← Book details Jannatan Wa Harirah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 10

Sashe 8

Jannatan Wa Harirah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin mota suke sai da akayi nisa sannan sai ga yaran aminu saman mashuna sunzo mai bankwana suka tarar da motarsu ta tashi shiyasa suka bi yar yanke. tsayawa sukayi malam yace yakamata tunda akwai guri mutafi da mutun biyu ko ukku acikin su. jazuli da muda ne suka shiga motar sauran suka masu rakiya har qarshen gari sannan aminu yace sukula da garinan dan Allah idan bagalle ya dawo su kamashi su ajiye shi har yadawo haka suka rabu mota ta hau hanya. cikin mota harira tace ma aminu nata a mafarkin nashiga gidan ku kamar yadda nashiga jiya. Ikon Allah zaulai tafa Malam yace inaso nayi maki tambaya akan miye sunan mahaifiyarki da mahaifinki. harirah tace banasani ba wallahi domin natashi a wannan garin a gurin wani tsoho kowa yana ganin shine mahaifina Ammah ni nasan ba shine mahaifina ba domin dana duba acikin allon tsafina naga mahaifina ammah banga mahaifiyata ba danayi duk nayi bincike akan mahaifiyata, to wani gida nake gani kamar wannan gidan naku. A kaf garin mu bani da an uwa ko dangi sai maciji, lokacin da nayi bincike akan allon tsafina anan aka nuna man shi an uwanane na jini. Mallam yace gidan da kike gani kince kar wannan gidan ko to kinsan a wane gari gidan yake ? Eh a garin yola gidan yake. Sai dai koda naje gidan babu kowa aciki. Ammah lokacin da nayi tozali da Aminu danayi bincike akanshi a cikin allon tsafina nagashi an uwanane najini. Sai anan aminu yace. taya zan zamowa an uwanki najini ? harirah tace bansani ba nima Ammah hakan nagani. Zulai dai mamakin harirah kawai takeyi. Sai yammah suka qaraso garin su harirah. suna shiga garin suka tabbatar da ba lafiya ba. Domin sun tarar da gawar macizan da ke gadin kowane sako da lungu na garin. hakan yasa harira fashewa da kuka tana fa in waye wannan wa kasheman anwana waye wannan azzalumin kamar zatayi hauka haka takeyi sai da mama zulai ta kamata ta riqe arshe ma ta rungumeta tana lallashinta. suna a haka sai wasu zaratan mutane da kaya jajjaye ajikin su sun masu awanya. Nan malam yace lafiya sukace ansakasu sukamo gimbiya harirah nan aminu ya alle dangar da da sukayi masu yacire rigarsa yaciro wuqarsa dake ugunsa yanafara yankan su a afa da hannu. muda da jazuli ma fitar da nasu makami sukayi nan take suka saka su malam a bayansu suka fuskanci dakarun da ke gabansu. muda da jazuli kowa da kwakiyarsa a hannu haka suka shiga yaqar wannan mutanan. aminu kam jarumin gaskene duk wanda ya riqa sai ya karyashi duk wanda yakaiwa nushi sai ya allashi harta kai ta kawo aminu mayar da wuqarsa yayi yasoke a ugunsa ya cigaba da yaqarsu da hannu duk inda yabi sai dai kaga mutane zub malam da zulai harda fauziyya mamakin qarfin aminu sukeyi yadda yake zubar da maza kasa nan take suka qarar da wayanan suka shiga cikin gari akan katangar fadar harira anan yan kibau suke suna tun karuwa suka fara harbo kibau nan jazuli ya shiga gaba shida muda dan kare Aminu da ahalinsa. wulwula makamansu sukeyi suna kare kibau da ake harbuwa. Wani saurayine ya fito a sama inda yan kibau suke ya aga hannu alamar su dakata. nan suka dakata da harbin. sannan yace sunana lemraz dan margeez. Gimbiya harira kinsanni nasanki nasan qarfin tsafinki shiyasa ban ta a gigin zuwa inda kike ammah kisani kullun da gurin kwace wannan garin naki bacci to nasamu labarin kin musulunta dan haka nashirya shigowa garin sai da nashigo garin natar bakinan. gimbiya hararih najima da sonki a irjina dan haka a yau dole ne kiyarda na aureki ko kuma na kashe kowa dake cikin garin nan. aga kai aminu yayi yakalleshi yace. kai maqaryaci a yau ba sai gobeba zan kai arshenka. jin haka yasa harira tace Aminu bazaka iya dashi ba dan yana da mugun tsafi babu wani abu dake iya tasiri a kansa. Aminu yace ai wallahi ko zan mutu sai naga bayan wannan azalumin dan haka idan yakai jarumi ya fuskaceni gaba da gaba. Jin hakan yasa leemraz yadiro daga saman gini sai gashi gaban aminu wani mahaukacin duka yakaiwa Aminu sai da Aminu yayi doguwar tafiya saman iska ya fa i somamme. Nan take gimbiya harirah tayi sama tana kwalla wata qara da kururuwa tun a sama iska karhunta dake cen gida a akin aminu sai gashi a damtsenta. sandarta dake cikin fada sai gata a hannunta nan take kayan jikinta suka sauya suka kuma baqaqe gashin kanta yatufke ya rabu gida bakwai koda ta diro qasa gashin kanta yazama macizai bakwai anan tabugawa leemraz sandarta yakare da tashi sandar nan take tartsatsin wuta yafita yayi sama yawatse nan yan kibau sukai ta fa owa. leemraz ya aga kai sama yayi yana motsi da baki kawai ya aga sandarsa yakama wulwulawa nan take wata guguwa ta turnuqe wajen tare da wata wuta jajir anan ya kawowa gimbiya harirah duka da sandar tare da wannan guguwar ita kuma ta kare nan iska ya auketa sai fa awa tayi a hannun Aminu nan ya ajiyeta gife yace barni dashi. PAGE 07 leemraz ya aga kai sama yayi yana motsi da baki kawai ya aga sandarsa yakama wulwulawa nan take wata guguwa ta turnuqe wajen tare da wata wuta jajir anan ya kawowa gimbiya harirah duka da sandar tare da wannan guguwar ita kuma ta kare nan iska ya auketa sai fa awa tayi a hannun Aminu nan ya ajiyeta gife yace barni dashi. nan Aminu ya karanta ayatul kursiyu ya tsaya a gaban leemraz muda da jazuli suka jefo mashi makamansu ya cafe yakama wulwulasu cikin warewa da jarumta. murmushi leemraz yayi yabuga sandarsa a qasa wasu halittu suka bayyana cikin sahu duk sahu hattun ne su ari sunyi sahu goma su dubu kenan nan sukayuwa aminu chah shima ya tunkaresu yana juwa kamar fanka sai zubewa sukeyi qasa kamar fari cikin minti biyar ya qarar dasu nan hankalin leemraz ya tashi. kamin yayi wani yun kuri jazuli da muda suka riqeshi yayi yayi ya kucce yakasa kucce wa nan suka kwace sandarsa ako aminu yayi wani tsale yakafawa leemraz kwakiyarsa a takiyar kansa sai ga kwakiyar a asa ta raba leemraz gida biyu nan take wata guguwa ta tashi leemraz da rundunarsa gaba aya wannan guguwar ta kwashe su tayi gaba dasu. malam da zulai harda fauziyya sumar tsaye suka da mamakin wannan abun kamar a film suke kallo sai dai gasu a zahiri abun ke faruwa. jazuli da muda hamdallah kawai sukeyi suna godewa Allah nan Aminu Allah akbar Alhamdullah bizal ni'imah Alhamdulillahi naza hazihil ayah ayatul kursiyu ala nabiyina muhammadun sallahu alaihi wasallam. Rugume junansu sukayi suka ha a kawunansu suna fara'ah. Su malam suka tako har kusa da su Aminu yace. Malam Aminu haka kuke fama da masu tsafi ? Aminu dariya yayi jin malam yau ya kirashi da malam yace baba kenan. Harirah arasowa tayi ta durkusa agabasu tacewa su Aminu dan Allah kubani wannan sirrin naku wanda yafi namu dan Allah gani a gabanku ina mai rusunawa agareku dan neman arzikin ku ina mai ratsuwa da Allah Alokacin da Aminu yakaran wannan ayar dana auna qarfinsa a cikin tsafina naga karfinsa da zai yaqi duniya zai iya gama da ita. Zulai tace kitashi a gaban mu kinzamo tamu kema. Fauziyya tace baki iya ayatul kursiyu ba ? Cewa tayi Eh ban iyaba. Fauziyya tace zankoya maki ita yanzu. Nan fauziyya ta fara karanta mata tana amsawa har qarshe. Harirah na gama karanta ayatul kursiyu karhunta ta yawatse sandarta ma ta karye. Mutanan garin ne suka fiffito cikin mamaki harda maccizan da aka kashe sai gasu sun biyo gayyar mutane. Aminu yace wai miya faru nidai na gannin a tsaye kawai. Nan jazuli yace lokacin da surukarmu wato gimbiya harirah takai wa leemraz duka munkaga wuta tayi sama data dawo muka ga ta kama yan kibau dake saman katanga nan muda yace mu karanta ayatul kursiyu kamin wutar ta kawo garemu. Nan duk muka karanta koda wutar takawo kanmu kewayemu tayi ta wuce alokacin duk wanda yake akwance sai da ya tashi haka muka ga wannan wutar na cinye abunda ke raye wanda muka ya mutu yana tashi. Nan gimbiya harirah tace duk wanda leemraz ya kashe da tsafi wannan wutar zata tasheshi dan karya tsafice. Mutanan garima kowa ya tashi wayanda aka aure suma sukace kawai munga sarqoqinda aka auremu sun zube a asa. Gimbiya harirah tace yanzu mushiga ciki dan Allah musamu muci abunci. Fauziyya dariya tayi tace yanzu naji zance dan ni nafara ganin blue da kore. To, su acici, malaikun tauna, fa in mama zulai. Mudah yace, mama karki laifin shalelen mai gida, zancenta gaskiyane. Jazuli yace, hmmmmn ai sanmakal, kai da ita. Suna fira cikin farin ciki suka karasa cikin fadar. Kuyan da kecikin fadar ne suka fara fitowa kowace dauke da kayan marmari dan suci, sai ruwa. Fauziyya tace nifa wannan baya aukata dan sai dai naci dan farfar owar hanji gudun karku kulle. Dariya malam yayi yace nikam inada aiki dama haka kike da ci kamar garar to gaskiya nafasa. kayiwa kanka qiyamul lailu wallahi da ka fasa aini matar manya ce ai ri on mahaukaci sai sarki cewar fauziya. mama zulai tace gwanda dakikace mahaukaci dan wannan mahaukar cin naki sai gidan sarki. Aminu kuwa shiru yayi yakasa cin komi sai kallon wani guri yakeyi bajimawa sukaji wani kamshi ya cika wajen kowa ya dakata da cin abinsa banda Fauziyya. Harirah ce ta qaraso cikin Shiga ta alfarma irin ta sarakai. Macizan nan kuwa sun take mata baya tare da wasu kuyanki mata su biyar. A haka ta qara so tace dasu kuyi haquri nabarku kuna jira. Mama zaulai cikin ranta race, yanzu wadda ke cikin wannan daular in ba dan soyayya ba bazata ita kwana akan gadona ba gaskiya duk inda sarauniya take wannan takai. Aminu kuwa wata nannauyar ajiyar zuciya yayi tare da hamdala ga Allah dan ganin yayi kamar ankara mata kyau da cikin ransa yace ina son ganin murmushinta sai sai duk tayi sai naji gabana ya fa i sosaiiii. A haka dai aka kammala cin abincin kowa da abunda zuciyarsa kecewa. Bayan sun kammala tace
Chapter 8 · 0% Book details