Sashe 3
Jannatan Wa Harirah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yaji da sauri ya jaye hannunsa saboda tuna da yayi da wani Abu. Cen yaji tace dan Allah kayi haquri tana hada hanuwanta biyu alamun roko nan fuskarta ta bayyana da sauri yace harira. Cikin tsoro tace suna jannat dan Allah kayi haquri hankali ta a tashe dan ganin jinin da ke kan fuskarshi da jikinshi ta dauka na wayanda ta kadene yanzu. Ai suman tsaye yayi jinshi ya dauke ganin yaqame kamar gunki yasa ta juya motar ta fece duka sun ganta kowa sai kiran harira yakeyi ammah aminu sai da suka daukeshi suka dorashi kan mashi. Har suka qaraso gida baice komi ba kawai wucewa yayi yanufi gida. Muda yace mai gida tsaya munwake maka jinin nan kar hankalin yan gida ya tashi. Tsaye yayi suka zuba mashi ruwa suka yi wanke jinin duk da bai fitaba sai da sanyi ruwa ya tashi sannan ya dawo hayyacinsa yana tunano abubuwa a baya. Nan yace ka barshi zan shiga ciki na sauya waya nayi wanka kuje kuyi sallar azahar idan anyi sallar la'asar kudawo. Aminu yana shiga gida ya cire rigarsa ya saka aciki wani bokiti dake baki toilat yacire dogon wandonsa ya jefa aciki yawuce cikin gidan kanshi a sunkuye yawuce dakinsa ya sauya kaya kwance yayi yana tuna nan jannat dake kama da harirar sa. Ita kuma jannat tana komawa gida ko parking batayi ba ta fito shiga ciki tawuce parlourn nata momeeey na magana ammah ina batajin momeeyn nata. Haka ta shiga cikin dakinta ta wuce toilat ta sakarwa kanta ruwa. Sai da sanyin ruwan yashigeta sannan ta sauke nannauyar ajiyar zuciya ta kai dubanta ga hannun ta wanda aminu ya riqa nan taga jini takama wanke wajen har saida yayi ja. Cikin zuciyarta take tambayar kanta waye wannan wanda ya riqa hannuna inba aljani bane wane mutun ne zai riqa hannuna haka Ammah har bugun zuciyarsa sai da naji a nawa hannun nifa har gudun jininsa inaji a lokacin bugun zuciyata da tashi bugu daya sukeyi haka jinmu tamakar wata gaba ta jikina haka naji jikina haka nakejin hannunsa. Jin shigowar mama ta katse mata tunanan ta dan tashiga tana kiran sunanta. AMINU. Mama zulaice ta shigo dakin tace. Ina wuni aminu nakawo maka abinci ? Jin bai amsa mata ba yasa ta kai kallonta gareshi taga yana ta murmushi gashi kwance yana kallon silin. Juyawa tayi ta fita dakin mama larai tashiga da sallama. Mama na zaune ta amsa sallamarta. Shiru mama zulai tayi sai da larai tace ina fatan dai lafiya naga kin shigo kinyi tsaye bakice komi ba. Zulai tace wallahi lafiya qalau yayan su aminu ne ya dawo to nashiga nace mashi na kawo mashi abince baice komi ba ammah kuma naganshi yanata murmushi. PAGE 03 AMINU. Mama zulaice ta shigo dakin tace. Ina wuni aminu nakawo maka abinci ? Jin bai amsa mata ba yasa ta kai kallonta gareshi taga yana ta murmushi gashi kwance yana kallon silin. Juyawa tayi ta fita, dakin mama larai tashiga da sallama. Mama na zaune ta amsa sallamarta. Shiru mama zulai tayi, sai da larai tace ina fatan dai lafiya naga kin shigo kinyi tsaye bakice komi ba. Zulai tace wallahi lafiya qalau yayan su aminu ne ya dawo to nashiga nace mashi na kawo mashi abince baice komi ba ammah kuma naganshi yanata murmushi. Dariya mama larai tayi tace Allah yasa dai lafiya. A'a lafiya qalau fa inaga fa ya fara soyayya. Soyayya kuma wace mai sa'ace haka Allah yabata nasarar fasa wannan dutsin ? Dariya zulai tayi tace aiko ansamu wace keda gudumar fasa wannan dutsen wai Aminu ya fara soyayya aiko da nafi kowa murna muddun aka samu yar sa'ar da tayi nasara shiga zuciyar shi. Tashi larai tayi zulai na biye a bayanta suka shiga dakin da sallama bai amsa ba kawai sai murmushi yake tayi shika dai abun Dariya ma ya basu. Dariyarsu tasa ya dawo hayyacinsa yace mamana kece da mama zulai ? Mikukewa dariya ? Mama zulai tace yaya Aminu wacece wannan dan Allah ka fada man sunan yar sa'ar nan. Cikin jin kunya yace bari nayi sallah idan na dawo zan fada maku. Mama larai tace tofa zancen ki da qamshin gaskiya zulai wata ta kwamashe zuciyar dan nan naki. Zulai dariya tayi ta fito cikin akin ta zuba mashi ruwa a buta kafin ya fito sai gashi sanye da irin kayanda yacire ta miqa mashi butar harda dan duqawa murmushi yayi yace. Mama zulai kenan nace ki daina duqa man ammah kinqi ko ? Dariya tayi tace yaya Aminu kenan nariga nasaba shiyasa. Alwala yayi zai fita yaga kayanshi cikin bokiti kamar yadda yabarsu yace mama zulai ina mashkur ? Inaga baya gidan nan wani Abu kake so ? Dama kayan nan da suka aci nake son ya sawo omo ya wanke man. Ayya to bari nasa akirashi sai ya wanke maka. To nagode yace ya fita cikin sauri ta dauki bokitin ta fara wanke kayan ita dai tana son farin cikin Aminu haka take mashi aiki kamar shine mijinta ba malam ba. JANNAT Zaune take gaban mama ta Kasa cewa komi gomi na tsatsafo mata duk da (A/C) dake kunne. Mama tace kinga fada man mike damunki baki da lafiya ne ? Girgizata mata kai jannat tayi, alamun a'a. a jikinta mama tayi, taji yayi sanyi sosaiii tace cikin qawayanki wata ta rasu ? Shima girgizata kai tayi alamun a'a. To miya faru, gashi kina zufa, kuma jikinki najishi da sanyi ? Fashewa da kuka jannat tayi. Mama tace banson iskanci, miye na kuka, ki buda baki kiyi magana inata tambayarki kinyi man shiru sai girgiza man kai kikeyi kamar wata qadangaruwa, ko wadda aka yankewa harshe. Daqar jannat tace, mama kiyi haquri wannan fitar da nayi nabuge wasu da mota. Mama tace inalillahi wa ina ilaihi raji'un, sun mutu ne ? Aa mama inaga basu mutu ba ankaisu asibiti naji wani yace akaisu asibiti wallahi mama naji tsoro sosaiii rungumeta mama tayi, tana bubbuga bayanta, alamar rarrashi. Kwashe komi tayi ta fa awa mama. Mama ajiyar zuciya ta sauke tace mungowa Allah. Jannat tace mom wallahi har yanzu inajin motsin hannunsa akan fatar jikina mom wallahi da ya kama hanuna sai da naji hannunshi Kamar hannun nasa yanitse cikin jikina, ba a iya fatar jikina najishi ba har atsokar jikina da qashina naji mom, har bugun zuciyarsa naji a tawa zuciyar, mom inajin gudun jinin jikinsa a hannuna, a lokacin da yake riqe da hannuna, da yacere hannunsa a nawa jinayi kamar an zare wata ga a ajikina. Mom bansan ya akayi ba nidai nagan ni a gida kawai. Mom mi ke faruwa danine mom idanuwansa da nakallah ba tsana, ko rashin sani nagani ba, na ga mamaki a shinfi e akan fuskarshi, mom wallahi duk yadda nake kama da dady wannan yafini, da dady na wallahi da kunta a haihuwa wani kamin Ni ko bayan ni da nace tabbas wannan an uwana ne, kawai dai naji ya kirani da wani suna wai harirah, gaban mom ne ya fadi. Tace tsohone ? Aa matashi ne ammah ga alama baya da aure ma ammah zai kai shekaru 35 haka ko zai kusa kaiwa. Momeeey tace. kin tambayi sunansa? Ko kinji ankira sunansa ? A'a mom jannat ta fa Momeeey ban ji ankira sunansa ba kuma a halinda nake ciki bansamu damar tambayar sunansa ba inaga kamar yasani ko yasan wata mai kama dani shiyasa yakirani da sunanta harira hakan ka ai naji ya fa a mom. Cikin tashin hankali mom ta tashi, ta fito akin jannat, ta nufi akinta, ta shiga tana neman wayarta, cikin tashi hankali. ANGAREN AMINU KUWA. Shigowa yayi bayan ya dawo sallar azahar ya tarar da mama zulai na shanya kayanshi yace mama zulai ba nace kidaina man aiki ba ? Kinsan idan baba yagani zai man fa Aminu kenan ba abunda mallam zaiyi dan nayi maka wanki ai rashin uwa kesa ayi uwar daki dan bana da aiki yaune yasa nayi maka wanki dan naga mushkur bayanan. Murmushi mai sanyi yayi yace nagode sosaiii. Hajarace tafito akinta tace kawuce ciki qannanka habibu da matarsa suzo jin kadawo sukazo ganinka. Cikin farin ciki yace an uwa mai da i kenan ina surukar tawa ? mama hajara tace tana akin ashibilo annanka mata ma sunzo da yaransu suna Baban aki. Takawa yayi yashiga baban aki anan yatarar da ananan nasa mata da yaransu. Nan Amina da khadeeja da Fatima suka tashi suna ga YAYA ga yaya samu da zuwa yayan mu da fatan kadawo lafiya. Yaran nasu ne kowa ya gaisheshi nan yace ina uwar surutu ko maku zo da ita bane ? Dariya AMINA tayi tace yaya kenan da ita muka zo ammah sun fita da habibu. Tare da matarshi yazo shima ta dakin mama ashibilo taje yin sallah. Nan ya zauna suka dan taba fira. Sai ga habibu tare da wata kyakywar yarinya mai kyau irin kyanta mai sanyi ne. tana ganin Aminu ta rugu da gudu tayi tsaye ta rungumeshi tana cewa. Kawo Babba wallahi tun da safe naso Nazo mama tace sai na dawo makaranta shine natafi Ashe abun baqin ciki zan gani a makarantar. Wallah abokiyata kuma babbar qawata masoyita jinin jikina malam qa'a'qa'u ya zagwa e mata kamar wanda Allah ya aiko haka Yakama jibgarta har sai da tayi fitsari wallah kawo ni kaina sai da nakusan suma tsabar tsoron dukan da yake mata. Cikin jimami Aminu yace kai na tausayawa wannan yarinyar. Kai dai bari kawo abun babu kyau sai ma wanda yagani yauwa kawo ina da magana dakai wai kai haka zaka tabbata bazakayi aure ba wallahi kawon qawata yayi aure har sai da ta kawo man cincin da di ilan ammah kai Dana tambayi mama yaushe zakayi aure shine tace bata sani ba idan naganka na tambayeka. Dariya yayi har da rufe fuska dan yaji kunya saboda malam ma yashigo yana jin firarsu dariya yayi irin tasu ta manta yace to kadaiji abunda fauziyya tace. Kabata amsa. Fauziyya saukowa tayi tana cewa la tsohon mijina mai furfura. Yace babban matata sannunki da zuwa gidana. Nikam ba matar ka bace ni matar masu sabon jinice yanzu, ada dai nake matar ka yanzu kam mama saki ukku dan likkafa taci gaba kai ya fito