← Book details Kuyanga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 17

Sashe 7

Kuyanga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau abin haushi sau biyu yanayi

Saida yagama gamsuwa kana yatsallaketa yabarta anan

Sam bayama damuwa yaga shin itan ta gamsun ko tana bukatar taimako

Kai!!! Yarima mamuguncine kai Aradu bakada hali 😡 kubarni dashi fans kada kufuto da jin haushinku ma wani yaji zanyi maganinsa yasin saiya kwashi kashinsa ahannu Alkur.an dan tusa kawai

Yauma haka ta tashi taje tayo wankan janaba kamar yadda MAHBUB ya koyarta dayake shidin me ilimin addinine dan har dan gemu yatsayar wasuma Uztaz suke kiran MAHBUB Yakan koyar da makarantar dare ga yara da manya na BAYIN gida maza ko mata

Saida yajera kwana uku ajere yana zuwar mata tun tana masa shiru tana kyaleshi har wata rana taki bashi hadin kai

Ta matse jikinta tana kuka tana ce masa itakam yakyaleta haka bata so Tagaji kuma yamayarta gida

Haushin kalamanta yaji wato tarainashi kenan tunda akan yana neman abinda yakeso ajikinta amatsayinta na baiwarsa hartanada bakin magana lallai xaiyi maganinta

Daya ga da gaske takeyi saiya zuciya ya wanketa da mari saida ta dafe gurin

Yace "kije kirike kayanki inada wadanda suka fiki komai taimaka miki nakeyi tunda naga ackn kewar masoyinki kike kuma kinkai munzali sannan inban nemekiba wazan nema kokinsan dan hakan nataho dake to walahi bari kiji indai gidane bazan koma yanzuba harsai lokacin danaga dama dan kaina

Yana gama fadin haka yasauka daga gadon bayan yasaka kayansa

Haryaje kofar futa zaifuta kuma saiya dawo da baya yatsaya akanta yanunata

"Kisani bawai Sonki nake yiba balle inga wulakanci indai nine bazaki karajin na kusancekiba zankawo kowace mace gidannan inada iko saidai kisani inhar kika kara karyan doka irin wancan to xaki fuskanci hukunci fin wancen Me zanyi da *KUYANGA* makaskanciya irinki.mmttss yaja tsaki yafuce

Tarushe da kuka tareda dafe kai *"YA ALLAH KAJI ABINDA BAWANKA YAKE FADAMIN ALLAH KA "YAN TAR DANI KASA INADA RABON FARIN CIKI ADUNIYA*!

Aranar wuni tayi tana kuka kanta har ciwo yafara taji inama zataga SAHABI ko zata fada masa kadan daga cikin damuwarta ko taji sanyi ckn ranta ko hakan zaisa ya maidata shi Nigeria

Aiko Dan halak sai gashi Allah yajehoshi gidan kawai domin yaganta don sun bata da yarima tun asilar daya kaita asibiti SAHABIN ne yayi fushi da yariman ganin irin faassarar da yafara masa

Dayaga bata falon saiya saka kansa ckn dakin nata yana rafka sallama jikinsa nabashi ko batada lfy

Yana shiga yahangeta karshen gado dake da kanta tanata kuka

Ai da sauri ya isa gareta yana tambayarta ko lfy

Tadago da sauri ganin shine yasa takara sautin kukan tana fadin "DAN Allah kataimaka ka kaini Gida kamayar dani Nigeria walh nagaji da Abinda yarima yakemin.

SAHABI arude yace mata "me yake miki?Zeenatu wane irin zalinci yake miki?

Bata boye masa ba don kada ta cuci kanta ta zayyane masa komai

Ya dafe kansa yana jin quna ackn ransa

Yakasa magana don takaici

Yace "kinada laifi kinxamo me biyayya wacce batada amfani awannan bangaren yarima bai dace yai mk hakaba tabbas sainayi maganinsa saiyasan cewar ya aikata ba daidai b maza taso hado kayanki daga yau kinbar zaman gidansa har Abada

Jin hakan yasa taji dan sanyi aranta

Da karfin guiwa ta sauko daga gadon

Aranta tanajin inhar zai mayarta gida toko inane ma zata bishi

Da sauri Sauri tahau hada kayanta a dan akwatin daya bata

Duk kayan kananun kayane shedanun kaya ma kuwa irin fitinannun da bazata iya shiga ckn mutane dasuba don rashin mutuncinsu

Doguwar riga dayace ackn kayan sai kayan da tazo dasu riga da zani

Hijab ta zura tunda riga da siket din jikinta sunkamata

Yarike mata akwatin ta mara mas baya har ckn motarsa dake farfajiyar gidan

Akan idon me gadi suka futa don har dagawa juna hannu sukayi

Yasan cewar inhar Yarima yadawo zai fada masa yafuta da ita toshiko bai damuba tunda gyara xanyi

Ackn motar yaita rarrashinta don tadaina kukan fadi yake "saikin fita daga damuwa sannan zanmaidaki gida Nig. Yanzu dai gidana zanfara kaiki kafin innema miki Bisa …………

A,a fa SAHABI muna gudun fadawa gidan jiya munfiso kafidda A'i daga rogo bawai kadora daga inda aka tsaya ba 🙄

To kodayake dai ance …………

Kubiyo Antun Sayyada da Shahida donjin meke gaba
[7/27, 4:35 PM] Ummi Tandama: 📿 *KUYANGA...* 📿

*_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*JINJINA GAREKU KAWAYEN ARZIKI SA'ADATU HUSSAIN AMINCI RADIO TAREDA SHAMSIYYA BAHUR MAMAN SADIQ R/K QUATERS*

*Nabilancy Luv* 💘
(Auntyn S&S)

40-45

Gidan da SAHABI Yake tamfatsetsene Dan yafi na Yarima komai da komai

Sashe biyune agidan kowanne daki kashiga bazakaso kafita ba kayan alatu tamkar kadauki new decoration kagudu dashi abubuwan kawata daki ba magana

Wani daki yakai *KUYANGA* wanda yake dauke da babban gado da kayan kallo acknsa da toilet da kujeru ack girman dakin yakai fili rabin filoti

Yanuna mata kujera yace "Zauna anan ki huta inxakiyi wanka ga toilet nan inkuma xaki kwanta ga gado nan

Kayanki kaf bayardasu xanyi bazaki kara sakasuba domin kwata kwata babu na arxiki ack

Yanzu zanfita zansayo miki Dogayen riguna kala uku natabbatar baxa,a dara kwana uku biza bata samuba sannan zantaho miki da magani sbd ciwon kan naki zantaho miki da abinci ma kada kisawa kanki damuwa baxan cutar kiba ba halin na daya da yarima ba domin ni ina zuwa kasar nan ne don hutawa ba wai don lalata da mata ko yin mummunar dabi,a ba dai kiyi hkr da abinda yayi miki haka kaddarar ki take kijure kixama me tawakkali Zeenatu watarana sai labari zanje baxan dadeba

Tace ahankali "Nagode

Yace "ba damuwa kigodewa Allanki.

Yajuya xaitafi kenan tace masa "Dan Allah kada kanuna masa muna tare ina tsoron abinda xai faru tunda shike da iko da ni da kuma.…

SAHABI yakatseta da Cewa "kwantar da hankalinki nasan kina cikin tsoro kuma kina neman taimako bazan bari yasan kina guna ba zankoma gidan ma yanzun gun me gadi inja masa kunne akan kada yagaya masa

Tayi ajiyar zcy tareda kakaro murmushi tace

"To saika dawo.

Yasa kai yafice

Kai tsaye Gidan Abinci ya wuce yasiyo mata me tsadar gaske

Kana yashiga pharmacy yasiya mata magunguna hardana ciwon jiki dana zazzabi da ciwon kan

Sannan yawuce gidan Yarima yai sa,ar kuwa Baidawoba

Yakebe da Me gadin yabayyana masa komai tareda bashi kudi cinhanci

Me gadin musulmine dan kasar cameroon ne yanajin hausa sosai

Yahau gyada kai yace "bazan fadaba insha Allahu domin natausaya mata yarinyar tanada kirki tun zuwanta nadaina zama da yunwa wannan Yaro bashida kirki sam, baya ganin karama ce Amma dai kaima kayi taimako Allah yabiyaka.

SAHABI yaji dadi yayi murmushi yace "Amin ngd.suka karayin musabiha yatafi

******
Abangare guda da YARIMA ANwar yadawo gidan bai neme inda takeba ko kusa ko alama domin cikin fushi yake da ita

Kwana yayi yana tuna yanda takasance atsakaninsu domin ta bashi haushi sosai wato don yana jin dadi ajikinta shine tasami hanyar rainashi har tana iya musanta masa da sa,insa dashi lallai dolene yayi maganinta domin bazai zauna da *KUYANGAR* Da bata ganin darajar saba zai gyara mata zama

Abu daya yake masa yawo akwanyarsa Baiwarta da YANDA take wajen ni,ima tabbas awannan fage yasan ta ciri tuta ba karya yarinyar tacika mace baitabajin macen daya kusanta yajita zam -zam kamar taba

Aikoda zaiyi fushi da ita na lokaci kalilan ne bazai iya rabuwa da itaba tunda ya dan daneta yaji wani abu aransa akanta yazaune masa kamar super glu aransa

Yakwana yana tuno Dadin dayaji ajikin *KUYANGA*

Da Gari yawaye sai yashirya zaifuta gidan wani abokinsa zasu je wani shoping har ya futa kuma yai tunanin yacancanta yaganota tunda baiji motsin taba ko batada lafiya

Yana kuma son dai yaganta domin shap dinta na burgeshi da cikar kirjinta

Yana shiga abin mamaki baiganta ba baikuma ji motsinta a toilet ba har lekawa yayi

Saiyaja yatsaya a tsakiyar dakin yana tambayar kansa "to shin ina wannan yarinyar taje ne?

Yai sauri yafuta yaleka kicin namma bata nan

Yazaga bayan gidan shine har lambu yagama zagayensa yana neme nemensa amma shiru ba bayaninta balle ma wata alamar ko tana gidan

Nan kuma jikinsa yafara sanyi kada dai guduwa tayi? Yatambayi kansa

Gabansa yafadi alokaci guda

Domin yasan inhar ta gudu ba iya kai kanta gida xatayiba tunda batada kudin jirgi balle wata hanya agarin da xata iya guduwa gida

Yatafi da saurinsa yatambayi me gadi yace masa shin ko yaga fitowar Zeenatun?

Me gadin yahau girgixa kai yana nuna tu,ajjibinsa azahiri yana fadin "bangantaba tun jiya rabona da insata a ido

Yarima yace "azamanka nayau aget kamatsa na awa nawa ko minti nawa?

Me gadi yahau sosa keya yace

"Eh to dayake dai yau natashi da bacewar ciki inata shiga toilet shiyasa bana ce ko sau nawa ma nabar get ba kuma nakan dade kafin nadawo.

Yarima yadafe kai yace "Shikenan ta gudu! Nashiga uku.

Me gadi yazabura yace "ta gudu? Zeenatun innalillahi wa innailaihirrajiun.

To yanzu ina za.aje aganta wata sani a kasar nan?

Yarima yaharareshi yace "koma wata sani ko bata sanin ba ai kana da hannu aciki tunda kana wasa da aikinka baka rufe gidan yadda yakamata.

Yajuya yabar Megadi da atsaye saroro

Aifa aranar yarima yarasa tsugum yanata Faman xaryar gun jami,an tsaron garin yana basu bayanin B'atan *KUYANGA* waiko Allah zaisa aganta ahanya

Kwana biyu sukai suna checking akanta amma shiru dole yahakura yakira gida yana tambayar mahaifiyarsa

Koda UMMAH taji abinda yake faruwa daga bakinsa ta kidime tahau yi masa fada

"Yarima kodai akwai abinda kake matane?ko takura mata kayi da ayyuka da fadanka?

Yarima yace "To UMMAH inma nayi mata fadan saita gudu? Banida ikon dazan matane?kawai dai yawon bude ido nakejin ta tafi tunda idonta yabude dama bakiga yanda take shigar kananan kayaba tana son tafuta gari nahanata ashe dai xata shammaceni tagudu

Jin Hakan yasa UMMAH ta yarda tahau fada tana cewa "to ai da ba guduwa yakamata tayiba saita fada maka maza take bukata saika dawo da ita gida ayi mata Aure yanzu kaga hakan ai sharri zata jawo maka ace kai ka koreta ko cutarta kakeyi yasa ta gudu gani da mahassada ackn gida (kishiyoyi)

Kuma dole kasan TAKAWA zaiyi fada amma kabarni dashi zansan mezan fada masa

Yarima yahau godiya yanajin dadi aransa
Chapter 7 · 0% Book details