Chapter 8️⃣
Kuluwa Yar Balai Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Da asuba ta shirya ta saka uniform sannan ta ɗau Qur'ani ta nufi hadda yau bata tsokani kowa ba, ta bayar da karatu sannan aka ƙara musu wani gab da za a tashi aljannun wata suka tashi, sanadiyar dukanta da wani mallami ya yi akai.
Duka ta ringa kaiwa duk wanda ya matsa kusa da ita, a hankali ƴan ajin suka fara bigewa abin yafi ƙarfin mallamai, duk wannan abin Hajiyar Allah bata motsa ba, tana zaune ta duƙar da kai kamar bata cikin ajin, mai aljannu ta zabgawa Kuluwa mari ta riƙo hijjab ɗinta har Qur'ani na neman faɗuwa.
Kuluwa ta fasa ihu ta fara fari da ido ta haye ruwan cikinta, ta ringa kai mata duka tun aljannu suna nan har suka gudu yarinya ta ringa kuka, tana faɗin a taimaka mata amman Kuluwa jibgarta take yi kamar ta samu jaka.
Da ƙyar aka ɗaga Kuluwa a kan yarinyar mutane, ta ƙwace Qur'anin ta tayi waje bata jira an tashi ba.
Yau ko sallama ba tayi ba Kaka ta ganta kamar daga sama, tana shirin magana ta wuce zuwa bedroom kaya ta loda a jikinta guda huɗu, sannan ta ɗaura uniform a saman kayan ta ɗau jakan makaranta.
Kaka ta shigo ta kalli fuskanta gabanta ya faɗi, domin idan har ta ganta a wannan ya nayin bata barinta fita ko ina, domin wallahi tana fita sai an kawo mata ƙara sama da biyar.
"Kulun majadun waya taɓa mun ke." Kaka ta faɗa tana shigowa.
Kuluwa ta raɓa zata wuce Kaka ta riƙo ta, juyin duniya taƙi sakin hannunta.
"Tun da so kike in faɗi in mutu shike nan jeki." Kaka ta faɗa tana sakin hannunta.
Kuluwa jikinta ya yi sanyi ta kalli Kaka, hawaye ya zubo mata, domin ta tsani taji Kaka ta ce zata mutu.
"Kaka marina fa akayi, kamar ni za a mara."
Koma waye wannan mai ƙaddarar na tausaya mishi da masifar Kuluwa, Kaka tayi zan cen a cikin zuciyar ta.
Kaka ta rarrashi Kuluwa tayi breakfast sannan ta bata labarin abinda ya faru a hadda.
Kaka ta rarrashi Kuluwa sannan ta faɗa mata ai ta rama marin, amman ita bata yarda ta rama ba.
Kuma tayi alƙawarin sai ta yiwa yarinyar mugun duka, duk yanda Kaka tayi da ita amman bata haƙura ba.
Ta ɗauko madubi ta yi kwalliya harda lipgloss red, fuska yasha powder.
Kaka ta bata hamsin Kuluwa ta ce.
"Daga yau na yanke miki bayar da kuɗin makaranta, Mallam zai rinƙa biya."
"To ki amsa wannan domin kin makara yanzu." Kaka ta faɗa tana miƙa mata kuɗin.
Kuluwa ta amsa ta fita bayan tayi addu'o'i, yau babu tsokana gidansu Ummi ta nufa.
Matar baban su tana zaune tana danna waya Ummi na wanke wanke.
Kuluwa bata kalli kowa ba ta cewa Ummi.
"Mallama shirya mu tafi makaranta."
Ummi ta miƙe ta shiga ɗakinta, bata jima ba ta fito sanye da uniform suka nufi ƙofar gida.
Hassana ta miƙe ta tare ƙofa cike da ɓacin rai ta ce.
"Wallahi babu inda za taje sai ta gama wanke wanken nan."
Kuluwa ta raɓa zata wuce Hassana ta riƙo ta.
"Ummi wuce ki jirani a waje gani nan zuwa." Kuluwa ta faɗa tana miƙa mata jakan makarantar ta.
Ummi ta wuce Kuluwa ta dawo da kallanta gurin Hassana, ta kwashe da dariya ta karkace ido ta mayar da bakinta gefe ɗaya, ta shanye ƙafarta guda ɗaya hannun ma haka, sannan ta nuna Hassana ta maƙale murya kamar na kutare ta ce.
"Kin yi babban kuskuren da kike hana Ummi zuwa makaranta, kuma daga yau ba zaki ƙara tafiya ba."
Hassana gabanta ya faɗi ta ƙara kallan yanda lokaci ɗaya halittar Kuluwa ta sauya.
"Dan Allah dan Annabi ki yi haƙuri wallahi ba zan ƙara ba." Hassana ta faɗa jikinta yana rawa.
Kuluwa ta daka mata tsawa ta ce.
"Karƙi ƙara kirana mace, sunana Ƙudus sarkin kutaren duniya."
Hassana ta nemi hanyar gudu, amman jin abinda Kuluwa ta faɗa ya dakatar da ita.
"Kina shiga ɗakin nan ba zaki ƙara tafiya ba har abada."
Hassana ta ƙame guri ɗaya.
"Zan gindaya miki sharaɗi, kuma idan kina san zaman lafiya dole ki yi biyayya, ko kuma na mayar dake duniyar mu."
"Wallahi zan yi biyayya duk abinda ka ce Baban mu." Hassana ta faɗa tana share hawaye.
"Daga yau duk aikin gidan nan ke zaki rinƙa yi, sannan kuma idan kika ƙara hora Ummi da yunwa daga rana irin ta yau kin yi bankwana da wannan duniyar." Kuluwa ta faɗa tana zagaye gidan.
Kuma idan kaga Kuluwa zaka ɗauka naƙasashiyar gaske ce. 😂
"Kuma duk lokacin da kika ga tayi ba dai dai ba ki tsawatar mata a matsayin ki na uwa." Kuluwa ta faɗa tana nannaɗe jikinta, daman gata siririya.
Hassana dai hawaye yaƙi tsayuwa.
"Idan mahaifinta ya ƙara yin mata wani abin kika riƙe." Kafin Kuluwa ta rufe baki Hassana ta katse ta.
"Wallahi ba zan ƙara komai ba dan Allah ayi mun afuwa."
"Zamu tafi kasar mu dan haka, a bamu kuɗin shan ruwa a hanya." Kuluwa ta faɗa tana gwallo idanunta.
Kuluwa ta tabbatar da idanunta yana razana mutane, shi ya sa take zaro su idan tana neman tsokana.
Kuɗi da yawa Hassana ta ɗauko Kuluwa ta zari dubu biyar, ta watsa mata sauran.
"Idan kika gayawa wani abin da ya faru, daga nan ki fara shirin tawowa duniyar kutare."
Hassana ta rufe bakinta.
"Bani guri ga ƴan masarauta na nan sun zo."
Da rarrafe ta shiga ɗaki ta kulle Kuluwa ta daka tsalle ta bar gidan.
Ummi tana zaune tayi tagumi.
Suka tafi makaranta, a hanya Kuluwa ta siyawa Ummi doyan ɗari biyar da ruwa.
Suna zuwa bakin makarantar suka samu an tare makara, Ummi ta miƙa hannunta aka yi mata bulala goma, sannan ta ƙara miƙa ɗayan hannun a yi mata na Kuluwa.
Mallam Usman ya daka mata tsawa ya ce.
"Wallahi ko mutuwa za tayi, yau sai na zaneta."
"Mallam daga duka sai mutuwa." Kuluwa ta faɗa tana miƙa mishi hannunta.
Ya daketa sannan ya ce ta share jan bakin data saka a lips ɗinta.
Kuluwa ta matsa gefe shi kuma yaci gaba da tare makara, ta duƙa ta share a jikin rigan shi kuma rigan fari ne.
Ta samu ƙasan rigar tayi mishi kiss kuma ya fito sosai, sannan ta share raguwan jan bakin a hijjab ɗinta.
Suna shiga makarantar, taga ƴan ajinsu gaba ɗaya suna tsaye a cikin rana.
Tayi kamar bata gansu ba zata shige taji an fincikota ta baya.
Yau nayi typing da yawa, sauran likes da yawa.*KULUWA*
*(Ƴar bala'i)*
Group 👇
https://chat.whatsapp.com/EEiLcD9ZnpbFRLSjSOZozT
Channel 👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaBJBOr8vd1H4qb9rd1a
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*
Allahumma Salli Ala Sayyadina Muhammad Wassalim
Written by ✍️
*Jagabar Jajirtattu*
(Ta Batulu)