← Book details Inuwar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 9 OF 9

Chapter 9: What If He Walks Away?

Inuwar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 12 min read

*******
After a week su inna suka koma can kauyen su don jikin Abby yanxu da sauki an saya masa reclining wheelchair kuma hakeem xe tura magabatan sa don kai kudin auren sa da kaunar sa yasmin wacce a yanxu ta gama sakin jiki da shi sosai he
s more than a boyfriend to her, he
s her home her safe place, bata Jin zata iya auran wani daban in bashi ba domin shi din me mahimmanci ne a rayuwar ta. Duk da an bashi ita hakan be sa ya yawaita xuwa gidan su ba, bawai don ba ya so ba se don lura da yai cewa ita bata son yawan xuwan nan duk da dai shi din be ki ace ya shafe shekaru yana kallonta ba amma kuma tunda ya fuskanci hakan ya ja burki da xuwan don befi sau 4 ya xo gabadaya ba
Ammah tsaye bakin window tana hangen professional masu ginin dake ayki ka
in da na
in, yau kusan kwana uku da fara sabunta gidan nasu wanda duk aykin hakeem ne wanda shi so yai ma su tashi daga wannan gidan ammah Abby yaki, tabbas tasan cewa xuwan hakeem rayuwar su alkhairi ne ammah a ranta take Jin wannan alkhairin ba kan yasmin ya dace ya fada ba, don tunda a ka kawo zancen cewa hakeem ya na neman yasmin da aure ta kasa cikakken bacci har wani fadawa tai don bakin ciki da takai ci, gashi bata samun bacci me dadi don data kwanta se tayi mafarkin yasmin da hakeem da dansu me kama da larabawa cikin daulaa don haka duk ta tayar da hankalin ta, taya za
ai tana ji tana gani er kishiyar ta ta tafi gidan hutu ta barta da yayan ta a wahale? Da ranta da lafiyar ta bayan kuma ga ita er tata duk da tana da kananan shekaru ammah still ay ita ma zata iya zaman aure kuma ita ma tana da kyan nata ba wai ba tada shi ba. Tunanin hakan ya gama jagula mata rai, hijabi ta dauka ta fice ta nufi hanyar waje, kai tsaye gidan neighbor din ta ta shige maman daddy, tana isa ta tadda ta tana kashe charcoal alamun ta gama girki, kujerar tsuguno ta janyo ta zauna ta zabga uban tagumi, baki bude maman daddy tace
me zan gani haka ni rakiyaa? wannan uban rama da kikai fah? Kinga yanda kika koma kamar bulalar mayu?
Ta fada tana tafe hannu, wani abu me daci ammah ta hadiye kafun tace
wallahi maman daddy ko bacci bana iya yi sam abun duniya ya bi ya isha ni, kina gani fa da gasken wannan asabar din za
a saka ranar auran nan, in akai auran nan shikenan ni na zama gantalalliya marar galihu da ni da yara na
ta karasa maganar kamar zatai kuka, murmshi maman daddy tai kafin tace haba
maman hafsa? Se kace ba ke ba? Yaushe duk kikai sanyi haka har wannan dan karamun abun xe tayar maki da hankali? Ayy ni shiru nai miki inga ko zaki mun maganar ko kuma ke kin yarda ay wannan abu da ranki shisa ma ban miki maganr ba, ammah tun da kin kawo kuka gidan mutuwa to wallahi se in da karfi na ya kare gun nakasa wannan auran.
Ta fadi tana huci. A rayuwar nan ba wacce maman daddy take so in ka cire
yayan ta da kuma mahaifiyar ta sama da ammah don tai mata abun da ko en uwanta na jini basuyi mata ba don haka ko me ammah zata ce tana so bata kasa a gwiwa face ta samar mata da solution. Ajiyar numfashi ammah ta ja kafin ta kalli maman daddy tace
toh yanxu me kike gani za
Kasa kasa maman daddy tai kafin tace
kin tuna labarin wani malami da na taba baki kwanaki sanda uwar miji na ta sako ni gaba?
Gyada mata kai ammah tai tana zare idanu kafin tace mata
ehhh na tuna shi
toh gun sa zamu
shiru ammah tai for some seconds ganin hakanne ya sanya maman daddy fadin
nasan fa bakya son ayki da bokaye duk abun ki, dan haka ki kwantar da hankalin ki wannan ba boka bane ba malami ne me temakon fisabillilahi
sosai ammah ta yarda da maganar tata don ita bata son ayki da bokaye don tana gudun wannan karin maganar ta Hausawa dake cewa kaikayi koma kan mashekiya, barin ma ita da ta tara
yaya mata.
Wallahi har na ji dama dama maman daddy don da in gaya miki bana iya runtsawa saboda wannan lamarin
karki damu ayy daga yau ma har da munshari se kinyi, toh amma yaushe zamu Je?
Ta jefa ma ammah tambayar
ay ni ko yanxu ma kika ce muje a shirye nake tsaff
dariya maman dady tai kafin tace ahh harda su azarbabi a lamarin naki? Se dai ki bari gobe don se na hada karyar da zan ma baban daddy kin san halin sa da shegen kwakwkwafi
hakane kam toh Allah ya kaimu goben
daga haka suka cigaba da tsara yanda tafiyar tasu zata kasan ce
wannan Kennan
A bangaren gidan mami kuwa ita da nazli yadda kasan an zare masu laka haka suke rayuwar, karma mamie don omair tun washegarin wacan ranar ya tattare kayansa ya koma apartment din sa na nan kusa da company acewar sa wai ayki ya masa yawa ne shisa ita kuma mami ta gane cewa don daddy na nan ne ya sanya shi tafiya donko ranar da dadyn ya tafi a ranar ya dawo. Sam mamie bata damu da daddyn sa wanda tun da ya tafi be kara bi ta kanta ba wanda if da sabo tuni ta Saba da wannan halin na sa, don indai ba ita ta kirawo shi ba to be taba kiranta if kuma yai picking call din to a dacin rai yake bata amsa, wanda hakan ya samu asaline daga abunda ya faru cikin familyn nasu wasu shekaru da suka wuce. A bakin nazli mamie take Jin cewa suhaila ta dawo nigeria don ta ga picture din su a status din yusrah sistern suhaila, sosai mamie taji ba dadi don tasan aunty fiddou ce ta hana ta kiran ta tsawon wannan lokacin don ba halin suhaila bane hakan don suhaila na son mamie sosai kamar ita ce ta haife ta ita ma kuma tana ma suhailar kallon er ta shisa ma tun a wancan time din ta bada goyan baya Gun hada auran omair din da suhaila don tasan suhaila bata da wani damuwa don sam batai halin maman ta ba.
bayan dawowar omair he noticed that taste din abincin gidan ya canza, although he enjoys mamie
s dishes ammah wannan ma be san yanda xe musalta dadin sa ba, ya haddace signature din girkin mamie wanda hakan ya sanya tun ranar farkon da ya ci abincin ya shaida cewa ba mami bace tai ba ammah se kuma ya samu kansa da kin tambayar wanda yai din don he enjoyed every single spoon na abincin shisa be ma damu da tambayar ba don sosai yake jin dadin sa. Tunda ya dawo be kara haduwa da yasmin da yake ma kallon someone da take Jin kanta kamar ta fi kowa ba se watarana da yamma guraren karfe 5 ya gama ayki a system din sa jikin sa sanya da wata ash singlet wanda ta bayyana muscular body din sa me mugun daukar hankali, bakin window yaje ya tsaya hannun sa daya rike da cup din coffee while dayan kuma ya xura shi cikin gashin kansa wanda ya mugun gajiya da shan gyara yana massaging din sa a hainkali. Kanta idanun sa suka fara sauka tana tsaye jikin mota tana waya tana dan murmushin da ya sanya dimples din ta duka guda biyu lotsawa, samun kansa yai da shiga bacin ran da be san dalilin shiba, gashi kuma ya kasa barin bakin window din on top of that se ya samu idanun sa da binta da kallo, kamar ance ta daga kai sama kawai ta hango sa, ayko nan take idon su suka gauraya cikin na juna kasa tai da idon ta da sauri tana jin xuciyarta na bugun saba
in saba
in don batai zatan ganin sa ba, shima barin window din yai yana me kara saka fingers dinsa cikin gashin sa amman wanna karan ba a hankali ba rather with frustration. Can kasan makoshi ya furta
damnn it
, what am I doing? Ya fada yana me dire coffee din hannun sa kan bedside table, takaicin sa daya data hango shi yanxu se ta dauka kallon ta yake, yaja karamin tsaki yana me kara jin haushin kansa, her presence annoys him, her calmness irritates him her silence feels too present, indai yarinyar nan zata cigaba da zama a gidan nan toh dole se dai ya koma nashi apartment din
**HAKEEM**
Zaune yake kasan carpet yana cin fruits din da maid din gidan ta kawo masa, saman kujera kuma mahaifiyar sa ce wacce suke kita sa ummi ke zaune cikin shiga ta alfarma tana masa magana cikin sanyin murya
duk da nasan baka damu da zancan mutane ba ammah still ina me kara ja maka kunne da yi maka nasiha, indai kasan you can
t protect her from your family member
s bad mouth gwara ka hakura ka samu daidai hierarchy din ka, Im not againt your marriage ammah kawai ina me kara tuna maka cewa su waye dangin mahaifin ka, kaine kawai gatan ta kaine zaka iya protecting din ta kuma in ka sake ka bada kofar raini to shikenan za
a samu matsala don haka ina me tunatar da kai karin maganar malam bahaushe da yake cewa se bango ya tsage kadangare ke samun damar shiga, Kazama very strict a kan duk wanda xe takura ma matar ka
murmushi hakeem yai yana me biting apple din dake hannun sa kafin yace
I assure you mother bazan taba barin yasmin ta sha wuya ba in sha Allah
toh gwara dai, Allah yai maka albarka ya kuma tabbatar da alkhairi
ya amsa da ameen sannan ya mike don yin shirin fita ayki. Har ya kusan fita ummi tace
yauwa hakeem na manta i wanted to send you to amina
s house tun jiya amman na manta, yanxu tunda zaka fita se ka kai mata sakon pls
sosa kansa yai yace
nasan na mata lefi don na mata alkawarin sake komawa amman ban kara ba
tabe baki ummi tai kafin tace borin kanya in kaje can ka mata ba ni ba, ka bude deep freezer akwai wasu medium bucket din fura da kuma manya manya na nono ka dauki guda biyu ka kai mata sune sakon nata
tana fadin haka ta wuce upstairs..
Horn yai bakin gate din gidan, after a while se ga gateman ya leko ta karamun gate, ba jimawa kuma ya koma ya bude babban gate din don an sanar da shi cewa ya bude masa gate din. Kai tsaye Hakeem ya nufi kofar shiga parlon ya danna bell din, ba
a wani jima ba me aykin ta bude masa kofar, tai leading din sa har xuwa parlor sannan ya zauna, can se ga matar gidan ta fito, tun daga upstairs data hango sa take murmushi gamida fadin
wata sabon gani wato dan zaka angwance shisa kake tai mana yanga koh?
sosa kai hakeem yai gamida yin kasa da kansa yana murmushi, har kasa ya rissina kafin yace
ina wuni mami
se da ta zauna sannnan ta ce lafiya lau hakeem ya gida ya su rumana da ummin taka?
Sunanan kalau kalau Alhmdllh
masha Allah bara na sa a kawo maka ruwa
da sauri yace a
a mami da kin barshi wallahi i
m Ohk
to se ka sha
Murmushi yai kawai, tana fadin haka ta mike ta nufi kitchen. Can ba jimawa se ga daya me ayki tata ta taho kanta a kasa tana tafiya hannun ta rike da try din fruit da drinks, tunda ta nufo sa yake kallon ta da wani kalar expression a kan face din sa,
s This possible? What on earth is she doing here? Me take a nan gidan?
ya jefawa kan sa tamabayar da be san amsar sa ba, da kyar ya iya dake wa ya ambaci sunanan ta da wani kalar lafazi da shi kan be san cewa yana da shi ba, deep down his heart yake hoping Allah ya sa he
s wrong, Allah ya sa ba itan bace ba, se dai ina dagowar da tai ne ya kara tabbatar masa da cewa ita ce, ita ce ke aykatau a gidan cousin sistern mom din sa? Toh amman me yasa ta boye masa? Hakan na nufin ba shida amfani a gun ta da har take wannan aykin ba tare da ta sanar masa ba?. Ware idanun ta tai sosai after having an eye contact with him, bata san sa
addah ta aje try din ba ita ma ta zauna kasan carpet din warwas kamar wacce aka cirewa laka a jiki, nan take komai da ya saba fada mata ya shiga dawo mata kamar yanxu yake fada mata
Yasmin in akwai abun da na tsana a duniyar nan to shine karya, I despise it with passion, dan haka ko me zakiyi mun in future kar ki yarda kimun karya ko kuma boye boye domin ina son mu gina rayuwa me cike da farin ciki da kuma yarda da juna
tuna abun da ya fada matan ya sanya ta rintse idanun ta da karfin gaske tana jin danasani da kuma takaicin boye masa gaskiyar da tai. Tana cikin wannan halin kawai se ga omair nan saukowa daga stairs cikin shigar fita ayki, idan sa akansu ya fara sauka particularly her, fuskar sa ba annuri ko kadan kamar na yauma ya fi na koda yaushe, kafin tai wani move se ga mami tare da nazli dake ta murmushi tun kan ta hadu da ya hakeem din da da take matukar yin missing a koda yaushe. Har yanxu Hakeem that was utterly shocked be daina bin ta da kallon da ta kasa fasaara shi ba, tabbas ta san ta bata masa she could sense that, hawaye ne ya shiga bin cheeks din ta da tuni sukai jawur, not minding su mami da nazli da suka tsaya suna kallon ta da mugun mamaki banda omair da ya dauke kai kamar be san da zaman ta agun ba
IS THIS HOW OUR LOVE STORY ENDS? WILL HE WALK AWAY YA FASA AURENA SABODA BOYE MASA GASKIYAR DA NAI? NO WAY I CAN
T LOOSE HIM, BAZAN BARI NA RASA MUTUM DAYA DA YASO NI FOR WHO I AM BA
END OF FREE PAGE
Payment amount: 500 naira..
Payment details:
Account Number: 9137717568
Name: Maimunatu Idris Abdullahi
Bank: OPay
Bayan payment, ku turo receipt zuwa:
09137717568
Nagode sosai da support
inku
SummaryInformation
DocumentSummaryInformation
WpsCustomData
iPhone
Normal.dotm
TECNO LD7
WPS Office
Normal
Default Paragraph Font
Table Normal
Times New Roman
Times New Roman
SimSun
Calibri
Calibri
Z&!),.:;?]}
3081-11.37.30
e2b25752d61d4fa1977ab8e096748bc0
Chapter 9 · 0% Book details