Sashe 6
Jannatan Wa Harirah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mata asusunta ma'ana bankinta, ta zo mata dashi. Amina tace to sai da safee, tace mata sai da safee, fauziyya naqara jaddadawa namanta garta manta. Amina ta auka bankin da tace ta auko mata wasu ku i zata saka, ko kuma tafiya zatayi dashe cen duk wanda yabata ku i ta saka. Bayan sun shiga gida. Aminu yace ku fito ga surukarku nan tazo. Da mugun gudu mama zulai ta fito, tana washe baki, tana maraba dake! maraba dake!! Maraba dake!!! hasken gidan nan ya bayya aiko kowa fitowa yayi, banda mama larai. Harirah cikin girmamawa take gaida kowa, suna amsa mata gaisuwarta suna fa a mata sunayan su. A haka habibu ya shigo yazo aukar matatar shi ya tarar da harira, cikin fara'a suka gaisa, Aminu yacewa mashkur kakaita akin mama ta gaishe da ita, idan sun gaisa ka kakaita akin mama zulai a cen zata kwana. mama zulai taji da in wannan maganar tashi sosaiii. shikuma Aminu ya wuce yace bari yayi sallar isha ya dawo. mashkur yawuce gaba tabi bayasa cikin ladabi, suka shiga akin mama larai da sallama a bakinta. Gimbiya jin takeyi kamar wannan gidan da ta shigo, shine gidan su. Kallon su takeyi, tanaji ajikinta kamar tashigo cikin danginta. mama larai ta amsa sallamar tace barka da zuwa, da fatan kinzo lafiya. usawa har asa tayi tana cewa, barka da wuni mama da fatan nasameku lafiya. jin muryarta da kalar durguson da tayi yasa mama larai mai da hankali kan harirah. Nan zuciyar larai ta doka da karfin gaske. Dan ban da fari da huraira tafi wannan da sai ta rantshe da Allah wannan huraira ce kanwar malam sai dai wannan baqace, Ammah wallahi har idanuwan irin na huraira ne da yadda take kallon mutane dasu haka harira ke kallo dasu. jin shiru yasa mashkur yace, tashi mutafi nakaiki akin mamata. tashi tayi ba musu mama larai na kallon bayanta da tafiyarta irin ta huraira nan take ta tuna ranar da za'a kai huraira akin mijinta Anas ko ina take yanzu ? aga hannu tayi tace ya Allah ka bayyanar muna da ita dan isarka da girmanka dan tsarkin mulkinka ya Allah tashafa addu'a. Habibu ne yashigo yimata sallama yace Ameeen mama sai da safe. To sai da safe Allah yamaka albarka yabaka zuru'a ayyaba. AMEEEEEN. JANNAT misalin karfe takwas na dare Dadyn ta ya dawo a parlour ya tarar da momeey ta kar i jakar hanunsa yace ina yarinyata ? Mom tace kabari kayi wanka kaci abinci sai na kira maka ita. Shafa fuskarta yayi hankali yace kinsan bana son sirrin mu ya bayyana a idan duniya dan haka dole nasan yadda zanyi na turata nesa da garin nan ko tabar qasar nan ma baki aya. Taka matatattakala yayi ya haye sama yashiga akin jannat, kwance take saman gadonta ta lumshe idanuwanta. Kamar mai bacci. Da sallama yashiga jin ta amsa mashi sallama yasa yasan ba bacci takeyi ba. Cen murya asa asa tace ina wuni dady na da fatan kadawo lafiya ? Lafiya qalau my jannat tashi muyi magana dake. Tashi zaune tayi ammah idanuwanta a rufe. Shalelena ki bu e idanuwanki mana ki ganni ko yau baki son ganina ? ewa tayi tayi tozali da mahaifinta sai taga kamar shima yayi mata kama da wanda yakira ta harirah. Abbana wallahi kuna kama dashi kamarku aya da wanda nagani ya kirani da harira a yau. Dady yace dakata kikwantar da hankalinki ki natsu bana son wani abu ya sameki yanzu haka nasa anyi bincike dan momeenki ta fa aman komi a waya hakan yasa da aka bincika aka tabbatar man da wa anda kika ka aya ya mutu. Cikin tashi hankali tace ya mutu abba na shiga ukku sai da momeey tace kar nafita Ammah na fita ga abunda na jawowa kaina. Dady yace yanzu karki qara fita zansa a shirya maki visa kibar asar nan tayadda sai kin gama karatunki sannan ki dawo zuwa lokacin bake ba har wanda kika ka e ya mutu an manta dashi. Anan momeee ta shigo akin auke da tray lemokane da kofi biyu sai dai sukaji zubewar trayn dake hannun momeey kichaaaa. A razane Dady da jannat suka juyo suna kallonta tace. Alhj aya ya mutu ayan fa ? kashe mata ido aya yayi ya kalli jannat hakan yasa ta fahimci qarya yakeyi wayau yake son yayiwa jannat in dan ta amince ta yarda ya turata qasar waje. Cewa tayi Allah ya jiqanshi ya jiqan kulluhin musulmi. Ameeen jannat da dady sukace. Jannat hawaye kawai takeyi tana Allah natuba ka yafe man wallahi bada niyar na ka esu ba qaddarace. Dady yace Allah yasan qaddace nima nasan qaddarace dan ko kiyashe baki ta a kashewa ba. Yanzu ki daina kuka idan kin amince zan shirya maki visa zuwa jibi sai ki wuce shikenan kiyi tayi masa Addu'a da neman gafara gurin ubangiji. Tashi yayi yace mom ta kawo masu abinci yau tare zasuci shi da mamansa jannat. Anan yaci abinci dan jannat ka ai taci koshi dady ne ya bata da kanshi bayan su gama yayi mata sai da safe ta amsa masa da sai da safeee dady. Yace i love you my daughter i love you too my dady. Fitowa yayi tare da mom tana auke da kwandon kayan da sukaci abinci ta fito dasu ta kai kiching. angaren jannat kuwa tun cikin dare akasa mai aikin su ta shirya mata kayanta dady kuma yasa aka nemamata jirgin safe akace sai da na arfe shiddah yace hakan ma yayi. Jannat a daren batayi bacci ba sai tunanan Aminu takeyi idan ta dawo hayyacinta sai ta kama istigfari tana neman gafarar Allah akan wanda akace ya mutu sanadiyyarta. tana zaune da misalin karfe biyar da rabi na dare sai ga momeenta ta shigo ta taddata zaune ido biyu tace har kin tashine ? jin shiru yasa momeenta ta kalleta da kyau taga idanuwanta sunyi ja sosaiii tace subhannallah miya hanaki bacci jannat ? Momeee tayi mata tambayar ne tana an girgizata. firgigit jannat tayi tadawo hayyacinta tace momeey tana fashewa da kuka. momeenta tace lafiya jannat kiyi shiru dan Allah. cikin kuka jannat tace momeee bazan qara jan mota ba momee yau gashi na kashe wani nayi sanadin rasa rayuwar wani momeee idan kun oyeni a nan duniya a gobe qiyama ya zanyi da laifin kisan wani. jannat takai arshe tana mai ara sautin kukanta, mom tace. ki kwantar da hankalinki insha Allah zamu nemi iyayansa mu biyasu diyya kuma mata maki addu'a da nema maki gafar Allah kema sai tayi dan Allah ki kwantar da hankalinki kiyi abunda ya kaiki kiyi karatu sosaiii ta yadda nida dadynki zamuyi alfahari dake. Dato jannat ta amsawa momeeey. momeey tace to kitashi kiyi wanka kinsan arfe shiddah ne jirginku yanzu ke ka ai aka jira dan ansaka kayanki a boot. tashi jannat tayi tashiga wanka bayan tafito tashirya sai filin girgi sai da jirginsu ya tashi sannan momeeey da dady suka dawo gida. cikin damuwa momeeey ta kalli dady tace. ammah yakamata musanar da jannat gaskiyar wa anda ta ka e bawanda ya mutu kuma musanar da ita gaskiyar waye ita dan gwanda tasan danginta kamin tamu ta auke mu. ciki tsawa da aga murya yace ya isheki kiman shiru ni jannat artace wallah ko babanta Anas ne zai dawo yace yasanta sai nasa an nisantashi da duniya banta a kisaba Ammah wallahi akan jannat. zan iya kumai idan kika sake tasan wannan lamarin hmmmmmn. kawai yace yayi shiru. jin haka momeeey yasa tasha jinin jikinta tace Allah yabaka haquri insha Allah babu wanda zaiji. BAYAN SALLAR ASUBAH Kamar yadda aka saba yauma an raba qur'ani hizib biyar biyar sai karatu akeyi ammah banda harirah zaune take tanajin sunayi kawai Aminu da ya auka ya duba matashi shikenan zai karanta sai yayi hizib biyar ya ajiye yasake aukar wani malam kallonshi yakeyi cike da mamaki cikin sa'a yau aka sauke Qur'ani saboda kowa yana nan kuma karatun aminu yau yasa kowa sai ara qaimi yakeyi bayan an kammala malam gabatar da addu'a ta kammala karatun Alqur'ani aka shafa addu'a sannan malam yace. Alhamdulilah ! Alhamdulilah !! Alhamdulilah !!! Yau muna alkhamis siddah ga watan muharam shekara ta 1447 hijiriyya. Kamar kullum ina maku nasiha yau nashihata akan ayar farko ta suratul qamar wato Surat wata. Da sunan Allah mai rahama mai jinqai. Allah yace tabbas haqiqa tashin Alqama ya kusanto tunda wata ya tsage. Tsagewar wata alamace daga cikin almun tashin alqiyama wata rana mutanan makkah sukacewa ma'aiki s a w zasuyi imani dashi idan har yakira wata ya sauko yatsage biyu. PAGE 06 Yau muna alkhamis siddah ga watan muharam shekara ta 1447 hijiriyya. Kamar kullum ina maku nasiha yau nashihata akan ayar farko ta suratul qamar wato Surat wata. Da sunan Allah mai rahama mai jinqai. Allah yace tabbas haqiqa tashin Alqama ya kusanto tunda wata ya tsage. Tsagewar wata alamace daga cikin almun tashin alqiyama wata rana mutanan makkah sukacewa ma'aiki s a w zasuyi imani dashi idan har yakira wata ya sauko yatsage biyu. Manzon Allah s a w yakira wata kuma ya tsage biyu aya yasauka kan dutsi aya kuma yashiga cikin jikin Annabi s a w ta angaren dama yafita ta hagunsa ya ha e da an uwansa ya koma sama. ammah mai makon suyi imani sai sukace abari mutanan da suka tafi fatauci gobe zasu dawo sai muji idan suma sunga watan ya sauko yatsage sai muyi imani haka kowa ya watse goben tanayi sai ga garin makkah yacika da ba i yan kyauyukan makkah duk su shigo sunata tambayar mutane jiya munga wata yasauko yatsage biyu daya ya sauka a dai dai dutsin uhudu miya faru ? matafiya suka shigo kafin atambaye su suka fara tambayar akan watan. Kuma suka tabbatar da sunga saukowar wata. Ammah wanda sukasa akira watan sai sukace tabbas sihirine kuma sirin muhammadu mai game duniyane. Yan uwana amusulunci kuma ana ina mai karga in ku akan duk abunda kaga wani yayi wanda kai bazaka iyaba ka kyaryatashi idan baka yarda ba ka barshi a baka yardar ba ammah karka aryatashi ko ka kafurtashi. yau abunda yafaru a wannan zama namu shiyasa nayi wannan jawabin domin ni mahaifinku kafin nayi hizzib biyar ana Aminu yayi