← Book details Kuyanga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 17

Sashe 3

Kuyanga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yakalleta yadauke kai yana so yai mata magana amma yarasa me zaice mata don baya son tana jin kunyar nan tasa shikam tana burgeshi amma baya son kunya shi faranse ne wayyayye

Gani yake duk kauyancin nan da zatayi masa bazasu shiryaba domin saiya wayarta kada tabashi kunya irin nayau

Da aka kawo musu abinsha kin dauka tayi saida yadaka mata tsawa

"Ke Dauki mana meye na kunyar!

Tasa hannu ahankali tadauki lemon taja ta rike takasa budewa

Yana kallonta tagefe taki budewa kanta akas!

Saida yashanye kana yakalleta yace "kawo inbude miki.

Ta mika masa ahankali

Yabude mata na gongwanine me gas

Taringasha ahankali kusan awa guda kafin tagama

Anyi rabin tafiya Tafara bacci takwanto da kanta kan hannun kujera yatsura mata idanu yana kallon kyakykyawar fuskarta da dan bakinta yaji kamar yakai hannunsa yashafata saidai yana gudun kada tafarka

Can bacci yai mata dadi saiga kanta ajikinsa

Yarasa yazaiyi da ita saboda mutane nakusa dasu suna kallonsu

Haka yabasar bai motsaba gudun kada ta farka takasa komawa

*******

Koda suka Sauka a England Kaitsaye suka hau mota ta haya har gidansa

Tamfatsetsen gidane da maimartaba yasiya don kawai insunzo karatu suzo suzauna ackn sa

Daki guda mekyau da tsari yakaita yace mata nanne inda zata ringa kwana

Dayake kayan jikinta riga da zanine tasanya hijabinta hannunta rike da carbi

Tazauna zagwade abakin gado tana so tayi sallah gashi bata san yazatayiba nafarko bata san inane gabas ba gashi Bandakin yawuce tunaninta batasan yanda zata sarrafa ruwa yazubo ba gashi ba agogo adakin

Data gaji da zama saita futo falon domin tambayarsa

Ta dade afalon azaune bayanan yana ciki tajiyoshi yafito daga wanka

Tananan zaune harya kintsa yafito

Yakalleta yace "Ya kika baro dakin kika dawo nananan Qalau ko?

Tace "Dama, Alwala zanyi inyi Sallah to bansan yazanyi ruwa yaxubo ba kuma bansan ina zan kalla ba gashi lokaci nakeson gani

Ya koma ciki yadauko mata agogon bango yadawo yace mata "Taho muje.

Ta biyoshi abaya har dakin da yace natane

Suna shiga ya ajiye mata agogon Akan mirro me lado ladone xata gane shi

Yashige bandakin yana kiranta

Tabi bayansa yaringa nuna mata yanda zata kunna komai takashe ckn Sauki

Da yanda zatayi wanka da shaya dakuma yanda intayi kashi zatayi fuloshin da duk abinda yasan dai zai gagareta

Saida ya tabbatar tagane komai kana suka dawo dakin yanuna mata Gabas sannan yace mata inta idar ta jirashi xaije yasiyo musu abinci yadawo

Kafin yadawo kuwa tagama komai don har wanka itama ta sallo ta maida kayan jikinta taxauna ta takure agado tana jiransa don yunwa takeji

Daya dawo yashigo yakawo mata abincin na take away sannan yabata wata ledar kaya yace "Ga kayan sawa nan kala biyar na Siyo miki kafin nakaro miki wasu gaba

Takarba da biyayya tana godiya

Daya fita yabarta tacinye abincin tas tana santi kunnanta kamar yacire

Tayi mamakin ma data iya cin wannan kalar abinci domin a ido dai yaburgeta dama gashi abaka ma gwanin dadi bata taba ganin irinsa ko a hoto ba

Ta wanko hannun tasha ruwa sannan tazo ga Ledar ta zaxxage kayan tana daddagasu daya bayan daya tana mamaki da yatsina fuska domin kayan basuyi mataba

Asalima tayi tsammanin ko canzan leda sukayi da wani domin kayan bana sawar "yar musulmi bane

Itakam ko da kudi bazata taba sasu ba rigunan "yan bigil suke kanana wanda in an saka zasu damewa mutum jiki

Ga Wanduna pensil ga "yan gajerun wanduna sai siket masu roba iya cinya da riguna marasa hannun harda bes tashan iska kayan sunyi kyau

Ga masu sawa Amma😉😊

Ta maidasu cikin ledarsu tana mamakin wannan kaya ai baxata taba iya sasuba haba aiko batada kunya wannan kayan sai a gidan mijinta yaushe

Sai bayan wasu awanni yashigo mata don ganin ko qalau take

Yana zuwa yaga kayan akusa da ita yahau tambayarta

"Baki bude kayan bane?nakine fa nasiyo mk yakamata kigwada ma ingani don inga wanda sukafi miki daidai sbd xankoma siya miki irinsu nan gaba.

Tace aranta "Aiki game k'areka.

Afili tace "kayi hkr nagansu baxan iya Sawa bane sunyi kanana dayawa.

Yahade rai baya son kauyanci da Raini fa

Yace "akan wane dalili tokisani nanba gida bane baxakiyi kauyan cinnan nakiba dolene kisaka su don awannan garin baruwan wani da wata dankin saka bame kallonki balle yaga laifinki kuma bazaki taba samini wadannan riga da zanin naku nagargajiya ba dan haka maza kisaka su ingani nabaki minti biyar ina jiranki afalo

Yana gama fadin hakan yajuya yafuce

Wani qululun bakin cikine yatsaye axcyr *KUYANGA* TABBAS tun daga yau tafara nadamar xuwa Turai lallai inko haka zata ringa shigar kayan arna gara bataxoba Gara kuma taita zama dana jikinta

Tasaka kayan agaba tana kallonsu data kalli agogo taga saura minti biyu lokacin daya bata yacika saitayi saurin tashi ta janyo ledar taciro wata riga me karamin hannu tacire ta jikinta tasaka dakyar

Sannan ta sille zanin tasaka wani dogon wando

Bata iya cire dankwalin kayan ba tabarshi akan nata don kada yaga gashinta

Takalli kanta a madubi

Ai dasauri ta rintse idonta tana fadin "innalillahi wa inna ilaihir rajiun.

Yanzu haka xanje gaban namiji?yanzu haka zanje gareshi yagannin nashig uku yau naga takaina 🙆🏼 meye mafita ………………?

*Fans kugaya mata mafita* 😂

*Auntyn Sayyada da Shahida ce* 👌🏼
[7/23, 10:28 AM] Ummi Tandama: 📿 *KUYANGA...* 📿

*_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*Dis Page i dedicated to my lovely Sister *NABILA RABI'U LADY* a writer of *BANI BANE* Always i solute you my Namesake. oh my Lord! bless her and help her everythings

*Nabilancy Luv* 💘
(Auntyn S&S)

15-20

*KUYANGA* Tak'ara kallon kanta a madubi taga agaskiya bazata iya futa gaban Yarima ahakaba ai taxama mara kunya kenan inhar yaganta ahakan..."bashi yabaki umarni daki sakaba " bashi yakawo miki don ki sakaba? Wata zuciyarta tace mata

Azancen gaskiya kayan sun mata kyau domin wandon yamatseta tsam !dam! Yafito mata da shap sosai abin gwanin burgewa dai

Ga rigar ta kamata tamkar ajikinta aka kirkireta dama ita ba ma,abociyar saka bra ba saiga nonuwa tsaye tsar ! Me sifar kan tasa ga nipple nan tsir ya nuna kansa

Ita kanta abin bai mata tsari ba balle kyangani domin sifarta tafito tamkar komai awaje yake

To yata iya inhar taki futa taje gun nasa zaizamo hakan tamkar ta bujirewa maganar sane sannan umarni yabata ba zab'i ba

Kuma ita din akan bin umarninsa take zaune sannan babu musu ko k'iwa atsakaninsu akullum ita din baiwa ce makaskanciya agunsa *KUYANGA* me hidimta masa

Ta tuno kalaman mahaifiyarsa da take ce mata "DUK ABINDA YA UMARCEKI DAKIYI KIYI MASA DONKI FARANTA MASA KECE MEYI MASA KOMAI ME KULA DA KOMAI NASA

Saikuma ta tuno da kalaman masoyinta MAHBUB da yake ce mata "KADA KIBARI AZALINCEKI KADA KIBARI ACUCEKI SBD KINA AMATSAYIN BAIWA KADA KIYI ABINDA BAI DACEBA ACKN BIYAYYA.

ta rintse idanu tana kwalla tana fadin "MAHBUB kayi hkr gashi anfara, zankuma karya maka doka Zanyi biyayya ga abinda bai daceba zanbi umarnin uban dakina.

Tana gama fadin hakan tafuce gurinsa

Yana zaune afalon yadora kafa daya kan daya yana latsa waya

Tun daga nesa yakura mata idanu itako kanta na kasa

Saida ta isa dab dashi tadago kanta taga ashe shid'in ita yake kallo saiTaji wata kunya ta mamayeta

Yai saurin kawar da ganinsa daga kanta yace "Very nice sunyi mk kayan daga yau sune Kayan sawarki kada nakara ganinki da zani domin nanba kauye bane ina mu,amula da wayayyu bazanso suga dawa nake tareba inhar ba kin kile ba tunda duk bakon danayi saikinzo kinyi masa hidima

Ta gyada kai kawai

Yace "oya muje kicin na nunnuna miki kayan amfanin da zaki ringayi akullum.

Ya wuce gaba tabi bayansa ad'arare

Yaringa nuna mata abubuwa komai har gas yanuna mata yanda zatayi amfani dashi domin acan gidan sarauta Manyan bayi ke girki ba yaransuba

Balle su iya komai su k'ananan Bayi saisun kai munzalin Aure ake fara Trenasu

Saida yaga ta kwashe akwanyarta na wasu abubuwan kana yace suje su zaga gidan domin can ma akwai abinda zai nunnuna matan

Tana gaba yana bayanta yana karewa mazaunanta kallo

Yawu yake had'iya kawai domin yasha Mamaki aransa yarinyar ta da ita amma komai yaji 😋🥴

Yakaita gurin shukoki don yace ita yakeso taringa basu ruwa kana yakaita gaiding nanma yace hurumin tane

Cai !! 🙆🏼 ashe zaki wahala *KUYANGA*

Yakaita yanunata ga mai gadinsa domin su san juna sosai tunda ita zata dawo girkin gidan zata ringa bashi shima

Au ainaxaci gadinma ita zatayi 😉🙄

Kwanan *KUYANGA* Biyar agidan takwashe komai akwakwalwarta ta iya kunna gas tayi masa sassaukan girki takan mikawa me gadi intayi

Girkinsa bai wuce indomie Cuscus da suyar dankali da doya da kwai sai sauran abubuwan da basuda nauyi masu Saukin yi

D'an wahala shiyasa bakada k'iba 😏

iyakarta dakinta in yana falo bata yarda tafito inba abinci zata kai masaba shima a kunyace take zuwa sbd kare mata kallo yakeyi duk kayan kuma data sanya saiya furta cewar sun mata kyau

Magana me tsayi bata hada su to me zatace masa ? Bayaga ina kwana ina wuni sai tambayar wani abun kuma

*******
Cikin Sati biyu yazamto tafara sabo da komai hatta kayan datake sawa matsatstsu yazame mata jiki tasaba dasu tunda yakaro mata wasu yakawo mata dayawa

Tun tana kunya inta sakasu harta daina
Yakawo mata manshawa masu kyau da man wanke kai da sabulai nagyaran fata dai

Tana tsafta sosai tana gyara kanta dayake tanada tsahon gashi da cika saidai kullum yasha gyara ko tayi masa manyan kalba ta bazo jelar kalbar baya aiko takanyi balain kyau dama ga fuska kamar ba india sosai kyanta yanata bayyana don hutu yanata shigarta ba koina take zuwa ba kullum bacci daga dakinta sai kicin sai falo

Sai intafuta kaiwa me gadi abinci ko aikin farfajiya

Zaman gidan yafara damunta to amma bayanda zatayi tunda baice tazo tafuta wajenba aibaxata iya futa batare da izinin saba

Yakan futa tun dare sai tsakar dare yadawo tarasa wane aikine haka kamar na barayi

Hhhh bakisan club yake zuwa ba kenan to zauna wataran zaki sani😅
Chapter 3 · 0% Book details