← Book details Kuluwa Yar Balai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 8 OF 9

Chapter 9️⃣

Kuluwa Yar Balai Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Kuluwa ta juyo suka haɗa ido da mallama Ikilima ta ce.
"Gidan uban wa za kije, ko baki gansu bane a can." Kuluwa ta kalli gurin sannan ta kama hannun Ummi suka nufi gurin.

Ta nemi gurin zama ƴan group, suka kewayeta suna bata labarin abinda ya faru tayi murmushi ta miƙawa Ummi doyan ta ce.
"Ki yi maza ki ci kafin mallaman su zo."

Ummi ta amsa tayi musu bismillah suka ɗau guda ɗai ɗai, wasu kuma suka ce alhamdulillahi,  Ummi ta kalli Kuluwa ta ce.
"Ba zaki ci ba.?"

"Idan zan ci ai ba zan baki ba, dallah mallama ki yi sauri." Kuluwa ta faɗa tana hararan ta.

Ummi ta cinye doyar tasha ruwa, Kuluwa ta kallesu gaba ɗaya sannan ta ce.
"Na san maganar Nazifi ne, wanda muka yiwa jifan shaiɗan."

Suka amsa gaba ɗaya.
"Ni dai yau bana ƙaunar hayaniyya dan haka, ku nemowa kan ku mafita." Kuluwa ta faɗa tana miƙewa.

Gaba ɗaya suka bita a baya ɗaya bayan ɗaya, kuma babu mallamin da ya gansu har suka fice.

Sun yi tafiya mai tsawo kafin su tsaya a bakin lambu, Kuluwa ta leƙa ciki sannan ta shiga bishiya ta haye kamar ƙadangare ta fara jefo mangwaro inibi da sauran kayan marmari, komai akwai na kayan marmari Kuluwa har tsalle takeyi zuwa bishiyar kusa da ita.

Tana shirin saukowa ta hango mai lambu yana tawowa.
"Kowa tashi ta fishe shi." Kuluwa ta faɗa tana dira daga bishiyar, ai tana rufe baki suka watse Kuluwa ta ɗaga murya tana cewa.
"Wallahi idan kuka bari ya kama ku to kamar damisa ne ya samu nama." Suka ƙara gudu mai lambu yana biye dasu, shi da wasu mutane guda uku kamar samudawa.

Ganin an kusa cin musu Kuluwa ta ce.
"Bibbiyu ta cikin window."

Suka rabe kowa bibbiyu Ummi da Kuluwa suna tare, kayan yana hannunta.

Sai da suka tsere musu sannan Kuluwa ta ciro riga ɗaya daga cikin rigar jikinta, ta zuba kayan marmarin ta haƙa rami ta ɓoye daga nan suka nufi makaranta.

Sai da suka leƙa ta window suka tabbatar babu mallami sannan suka haura, a hankali sauran suka ringa shigowa ta window su goma.

Mallam Usman ya shigo cike da mamaki yake kallan tawagar Kuluwa, domin ɗazun an yi ta cigiyarsu amman ba a gansu ba.

Ya umarci Kuluwa ta fito ta tsaya gaban allo, ta tsaya ta ɗaure fuska suka haɗa ido da Nazifi tayi murmushi ta kau da kai.

"Daga ina kuke.?" Mallam Usman ya faɗa yana rubutu a saman allo.

"Babu inda muka je." Kuluwa ta faɗa tana hararan ƴan ajin, ganin sun zuba mata ido.


"Kun gansu a cikin ajin nan tun ɗazun.?" Ya tambayi ƴan ajin, suka amsa da eh.

Mallam Usman ya dakata da rubutu yana ƙare musu kallo, yana mamakin yanda suke jin tsoran ƙaramar yarinya, amman yau duk sai ya yi maganinsu.

"Kowa ya miƙe tsaye ya ɗaga hannu sama." Mallam Usman ya faɗa yana zama a kujeran zaman mallamai.

Kowa ya miƙe ya ɗaga hannu mallamin ya ce.
"Kowa ya rufe ido." Ya faɗa ba tare da ya kallesu ba.

"Wannan ai iskanci ne." Kuluwa ta faɗa ƙasa ƙasa, amman sai da yaji abinda ta faɗa.

Ta shige tsakiyar ɗalibai ta zauna ganin haka ya yi saurin cewa.
"Maza dawo ki zauna a farko." Kuluwa ta fito tana hararan shi.

Sai da suka yi tsayuwar awa ɗaya sannan ya ce zu zauna.

Mallaman makarantar suka shigo gaba ɗaya harda shugaban makaranta.

Suka umarci Nazifi ya fito ya tsaya gaban allo, ya fito hannu maƙale da igiyi an naɗe ta wuya.

Shugaban makaranta ya ce.
"Duk wanda ya san yana ɗaya daga cikin masu jifan Nazifi ya fito gaban allo."

Kowa ya yi shiru babu wanda ya fito juyin duniya sunƙi fitowa kuma ya tambayi ƴan ajin sun yi shiru.

Nazifi ya ce.
"Ranka ya daɗe na yafe musu."

"Ko ka yafe musu dole ne makaranta ta hukunta su." Mallam Usman ya faɗa.

Sallama suka ji a bakin aji, mai lambu ya shigo suka gaisa sanna ya ce.
"A cikin ɗaliban wannan makarantar an samu wa inda suka yi mun ɓarna, bayan kun yi mun alƙawarin babu wanda zai ƙara shiga mun lambu."
Shugaban makaranta ya dafe kai ya kalli Mallaman gaba ɗaya ya ce.
"Ku sameni a officer." Ya fita mallaman suka bishi a baya.


Mallama Ikilima ta cewa Mallam Usman.
"Da alama yau madam bata so fitowar ka ba."

"Banganeba.?" Mallam Usman ya faɗa cike da mamaki.


Mallama Ikilima tayi shiru suka ƙarasa officer ɗin shugaban makaranta.

Ɗaya daga cikin Mallaman makarantar ya janyo Mallam Usman gefe ya ce.
"Ka duba ƙasan riganka."

Cike da kunya da mamaki yake kallan ƙasan rigar, wato wannan dalilin ne yasa Mallama Ikilima tayi mishi magana ɗazun, kuma ya san wannan aikin Kuluwa ne lallai ta ɗibo ruwan dafa kanta, wallahi yau sai ya sauke mata abin da yake kanta.


Ya kama ƙasan rigar ya riƙe suka zauna aka tattauna akan yanda za a ɓullowa lamarin, bayan sun samu mafita suka kira mai lambu suka bashi haƙuri, kuma sun tabbatar mishi wannan shi ne na ƙarshe.

Bayan fitan mallamai ƴan group suka haɗe kai Kuluwa ta ce.
"Wallahi yau makarantar nan akwai ƙura, dan haka kuzo kuji mafita."

Suka haɗe kai baka jin abin da suke cewa, sai da suka gama tattaunawa sannan Kuluwa ta miƙe ta kalli ƴan ajin gaba ɗaya ta ce.
"Kowa ya san yau babu mai ƙwatar mu a cikin makarantar nan, dan haka ina da shawara." Kuluwa ta cigaba da magana.
"Duk wanda yake tare dani yazo kusa dani, kamar wasa gaba ɗaya ajin suka miƙe duk yawan su.

Mazan suna zaune suna jin daɗin yau za a yi musu maganin Kuluwa.

Kuluwa ta fita waje suka bita, sun jima kafin su shigo suna dariya kowa ta nemi gurin zama.


Mallaman makarantar gaba ɗaya suka dawo cikin ajin, Kuluwa tana hangosu ta ce.
"Kowa ya shirya."


Mallaman na shigowa cikin ajin.


Ta Batulu ce.........✍️*KULUWA*
*(Ƴar bala'i)*


Group 👇

https://chat.whatsapp.com/EEiLcD9ZnpbFRLSjSOZozT


Channel 👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaBJBOr8vd1H4qb9rd1a


*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*


Written by ✍️
Sa'adatu Ta Batulu
Chapter 8 · 0% Book details