← Book details Kuluwa Yar Balai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 3 OF 9

Chapter 3️⃣

Kuluwa Yar Balai Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Mai ƙibar  ta buga Kuluwa da ƙasa Kuluwa ta kwaso ƙafafunta, suka haɗu da Ummi suka yi mata duka sannan suka tafi Kuluwa ta ɗaga murya ta ce.
"Fankan fankan bata kilishi."

Suna tafiya suna  tsokanar mutane da zasu rabu Kuluwa ta cewa Ummi.
"Ki shirya da wuri anjima ki biyo ta gidan mu."

Kuluwa ta karɓi Qur'anin ta nufi gida kaka tana zaune tana jan charbi, taci abinci ta ɗau allo kaka ta bata hamsin.

Kuluwa ta karɓa ta nufi makaranta an biya mata karatun, ta zauna cikin yara haka ta ringa tsungulin ƴaƴan mutane tana faɗin.
"Duk kun cika mana kunne."

Ƙarshe dai Mallam ya sallami Kuluwa domin kullum haka suke yi.

Tazo wucewa taga Sa'idu yana gyaran wuta  daman ranar ya mareta, ta janyo tsanin ya faɗo tayi gaba tana dariya ta nufi gidan mahaifinta.

Babu kowa a tsakar gidan ta lallaɓa ta shiga kitchen, tukunya, ta gani a wuta ana dafa wake ta ɗauko gishiri mai yawa ta zuba ta lallaɓa ta fito.

Tayi sallama.
"Baƙar jaraba tauraruwa mai wutsiya." Mama ta faɗa tana hararanta.

Kuluwa tayi kamar bata ji abinda ta faɗa ba ta nufi ɗakin Mallam kamar yanda yara suke kiranshi.

Har zata shiga ta juyo ta kalli Mama ta ce.
"Dan Allah ina jin yunwa."

"Wallahi sai dai ƙamshi ya kasheki amman baki da rabo acikin abincin nan mayya kawai." Mama ta fada tana shiga kitchen.

Kuluwa tayi murmushi ta shiga ɗakin Mallam yana zaune yana karatun Qur'ani, ta duƙa ta gaishe shi sannan tayi shiru tana wasa da hannu.

"Lafiya.?" Mallam ya faɗa yana ajiye Qur'anin hannunshi.

"Daman kayan abincin mu ya ƙare  shi ya sa nazo in faɗa maka." Kuluwa ta faɗa tana kallanshi.

"Lami bata aika muku da shinkafa ba.?" Mallam ya faɗa cike da mamaki.

Kuluwa ba tayi mamakin hakan ba domin ta jima da fahimtar matan mahaifin nata makirai ne.

Kuluwa tayi ƙasa da kai Mallam ya kira Baba lami ta shigo tana raba ido.
"Ina shinkafar dana bayar ki aikawa Kaka.?"

Baba lami ta fara kame kame data ga babu wani mafita sai ta ce mishi.
"Na aika mata dashi."

Kuluwa tayi karaf ta ce.
"Eh tabbas ta aika dashi, sai yanzu na tuna."
Mallam ya yi mata faɗa akan ta rage shiririta, Baba lami tana tsaye tana ƙarewa Kuluwa kallo domin bata yarda da wannan maganar data faɗa ba.

"Yunwa nake ji."Kuluwa ta faɗa tana kallan mahaifinta.

Mallam ya ce.
"Kije gurin Mama ta baki abinci."

Kuluwa ta miƙe tayi sallama da Mallam ta fita, babu kowa a tsakar gidan ƙasa ta ɗiba da yawa ta buɗe tukunyar ta samu an zuba shinkafa ya kusa dafuwa ta barbaɗa a sama, tayi gaba tana dariya tana barin unguwar taga wata yarinya tana siyar da awara.
"Zoki bani ala koro kasuwa."

Yarinyar tayi banza da ita Kuluwa ta janyo robar, gaba ɗaya awarar ya zube ta ɗibi guda huɗu ta ce.
"Wannan sun ishe ni, ki kwashe sauran Allah ya koro kasuwa ƴar baƙa." Yarinya ta fashe da kuka.

Kuluwa ta gama cin awarar sannan itama ta fashe da kuka, mutane suka fara taruwa suna tambayar abinda ya faru, Kuluwa tafi mai awarar kuka.
"Saboda ta ce in bata ala koro naƙi, shine ta zubar mun da shi." Kuluwa ta faɗa tana cigaba da kuka.

Mai awara ta saki baki tana kallanta aka taru anata bata haƙuri, Kuluwa ta samu leda ta zuba awarar ta saka yaji ta miƙawa mai awarar ta ce.
"Da na san zaki zubar mun da shi wallahi dana baki, amman kije bakomai Allah ya mayar mun da alkhairi."

Mutane suka ringa yaban Kuluwa suna saka mata albarka, mai awara makircin Kuluwa ya sumar da ita a tsaye.

Kuluwa tayi gaba tana tunanin abinda zata yiwa Baba lami, baba ya bata kayan abinci ta basu shine ta ɓoye kamar yanda ta saba, wallahi wannan lokacin bata ci banza ba sai ta biya harda riba.

Kuluwa taje gida ta ɗauko shinkafar data karɓo gurin Asabe dilalliya, ta shiga ɗakin Kaka ta na faɗin.
"Mallam ya bayar da shinkafa a kawo muku."

"Ina kika baro Qur'anin naki.?" Kaka ta faɗa tana tsareta da ido.

"A ɗakin Mallam." Daga haka ta zauna ta janyo kwanon data gani a rufe, kwaɗon zogale yasha tumatur yana ta ƙamshi.

Ta cinye tasha ruwa sannan ta kwanta tana tunanin irin abinda zata aikatawa Baba lami, wanda zai girgiza duniyarta.

A haka bacci ya kwasheta har akai sallar azahar bata farka ba, Kaka ta yayyafa mata ruwa daman Kuluwa akwai nauyin bacci.

Ta miƙe tayi sallah ta zauna tana hararan Kaka, ganin zaman ba zai fisheta ba yasa ta miƙe ta ɗibo ruwan zafi a kitce ta shiga tayi wanka ta fito.

Riga da zani tasa zanin dai dai gwiwa ta ɗaura aka samu powder ta shafa, ta zauna ta ɗauko gazal ta zana tun daga gira ta haɗe da kunne, ta ɗauko kwalli ta shafa a baki sannan ta ɗaura da lipgloss.

Ta shafa turare ta ɗau madubi, ta fashe da dariya tana yi tana gwallo.

"Oh ni Kulun majadun daman haka nake da kyau kamar, sarauniyar Ingila."

"Sai dai sarauniyar mahaukata amman bana ƙasar waje ba." Kaka ta faɗa tana hararan ta.

"Kakus maine ne abin baƙin ciki dan Kuluwa ta fiki kyau, kin ci zamaninki kina neman kici na wasu."
Kaka tayi banza da ita, Kuluwa ta ɗauko babban madubi ta ajiye a gabanta, ta fara tafiya tana lanƙwaye jiki kamar zata karye.

Ummi tayi sallama ta shigo itama da kwalliyar hauka, irin na Kuluwa suka haɗu a gaban madubi suna waƙa, suna yi suna fari da ido yanda kasan gayyar mahaukata.

Kaka duk yanda tayi banza da ita sai da suka sakata dariya.

Har la'asar suna waƙa a gaban madubi Kaka ta ƙwace madubin ta kora su, suje suyi sallah.

Suna idar da sallah Kuluwa ta ce.
"Kakus ina jin yunwa."

"Ki duba abinci a kitchen." Kaka ta faɗa tana shiga bedroom.

Daga cikin kitchen Kuluwa ta kira Ummi, tana cewa.
"Yau gidan mu babu abinci, zo mu tafi bara tun dare bai yi mana."

Kuluwa ta yafa gyale suka nufi hanyar fita Kaka ta kirata tana cewa.
"Ki zo in gyara miki ɗaurin zanin nan kamar za a tsallake wuta."

"Ai yanzu haka ake ya yin ɗaura zani a sama." Kuluwa ta faɗa tana yin waje da gudu Ummi ta rufa mata baya.

"Ubangiji ya nuna mun ranar da Kuluwa zata yi hankali, yarinya kamar kwancen aljanu."

Banyi alƙawarin update kullum ba, likes and comments sannan kuyi sharing.


Ta Batulu ce........ ✍️*KULUWA*
*(Ƴar bala'i)*


Group 👇

https://chat.whatsapp.com/HDAsWBYpkZP5YJSNFPR5I8


Channel 👇

https://whatsapp.com/channel/0029Vb6Kd5SFnSz8T3XpQ22g


*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*


Written by ✍️
*Jagabar Jajirtattu*
*(Ta Batulu)*
Chapter 3 · 0% Book details