← Book details Kuyanga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 17

Sashe 15

Kuyanga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da taji dai shiru ba,a shigo dakinba saita dire junior tafuto tana kiran zulaihat saitaga bakowa atsakar gidan

Ta dau buta tashige bandaki abinta dama fitsari takeji ga cikinta yana murdawa tunsafe dama take Dan shiga toilet din tana ba haya

Acan waje kofar gida Yarimane yazo gunta yanata Neman Wanda zai aika yaji shiru tsit babu gilmin mutane sbd whether ta sanyice da wuri ake shigewa akwanta

Yananan tsaye dai dayaga zai tsayu agun saiyayi kokarin yacusa kansa kawai domin dama sallama yazo yi mata yaga dansa kafin gobe yatafi Turai abinsa

Adaidai sadda yazo saka kai cikin gidan alokacin ne Yaga fitowar mace aguje tayo waje daga ciki afurgije ba gaskiya atare da ita ta bangajeshi tazura da gudu

Baiyi kasa aguiwaba yabi bayanta yazage karfinsa yacimmata acan nesa da gidan yadamqeta

Wa zai gani inba Jakadiya ba

Tana ganinsa tasan yaganta sai jikinta yayi sanyi tunda tasan asirinta yagama tonuwa ayau

Yace mata "jakadiya kece dama?meya kaiki bangaren bayi awannan Daren meyasaki uban gudunnan ?

Take tarasa ta cewa ta diririce tafara kuka tana fadin " karufamin asiri kamar yadda narufa maka

Yanuna kansa "kika rufa min kamar Yaya?

Tace " Eh Ai inada wani sirrinka da bakowa yasaniba sai ni da mutanenka dakasa aikin

Yarima ya mamakantu da maganar jakadiya ya nuna kansa yace "Sirri kuma?ni nasaka aiki ?to akan me nayi aikin dahar kika Sani?

Tayi wata dariya kana tace " kasani cewa akan kunne na naji kabada Umarnin aje akashe Bawa MAHBUN kawai don son rai da kishin da kake dashi nasan komai yarima ayanzuma daka ganni nima akan aiki nake

Yace "wanne aiki kikaje gidansu Zeenatu awannan Daren ?

Jakadiya tace " aikin kisan kai...

Dasauri yawatsa mata Tambaya "wa kika kashe ?kada dai Zeenatun?

Ta girgiza kai babu tsoro atare da ita don tasan me ta taka " Dan Zeenatu nakashe amma mahaifiyar kace tasani hakan

Yadafe kansa "wa,iyaxubillah D'an nawa kika kashe?

Tace " kayi hkr banida laifi

Yaharxuko kanta "Kinfi kowa laifi kuma saina hukuntaki bazan kyale kiba

Tace " idan har katonamin asiri tokamar mahaifiyarka katonawa sannan nima saina tona naka asirin nabaya

Tana gama fadin haka ta tawuce abinta tabarshi da tarin bakin ciki

Kai yadafe yana fidda hawaye

Jakadiya ta cuceshi yana matuqar son Yaron nan SBD shi yazo gidan tabbas mahaifiyarsa ce taja masa komai Ashe dama ba kaunar jininsa takeba

Ihu da hargowa yajiyo ta cikin gidan Su Zeenatu itada Zulaihat ne suke kuka da karfi da neman dauki ganin anzo ankashe yaro hargida

Dayake ta bayan gidan yake tuni yai saurin barin gurin kada wani yaganshi yashiga zargi

******
Kuka sosai sukeyi gidan yacika da mutane anata jajanta mata narasuwar jaririn ta Wanda akashigo hargida aka kasheshi

Kowa mamakin wannan Abu yakeyi anata fadin lallai duk yanda akai makashin yana ckn gidan kafin tashiga bandakin haka bayan makashin yafito zulaihat ta shigo gidan

Da filo akai amfani wajen danne shi harya mutu

Saida safe aka sallaceshi aka kaishi

Da yarima aka kashi aka binne yanaji yana gani dole yai shiru bai iya bayyana wacce takashe yaronsa abin sonsaba

Ranar dama fushi yayi da mahaifiyarsa bayan adaren yaje yai mata bore da kuka akan ta aika ankashe abin sonsa jinin jikin sa

Mai martaba ma yaji mutuwar Yaron dakansa yataka yaje yaiwa *KUYANGA* Ta,aziyya domin yana son Yarinyar aransa domin Nutsuwarta

Kwana tayi tana kuka tana tuno fuskar yaronta

Aranta kuwa tanajin bazata taba yafewa Wanda yai mata wannan abuba don ancuceta saida akaga tafara kaunar yaron aka rabata dashi

UMMAH kuwa ranta fes ta cikawa jakadiya alkawarinta na abubuwan datace zata bata

Ammafa agun yarima bata jin ta dadi shiga daya shiga biyu saiya gaya mata magana tamkar ba mahaifiyarsa ba

"Kinji dadi kinraba Dan tahaliki da duniya kunji Dadin hakan Kuda Allah kuncuceni kunrabani da farincikina.

😏kunjishifa kaika manta daka sa aka raba bawan Allah da duniya Ashe abun ba dadi

Kwana uku da faruwar hakan LAMIDO yazo yi mata gaisuwa

Tafito cikin hijab har kasa

Yakura mata ido harta iso gareshi tagaidashi ckn ladabi

Ya amsa yana kallon Dan karamin bakinta mekamada alawar lollipop

Yace " ZEENATU ya hakuri kuma?

Ckn sanyin muryarta tace "Da Godiya

Yace " Allah yajikansa yabaki hakurin rashinsa

Ahankali tace "Amin nagode"

Yaso yafurta mata wata kalma saikuma yafasa

Yaimata sallama yatafi

Yauma binshi tayi da kallo

Yanda yake takunsa na kasaita da iya tafiya ta sarakai abin birgewane kokusa Yarima baikamoshi akomai ba Tabbas LAMIDO na daban ne

Ayau tayiwa Allah godiya dayasa zata zamo mallakinsa donta farajin wani Abu akansa

Abin mamaki ma da dare kasa bacci tayi tayita juyi akatifa tana tuno irin yanda yake maganarsa da tsari da tausasawa ga iya kallo kodon idanunsa Sexy eyes ne gashi da kyau da tausayi

Tabbas Samun Namiji irin LAMIDO sai antona

Tooo🙄😳fans *KUYANGA* me kuka fuskanta ne a Heart din KUYANGA

To kodai ta kamu ne ???

Muje zuwa
[8/8, 8:11 PM] Ummi Tandama: 📿 *KUYANGA...* 📿

*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏻 ASSOCIATION_*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*Nabilancy Luv* 💘
(Auntyn S&S)

90-95

FAATU ce A zaune aturakar mai martaba bayan yagama cin abinci yadubeta yace "Kince kinada magana inajinki meke tafe dake akwai damuwane?

Ta gyara zama tace "Dama maganar LAMIDO ne Naga tunda har anyi sadakar arbain din jaririn Zeenatu nace to me zai hana atsaida ranar Auransu da LAMIDON ba tunda har ya amince kuma naga kamar yafara sonta

Murmushi Sarki yayi yace "To babu komai sai a tsaida Wata daya mai zuwa sai adaura Auran nasu bamusan me Allah ya ajiyeba kuma Inaso aranar da za,a daura Auran ayi bikin dorashi Kan karagar mulki natsufa yakamata nayi murabus nadorashi akai duk abinda nakeyi wanda yakamata yake kaina zai iya sannan ya cancanta don haka zansa ayi shela agari kowa yasanda wannan rana

FAATU tace "To amma Takawa kana ganin wannan abun dakayi bazai kawo rabuwar kai atsakaninsa da Dan,uwansa yarima ba mahaifiyar safa ta kudurci dantane zai zama sarki natabbata zataji ba dadi koma tayi bore

Sarki yace "Nike da iko da komai daga kan mutan gari da bayi da ku kanku iyalaina da dukuma Sarautar kanta Dan haka babu me canzamin zabin da nayiwa Garina

Ckn biyayya FAATU tace " angama ranka ya Dade Allah yaja kwana yakara lfy

Yace "Amin Fatima. Inkin futa kituromin LAMIDO

tace "To.

Bayan futarta tazarce Dakin MAMAH domin takai mata wannan batu sbd duk abinda take ciki saita sanarta kuma bata zartar da komai saida izininta

Jakadiya na zaune kusa da MAMAH tana mata hira

Shigowar FAATU yasa ta tsahirta tareda gaisata

FAATU ta amsa tareda zama kusada MAMAH

Ta zayyanewa MAMAH komai na abinda Mai martaba yatsara na bikin LAMIDO da *KUYANGA* Da kuma bikin nada LAMIDO Sarki da za,ayi

Jakadiya na qunsa tafuce da rawar jiki ta nufi dakin UMMAH Donkai mata Rahoto

UMMAH taga shigowar Jakadiya hankali atashe

Ranta yai matuqar baci dajin wannan kalami daga bakin Jakadiya kamar ta Dora hannu aka tayi kuka taji

Inama tana da damar da zata hana wannan Nadi

Jakadiya tace "Kibar komai ahannuna domin nima bazanso adora Lamido INA gani ba zanso ace Yarima ne zaizama sarkinmu

UMMAH ta gyada kanta tana fadin "Nagode jakadiya nasan ke me qaunata CE

Jakadiya taxo futa adakin kenan sukai kicibus da Yarima shima yashigo dakin UMMAH

Kallon kallo sukaiwa juna ko gaidashi Jakadiya ba tayiba kowa aransa akwai abinda yake ayyanawa akansu

Yaxauna akan kushin yana fadin "UMMAH naxo gaya mikine zantafi turai nan da kwana biyu nagaji da zama agarinnan babu masu sona

Tace "Kamar yaya babu masu sonka baya gamu nida mahaifinka

Yace "Hhhmmm adane kike sona amma ayanzu kam dagake har TAKAWA babu me kaunata kinrabani da gudan jinina kinkuma ki sanyawa Takawa ya yafemin yafaina fushi dani

Tace "YARIMA kai kake janyo komai gashi yanzuma zaka tafi kuma kasan bason tafiyarka yakeyiba Danhaka tafiyarka daidai take da karin wani laifin kanka sannan kuma abinda nayi daidaine agunmu nidakai domin inhar Yaron ya girma xai iya tasowa ackn wani yanaya na mugayen halayya ko kuma muzama abin kwatance

Inaso kacireshi aranka kafuskanci abinda ke shirin Kasantomu na Nadin Sarauta da mai martaba zaiyi akan kaninka LAMIDO

Yarima ya gyara zama da firgici akan fuskarsa yace "Da gaske UMMAH yanzu haka Takawa zaimini SBD yabakanta min rai. Tabbas saina dauki mataki sosai akai

Waye ya kawo miki wannan labarin?

Tace "JAKADIYA CE

yace "shikenan.

Yafuta yanufi Dakinsa yadebo kudi masu yawa aljihunsa yafito yanufi sashin da Jakadiya take

Cikin ikon Allah Yatararta Ita kadai kuwa

Tanaganinsa gabanta yafadi ganin irin kallon da yayi mata dazu tana ganin ko akwai manufarsa ta hakan

Yakalleta ba fara,a afuskarsa ya mika mata kudi ahannunsa yace "Karbi wannan !
Jiki na tsuma ta karba

Tace "na menene wannan?

Yace "Nakine aiki zansaki

Tace '"aikin meye hakan? Wannan uban kudi yafi karfina

Yace "Yanda kika zama makisiya shine nakeso ki kashemin wani nima

Ta zabura "Baxan iya ba walh

Yadaka mata tsawa "zaki iya !! Waishinma kinji kowaye?

Tace "waxan kashe?

Kaitsaye yace mata "LAMIDO!!

taji dirar Kalmar akunnenta tadira gefe tana miko masa kudin "karbi kudinka bazan iya kashe LAMIDO ba ka kaiwa wadanda sukai maka aiki akan MAHBUB suyi walh bazan iyaba

Yadaka mata harara yace "babu Wanda zansa yayi saike don haka kisani k'in yinki yana daidai da tonuwar asirinki

Yana gama fadin haka yajuya yabar ta tsaye atsorace take da wannan lamari ina ita ina iya kashe LAMIDO to yanzu yazatayi gashi tana bukatar kudin sbd yawansu yakai ace tagina kanta da rayuwarta na wasu shekaru toshin yanzu Yaya zatayi ? Rana zafi inuwa Quna!!

Mafita ce tazo mata arai gara taraba kudin biyu taje tasami Fadawan da taga yasa su kashe MAHBUB tabasu sutayata aikin

******

Abin Duniya yadami Yarima gashi da gasken Gaske Mai martaba yajuya masa baya ko gaisuwarsa baya amsa masa don hakan ma ya qudiri niyyar kawar da LAMIDO domin yazamo dolen sarki yanad'ashi agaba yakuma Auri *KUYANGA*

Shawara ya yanke natafiya Turai tun agobe domin in aka kashe LAMIDO kada adora zargi akansa gara ayi bayanan

Da safiyar Lahadi ya daga ko sallama da Mahaifinsa baije yayiba yabarwa UMMAH sallahun tagaya masa

Itako dama ranta baiso ba
Chapter 15 · 0% Book details