Sashe 4
Jannatan Wa Harirah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
cikin kwali ga Matan kanan su hudu kaji dasu nikam nayi nan. Wucewa tayi tana cewa kawo baba zan dawo idan tsohon nan yafita na karbi tsarabata. Mamanta amina tace zan maki dukan tsiya Baban namu ne tsoho. Dariya sukayi mallam yace to yanzu dai ka dawo ya kamata kayi aure dan Allah. Ka duba habibu gashi nan yayi aure. Baba zanyi shine ma yanzu ya dawo dani. Ashibilo ta fito tare da matar habibu gaishe dashi matar habibu tayi ya amsa cikin fara'a yana sawa auren su albarka. Cewa yayi kowa yazauna nan take kowa ya zauna dan kowa yaqaqu ya jin maganar auren Aminu, mama zulai tasake tambayarsa yar ina ce miye sunanta ? Bayan sun zauna cikin natsuwa yace sunanta harira Ammah yau ahanyata ta dawowa naga wata mai kama da ita sak sai dai ita inaga yar mai kudi ce dan a cikin mota take tace sunanta jannat nan ya kwashe komi ya fada masu har musuluntar wayannan azzaluman. Malam yace ammah kasan ba ayaqi a wannan watan mai alfarma ko ? Yace baba ba yaqi bane wannan fadane ai, saboda yaqi tsakanin gari da gari ko qasa da qasa ko qabila da qabila ammah wannan tsakanin mutanan daji ne da manoma kuma anyi nasara tunda fiye da mutun ari 200 sun musulunta. Allahu Akbar kowa yace. Sannan yace to zance harira kuma acen dajin illela akwai wani daji dake mararar bar Nigeria da Niger to a cikin dajin muka shiga muna farauta munfara kama dabbobin ciki sai muka fada hannun wasu mutane. Ashe dajin nasune suna nada wata sarauniyace mai tsananin karfi da tsafi. Shigar mu dajin Ashe an daure dajin sai dai a shiga ammah ba'a fita ciki munyi farauta mun gama kama dabobin mun ibi kayan marmarin da zamuci kawai muka kasa fita muna ta kewayan dajin anan wasu macizai suka kewaye mu sai ga mutane sun fito sun kewaye mu kowa da kibiyarsa dawasu kalar tufafi ruwan ganye dawani tsanwan Abu agoshin su mai sufar maciji sai haske yakeyi. Haka suka tasamu gaba har gaban sarauniyar su, hada idanuwa da nayi da ita sai naga kamar Gwaggo tace huraira tsaye a gabana sai dai ita wannan bata da jiki kuma baqace mai kyaun gaske sannan budurwa ce iyakarta shekaru shabakwai. Umurni ta bayar da cewa a rufemu a cikin kurkunta haka aka sakamu cikin kurkukun tsawon kwana ukku sannan aka fito damu anan akace waye Babba a cikin mu nace nine aka fiddo dani sauran aka mayar dasu a cikin kurkukun aka bani wakiyata nan take aka fitar da jarumai wa anda duka kamosu akayi kamar yadda aka kamomu. Akace duk wanda yayi nasarar kashe abokin karawarsa yatsira idan yana son ya tsiratar da mutanensa to zai sake karawa da wani jarumin aciki idan yakashe shi to ya tsiratar da yan uwansa. Anan kowa yaja abokin karawarsa muka fara bugawa na lura da wanda nake fa a dashi yana da sihiri a jikinsa hakan yasa na karanta ayatul kursiyu abayyane nan take har sarauniyar sai da jikinta ya kama rawa suka toshe kunnunwansu. Haka n yasa bayan na gama karantun makami mashi sara a wuya nan take kansa ya ya i a asa baqara karawa da wani shima ya tabarshi biyu hakan yasa aka kamani aka kaini gaban sarauniya nan ta fara tambayata. Miye Sunanka ? Nace Aminu tace wa anne kalmomin tsafi ne makaranta yanzu ? Nace ba kalmomin tsafi bane ayar alqur'ani ce. Nan tace aje dani a wani gurin dan ta tabbata duk wanda yashiga baya fitowa ba ta a saka wani bil adama ba komi tsafinsa ya fita. Wata babbar rijiyace aka jefani acikin rijiyar akwai wata babbar zakanyace wadda ban ta6a ganin zakanyar da tayi girmanta ba. Bayan an jefani a cikin rijiyar nan na fara neman kare kaina ita kuma tana qoqarin sai ta rauratani kamin ta cinyeni na lura bata jin yunwa hakan yasa take son raunatani. Bayan najima ina kare kaina naji na fara gajiya hakan yasa na fara kaimata nawa martanin nafara kai mata sara tana gocewa tsalle nayi na taka turkenda take daure ajiki nayi sama sosaiii nace bismillahi rahmanin rahim na sauke mata wakiyata a tsakiyar kanta kawai ta rabe biyu. Anan naga kowa hankalinshi ya tashi nan suka zu e makaman su suka durkusa kan guiwuyin su. Budewa akayi nafito daga cikin rijiyar ashe komi dake faruwa suna gani a allun tsarin su nan aka akaini wani guri ni da abokaina aka kawo muna abinci makaci mukayi wanka bayan mugama hutawa mun gabatar da sallolin da ke kan mu mukayi sallar isha duka atare muka kwanta. Cikin dare aka shigo inda muke akace nazo sarauniya na nema na nan na tashi nabi bayan an aiken har muka isa fadarta. Tabbas fadarta babbar fadace tasha ado, ga macizai nan ta ko ina, suna sunkuyar da kai agareni alamar jin jina. Na tarar da ita cikin fararen kaya komi na fada kuma farine macizan ne kawai baqaqe Amman na kusa da ita fararen macizaine. Anan tanuna man kujera tace na zauna . Bayan na zauna tace ni sunana harira nice sarauniyar wannan gari baki daya wannan dan uwana ne hari tanuna man wani qatun maciji ba i shine an uwanta tanuna man wata macijiya fara tace itace matar an uwanta. Macijin zuwa yayi yakewayeni yana kallon idanuwa nima haka gama kallonta yakoma kusa da ita yatsaya tace dan uwana ya aminta da kai. Tasowa tayi ta qaraso wajena ta zauna takamo hannuna nan naji irin abunda naji Dana riqa hannun jannat ayau. Cikin sanyi murya tace man tabbas tana sona kuma nine wanda zata aura. Nace mata Ni bazan aureta ba saboda ba addinin mu aya da itaba sannan ita mai tsafice Cewa tayi zata iya shiga addina dan ta aureni yanzu dai itama ta musulunta kuma yanzu haka tana jiran dawowata dan naji a aura aure muna aure. PAGE 04 Tasowa tayi ta qaraso wajena ta zauna takamo hannuna nan naji irin abunda naji Dana riqa hannun jannat ayau. Cikin sanyi murya tace man tabbas tana sona kuma nine wanda zata aura. Nace mata Ni bazan aureta ba, saboda ba addinin mu aya da itaba, sannan ita mai tsafice. Cewa tayi zata iya shiga addina dan ta aureni, yanzu dai itama ta musulunta, kuma yanzu haka tana jiran dawowata dan naji a aura aure na da ita. To kunji abunda ya dawo dani. Malam yayi ajiyar zuciya yace, to yanzu zata yadda ta dawo nan da zama ? ko kuma acen kaima zaka zauna. Aminu yace, tace idan na aureta acen zan zauna. Malam yace aa ni banyarda ba dole kadawo kusa dani ka zauna dan yanzu ko yarta bazan aurawa wanda ba an garin nan ba, bare kai ka auro wata yar wani gari kuma kazauna da ita acen. Aminu yace, dady kenan bazaka amince na aureta ba ? Eh bazan amince ba, idan kuma ka aureta to ka zauna acen karka sake dawowa dan babuni babu kai. Fashewa da kuka amina tayi, tace baba dan Allah. Dakatar da ita yayi yace, karki roqeni, nagama magana, sai yaza a ko mu ko ita. Malam ya juya zai fita, yaji muryar zulai tana cewa, mallam karkayi haka, akan ana, nasan kafiya ba halinka bane, wannan ma kana da dalilinka, ammah dan Allah karka ce ya rabu damu akan burinsa. Juyawa tayi ta kalli Aminu tace, yaya Aminu yakake jin harira aranka ? Aminu yace ina jinta takam rayuwata, wallah baba bazan iya za ar wata ba akanku, ammah tabbas idan na rabu da harira zan rayu cikin ku tamkar matacce. Mama zalai tace, dan Allah malam ka fada muna dalinlinka na yake wannan hukuncin, kuma ina neman kasassautawa ana wannan hukuncin, domin kafini sanin akan yana da damar ya aureta, sai dai muganshi tare da ita. Ko yazauna cen, sai dai miji labari, Ammah tunda kaga ya dawo, to tabbas yana neman amincewar ka. Kasan waye Aminu, da kafiyarsa. Malam juyowa yayi, idanuwansa cike da hawaye yace, tabbas hakane, Ammah bana son na rabu dashi, dan nasan yadda yake sonta zai iya rabuwa damu akan ta, nikuma bana son yadda na rasa dan uwana Usman da yar uwata huraira, narasashi shima. Zulai tace malam zaka yadda idan ita harirar ta yadda da ta dawo nan da zama ? Cewa yayi na amince, tabbas malam yana son zulai, duk da itace macce mai qananan shekaru a cikin matansa, kuma matan nasa, suna shayinsa sosaiii. Ammah ita zulai tana iya magana dashi akowane irin yanayi yake ciki. Zulai tace to zamu shirya muje muganta, sai ayi auren mudawo da ita. Dariya kowa yayi habibu yace sai mama zulai farar uwa. Dariya malam yayi sosaiii, anan Fauziyya ta shigo, tana cewa miyasa mijina mai furfura dariya haka ? Kama hannun malam tayi tace naji ana maganar aure wazaiyi ? Malam yace kawonki babba ne zayyi aure. Zamu tafi gobe garin da matar take. Kama ha6a tayi tace, aiko akwai magana yau, zan fadawa qawayena, kawo na aure zaiyi basunce babu maccen da zata aureshi ba ? Dama nace ai kowace warya da abokin gurbinta, tabbas kawo aminu shima Allah zai kawo mashi mata. Juyawa tayi ta kalli Aminu tace, natayaka murya yanzu dai muje kabani tawa tsaraba. Malam yace kibari muyi addu'a to . Dafe kai tayi tace, shifa gidan mallam haka yake, to kuyi ku gama azo abani tsarabata. Khadeeja tace ke wai mizaki bawa kawon naki, matsayin gudun mawar aurensa. Fauziyya tace, mama khadeeja wannan sirrine, tsakanina dashi, ai ba sai kowa yaji ba. Mallam yace harda ni Mijin naki bazanji ba ? Dariya tayi tace tab harkai ma bazakaji ba. Nan sukayi addu'a suka shafa, Fauziyya ta kama hannun Aminu suka fito yace, yanzu lokacin sallar la'asar yayi, bari nayi sallah idan na dawo sai na baki tsarabarki. Da to, ta amsa mashi, ta auki buta, ta zuba mashi ruwa, ta bashi yayi alwala suka fita harda malam da sauran yaran gidan. angaren Jannat. Momeeen jannat kuwa tana shiga, ta dannawa mijinta kira yana office yaga karanta, ya auka yace, fatan dai lafiya ? Tace wallah ba lafiya yarinyar nan tafita, to ta dawo nan takwashe komi ta fada mashi. A cikin tashin hankali a muryarsa yace kibari nadawo, zanmuyi magana,