← Book details Kuluwa Yar Balai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 5 OF 9

Chapter 5️⃣

Kuluwa Yar Balai Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Suka samu guri suka zauna amarya ta fito suka gaisa, Kuluwa ta ce.
"Da kawu Nuhu da mahaifiyata uwarsu ɗaya ubansu." Daman kafin su ƙarasa gidan sai da suka tambayi sunan angon.

Amarya tayi musu fara'a sosai ta zuba musu abinci da lemu suka zauna, bayan sun gama da za su tafi ta ɗauko leda babba da ƙarami ta zuba musu cin cin dublan, babbar leda su kaiwa mahaifiyarsu ƙaramin nasu.

Suka amsa suna washe baki da za su tafi ta basu ɗari biyar su hau mashin.

Suna fita suka sai babbar leda suka zuba kayan aciki, suka tsaya suka sai farar powder suka shafa gaba ɗaya fuska, duk wanda ya gansu sai ya furgita idan kuma yara ne sai su hau gudu.

Wani yaro yana haɗa ido dasu ya fashe da kuka yana gudu yana faɗin aljannu, kamar da wasa mutane suka fara gudu Kuluwa Ummi suma gudu suke yi suna faɗin.
"Maraba daku bil'adama."

Abu kamar wasa matasa yara tsofaffi gudu suke gashi babu huta nepa, kuma gari ya yi duhu farar powder kawai kake hangowa da idanu.

Duk wannan gudun Kuluwa na riƙe da leda akai, ta bayan gari suka yi yanke ƴan mata da samari ana ta zance, sun biyo ta bayan gidan mai gari suka ga Sa'ida yarinyar mai gari tana rungume da wani namiji, Kuluwa tayi baya gonakin da suka baro suka koma.

Kara ta ɗibo masu yawa ta dawo har yanzu suna rungume da juna ta ƙara shafa farar powder.

Ta miƙawa Ummi kayan hannunta Ummi ta amsa ta ɓuya a bayan gurin ta yanda babu wanda zai ganta.


Sa'ida da saurayinta Ahmad sun jima suna aikata kuskure, babu wanda ya sani har ciki sun taɓa zubarwa sau ɗaya.

Sa'ida tana ƙaunarshi da gaskiya wannan dalilin yasa, daya nemi ta bashi kanta babu wani tunani ta amince, shi kuma ba ƙaunarta yake yi ba sha'awarta yake yi.

(Kuskuren da ƴan mata ke aikatawa kenan a wannan zamanin, kuma wallahi duk namjin kirki wanda yake ƙaunarki da gaskiya, ba zai nemi taɓa jikinki ba ballantana har ya nemi yin lalata dake Allah ka tsarkake mana zuciya)


Kawai suka ji an daka musu tsawa, zasu gudu Kuluwa ta maƙe murya ta ce.
"Duk wanda ya ƙara taku ɗaya sai na shanye ruwan ƙoƙwan kansa."

Saurayin harda fitsari a wando.
"Wato ku ƴan iska koh.?" Kuluwa ta faɗa tana zaro ido.

Suka zube a ƙasa suna bata haƙuri.
"Ina can bangon duniya yarana suka kirani, suka faɗa mun iskancin da kuke aikatawa, daman sun jima suna bibiyarku amman baku daina ba, yau gani da kaina zan yi muku hukunci dai dai da abinda kuka aikata." Kuluwa ta faɗa tana hararan su, da manyan idanunta masu ƙyalli.

Sun kasa magana sai kuka suke yi Kuluwa ta ce.
"Duk wanda ya ƙara buɗe baki sai na tsayar da bakin." Kamar anyi ruwa an ɗauke, kuma gurin mutane basu cika bi ta hanyar ba.

Zan gindaya muku sharaɗi kuma idan kuka ƙi bin umarni na, sai na mayar daku alade da aladiya.

Suka fara kaɗa kai gashi babu halin magana.
"Lallai kuyi aure da gaggawa idan kuma ba haka ba, zakuji ana cewa maraba da zuwa duniyar aladu."


"Ina so ki yi mishi bulala goma yanzu." Kulawa da faɗa tana miƙawa Sa'ida dorina, a gurin ta tsinta dorinar mai gari ce yara suka jefo gurin.

"Wannan shine hukuncin iskancin da kuke aikatawa." Kuluwa ta faɗa tana zaro ido.


Sa'ida tana ƙaunar saurayinta ba zata iya dukansa ba.

"Hhhhhhhhh wato ke sarkin soyayya lallai zaki yi nadamar hakan." Kuluwa ta faɗa tana ƙara maƙale murya.

"Karɓa kayi mata bulala talatin." Ai kafin Kuluwa ta rufe baki har ya ɗau dorinar ya fara tsuga mata a jiki.


Sa'ida ta fara ihu tana neman taimako Kuluwa ganin asiri zai tonu yasa ta ce.
"Ka cigaba da dukanta har sai na ce ka tsaya."

Tana gama faɗa ta riƙo hannun Ummi suka bar gurin da gudu.


Daga haka suka raba kayan kowace ta nufi hanyar gida.


Abinda ya faru bayan su Kuluwa sun gudu, Sa'ida ihu take kamar ana yanka namar jikinta, shi kuma ƙara zabga mata dorina yake daga ƙarshe ihun ya yi yawa mutane suka taru, da ƙyar aka riƙe Ahmad yana ƙoƙarin sai ya koma ya cigaba da dukanta.

Sa'ida sai kuka take yi tama kasa tashi ƙarshe mai gari ya shiga da ita gida, Ahmad kuma ya saka a kulle shi zuwa gobe da safe.


Kuluwa tayi sallah ta wanke fuska kitchen ta shiga, tuwo ta gani tun na rana da alama ba a ɗaura girki a gidan ba.


"Kakus mai ya hana baki yi girki ba." Kuluwa ta faɗa tana zama kusa da ita.

"Saboda gantalallen ubanki bai kawo cefane ba." Kaka ta faɗa cike da jin haushi.


Kuluwa ta janyo ledar data shigo dashi ta fito da komai na cikin ledar sannan ta ce.
"Gidan Maman Ummi muka je shi ne ta bayar da wannan a kawo miki."

Kuluwa ta san halin Kaka shi ya sa take bin ta a hankali, kuma idan taji yanda aka samo wannan kayan to ba zata ci ba.

Kuma da gaske ne babu kuɗin cefane kayan abincin ne kawai, suka zauna suka ci sauran suka ajiye Kaka ta fara yi mata faɗa kamar yanda ta saba a kowace dare.

"Wai dan Allah Kaka bakin ki baya yin zafi idan kina magana." Kuluwa ta faɗa tana juya ido.

Kaka tayi alwala ta hau darduma Kuluwa ta kwanta tana tunanin bom ɗin da zai tashi gobe a gidan Mallam, Baba lami ga Asabe dilalliya lallai za a sha kallo.

Da sassafe za taje gidan domin taga yanda komai zai wakana a haka bacci ya ɗauketa cike da farin ciki da burin gari ya waye.


Dajine mai cike da tsoro da furgici tana tsaye da ƙwarya a saman, tana sanye da jajayen kaya, tana kiran sunan Samad Samad Samad sai da ta kira sau uku ƙwaryan ya fashe yana kamawa da wuta.

Daga bayanta taji an ce.
"Lallai ki nemo ta a duk inda take domin ita ce cikar muradinki, idan babu ita har abada burinki ba zai cika ba ki nemotahhhhhhhhhh." Cike da amoh maganar ta ɗauke. Hajiya Falmata kenan muguwar mace, makira kuma mace mai fuska biyu.


Karku ruɗe ƴan amanata muna cikin Kuluwa har yanzu.


Yawan likes ɗinku yawan typing ɗina


Ta Batulu ce............✍️*KULUWA*
*(Ƴar bala'i)*


*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*


Channel 👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaBJBOr8vd1H4qb9rd1a


Group 👇

https://chat.whatsapp.com/EEiLcD9ZnpbFRLSjSOZozT


Written by ✍️
Jagabar Jajirtattu
(Ta Batulu)


6️⃣
Hajiya Falmata mace mai duniya taƙama izzah rashin mutunci zalunci duk ta haɗa, matsafiyyace mai neman ɗaukaka da suna sai dai har yanzu burinta bai cika ba.


Tana zaune a Kano unguwar ɗan ladi na sidi, mijinta Alhaji Hashim ya rasu tana da ƴaƴa guda uku mata, Sakeenat Salma Sa'adatu, sannan tana da yarinya Fatima, da ita tazo gidan sai ɗan kishiyarta Samad.


Babban burin Falmata ganin bayan Samad sai dai duk yanda zata yi abin yaƙi, domin Samad mutum ne mai addini kuma ya riƙe azkar da karatun Qur'ani.

Mahaifiyar Samad ita ce uwar gida bayan haihuwar Samad Alhaji Hashim ya auro Falmata, lokacin da mahaifiyar Samad Hauwa'u ta samu cikin na biyu Falmata ta sadaukar da ita da jaririn cikin.

Babban burin Falmata Samad ya auri Fatimah, domin dukiyar ta dawo hannunta gaba ɗaya Alhaji Hashim ta sadaukar da jinisa, yanzu Samad kawai ya rage kuma yana yi mata biyayya kamar ita ce ta haifeshi, tayi nasarar haɗashi aure da Fatima amman har yanzu bata cika burinta ba, dodo ya tabbatar mata da cewar akwai jinin da zata samo wanda shine cikar burinta da muradanta.

Sai dai duk inda za aje ba a samo irin wannan jinin ba, kuma har yanzu bata haƙura ba Fatima tana da kirki Samad yana jin daɗin zama da ita, amman itama bata da kirki ƴan aikinta suna kuka da ita, kuma duk cikin da take samu an riga an sadaukar dashi, ba tare da sun san dalilin hakan ba sun yi magani har ƙasar waje amman ba a dace ba.


Kuluwa da sassafe ta tashi taje hadda ta dawo, ta zauna Kaka ta dama koko Kuluwa taje siyo ƙosai, gidan akwai mutane ta fita can ta ƙara dawowa ta cewa mai ƙosan.
"Inji Baban Abba ya ce ki bashi ƙosai na ɗari biyar."

Mai ƙosai taji an ambaci sunan mijinta ta karɓa ta zuba, Kuluwa sai data kai bakin zaure sannan ta ce.
"Wallahi babu wani Baban Abba daya aiko ni, hasalima ban san shiba sunanshi na tambaya." Tana gama faɗa ta zura da gudu.

Sun gama karyawa ta biya gidansu Ummi ta kirata suka nufi gidan Mallam, girkin Baba lami ne a can suka yini kuma aka hanasu abinci, ƙarshe Kuluwa ta ɗauke abincin Mallam ta fita dashi gurin mai sayar da nama suka nufa.

Suka gaisa Kuluwa ta ce.
"Baba lami ta ce ka bata nama na dubu biyar, anjima zata aiko maka dashi idan Ya Salis ya dawo aiki."

Mai nama ya zuba mata Kuluwa ta amsa, suka nufi gida a zaure suka zauna sannan ta fito da abincin Mallam suka cinye tass, ta raba namar gida biyu suka cinye ɗaya suka sha ruwa sannan ta lallaɓa ta mayar da kwanon.

Ta fita suka shigo da Ummi lokacin Baba lami tana ɗaura alale, daman tana yin na saidawa Kuluwa ta zauna tana taya ta bayan sun gama, ta fito da nama ta yiwa Baba lami bismillah, aiko kamar jira take yi babu kunya ba tsoran Allah ta gyara zama, duk da cewar ta hanasu abinci amman haka ta zauna aka cinye namar da ita.

Mama tana ta leƙe domin wallahi ta saka rai, Baba lami har da jefa mata takarda bakin ƙofa.

Bayan la'asar Asabe dilalliya tayi sallama suka gaisa da Mama, sannan ta kalli Baba lami ta ce.
"Yaune cikar alƙawari, zan wuce na ce bari in tsaya in karɓi kuɗin wake."

"Bangane kuɗin wake ba.?" Baba lami ta faɗa tana dakatawa da tsame alale a wuta.

"Kin ga bana san rainin hankali da rainin wayyau, ki ɗauko mun kuɗina ki bani cikin ruwan sanyi." Asabe ta faɗa tana cire mayafin kanta.


Baba lami tayi banza da ita sai data kwashe alalen a wuta zata shiga ɗaki, Asabe ta riƙota.
"Zaki bani kuɗi na, ko kuma sai na kira masu ƙwatar mun.?"

"Kije ki kira duk uban da zai karɓan miki, ina jiranshi."

Dambe ya kaure tsakanin Asabe da Baba lami.

Mama ta ringa dariya tana tafi, daman tana jin haushin hanata nama da suka yi.

Asabe dilalliya ta yiwa Baba lami duka sannan ta ɗebo mata ƴan sanda, ko da aka tambayi Asabe dilalliya ta faɗi abinda ya faru, ta zayyano duk abinda ya faru, Baba lami ta mulmulo zagi tana tsinewa Asabe.


Koda Baba yazo belin Baba lami sun hana domin ta yiwa DPO rashin kunya, kuma ya rantse sai ya yi maganinta Kuluwa duk abinda yake faruwa tana tsaye tana gani, babu tsoro ko nadama a cikin idanunta hasalima wallahi taso abin yafi haka.

Baba lami a cell ta kwana ga dukan data sha gurin Asabe dilalliya, Kuluwa daga nan suka nufi gidan mai gari yana zaune da mutane ana fadanci.

Ta zube ta kwashi gaisuwa sannan ta fashe da kuka.


Mai ne Kuluwa zata yi gurin mai gari??


Yawan likes yawan typing, bana yin update ranar juma'a, amman idan kuka yi likes zaku samu ko babu yawa.*KULUWA*
*(Ƴar bala'i)*


Channel 👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaBJBOr8vd1H4qb9rd1a


Group 👇

https://chat.whatsapp.com/EEiLcD9ZnpbFRLSjSOZozT


*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*


Written by ✍️
Jagabar Jajirtattu
(Ta Batulu)
Chapter 5 · 0% Book details