← Book details Matar Damisa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 57

Sashe 42

Matar Damisa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mommy ta sanar musu duk abunda ya faru, da doguwar suman da yayi, tashinsa kuma ya kawo masa waraka gaba ɗaya,."
suka ce "ikon Allah kenam, ku duba kuga baya iya tashi balle tafiya gashi kuwa lokaci guda Allah ya kawo masa waraka, Allah ya ƙara bashi lafiya.." Mommy ta amsa da "Amiin"
tashi tayi tana faɗin "kunsha hanya bari na kawo muku abun taɓawa.."
ta nufi kitchen ta jido kayan abinci ta kawo muku, kowa saida ta zuba masa a plate tuwon shinkafa da miyar Ogusi ta kuma zuba musu ferfesun kifi, ga kayan fruit yanda ta zuba a faranci...

Sai da suka ci sukayi nak sannan suka tashi suna faɗin "masha Allah mu zamu wuce, insha Allah zamu dawo da zaran Junaid ya dawo.."
Da haka suka rabu cikin Aminci,
Mommy wuce wa ɗakinta tayi ta shiga toilet domin yin wanka, shap-shap tayi wanka ta fito ta shirya tab sannan ta ɗauki key ɗin motarta ta fice
kayan abinci ta ɗauka taje tasa a seat back gaba ɗaya, itama ta shige cikin motar takarya kwana a hankali sannan ta miƙi hanyar da zai sadata da gate, kafin ta iso ma maigadi ya buɗe mata gate tayi ficewar ta,

******
Junaid zaune yake akan kujera ya kifar da kansa a bakin gado hannunsa yana riƙe dana Ayush,
Ayush sai da ta shanye ledar jini har uku hakan ma tana neman ƙari ga kuma ledar ruwa biyar,
Bayan Mommy ta shugo asibiti baki ta sake tana kallon ko ina, asibitin yayi wayam babu kowa, waɗanda suka suma kuma da zaran sun farfaɗo hanyar guduwa suke nema, amma duk da hakan ta tarar da wasu a sume a ƙasi, tace "nashiga uku meke faruwa ne a wannan asibitin, daman saida nace wa Junaid karya zo har saina musu bayani tukun gashi yanzu sun tsotstsorita, wayyo Allah.." da sauri ta nufi ɗakin da aka kwantar da Ayush tana buɗewa kuwa ta samu Junaid gashi yana zaune ya kifar da kansa, idonta ta kai kan 2 Doctors da suke kwance a ƙasi, ƙarisa shugowa ciki tayi ta ajiye kayan abincin, ta ɗauki ruwan ƙanƙara ta fara binsu ɗaya bayan ɗaya tana feffesa musu suna tashi kuwa kowa zai nemi hanyar guduwa, duk waɗanda suka suman nan sai da ta farfaɗo dasu,
asibitin sai ya zamo babu ma'aikata ko ɗaya duk sun gudu, sai majinyatan asibitin da bazasu iya tashi ba ko kuma waɗanda ba'a cikin hayyacinsu suke ba..

Mommy koma wa room ɗin da Ayush take tayi, itama kujera ta jawo ta zauna tana faɗin "kaga abunda nake gaya maka ko? gashi duk ka korar mun da ma'aikatan asibiti sun barmun majinyata, saida nace maka kada kazo..." kafin ta ƙarisa maganar Junaid ya daka mata dirarren tsawa tareda faɗin "Mom ni mahaukaci ne? ki gaya mun meye dalilin da yasa ake gudu na, shin akwai wani abun tsoro ne a jikina? ki gaya mun....."
ganin yanda yake mata magana da tsawa yasa Mommy tasa hannu ta zabga masa mari a saman face ɗinsa tana kuka tace "dole kowa ya nemi tsira daga gareka My son, mutuwa fa kayi, kuma kowa yasan ka mutu, ganin haka yasa Ayushert itama tayi ƙoƙarin kashe kanta, gata nan a ƙwance, har anzo za'a maka wanka ka tashi, ya za'ayi kowa bazai yi gudunka ba, shin kasan irin tsananin jinyar da kayi ne? ko motsawa baka iya yi, gashi lokaci guda ka tashi bayan doguwar sumar da kayi, toh yanzu kaji dalilin da yasa mutane suke guduwa maka..."

Hawaye ne yake zuba a ido Junaid yana karkaɗa kai ya maida kallonsa kan Ayush, yakai hannunsa yana shafar fuskarta...

ita kuwa Mommy ƙarewa Junaid kallo take gaba ɗaya ya canza mata, kamannin mahaifinsa sun fito a fuskarsa, har tsayin gashin kafin ya aske, da kuma ƙirar jiki na jaruman sarakuna,
hawaye ne ya fara gangaro wa mommy, tana kallon Junaid da suffar mijinta,

Bata taɓa ganin fuskar mahaifin Ayush bane amma fuskar Junaid yafi kama dana Sarki Raamud,
(kodan saboda tsayin gashin Junaid ne yasa nake ganin haka oho😅)

duk da mahaifin Junaid da kuma mahaifin Ayush twins ne masu kamanni iri ɗaya shiyasa bazaka banbanta kamannin wa yaran suke yowa ba,

inka lura Ayush da Junaid suna ɗibar kama, Mommy ta daɗe da fahimtar haka sai dai bata kawo komai a ranta ba....

*ASMEETAH NOVEL✍️✍️*

typing📲

🐅 *MATAR* *DAMUSAA*🐅
(the wife of a tiger)

*written* *and* *story* *by*
*Asma'u Muhammad Auwal*

( *ASMEETAH NOVEL* ✍️)

*WhatsApp me 09065443871*

*Laifin Daɗi qarewa*

*FREE BOOK ZAI ƘARE NE A ƘARSHEN BOOK ONE*

*BOOK TWO DAZAN SHIGA SOON PAID NE,*
*YANA TAFE DA SABON SALO, DA KUMA CAKWALKWALIN CAKWAKIYA, KADA KU BARI A BAKU LABARI DOMIN GANI DA IDO 👀 YAFI JII👉👂*

*MATAR DAMUSAA BOOK 2 PAY ONLY 150👌👇👇👇*

*ASMA'U MUHAMMAD AUWAL,*
*9065443871, OPAY BANK.*

*OR*

*ASMA'U MUHAMMAD AUWAL,*
*2267236949, ZENITH BANK*

*SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER*
👇👇👇
*09065443871*

https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________

💫💫 *{{N W A}}* 💫💫

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم

*BOOK ONE*
🅿️ ------->87 & 88 <-------

******* Daƙer Mommy ta lallami Junaid yake cin abinci, ita da kanta take feeding ɗinsa ko loma biyar baiyi ba yace "na ƙoshi da tuwon ni milk nake so" Mommy tace "bazaka taɓa ferfesun kifin bane?" kawar da kai gefe yayi sannan yace "idan naci kifi ba halin shan milk, ni kuma idan ban sha milk ba bazan ji daɗin baki na ba.."
Ajiyar zuciya Mom tayi sannan tace "toh ga kayan fruits yanda na haɗo maka"
tasan indai yasha milk bazai buƙaci wani abu ba,
taɓe fuska yayi ya ɗan turo ƙaramin bakinsa yana kallon haɗin fruits, yana yatsine fuska yace "indai ba milk ba bana son komai." Mommy tana jinjinawa wannan miskilanci na Junaid ba yanda ta iya dashi haka ta buɗe murfin flask tana tsiyaya masa milk mai kaurin gaske a glass cup tace "to gashi nidai in har zaka ƙoshi ai ba wani abun tada hankali.."
Hannu ya miƙa ya karɓi cup ɗin milk, idonsa kuwa yana kan Ayush wanda har yanzu bata farfaɗo ba..

Kai ya kifa yana kurɓan madaran, a hankali yake motsa sweet lips ɗinsa, da haka har ya shanye,
bayan wasu mintuna suka ji anata ƙiraye-ƙirayen sallar mangarib, Mommy ta kalli Junaid sannan tace "kaje kayi sallah daga nan kuma saika wuce gida kaima ka kwanta ka huta ko..?"
girgiza kai yayi sannan yace "bazan yi nisa da Yushert ba a halin nan da take ciki, zan zauna tare da ita har Allah yasa ta farfaɗo, kula da ita ya rataya mun a wuya..." ya ƙarisa maganar tareda miƙewa tsaye ya kuma cewa "zanje nayi sallah amma kuma zan dawo.."
Jijjiga masa kai kawai Mommy tayi ta kasa cewa komai,
har saida Junaid ya fice daga room ɗin kafin Mommy ta kawar da kanta daga kallonsa da take, ita har yanzu ta gagara gasgata wa shin Junaid ɗinta ne ko kuma sauya shi akayi aka maido mata da mai siffar mijinta, haka ta wuni tana wannan tunanin, dogon numfashi taja tareda sa hannu tana buga goshin ta alamar ciwo yake mata, daƙer ta iya motsawa ta tashi tana jan ƙafa da haka ta shige toilet ta ɗauro alwala, sannan tasa hannu ta murɗe mariƙar ƙofar toilet ta fito tana jero addu'o'i,
ƙarisa shugo wa cikin ɗakin tayi tana hamma tasa hannu tana kare bakinta ido a lumshe, tsananin bacci ne yake damun ta, ga yunwar da take ji! shimfiɗa sallaya tayi ta zura hijab ɗinta sannan ta tsaida sallah, har tayi nisa cikin sallar ta taga wani irin haske ya bayyano, haske mai kashe ido, tsabar tsananin ƙarfin hasken nan Mommy tana sallah ta ƙanƙame idonta sosai kuma Allah bai nufe ta da katse sallar ba haka ta cigaba da yinsa ido a rufe,
irin hasken da ya taɓa fito wa Ayush lokacin da ta ajiye littafin tarihi a ƙarƙashin gado shine ya ƙara fito wa a yanzu ma,
wani mutum ne ya bayyana a cikin hasken nan, shi ba mutum ba kuma shi ba biri ba, gashi nan tsayayyen mutum ne jikinsa duk gashi, daga kayinsa zuwa fuska har wuya irin na biri ne sak sai tarin gashi sannan yana da jelaa!!!
Wannan shi ake ƙira da *NARASIMHA* mai bada kariya a masarauta, tsohon biri kuma ƙirƙirarren tsafin Sarkin Zaid wato Mahaifinsu Sarki Raamud, baya cutar wa aikinsa shine temako da zaran an nemi temakonsa, har iyau a masarauta yake zaune yana rayuwa ne a cikin madubin tsafi,
NARASIMHA Amanar Sarki Zaid ne, yana kallon duk tsiyar da Sarki Raamud yake aikatawa har Allah ya kawo ƙarshen ta'addanci,
A yanzun ma an turo shi ne don yazo ya temaki Ayush, bazata iya tashi ba har saida temakonsa,

hannu yasa ya yi wa Ayush ɗaukan luɗa sannan ya ɓace da ita, yana tafiya kuwa hasken ya washe daiden lokacin da Mommy ta idaar da sallah da sauri ta miƙe tsaye a ruɗe tana ware manya-manyan eyes ɗinta, ta waiwayo bayanta a tsorace ganin gadon da Ayush take ƙwance wayam babu kowa a kai taja da baya a kiɗimai ta dafa ƙirjinta tana faɗin "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, ina Ayush take, wayyo Allah na.." ta fara kuka tana surutai ta fara dudduba wurare tana ƙiran sunan Ayush amma shuru ta leƙa ƙarƙashin gado bata ga kowa ba ta nufi toilet da gudu tana ƙwalla mata ƙira nan ma babu kowa, ganin bata ganta ba yasa ta saddaƙar tasan wannan hasken data gani ne ya ɗauke ta, zama tayi a bakin gado tana kuka ta kifar da kanta saman pillow..
Chapter 42 · 0% Book details