Chapter 7️⃣
Kuluwa Yar Balai Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
Juyin duniya Kuluwa taƙi magana mai gari ya sallami ƴan fada akan su bashi guri, ta gyara zama ta ce.
"Ranka ya daɗe daman wani abu na gani wanda hankalina ya tashi, kuma naji ba zan iya shiru ba sai na faɗa maka."
Mai gari ya gyara zama Kuluwa ta harari Ummi data zuba mata ido.
"Munje hospital bani da lafiya, a can naga Sa'ida taje zubar da ciki." Kuluwa ta faɗa babu tsoro ko shakka a cikin idanunta.
Mai gari ya fara salati yana sallalami.
"Idan baka yarda ba zaka iya zuwa da ita hospital a duba ta." Kuluwa ta faɗa tana miƙewa.
"Idan kuma nayi binciken na gano ƙarya ne.?" Mai gari ya faɗa.
"Ka yanke mun hukuncin da kaga ya dace dani." Kuluwa ta faɗa tana yin gaba Ummi na take mata baya.
"Ummi zo muje kasuwa." Kuluwa ta faɗa tana sanja hanya, sun kusa kaiwa ta tsaya.
"Kakus bata nan kuma, ina jin cin kaza dan haka muje gida."
Suka nufa gida a hanya taga mai siyar da kayan miya, ta ce.
"Tattasai da albasa na ɗari biyu."
Ya bata sannan ta karɓa tayi gaba tana faɗin.
"Zan biyaka idan na samu kuɗin da ba zan yi amfani dasu ba."
Gab da za su shiga gida ta tsaya gurin mai shagon unguwarsu ta sai maggi na ɗari biyu, tayi gaba tana cewa.
"Zan rubuta sunan ka a cikin littafina koda na mutu, karka bari a fita da gawata sai an biyaka kuɗinka."
Gida ta shiga ta duba inda Kaka take ajiye makulli, ta buɗe ɗaki sannan ta kamo kaza babban ciki.
Ta kalli Ummi ta ce.
"Danne mun kanta." Ummi ta danne kan kaza.
"Yanzu sai ki faɗa mun addu'ar da ake yi idan za yanka kaza." Kuluwa ta faɗa tana ɗaura wuƙa a wuyan kazar.
"Nawaitu zabri yanka." Ummi ta faɗa Kuluwa ta yanka kaza har sai da kai ya kusa fita, bayan ta mutu suka ajiye a gefe aka kunna wuta.
An fige kaza an dafa sai tashin ƙamshi gidan yake yi, an gama Kuluwa ta ce.
"Babu mangyaɗar suya."
"Kaza a haka tafi daɗi." Ummi ta faɗa suka raba kaza biyu, Kuluwa ta ɓoye rabin ɗayan kuma suka ci.
Bayan sun gama suka gyara gurin suka zubar da gashin kazar, suka gyara gidan harda saka turaren wuta.
Suka zauna suna fira Ummi take bata labarin saurayinta Nazeer, ranar kam Kuluwa ba a ƙara fita ba ta kwaso kayan makaranta suka wanke, suka goge gobe Monday akwai zuwa school.
Kaka ta dawo tayi farin cikin ganinsu a natse, suka ta yata girki bayan an gama suka ci abinci suka ƙoshi, sannan Kuluwa ta raka Ummi gida.
Bayan sunje gidan Ummi ta rako Kuluwa gida, haka suk ringa yi idan Kuluwa ta raka Ummi sai itama ta rakota, Kaka ganin abin yaƙi ƙarewa ta kori Ummi gida.
Kuluwa da wuri ta kwanta bacci domin tana san tayi sammako, zuwa gidan Mallam tayi kallo daga nan sai ta wuce school.
A ranar mai nama yazo karɓan kuɗi sabon tashin hankali, Baba lami ta rufe ido ta zageshi tass kuma ta yi rantsuwa ba zata biya kuɗin ba.
Mallam ya tambayi mai nama abinda ya faru, ya bashi labarin yanda suka yi da Kuluwa Mama tayi saurin fitowa har zani yana neman faɗuwa ta ce.
"Tabbas ɗazun ta aiki Kuluwa siyo nama, wallahi nima shaidace."
I'm sorry uzri ya riƙeni yau kuma nayi alƙawarin update.*KULUWA*
*(Ƴar bala'i)*
Group 👇
https://chat.whatsapp.com/EEiLcD9ZnpbFRLSjSOZozT
Channel 👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaBJBOr8vd1H4qb9rd1a
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*
Allahumma Salli Ala Sayyadina Muhammad Wassalim.
Written by ✍️
Jagabar Jajirtattu
(Ta Batulu)