan kana jin yunwa"

"Please Mom leave me a lone, am really tired".
Junaid ne mai maganar cikin gaga'ar bacci.

"Junaid kaje ka duba jikin yarinyar nan kuwa?"
A cewar Mommy.

"Wata yarinyar?..."
yana magana tare da yatsina fuska!

"ka manta da Ayush kenam? nayi tunanin jiya ka koma gurinta, Junaid marainiya ce fa kuma amana ce a garemu idan kuwa mukaci amana sai Allah ya tambaye mu."

Junaid tashi yayi ya zauna ya ta6e fuska tare da turo karamin lips d'insa wanda suka ci maroon color sosai yana fad'in
"Mom ke fa kika d'orawa kanki wannan amanar fa, ba wai Allah ne ya d'ora miki ba, nine Allah ya baki amanata....…."

"Junaiddd please ka zamo mai taimako mana,
Ba haka mahaifinka yake ba, shi mutum ne mai son taimako.......

Kafin ta 'karisa maganar ya katseta da cewa "I known Mom, hakan yasa ya taimaki wacce tayi sanadiyar barinsa duniya ba, haka kike so nima ya faru da ni KO?..."

Ya juyo yana kallonta da shanyayyun idanuwansa wanda bacci ke shirin ya'kar su, daker yake lumshe idon sa domin jiya bai samu wadataccen bacci ba....

Ran mommy ya sosu da jin kalaman Junaid sai dai ba yanda ta iya dashi
"ka tashi muje muyi breakfast sai kaje ka dubo Ayush, idan kuma baza kaje ba ni zanje ni"
Tana kaiwa haka ta tashi tabar d'akin....
Chapter 17 · 0% Book details