← Book details Jannatan Wa Harirah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 10

Sashe 1

Jannatan Wa Harirah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Root Entry WordDocument 0Table Data JANNATAN WA HARIRAH MALLAKIN ASRAL. MY WHATSAPP NUMBER +2349135641310 Wannan labarin qirqirarrene banyin shi dan cin zanfin kowa ba Allah yasa mudace da Alkhairi dani da ku Ameeeen. PAGE 01 Dasunan Allah nake farawa Allah kayi salati ga shugaban halitta annabi Muhammad s a w da iyalansa da sahabbansa Allah yaqara masu yarda. Ina farin ciki ina miqa cikkiyar godiyata ga Allah da ya bani iyalai maza da mata mahaddatan Alqur'ani da wanda basu haddace ba ammah sun sauke alqur'ani suna kan haddacewa da kuma wayan da ke kan hanya sauka tabbas ba wayauna bane ba dabara ta bace Allah ne ya qaddara man haka ina godiya sosaiii akan wannan ni'ima Allah ya maku Albarka kuda iyayanku mata dasu tayani wannan aikin dani kaina mahaifin ku. Duka kowa ya amsa da ameeeen. Sai da kowa yayi tsit sannan Malam yacigaba. Yau mun kammala saukar Alqur'ani wadda mukeyi duk bayan kwana ukku wadda muka sabayi ayau zan maku nasiha akan abuwa kamar yadda nasaba ko da yaushe Allah subuhananahu wata ala yace. Kukare kanku da iyalanku daga shiga wuta. Wannan magana ba tawa bace maganar Allah ce sannan akwai abubuwa da dama da mutun zayi dan yakare kansa da iyalansa daga shiga wuta na farko sallah yaku ahalina karkuyi wasa da sallah dan rashin yin sallah ba a lokacin ta ba shine wasa da ita kuma wasa da sallah musamman gareku mata domin su maza sai nasakasu gaba muke zuwa sallah ammah ku mata bana da sani akan yadda kuke ibadar ku dan haka larai hajara ashibilo da zulai kune iyayan wayannan yara dan Allah kuqara kula akan su nasan kunayi. Sannan dan Allah karku raba man kan yarana yadda suke ahaka tamkar uwa daya ta haifesu ku barsu a haka dan Allah fatana Allah ya biyaku da gidan Aljannah. Suka amsa da Ameeeen insha Allah. Yau muna larabane biyar ga watan muharram hijira fiyayyan halitta annabi Muhammad s a w nada shekara dubu aya da Dari hudu da Ashirin da biyu wannan shekara ana karanta da khairiyya dama shekarar da ake cewa khairiyya shine shekarar da aka farata ranar litanin laraba alkhamis juma'a ma'anar khairiyya mai alkhairi dan ta fara a ranar alkhamis. Wannan wata na muharram yana daya daga cikin watanin masu girma abubuwa na farin ciki da baqin ciki sun faru a cikin wannan watan ba'a yaqi acikinsa kuma a wannan watan ake azumin tasu'a da asura wanda annabi s a w ya sunanta muna shi domin ya tarar yahudawa na azumin goma ga wannan watan sai ya tambayesu shine suka fada mashi cewa sunayin azumin ranar domin a ranar ce Allah ya kubutar da annabi musa da mutanansa banu Israel' daga zaluncin far'auna kuma a ranar aka hallakar da fir'auna. Sai manzan Allah s a w yace aiko mu yafi dacewa da muyi wannan azumin dan haka idan ni yanzu na kame bakina zanyi azumin wannan shekarar idan shekara tagaba tazo sai nayi na ranar tara ga wata da goma ga wata. A wannan watan kuma Allah ya halicci ararshi da kursiyu da alaqamain kudura da lauhul mahafuz. A wannan watan kuma mukayi rashin shugaba na garshe a cikin jagoranci musulunci na duniya wata jikan annabi s a w Hussaini dan Aliyu dan Abu dalib dan Nana fadima yar Muhammadu rasullullahi s a w a karbalah. A irin wannan watan ne bayan shekara goma sha bakwai Autar mu takirani. Da farko dai ni sunana abubakar Ibrahim ina da qanne wanda ke bina mai suna Usman Ibrahim sai Autar mu wadda aka Haifa a lokacin ina da shekaru shabiyar aduniya Usman kuma Yana da shekaru goma bayan haihuwarta mahaifiyar mu Allah ya karbi ranta hakan yasa Baban mu yasaka mata sunan mahaifiyar mu hurairah muna sonta sosaiii. Alokacin da huraira takai shekaru biyar mahaifin mu ya rasu munyi kuka sosaiii daganan qanena Usman yace zai bar garin nan yatafi neman kudi naso na hanashi a lokacin ammah ina yatafi ya bar ni wanda har yanzu bansan inda yake ba na dauki Kanwar mu da muke cewa waleeeda hakan yasa bayan rasuwar mahaifin mu da shekara daya nayi aure na auri larai dan lokacin inada shekaru ashirin da daya waleeeda nada shekara shiddah. To hardai ta girma itama tayi aure ta auri wani almajirina anas to bayan rasuwar mahaifin sa ne yakuma gida tare da ita damuwar waleeeda akan rashi haihuwane dan tafi shekaru bakwai bata ko samu ciki ba anan nan wata rana Allah yacika burin waleedah ya albarkaceta da samun ciki tazo har nan gidan ta sanar dani munyi farin ciki nida larai da hajara da ashibilo lokacin ban auri zulai ba kwatsam rana irin ta yau ta kirani cikin farin ciki tana fada man ta haihu ta haifi yan ukku sai dai biyu matane daya namiji ne matan duka mutane ne ammah namijin macijine. Hakan yasa duk mutanan yankin sukaji haihuwar da wanda suka santa dama wayanda basu Santa ba. Takirani bayan sunan yaran tace an saka masu hassana da husaina da alsasaini ta fada man zata kawo man su dukan su nagansu. Tun daga ranar bansake samun wayarta kuma natai garin basameta ba bansamu Mijin nataba har yanzu basan inda inda take ba koda ko labarinta kamar yadda narasa Usman qannena haka narasa yar uwa ta waleeeda wadda idan naganta nake tunawa da mahaifiyar mu Allah ya mata rahama. Ina rokon Allah ya bayyar man dasu idan kuma suma basu raye Allah yamasu rahama ya gafarta masu yasa aljannace makomar su damu baki daya. Kowa ya amsa da ameeen. Malam yace larai abamu abunci dan Allah muci. Larai ta tashi tana murmushi taje ta kawo abinci zasu fara ci yace na manta ban fada maku ba ku dinga saka yayan ku cikin addu'a Allah yashirye shi ya rabashi da wannan halin. A baban tray aka kawo abinci manya yaransa maza suka sauko suka saka hannu tare malam akaci tare dashi. Su kuma qanana aka zuba masu nasu. Sannan matan aka zuba masu nasu sukaci yaransa mata goma shadaya ne shidda an Aurar dasu biyar ne yanzu a gabansa. Mazan kuma su 19 daya yayi aure habibu Aminu shine babban yaron gidan shine ake cewa ayiwa addu'a Allah yashiryashi. Akwai mahaddatan alqur'ani su biyar bakwai kuma sun sauke sun fara Haddad suma Bayan sun gama cin abinci kowa yafito tsayawa sukayi cak ganin yaya aminu ya shigo. Nima kallonsa nayi, Aminu faffa an mutune, ga tsayi, yana sanye da rigar saqi, damatsansa a waje, hakan yasa nagane ba qaramin mur an jikine dashi ba, ba ine yanada saje afuskarsa yana da dara daran idanuwa, gasu farare ba in kwayar idanuwansa, ba ine sosaiii harshe i sukeyi, masha Allah hancinsa kuma har baka, la ansa ba ene suma, haka aka haifeshi, dan Aminu ko goro bayaci balle shan taba da sauran kayan maye. kallonsu yayi yace lafiya kuka tsaya kuna kallon mutane kowa ya wuce Yakama aikin gabansa. MALAM ne ya fito sukayi ido biyu da aminu sunkuyawa yayi yace. Baba ina kwana fatan nasameku lafiya. MALAM yace lafiya qalau dan larai haka yake kiransa idan yana son tsokanar an nasa. Murmushi Aminu yayi dan kiransa da an larai malam ne ka ai ya isa yakirashi da wannan sunan. Aminu ina ka tafi yau watan ka ukku bansakaka a idanuwana ba. Baba ina nan lafiya qalau wallah mun fita farauta ne har mun kusa shiga Niger ammah dai yanzu gani na dawo baba. To Allah yayi maka Albarka dan Allah ka daina wannan abun yanzu dubi gashin kanka dubi shigar jikin ka sannan wayannan maka man banta a ganin su ba ban ta ajin sunansu ba. Dariya aminu yayi yace Babba wannan shine hanwaqi wannan kuma kwakiya wannan kuma kasanshi gariyo ne da barandami ga adda wannan kuma wuqace mai zarto. MALAM yace to ni ban tambayeka suna yan su ba dan Allah ka daina wannan kayi aure. Gaban Aminu ne ya fadi jin malam yace yayi aure ya kama yaji wani sanyi cikin zuciyarsa tunawa da yayi da wadda yake so. Yace insha Allah baba nan bada jimawa ba zanyi aure. Allah yayi maka Albarka tashi kashiga ciki. Larai larai malam ya kwalla mata kira. Naam malam Kizo ga danki nan ya dawo ki zubo mashi abinci yaci shima tunda ya makara mun kammala cin namu da tare Zamuci. Cikin farin ciki larai tafito daga kitching dan ganin yaron nata dauke take da abinci ta shiga daki Yana tsaye cikin dakin yana rataye jakarshi. Kama hannunshi tayi ya juyo yana kallonta yana murmushi yace. Mamatah. Ina kwanah. Bata amsa gaisuwarshi ba tace dan Albarka zauna kaci abinci yace to sai da yakammala cin omamen tuwon yace. Mamana bari na gaishe da mutanan gidan nan kuma zan fita idan na dawo akwai labari. Fita yayi yashiga daki daki yagaishe da kowa cikin nishadi da farin ciki suke amsawa masu dan yana girmama su kamar yadda yake girmamma mahaifiyarsa larai. Ba ruwansa da ya girmi zulai haka yake durqusawa ya gaisheta itama bata amsa gaisuwarsa sai dai ta duqa ta gaisheshi sai dai yayi murmushi ya tashi. Bayan ya kammala yacewa mashkur yaje daki ya duba cikin jakarshi yakwasu duka Alewan da ke ciki ka kaiwa mama zulai ta rabamaku. Mashkur yace mungode yaya Allah yaqara arziki ya kareka daga dukkan sharri. Ameeen aminu yace. Sannan ya fita. A kofar gidan kuwa cike yake da mutane kowa gaishe dashi yake yi cikin fara'a da girmamawa. Haka ya wuce su ya shiga cikin wata rumfa mai kallon gidan su cikin tsan gayar mahaifin nashi acen yaje, duk da yau laraba yan makarantar tashi basu fara zuwa ba Almajiran malam ko sunyi wajen bara. yaransa suka kawo masa kujera gafaka irin ta da wadda akayita da katako mai part biyu majigini da masazauni minzali ya dauko majingini muda kuma ya dauko mazauni anan suka hadata ya zauna kowa ya shigo ya zauna tunda agurin akwai tabarma. Bayan sun hada baki duka sun gaisheshi ya amsa yace. To gani na dawo cikin iyawar Allah kuyi haquri nasan tafiyata dole a samu damuwa dan kamar na bar baya da kura dan Allah kuyafeni yanzu duk mai wani korafi zai iya fadi insha Allah zanyi iya qoqarina na magance maku damuwarku. Wani dattijo ne ya tashi yace. Yaro
Chapter 1 · 0% Book details