← Book details Inuwar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 8 OF 9

Chapter 8: A Proposal She Wasn

Inuwar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 29 min read

t Ready For
Washe gari friday ta tashi da safe kamar kullum tai duk gyaran gidan da dumamen abinci, yau sam ba tada niyar xuwa ayki don so take taje ta kula da mahaifin ta. Tana cikin juya ruwan zafi a cikin wani ribabben plass se ga ammah ta fito daga daki tana hamma kamar zata hadiyi babu, direct inda yasmin din take ta nufa fuskar nan tata da taci uban bleaching a hade
uban me kike har yanxu baki wuce ayki ba?
Murya na rawa yasmin tace
daman-daman ina so in ce ko zaki fadawa mami abby ba lfy bazan samu damar xuwa ba se ya..
Marin data zabga mata ne ya sanya ta hadiye zancen nata tana yarfe hannaye, ammah na huci tace
dan ubanki so kike a kore ki a aykin koh me? Toh Wallahi ko mutuwa yai se kin je, dan haka xo ki wuce ko na kara miki wani kin san hali na, daman tun jiya ina ciki dake
ta karashe maganar tana huci. Duk abinda ke faruwa innah bata sani ba har yasmin din ta bar gidan don Allah yayi ta da dan banzan nauyin bacci don tsaf se a sace ta bata sani ba. Tana isa bakin titi taga ba motar gidan mami a inda habu ya saba yin parking, wayarta ta zaro tana kallon lokaci taga 7:48 still da sauran lokaci, tana taye agun can se ga motar ta karaso hakan ya sanya ta yin ajiyar xuciya don ta dauka ya gaji da jira ne ya sanyashi ya tafi.
A gafarce ni yau na makara wlh kin san garin akwai sanyi sosai kuma abun mamaki duk da safiya ce yau amman na tarda go slow
ya fadi hakan yana me figar motar da gudu.
ko da suka isa gidan a parlor ta tadda nazli da mami, har kasa ta durkusa ta gaishe su jiki ba kwari don har yanxu bata gama recovering daga marin da ammah tai mata ba, mami ta dube ta cikin kulawa tace
morning jasmine how
s your night
Alhmdllh
ta fada takaice, mami tace taje kitchen akwai breakfast dinki acan, godiya tai ta tashi tana jan kafa ta bar gun, mami ta maida duban ta kan nazli dake pressing phone din ta tace
je ki ki duba omair tun da ya dawo jiya be fito daga room din sa ba
haka nazli ta mike tana turo baki don jiya se da ya kusan mammake ta akan ta batai masa knocking ba. Tana shiga parlon sa taga baya nan, don haka tai yunkurin nufa dakin da tasan definitely yana can, daidai ta taba handle din kofar se gashi nan ya bude kofar, sanye yake da wani hoodie white color wanda sosai yai kyau fatar sa me kyau da sheki ta kara bayyna wanda hakan ya sanya nazli furta
woow brother kaga yanda kai kyau kuwa?
Ta fada tana kara admiring brothern na ta. Cikin dacin rai omair yace
what?
Ba komai u just look good ne as always
ta fada tana turo baki, juya kyawawan idanun sa yai gamida sakin wani karamin tsaki kafin yace
what brought you here?
Ohh mami ce, she said I should call you tana downstai..
be jira ta karasa maganar ba yai banging kofar tasa wanda saura kadan ya hada da nata face din, ayko ta koma gun mami tana hade rai kamar wanda aka daka. Cikin natsuwa yake taka stairs din idanun sa na kan smartphone din dake hannun sa, fuskar nan tasa a hade but looking handsome as always. Zama yai a kasa kusa da kafar mami ya gaida ta cikin harshen Turkish despite ya gaishe ta daxu da subh, amsa masa tai cikin natsuwa tace
are you not hungry? Na san jiya ma tun Fettuccine Alfredo din da kaci baka kara saka komai a bakin ka ba se coffe
without looking in to her eyes yace
I wasn
t hungry yesterday shisa, but I will make tea right away
yana fadin haka ya mike ya nufi haryar kitchen. isowar sa bakin kitchen din yai daidai da fitowar yasmin wacce ke rike da jug of pineapple juice a hannun ta, duk cikin su ba wanda ya lura da wani coz duk idanunsu da kuma tunanin su basa a tattare da su, wanda hakan ya sanya su yin kicibis da juna, ayko nan take drink din dake cikin jug din ya xube jikin white hoodie din nasa
Subhanallah, Im so sorry I didn
t mean to, I didn
t see you.. I
yasmin ta fada cikin tashin hanakli. Uffan be ce da ita ba se ma stepping back da yai slightly gami da kurawa stain din dake jikin rigar tasa ido wanda ya kara saka ta feeling so guilty coz expression din face din sa was unreasonable yet distant cold. Ana haka se ga mami ta karaso, bayan fuskantar abun da ya faru ya sanya ta maida kallon ta kan yasmin kafin tace
jasmin, are you okay badai ki ji ciwo ba ko?
Ta fada very gently,
ehh mami, Im sorry ban kula bane ba shine na..
Shiru tai da maganar ganin Omair ya bar gun without a single word, tai kasa da kanta tana Jin ba dadin abun da tai masa, muryar mami ce ta tsinkaya tana fadin
karki damu kanki kinji, don
t bother your self kinji? Coz it was an accident, ba wanda ya wuce yin haka
jiki a sanyaye tai nodding head din ta kafin tace
toh mami, bari ma gyara gun
tana gama fadin hakan ta bar gun ita kuma mami ta koma gun zaman ta fuskarta dauke da murmushi. Se da lokacin sallar juma
ah tai sannan ya fito don xuwa masallaci, don tea din nasa da breakfast din sa ita da kanta gai masa don tasan tunda ya koma baxe kara fitowa ba se abu me amfani sosai, mami ta dube sa kafin ta ce da shi
har ka shirya kenan?
A takaice ya bata amsa da
daga haka yai mata sallama ya nufi downstairs a ranta tana ta faman jujjuya maganganun da hajja da aunty fiddou suka kira ta suka gaya mata yau da safe. Duk da yasmin na son komawa gida ammah haka ta daure ta jira har habu ya dawo daga masallacin jumaah sannan mami ta barta ta tafi, ko da ta isa parking lot wata mota ta gani a parke very close da wacce habu ya saba daukar ta da shi, motar se faman kyalli take, daidai ta nufi motar da zata maida ta gida don habu ya ce ta shiga ta dan jira shi yana xuwa se kawai taga an bude wannan motar da batai zaton akwai mutum a ciki ba, saurin yin baya tai don ta tsorata sosai, kallo daya yai mata ya dauke kai gamida barin gurin, da sauri ta shige cikin motar tana maida numfashi don ta tsorata sosai
ko da ta isa gida ta tadda innah ce ita kadai a gidan se su hafsa da suka dawo daga makaranta tuntuni, ammah ta tafi tun safiya kaima su abby abincin kalace, itama innah yasmin din take jira ta dawo ta rakata can asibitin, ba yadda innah batai da ita ba akan da ta zauna ta ci abinci ammah se tace mata she
s Ohk ta ci a can inda take ayki, dan haka ko 10mins basu kara a gidan ba suka wuce asibitin. Da mamaki shimfide kan fuskar yasmin take kallon tilin kayan fruits, ruwa, drinks da duk wani abu da marar lafiya ke bukata a space din da abbyn yake, tambaya fall a bakin ta mah kuma ta kasa don bata fiya son yin dogon magana ba more especially da waenda suka girme mata. Jikin abbby yayi sauki sosai, ita dai da ido take ta bin gurin hoping ko zata ga hakeem ammah shiru, tanata zauna agun tana ta faman tunane tunanen da ita kanta bata san dalilin yun su ba. Muryar inna ce ta dawo da ita daga tunanin da take don ta tambayi question din dake makale a ran yasmin din tun daxu
lawal wa ya kawo duk waennan kayan alaton nan gun iye? Ko dai na waencan bayin Allahn ne suka baki ajiya?
Ta tambaya tana satarwa kallon gadon wani tsoho da familyn sa suka kusan cika dakin. Kawu lawal ya kara gyara zaman sa kafin yace
wannan dai likita dan albarka wanda ya biya kudin magani shine jiya bayan kun tafi ya jido duk kayan nan, Wallahi yaron na da matukar kirki sosai don badan shi ba da jiya yunwa ta kashe ni, se guraren 10 sanna ya bar nan gun, Ashe shima likita ne, wallahi sosai yaron ya kwanta mun a rai sosai, dabadan mariya saura wata 2 bikin ta ba ay da na nema ma mata auran sa da kaina in xe yarda kenan
ya karashe zancan yana washe hakoran sa da goro yai wa lahani.
tirr ammah dai lawal akwai ka da son xuciya wanna yarinyar taka me gutsurarren hanci zaka hada shi da ita? ina lefin ma yasaamin er kyakyawa da ita son kowa kin wanda ya rasa
hade rai ammah da kawuawal sukai Jin abin da innah ke kafa, ci gaba da magana inna tai
duk ma ba wannna ba amma gsky wannan yaro dan aljannah ne in sha allahu, jifa kaya kala kala, ya kyauta sosai Allah dai ya biya sa
duk suka amsa da ameen banda yasmin da haka kawai taji xuciyar ta na dukan uku uku. Guraren karfe 1:15 yasmin na zaune kan daddumar da innah ta aro masu gun ahalin wannan tsohon tana laxumi bayan ta idar da sallah se ga doctor sambo nan ya xo duba abby shi da wasu nurses guda biyu, ko daya gama yai ma abby ya jiki sannan ya juya dan barin gun, inna ce tai saurin dakarar da shi da fadin
dakta yaushe wannan dan albarkan ze xo ne? Wallahi ka ganmu nan duk shi muke jira ya xo mu kara masa godiya ammah kaji sa shiru
ta fada tana yake hakoran ta da suka ga duniya, Murmushi dr sambo yai kafin yace
wai doctor hakeem?
Inna tai saurin noddding head din ta ya yin da yasmin ta kara baza kunne tana jiran ta ji me dr sambo xe ce,
ayy iya laraba da alhamis kawai yake shigowa nan asibitin don a asibitin mahaifin sa yake ayki a ragowar kwanakin ammah dai zaku iya ganin sa ya xo nan din if Allah ya nufa
yana gama fadin hakan ya bar gun suma nurses din suka rufa masa baya. Haka kawai ta tsinci kanta da bacin ran da bata san dalilin sa ba, guraren bayan la
asar suna shirin komawa gida kwatam suka jiyo sallamar sa, dago kai yasmin tai da sauri ayko suka hada ido ya sakar mata murmushi iri tai kasa da kanta tana Jin heart din ta na beating very fast gefe guda kuma tana Jin farin cikin da bata aan dalilin sa ba, se bayan da suka gama gaisa wa da su innah sannan tace da shi
ina wuni
ba tare da ta kalle sa ba, amsawa yai cikin sakin fuska kafin ya maida duban sa kan abby dake kwance yace
baba munyi magana da doctor sambo yace gobe za
a sallame ka
se kima yau shiruu yana me adduar Allah ya sa ya yarda da abinda ya xo masa da shi din dan ya kula yasmin gun mahaifin ta ta gado natsuwa da kuma tarbiya gabadayan su idanun su na kan hakeem banda yasmin dake wa sa da fingers din ta ammah kunanta na jiran jin zancen sa, se da ya tattaro natsuwa sosai kafin yace
a asibitin da nake ayki akwai foundation din da suke kula da masu lalurar stroke, in ba damuwa baba zanso ka amince ay transferring din ka xuwa asibitin don kula lafiyar
tsitt kake ji, kowa na mamakin abin da hakeem din ya fada, with shock yasmin ta dago ta kalle sa, he looks so serious, ta kula ba wai don son da yake mata kadai ya sanya yake wa familyn ta hidima ba kawai dai yana yi ne don Allah, da kyar abby ya iya fadin
bawan Allah baka sanni ba ban sanka ba duk da dai ance na Allah basa kare wa ammah wannan dawainiya tayi tayi yawa, i think stroke is my destiny zan cigaba da adduah da kuma godema Allah har sanda zan koma masa kai kuma Allah yai maka albarka
abby ya fada da muryar sa da bata wani fita sosai, yasmin batai mamakin Jin abinda mahaifin ta ya fada ba don ta san halin sa baya son daurawa kowa nauyin sa,
haba malam kai kanka baka Jin dadin yanayin da kake ciki zaka ce a
a? Kadai duba ka gani wannan bawan Allah ya xo zai taimaka ammah kuma kace a
a ay be yi dadi ba abun
ammah ta fada cikin tausasa muryar da yasmin bata taba ji tayi amfani da shi ba, nan su innah ma suka saka baki da kyar abyy ya yarda da bukatar hakeem all in the name of be son ya wahalar da shi. Se da ya tabbatar basu bukatar komai sannan ya mike ya bar gun yana ma abby Allah ya kara sauki. hakeem be kira ta ba se bayan sun koma gida sannan, ko da tai picking call din rasa abun fadi tai dan bata ma son ta Ina zata fara masa godiya ba, tsaf ta gane cewa ba wani foundation ya dai hakan ne don ya taima ki abbyn,
hello your majesty?
Muryarshi me dadin sauraro ya daki kunan ta, a hanakli tace
mun gode sosai Allah ya biya ka da gidan aljannah
se da hakeem ya numfasa kafin yace
jasmine ki daina mun godiya, I did dis all because of Allah kinji? Allah ya bama abby lfy
a hankali ta furta
ameen, toh kaima Kace ameen da adduar da nai maka
Murmushi ya saki me sauti kafin yace
ameen ya rabbi jasmin
daga haka yai mata sallama dan yana da patient din da zai yi attending. Washe gari asabar akai discharging abby, ranar Monday kuma ya koma hospital din su hakeem don duba lafiyar sa kamar yadda hakeem din ya buka kuma har yau be san tana yin aykatau ba don daya tambaye ta mesa ba
a taho da ita hospital din ba se tace masa ambar mata jiran gida ne daga haka kuma be kara tamabayar ta ba har abby yai sati guda yana xuwa asibitin tare da kawu lawal. A bangaren gidan mami kuwa yasmin sosai ta maida hankali ta kan aykin ta, duk wani abun da xe sa tai crossing part da omair se da ta dakile shi don tun wancan ranar har yau bata kara ganin sa ba se dai taga giftswar sa.
NOTE: (Ischemic Stroke shine stroke din daya samu Abby caused by a blood clot blocking blood flow to the brain, wanda bai fiya effecting maganar mutum ba shisa Abby ba wani sosai yake shan wahalar magana ba though yana struggling kadan kadan)
***********
Soosai sukai sabo me karfi da Hakeem sabon da bata taba zaton cewa zatayi da wani bil adama ba, don duk rashin san maganr ta indai da hakeem ne takan saki jiki sosai saboda he
s very kind and well mannered uwa uba kuma ya iya magana. Indai ba ayki take ba toh tabbas tana makale da shi a waya, a halin yanxu komai nashi ta sani shine dai har yanxu be gama fuskantar abunda take ciki coz yasmin tayi phd a iya nuna komai ba komai bane ba don har yanxu be san tana aykatau ba. A bangaren ammah ko bata samun damuwa da ita sosai saboda inna na nan don koma za tai se dai tai a bayan idon innar. Wata ranar alhamis bayan kawu lawal sun dawo daga asibiti shi da abby da a yanxu ya fara samun sauki sosai don yakan iya motsa jikin nasa duk da yana Shan wiya kafun yai hakan wanda likitan dake kula da shi ya sanar dasu cewa baban nasarace daya fara motsakar arm da leg din sa duk da ko yana Shan wuyan yin hakan sabanin da da sam baya iya yin komai kuma baya ji ko an taba part din nasa ammah yanxu Alhmdllh har maganar sa ma ta fi na da fita, all thanks to Allah and Hakeem. Watarana kawu lawal ya sa aka kira ammah, inna da kuma ita Yasmin din dakin abby, bayan sun zauna inna tace
kai lawal lafiya muna cikin zama zakai mana kiran gaggawa haka? Kodai jikin ibron ne ya kara tashi
ta karasa maganar tana kallon abby da idanun sa ke a rufe. gyaran murya kawu lawal yai kafin yace
Lfy kalau inna don abun alheri ne ya same mu gabadayan mu
Gabadaya suka xuba masa ido banda Yasmin da kanta dake kasa, innah tace
tohh wannan wani abu ne haka iyeeh?
Kawu lawal ya bata amsa da fadin
wannan yaro de likita ya same ni yace yana neman izinin fara neman yasaamin in har ba ai mata miji ba, ni ko nan take na ce masa ba ai mata ba kuma nace na bashi dama ko yanxu yake son a daura aure za
a iya daurawa don yaron ya burge ni daya mutumtani ya xo ya same ni da wannan maganar ya kuma girmamani ya kuma nuna cewa ni uba ne a gun yasamain, haka shima uban yasaamin din yace shi bashida damuwa matukar yasaamin din tace tana so toh ya bada go ahet
ba su inna ba ita kanta Yasmin din tayi mugun mamaki da ya sanya ta dago kai tana kallon uncle din nata coz hakeem beyi mentioning xe aywatar da hakan nan kusa ba though he kept mentioning that he
s very serious about her and he want to marry her amma batai zaton da wuri haka ba don dudu basu fi 2 weeks sa haduwa ba. Inna ce ta rangada buda tana me rungumo yasmin din jikin ta gamida fadin
kai Alhmdllh Allah mun gode maka, daman ance me hakuri shi kan dafa dutse ya kwankwadi roman sa, kai madallah Daman Wallahi ina tai wa yasaamin kwadayin yaron nan dan yaron akwai hankali da mutunta na gaba da shi, toh Allah ya tabbatar da alkhairi don wannan hadi ya ma hadu don ita kanta jikar tawa bata ce a
a ba don yaron masha Allah son kowa kin wanda ya rasa, ita ma baza ma ta fara cewa a
a ba ko yasaamin dita?
Ta kare zancan tana kara manno yasmin jikin ta wacce sam hankalin ta be tare da ita coz tama rasa me za tai kuka zatai ko dariya? Da kyar ammah ta hadiye wani abu me mugun daci da ya tsaya mata a makogaro tsabar bakin ciki da takai ci, ko ba
a fada mata ba ta san hakeem dan masu hannu da shuni ne don ko fatar jikin sa ka kalla zaka tabbatar da hakan, ta ina ma za
ai haka ta faru? Ina ai baze yu ba er kishiya ta auri wannan tsalelen mutumin? kuma da rai na da lafiya na? A
a baxe yu ba Wallahi
ammah ta ayyana duk wannan abun a ranta tana me hura dan hancin. Kawu lawal ya maida duban sa kan yasmin da duk jikin ta ya gama yin la
asar kafin yace
ke! Kinji duk abinda muka fada ko? Ina fatan kema zaki saki jiki ki nuna masa kauna don yaron da gaske yake ba yaudara yaxo yi ba don yace ma nan kusa manyan sa zasu xo
shiru yasmin tai don bata san me zata ce ma wan mahaifin nata ba ga idon ammah dake ta mata yawo a jikin ta don kallon ta take kamar zata cinye ta jira kawai take ta ji me zata ce, mikewa tai ba tare da ta ce komai ba ta fice daga dakin, tana jiyo sanda inna ke sakin guda tana fadin
kai wannan abu ya mun dadi dan bakin ciki yau se dai ya mutu
kusan 10mins tana rike da wayarta karar ringing tone din wayar ne ya dawo da ita daga tunanin da take, as expected shine ke kiranta, har kiran ya katse batai picking ba and she doesn
t know why tai hakan. Gabadaya ta kasa bacci she
s feeling a little bit nervous coz se take ganin kamar zaren ba kalar yadin bane ba but still theirs something she
s feeling deep down about him something very strange something she have never felt before. Tun da ya kira sau uku yaga batai picking ba ya kyale ta kawai don be son ya takura mata sam.
Washe gari ta shirya da sassafe kamar kullum habu yai dropping din ta a gidan mami, ita tai aykin gidan kaff coz bahar ba tada lfy, tun da ta xo ta kula da yanayin mami kamar ba dadi don tayi looking kamar ita ma bata da lfyn. Tun bayan dawowar omair Nigeria familyn dadyn su omair suka tada bori sosai gami da sako ita mamin a gaba kan cewa ita ta xuga dan nata ya ce ya fasa auren Suhaila, yau wannan ya kira yai mata kalar tasa dibar albarkar gobe wannan ma ya kira yai nasa don sun so ma su xo gidan mamin amma mahaifin suhailan ya tsawatar musu don ya ce shi baxe saka omair ya auri er sa don dole ba tunda yace be so shikenan a hakura Allah ya hada kowa da rabon sa don shi sosai yake respecting feelings din mutane more especially omair da bama ka gane yana son abu ko baya so ba. A bangaren daddyn nasu sosai ya bude ma mami wuta akan cewa ita ta kitsa komai saboda wani manufa nata daban and yace mata komai omair ke yi ita ke sangarta shi, sosai abun ya bata mata rai don maganar su hajja da sauran en family be dake ta ba amman na dadyn nasu ya taba ta coz ta dauka shi ne mutum na karshe da xe yarda da wannan zancan amma se gashi yana cikin masu sukar ta. Guraren 12 lokacin yasmin na blending fresh fruits da bahar ta fada mata tai blending ta kuma yi storing a fridge taji kamar motsin mutum, da sauri ta juya ayko da saurin tai kasa da ido tai don bata son ma tana kallon cikin idon sa me bal
in kwarjini, take cikin din ya dauki kamshin turarensa me mugun kamshi, cikin natsuwa ya fara takawa cikin kitchen din hannun sa dauke da mug din da ya sha coffeen da mami ta sanya nazli hada masa, fuskar nan tasa a hade ko kallon inda take beyiba yai dumping cup din cikin sink har cup din na making sound din da ya sa ta dan tsorata kadan, daga haka ya fita daga kitchen din ba tare da ya kara kallon inda take ba. Yana fita ta koma gun cup din ta shiga dauraye wa tana me turo dan karamin pinkish lips din ta don yadda ya tsorata ta ba karamin bata mata rai yai ba. Fitar sa da kusan 3mins se ga mami ta shigo ita da nazli, shirin wani abinci suka shiga yi wanda da ka gani zaka san ba na nan bane ba, ba wanda ke magana cikin su coz har face din su looks so serious, mami ta saka yasmin din ta yanka mata fruits ayko ba shiri ta shiga yin hakan, dining din sama suka kai komai da komai da sukai, mami tace mata kar ta tafi ta tsaya ita da nazli su daura abinci don anjima kadan zatai baki, haka ko akai ita da nazli suka shiga kitchen din suna girkin ba me cewa kowa komai don nazlin ma playing wani Turkish drama tai a ipad din ta while cooking even though ma duk yasmin ce ke yin aykin. Guraren 3 aka xuge gate din gidan, da sauri nazli ta bar kitchen din ba tare da ta bi ta kan ipad din nata ba, kofar parlor ta bude ta tsaya tana kallon mahaifin nata that was on a phone call, yana karasowa bakin kofar ta nufesa tana murmushi da ya kara bayyana kyawun ta,
geldin daddy
(barka da xuwa daddy) shima ya mayar mata da murmshin gamida da mata side hug sannan yace
ol k
(na gode daughter) daga haka ta matsa masa ya shiga sannan ta amshi dan karamin trolly bag din sa a hannun habu sannan ta kullo kofar parlon. Se kallon ko ina na gidan yake, A haka har suka karasa upstairs inda mami ke a zaune tana jiran karasowar su, mikewa mami tai ta nufi in da mijin nata yake tai ma masa sannu da xuwa ya amsa mata cikin natsuwa, kallon ko ina yake kafin yace mata
where
s he?
s in his room, but would you mind taking shower, eating and resting before you dive into the matter? Coz I could see that you are tired
shiru dady yai for some seconds kafin yace
alright then
daga haka mami ta amshi trolley din hannun nazli sanan ta ce da ita ta je ta sanar ma brother din ta cewa dad din sa ya dawo. Ko da nazli ta shiga part din na sa ba ta samesa a parlor ba, don haka ta karasa bakin room din sa ta shiga knocking a hankali gamida kiran sunan sa, ta shafe kusan 2mins a tsaye a gun before ta bar gun don ta kula be da niyar budewa, ko da ta koma bata ga kowa parlon ba don haka ta wuce can kitchen in da ta baro yasmin na girki. Har daddy yai sallah yai wanka kuma yaci abinci omair be fito ba shi kuma daddy be kara tamabayar mami ina yake ba, satar jiki mami tai ta nufi part din omair din, ko da ta taba kofar se taji shi a rufe alamun ya saka key ta ciki, nannauyar ajiyar xuciya mami ta sake kafin tace
open the door
tana fadin haka ta koma kan daya daga cushion din parlon ta zauna, ayko bayan 40secs se gashi ya bude kofar, kallon sa ta shiga yi sama da kasa, sanye yake da dark brown jallabiya, ajiyar xuciya tai kafin tace
ba zaka fito ka gaida dad din ka ba?
Bace komai ba se nufar kofar fita da yai ita ma ta mike ta bi bayan sa, daidai ze murda handle din kofar aka budo kofar, daddyn sa ne ya bayya na fuskar nan tasa a hade wanda sosai kaman sa da omair din ya bayyana, matsawa yai baya sannan a shake yace
welcome bac..
ayy daddy be bari ya karasa ba ya dauke shi da wani marin da nan take fararar fatar sa ta koma jajir, ko hannu be sa a face din nasa ba coz beyi mamakin hakan ba, da sauri mami ta nufi daddy tana fadin
dan Allah ka yakuri, calm down please ka bar
da sauri ya daga mata hannu yana huci hakan ya sanya ta yin shiru tana me girgiza ma omair din kai alamun he should not act bad. Da kakkausar muryar sa ya fara magana cikin fada yana fadin
who the hell do u think you are ehh? You broke an engagement with your sister just like that, do you think our family is a joke? Ko an gaya maka cewa kai ka haife mu ne? To bari in fada maka wani abu tittle din da kake ji da shi kake kuma daga kai saboda shi ni na baka shi and if I wished zan iya amshe shi a ynxn nan. saboda
kai ba wanda ya isa da kai shine har zaka je ka samu yarinya kace mata wai ba zaka aure ta saboda tsabar baka da kirki kai burin ka kawai ka kunya ta ni a bainan nasi koh? Baka taba Jin magana ta if nace kai abu indai be maka ba toh kai ba zaka taba yarda kai ba for goodness sake me aybun suhaila da xe ce wai ba xe aure ta ba bayan duniya ta gama sanin wannan hadin eh?
Ya fada looking at mami da idanun ta suka kada sukai jajir sannan ya dauke ido daga kan ta yace
what am i even expecting from you bayan kece kika kitsa masa all these? ke ce kika ja komai kece dan hak..
calmly omair yai interrupting dad din nasa da fadin
all I said was am not marrying suhaila because Im not interested and I believed that I have the right to do so, so please sir stop blaming my mom coz she knows nothing about dis,
baki bude daddyn nasa yake kallon sa kafin daga bisa ni yace dashi
alrigh then, kaje ka auri duk wacce ka gadama if you wish ma ka zauna a haka but I promised you that bazan kara saka ka dole ba, ita da take saka duk hakan se ta san yadda zatai da kai
yana fadin haka ya fice daga dakin a fusace. Mami ce ta kalle sa kafin tace
why omair? Why would you talk to him that way? Mesa zaka ma masa magana bayan kasan duk hakan be kamata ba ehh? Kaga dai yanxu me ka ja for talking back koh?
Without looking at her yace
Im so sorry mother but I can
t resist seeing him blaming you for what is not your fault
ajiyar xuciya mami tai kafin tace
your grandma and others are coming by in the next one hour, dan haka please ka kama kankan ay komai a hankali kaji?
nodding kansa kawai yai without uttering anything coz ba abun da xe hana sa magana more especially yaga ana neman disrespting mom din sa
Karfe 5 dot motar su hajja ta iso gidan, dis time around da uncle ameen wanda ake kira da Dr kuma kani ga daddyn su omair mahaifin sulhaila and yusra se matarsa aunty fiddou da kuma hajja baba da karama, ko da suka shio gidan se faman hura hanci take har suka isa cikin baban parlon daddyn, haka nan aka shake su da kayan ciye ciye kala kala ammah ko kalla ba suyi ba gabadaya jira kawai suke daddyn ya fito suji me xe ce akan wannan alamarin daya faru. Ko da ya fito ya gaida hajja ta amsa ciki ciki, ita ta fara maggana tana share kwallar da ta xubo mata
surajo mesa kai da danka kuke gudun hada jini da xuri
ata ehh? Haka shekarun baya kai wannan abun yanxu kuma tarihi ya kara maimaita kan sa? Ko dai kaine ma kace masa ya fasa ko kuma matar ka ce tai hakan don ta hada sa da waennan en uwan nata dake kama da aljanu? Toh Wallahi in ma ita ce ko kaine dukan ku baku isa ba don aure kam se anyi shi wlh..
daidai nan omair ya karaso cikin parlon, zama yai a kasa ya gaida su, ba wanda ya amsa masa se uncle din sa da hajja da ta amsa kamar bata so, ita ko aunty fiddou ji take kamar taje ta hada kansa da hango don tama fi er tata shiga tashin hankali da wannan abu daya faru, ita kuma hajja karama bata ma san me take ji ba don ita xuciyar ta da brain din ta ma baya tare da su don ko tuni ta tafi tunanin abin da ya faru shekarun 32 da suka wuce iwal haka. Dr yai kasa kasa da voice din sa sanna
hajja me ya kawo wannan maganr pls? be kamata Ana maimaita abun da ya faru baya ba let
s bygone be bygone mun? Beside ya fadi ra
ayin sa ne kawai so ba lefi yai ba ne ba, she
s still his sister ko ya aura ko be aura ba ba abinda xe canza hakan kuma
cikin zafin rai hajja ta da katar da shi da fadin
anya ameenu ba
a canza mun kai a asibiti ba? er taka kake so ka bada gudu nmawar ballawa xuciya se kace ba jinin ka ba? Toh Wallahi kar ka kara saka bakin ka anan in dai kasan
baraka zakai
tana gama maganar ta maida kanta kan omair da tuni yaji kansa ya wani yi masa nauyi tun bayan da hajja ta fara daga murya don sam be son hayaniya kuma duk sun san da hakan don tun yana yaro da wannan dabi
ar ya tashi.
Omair
Hajja ta fada lowering her voice,
ya amsa ba tare da ya kalle ta ba, kowa na parlon kallon sa kawai yake banda mami da tunda tai kasa da kanta bata sake dagowa ba, daddy kam ji yake kamar ya gaggaura masa mari
gaya mana mesa baka son auran suhaila kuma? tayi maka wani abun ne?
Kusan 10 secs be ce komai daddy da haushi ya cika sa yace
ba magana ake maka ba
da sauri hajja ta daga masa hannu kafin tace
ba ruwan ka surajo ka daina masa tsawa
she did nothing wrong, kawai bana so ne kuma..
daga haka yaja bakin sa yai shiru. Dogon numfashi hajja ta ja kafin tace
ka tabbatar da abinda ka fada gaskiya ne ba wani abun kuma a kasa?
Gyada mata kai yai kawai, daga haka hajja tace
ya fadi iya gaskiyar sa don haka wannan magana babu ita yanxu tunda yace be so ay nasan ita suhailar na da masu son ta koh? Se ta kawo wani ai mata aure da shi
da sauri aunty fiddou ta dago kai tana kallon hajja da wani expression a fuskarta, sam batai zaton haka daga gun hajja ba, don se da ta kira ta na kusan kwanaki ta ringa xugata akan cewa mami ce ta hada komai kuma ita hajjar sosai ta hau ta zaune, don she tot ma zata saka a daura auran a nan cikin gidan daddyn ammah se gashi ta canza direction? She never saw that coming sam daman mijin ta sallamemmme ne don Dr ko me omair ya ce baze taba musa masa ba don yana kaunar yaron tun yana karami,
Hajja mu ne fa manyan sa ba shisa don kawai yace beso se a biye masa? toh me yake nufi damu ehh, gaskiya a kara duba wannan lamarin
daddy ya fada looking so serious don ransa ya baci da wannan abu da tai,
surajo dakar ni, nace tashi ka dake ni tunda ka maida ni kayan banza kayan hofi, dukan ku kunfinison su ne ko me kuke so ku ce mun ehh?
Shiru daddy yai yana huci, something most be done coz baxe bar wannan maganr haka ba, xe daura masu aure ba tare da sanin hajja ba don yasan ita tana son auran kawai dai son da take ma omair ne ya sanyata mance duk kalar son da tai ma auran suhailan da omair din.
Am sorry to say but hajja dis is not fair and zan daura masa aure da suhaila ko yana so ko be so saboda hakan shine ya dace
baki bude hajja ta tsaya kallon sa kafin tace
auhoo ba shakka, ashe surajo ba dadi abun sanda kaje ka auro mana bare ka bar shakikiyar ka kace bazaka aura ba akwai wanda yai maka hakanne ehh? Se kai shaffafe da mai zaka ce kai baza
a maka ba ko? Toh Wallahi kaima se ka dandana kaji daman abun da kai shi za
ai maka, ba uban da ya isa ya daura ma jika na aure se dai in shi yace yana so, haba se kace a garin gaba gaba muke? Yace ya fasa ba se ay hakuri ba wai kai sanda ka xuba naka zamanin haka akai maka ehh surajo? Toh daura masa auran tunda ni ban isa da kai ba
tana gama fadin haka ta figi mayafin ta ta kalli hajja karama tace
xo ki maida ni gida
ba musu hajja karama ta mike ta nufi bayan ta, mami ma ta tashi don yi masu rakiya ammah hajja tace
rike kayan ki ban bukata
Jin haka ya sanya mami dakatawa, har hajja ta fara sauka daga stairs se kuma ta juyo baki bude tana kallon aunty fiddou da har yanxu she
s seating, ji take kamar ta kwalla kara ko zata ji sanyi ranta, yanxu ya zatai da mutanen data gamai wa bragging akan cewa omair suraj owner of dominion outo shine xe auri yarta? Dan gayu dan birni kyakyawa ajin farko wanda ake suma a kansa? A ranta ta ayyana cewa ko komai nata xe kare se ta tabbar cewa omair ya auri suhaila
me kika wani zauna kamar gurguwa?
Muryar hajja ta dawo da ita daga duniyar tunanin da ta shiga, kamar an caka mata allura haka ta tashi fuuu ta raba ta gefen hajja ta wuce ta barta nan tsaye baki hangame. Su hajja na tafiya yai shirin nufa office don daman yana da abun yi wannan stupid zaman ne ya sanya shi be tafi ba. yana fita parlon kasa ya taddata tana saka turaren wuta a parlor kallon daya yai mata ya fice yana jin ransa na kara baci don ganin ta da yai ba karamin kara bata masa rai yai ba
Still on free pages
INUWAR KADDARA (THE SHADOW OF DESTINY)
By moon
Chapter 8 · 0% Book details