← Book details Inuwar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 5 OF 9

Chapter 5: One Saw a Liar. The Other Saw a Future.

Inuwar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 20 min read

YASMINE
Gama wanke dishes din keda wuya wayarta dake cikin aljihun rigar ta ta fara ringing, da sallama bakin ta ta kai wayar kunne, daga daya bangaren saddiqa tace
ynx email ya shigo, wai yace ki kai masa can din
dan jimm yasmin tai kafin tace
toh shikenan na gode
daga haka sukai sallama, kamar daga sama taga nazli ta shigo cikin kitchen din, ointment din da mami tace ta bata tun dazu ta mika mata ba tare da tace mata komai ba, amsa yasmin tai tai mata godiya, instead of nazli din ta fita daga kitchen din se ta haye kan chair din dake kitchen din ta zauna ta cigaba da danna wayar ta a nan gun, ita dai yasmin ta cigaba da goge gogen ta, after some minutes se ga mami nan ta shigo, turus tai tana kallon nazli that was busy pressing her phone bama ta san da shigowar mahaifiyar tata ba, bata ankara ba taji an fizge wayar tata daga hanun ta, da sauri ta dago kai, hada ido tai da mami dake kallon ta rai a bace tace
get out
ba musu nazli ta mike daga kan kujeran kanta a kasa ta bar kitchen din, mami ta bita da ido har ta fice kafin daga bisani ta maida kallon nata kan yasmin da ta maida hankalin ta kan abun da ke gabanta tace
bahar zata kawo takeaway a xuba ma hajja abinci a ciki
tana fadin haka ta fice ta bar kitchen din ba tare da ta jira amsar yasmin din ba. Se guraren karfe 4 sannan su hajja suka tafi bayan an masu packaging takeaways din a cikin basket, suna tafiya ita da bahar suka kara tsaftace gidan yadda ya kamata suka saka turaren wuta a ko wani lungu da sako na cikin gidan, bayan tayi sallah ta ninke prayer mat din ta aje shi kan bedside drawer, dakin da bahar take ciki tai knocking a hankali sannan ta dan ja gefe ta tsaya, bude kofar bahar tai da alamu itama bata dade da idar da sallar ba don ta hango prayer mat a floor din dakin,
ummm aunty na idar, daman na xo nai miki sallama ne
ta fada tana me wasa da gefen hijab din nata, daman bahar din ita ta sanar mata da sakon mami na cewa if ta gama aykin taje habu ya maida ta gida, murmushi bahar tai tace
toh Allah ya kaimu gobe da safe journey my dear
daga haka sukai sallama ta fice, gabadaya se taji wani iri da taga mami bata wani kulata ba se take ji kamar tayi mata lefi ne, tana fita ta tadda habu nata faman goge daya daga cikin motar gidan, a hankali take takawa kamar bata son yin tafiyan don tana tuna cewa gida zata koma se mood dinta ya kara baci, ko da ta shiga motar se tunanin yanda zata cema habu ya aje ta a hanyar wannan car company din take don so taje ta bayar sannan ta wuce gidan, bata Jin zata iya fada masa cewa ya sauke ta a wani gun don haka tai shiru bata ce masa komai ba. Ko da yai dropping dinta se da ta tabbatar ya yi nisa sosai sannan ta tsari adaidaita ta kwatanta masa gun da ze kaita don akwai kudin da mami ta bata a pocket din ta
Ta tsaya a gaban Dominion Auto karo na biyu, amma wannan karon xuciyarta tana bugawa da sauri fiye da jiya. Yau batare da kauyanci ba kai tsaye ta nufi gun receptionist
in jiya wanda ta gane ta nan take. Tun kafin yasmine tai magana tace
good evening ma, thank you so much for your honesty Please, have a seat
ta fada cikin mutuntawa. Yayin da receptionist din ke making call idonta yasmin ya sauka zuwa wani babban showroom, wanda wasu motoci masu tsada suke kyalli a
ashin wani haske, bata san sanda ta mi
e a hankali ba kamar ana janta ta taka cikin nutsuwa idonta ya kasa daina kallon motocin.
Subhanallah
ta furta a hankali tana me ta
aya daga cikin motocin a hankali kamar ba gaskiya ba, nan fa gilashin ya nuna hoton ta kamar wata
aramar yarinya a cikin babban duniya. Muryar receptionist ya dawo da ita daga duniyar da ta tafi da sauri ta nufe ta
s go ma
nan ta shiga bin ta a baya kamar wata jela har suka shige elevator wanda xe kai su 4th floor wanda nan ne office din his excellency omair suraj yake
ko da suka fito daga elevator sosai take bin ko ina da kallo don gun ya burge ta saboda tsari da haduwar sa se mutum ya rantse yace ba a kasar yake ba duba da tsarin gun. A haka har suka isa bakin kofar office wanda kamar hadin baki duk su biyun suka ja suka tsaya, bayan tattaro jarumta receptionist din ta fara knocking door din kamar tana tausayin kofar, sau biyu tai knocking daga haka bata kara ba, seda sukai kusan one minute sannan sukaji ance
come in
sauke ajiyar xuciya tai sannan ta kalli yasmin that look so pale tace
a nan zan barik ki karasa ciki
wato matar nan na Jin hausa shine tai ta saka ta turanci kamar a america
. Ta fada cikin ranta a zahiri kuma tai saurin fadin
but-i
bata jira jin maganar yasmin din ba tai saurin barin gurin, ajiyar xuciya yasmin tai tana me kara seseta natsuwar ta don haka kawai ta samu kanta da jin tsoran shiga cikin office din, after a while kawai tai bisimillah ta murda handle din kofar ta shiga cikin office din a hankali. Sosai ta shagalta da kallon haddaden office din nasa, the air was cool, perfumed faintly with something expensive, duk da yaji an shigo amma he didn
t look up immediately, he was leaning back on his chair, one hand resting on the desk, the other holding a pen writing something in that sharp, precise way that matched his personality. Bakin ta dauke da sallama ta karasa shigowa, ba tare da ya dago kai ba ya amsa ciki ciki using his deep voice, kasa karasowa tai ta tsaya daga can nesa, a hankali ya dago kan sa yana me aje pen din hannun sa gefe guda, Just as she had imagined, his face carried the same cold perfection sharp, unreadable, impossibly elegant and heartbreakingly handsome, se da ta shafe kusan 1min be ce ba bata ce ba, can dai tai breaking silence din da fadin
ina wuni, Im the..
Strictly ya katse ta da fadin
who are you and who let you in?
When he finally spoke, his voice was low and deep, it wasn
t loud, but every word sound like an order. Chak ta chake don batai expecting hakan ba though tayi noticing kamar ba wani ishashen kirki gare sa ba duba da yadda ya barta nan tsaye kamar wata statue, bata ce masa komai ba ta saka hannun ta cikin hijab dinta ta zaro wallet din that was inside her pocket ta nufi inda table din nasa yake tai dropping din sa kafin nervously tace
dis is what brought me here
Where did you get my wallet?
Ya jefa mata tambayar, shiruu ta danyi kafin tace
na fa
a jiya
I found it on the road
And you expect me to believe that?
Nan take hawaye ya cika idonta muryarta na rawa tace
Wallahi ban dauki komai ba
duk wannan abun da ake bema dago ya kalle ta ba
you think you can walk into my company and lie to me?
Yafada gami da kai hannu ya dau wallet din ya shiga cire, driving license, ID card, black card, contact card, da membership card din sa da kuma wasu cards din da bata san na me ba, Jin ta yi Shiru bata bashi amsa bane ba ya sanya shi dago idanun sa masu cike da kwarjini ya daura a kan nata da hawaye suka cika shi famm, ita tai saurin daukewa tana Jin kirjin ta na bugun dubu dubu, mamaki ne ya cika shi sedai be bari hakan ya nuna a kan fuskar sa ba
here for your honesty
ya fada yana tura mata wallet din gaban ta ba tare da ya cire dollars din dake ciki ba, a sanyaye tace
I didn
t do it for money
everyone does something for money
ya fada looking at another direction daban, kamar daga sama muryarta me sanyin dadi ya sauka kan kunnan sa tana fadin
not everyone sir and that includes me
tana fadin haka ta juya, sosai yaji zafini amsar data bashi don ji yai kamar ta kunduma mashi zagi, he
s unused to being challenged don haka da sauri ya dago idanun sa ya daura a kan yasmin wacce take daff da fita daga kofar,
you are either arrogant or stupid
kamar wacce aka xuba ma ruwan zafi a jiki haka ta ji dan haka da sauri ta juyo ta kalle shi, shima kallon ta yake direct cikin ido, bata taba zatan cewa aykin alkhairin da tai xe jawo mata zagi ba da tun farko bama ta soma ba, anyi mata abunda ya tattaka wannan ammah sam bata damu ba amma shi kam abun da yai mata ya sosa mata rai har bata san sanda taji idanun ta na yunkurin kawo ruwa ba a karo na biyuu
Ta shafe kusan 30mins a nan tsaye bakin company din bata ga adaidaita ko daya ba se manyan motoci dake wucewa kamar ruwa gashi yamma tayi, nan gun ta durkushe ta rike kanta dake mata wani irin ciwo, can dai ta mike, duk da dai akwai dan tafiya tsakinin babban titin da inda take ammah ganin if ta tsaya anan zata shekara bata samu abun hawa bane ba ya sanya ta mikewa ta fara trekking, har ta kusan isa titi se ga wata hamshakiyar mota da ta dan jima kadan da wucewa ta dawo baya tai parking daidai inda take, sam bata lura da cewa ita motar ta tsaya wa ba don haka ta ciga ba da tafiyar ta kan ta a kasa, ganin hakanne ya sanya me motar yin gaba da ita kadan gami da yin parking, se da ya ga ta iso inda motar tasa take sannan ya fito daga ciki. Kyakkyawan gaske ne na ajin karshe kana ganin sa kaga dan kwalisa me class, dumm taji xuciyar ta ta buga ganin mutum ya tsaya yana kallon ta, da sauri ta wuce sa tana ta faman adduah a ran ta don ta tsorata da ganin mutum a gaban ta haka nan, ganin yana binta ne ya sanya ta kara saurin ta, shima kuma hakan yasa ya kara don kada ta bace masa, can dai ya lura da cewa ta tsorata don haka ya ce
Assalam alaiki, yakuri baiwar Allah ki tsaya ba cutar dake zanyi ba
sarai taji me ya ce ammah tai banza da shi ta cigaba da tafiyar ta duk da dai ta dan ji relief da yai mata magana ba wai cigaba da binta yai ba without saying anything ba, haka bawan Allahn nan ya ringa binta har suka kusan isa titi yana mata magiyar ta tsaya ta saurare shi ammah sam ta ki kulasa, se da taga dai da gasken ba daina binta xeyi ba unless ta bashi attention din ta sannan ta dan rage saurin da take hakan yasa ya samu ya cin mata, ajiyar xuciya ya shiga yi kafin yace
Im so sorry ina ta binki nasan na bata miki rai
ya karasa maganar da kyar yana me kai inhaler din sa baki wanda hakan ya tabbatar mata da cewa he
s asthmatic, ita dai bata ce masa komai ba har ya gama inhaling inhaler din sannan ya kara da cewa
kin sani exercise din da ban shirya ba, anyways it worth it. well
sorry to say young lady but I won
t stop following you unless kin ban attention din ki
still batai responding masa ba ta ci gaba da tafiya duk da dai ba sauri take ba wannan karan don tun da ta ga ya fito da inhaler se kuma jikin ta yai sanyi don tasan kalar wahalar da masu asthma ke sha don wata classmate din ta na dashi. a haka suka cigaba da tafiya har suka iso main road, nan ma dai Shiru ba nappep din ko anguwar ta manya ce shisa ake wuyar samun nappep din,
Ki yi hakuri nasan is not proper for me tna tsayar dake on the road, but wallahi, something in my heart moved when I saw you. I don
t even know your name, but I already know I want to spend the rest of my life making you smile, I want to know you
to understand you
and, if Allah wills, I will spend my life cherishing you, so pls my lady give me a chance, please ki taimaka ko number din ki ne ki bani so that ma yi magan ta waya
ya fada kamar ze yi kuka, ajiyar xuciya yasmin tai, she could feel the sincerity in his voice, tabbas da ya san ita wacce ko kuma ya natsu ya kalle ta da tun farko be wahalar da kansa ba ya biyo ta har nan, don ita da shi ma ba hadi sam don kallo daya za kai masa ka gane cewa he was born with a silver spoon in his mouth, katse mata tunani yai da fadin
please!!!
Ya wani ja kalmar please din kamar yaro karami wanda hakan ya sanya wani murmushi escaping through her lips ba tare da ta sani ba, wayar sa ya ciro ya mika mata making a puppy eyes yace
dan Allah ki sa mun kuma karki ban wrong number
samun kanta tai da amsar wayar ta saka masa number din nata, kiran layin yai se gashi keypad din ta ta fara ringing,
kiyi picking call din mana?
Ya fada yana tsare ta da kyawawan idanun sa, ciro wayar tata tai yai mata alamu da ta kara a kunnan ta, a karo na biyu tai murmushi don she founds his actions very funny, ba musu ta kara a kunne bayan tayi picking
hello dis is your feature husband
s number
ya fada yana sakar mata murmushi, sauke idanun ta tai kasa tana me blushing, a na cikin haka se ga wani me nappep nan ya nufo inda suke, ya san ba zata shiga motar sa ba shima kuma baze yi insisting hakan ba don ya kula tana da tsoro da kuma kamala. Tsayawa yai yana kallon nappep din wondering me xe ce masa ya tsaya, kafin yai wani yunkuri ta tsayar da nappep din ta fada masa in da xe kaita, sannan ta shige, ganin me nappep din xe wuce ne ya sanya sa saurin ciro kudi masu yawan gaske ya aje a gefen ta sannan yai saurin barin gun ba tare da ya jira ta cewar ta ba duk da yana son ya tambayi sunan ta ammah kuma gudun kada ta dawo da kudaden da ya bata ne ya sanya sa kin tsayawan..
Bawan Allah dan Allah ko zaka iya juyawa gun wancan mutumin?
Ta fada tana dan dardar,
anya kuwa hajiya? Gaskiya yamma tayi se dai ki sauka ki samu wani don ni yanxu sauri nake zani gida lokacin tashi na yayi, kawai ki dafe kudaden ki ko kimun sadaqa in yawa yai miki
tuna wahalar da ta sha kafin ta samu nappep dinne ya sanya ta cema ma me nappep din su je kawai. Ji tai duk ta manta da bakin cikin da wancan watsatsen mutumin a dasa mata , duk da dai ta ji dacin abun da yai mata ammah se Allah ya kawo wannan bawan nasa da maganganun sa suka mantar da ita wancan bacin ran.
*****
5pm daidai ta isa gida wanda tun kan ta karasa shigar da kafafun ta ciki taji xuciyar ta ta kara jagule wa sosai, bakin ta dauke da sallama ta karasa cikin tsakar gidan da ba kowa a cikin ta, wanda hakan ya tabbatar mata da cewa su hafsa na makaran ta, dakin da Abby ke ciki ta nufa, ta gaida shi ya amsa mata ya tambaye ta ya aykin ta bashi amsa da Lfy kalau Abby, daga haka ta mike ta bar dakin ta nufi na ammah tai mata sannu da gida, ciki ciki ta amsa mata kafin daga baya tace
ga abinci can ki dauka
ta fada tana nuna mata wata er karamar cooler,
toh na gode
sam bata jin yunwa ko kadan ammah gudin kartai musu a hanata na dare ya sanya ta daukar coolern ta fice, babu kowa dakin don su hafsa na Islamiyyah harda su twins, hijab dinta ta rataya jikin kofar dakin sannan ta fiddo da kudin daya bata daga aljihu tana kallo, haka kawai taji ta tuna da rude man dinnan, tsaki tajaa sosai which is not her habit, mayar da kudin tai cikin pocket din ta, tana son ta kawo wa siblings din ta chop chop din da mami ta bata ammah tana tsoro kar ammah ta sata a gaba ta ga kamar wata duniyar ake bata a gidan mamin. Tana zaune har kusan 20mins bata ji ammah ta sata ayki ba which is unusual don haka ta janyo quranin ta ta shiga yin bita har se da ta ji kannen ta sun dawo sannan ta rufe don baza su barta tai karatun ba. Bayan ta idar da sallan magrib ta karasa kofar ammah tai sallama sannan ta tambaye ta me za
a a dafa,
taliya da manja da yaji, kije gidan auntyn haske ki amso mun murjin taliyar saura kuma ki tsaya gun gantalallar me awarar nan don wlh kika dade se na daka ki a gindan nan.
Tafiya take cikin duhun daren nan, don ko hasken fitila babu wayarta ma ta dauke don battery din ta ya fara samun matsala shisa take saurin sauka, ita kadai ce a layin se wasu maza da take jin maganar su a bayan ta, gabadaya ta tsorata da lamarin mazan duba da kalar hirar da suke ga muryar su kana ji kaji na original smokers, kiris ya rage bata saa gudu ba bayan ta jiyo muryar daya daga cikin su daf da kunnuwan ta, da sauri ta matsa gefe tana ambaton sunan Allah gamida kankame jikin ta, kan kace me mazan da zasu kai su 5 suka zagaye ta suna bin ta da kallo kamar sunga nama,
kai kaga wata baturiya kamar ka lashe?
wani me xubin mayunwata daga cikin su ne ya fadi maganar yana me tande baki kamar maye,
jar uba ashe dai bani kadai nake gani ba da fari na dauka abar ce ke sani nake gani ba daidai ba ashe ashe rayality ne
haka suka sata a gaba suna ta faman sambatu gashi daga tayi runkurin guduwa se su maza su tare mata hanya, haka suka dinga wahalar da rayuwar ta kamar mage ya samu bera, wani dan zalama ne daga cikin su yai yunkurin kai hannun sa jikin ta ayko ta daddage ta kwalla wata siririya kara wacce ta janyo hankalin wasu samari da suka xo wucewa, ganin hakanne ya sanya su tarwatse wa don kar ta san kar ne tsakanin su, xubewa tai bisa knees dinta tana sakin wani kukan bakin ciki, ta rasa me taiwa mutane da wasu sam basa son ganin ta tana rayuwa kamar sauran mutane, if she could remember correctly dis is the 4th time da akai attempting molesting din ta, na farko malamun islamiyyar su, na biyu kuma a school na uku kuma wani cousin din ta a kauye ga kuma na yau don Allah ne kadai yasan me waennan bayin nasa zasuyi mata da Allah be kawo waenan samarin ba, sosai take kuka har numfashin ta na daukewa,
Sannu baiwar Allah, ina fatan dai basu miki komai ba koh?
Matasan suka tambaya, da kyar ta samu ta gyada masu kai,
tashi mu rakaki gidan ku, kada kuma mu barki ke kadai wani abun ya kara faruwa ba fata ake ba
jin abunda suka fada ne ya sanyata mikewa xumbur kamar an tsikara mata allura, se a time din mazan suka lura da fuskar ta da sauri dayan yace
Auuu Ashe ma yasmin ce, me ya fito dake haka da duhunnan bayan ga umar a gida
kallon rashin sani take masa don haka tai gum da bakin ta aranta tana mamakin a ina ya santa bayan ita ko me kama da shi bata taba gani ba. Ganin she
s confused ne ya sanya shi cewa
muje mu kaiki gida
a hankali tace
na gode Allah ya saka da alkhairi, ammah ba gida zani ba
ba komai, ina zaki toh?
nan baya ne ba nisa..
Haka matasan nan suka tasa keyar ta gaba suka kaita har gidan antyn haske, shiga tai ta gaida auntyn hasken sannan ta fada mata sakon ammah, mikewa tai ta dauko mata robar da taliyar ke ciki sannan tace
ayy tun da rana na gama ita nake jira ma ta xo ta amsa, da har zan tura yara su kai mata ammah se na tuna tace bata son kowa ya kawo mata zata ayko me amsar
ita dai yasmin bata ce komai ba se amsar robar da tai tai mata se da safe, daidai ta juya se ga sallamar wannan matashin cikin gidan, kallon sa take tana mamakin me ya shigo da shi cikin gidan matan aure ko dai bashida kai ne, muryar auntyn haske ne ya katse mata tunanin da take,
dan albarka ka dawo kenan? Yau ma ay na dauka gun abokan naka zaka kwana, ace mutum yai ta gudun gidan su? Baban ka tun yana fadan harya gaji yayi shiru, ya kamata kaima kanka fada haske tunda ka dawo baka zauna ba se fice fice da kake ba ma kada lokacin mu.
toh aunty a yakuri za
a gyara
sim sim yasmin tai zata fice se ta jiyo muryar auntyn haske tana cewa
yasmin kun ko gaisa da dana haske kuwa? nasan ba lallai ma ki tina sa ba don sanda ya tafi kudu neman kudi ba kida wani wayo sosai, haske ka gane ta kuwa? er marigayiya ce fa me kukan nan sosai
ta fada tana dariya, a sanyaye yasmin tace
ina wuni
tana fadin haka tai saurin ficewa daga gidan, luckily kuma abokin nasa baya wajan dn haka tai saurin barin gun, haka kawai taji kuma bata bukatar temakon nasa wanda ma yai mata a farko Allah ya sa masa albarka. Tana isa gida ta kunna wuta ta dora taliyar, tako ci sa
a ammah bata nan ta shiga gidan makociyar su maman daddy, ko da ta dawo ma batai mata fada ba don ta ta dan jima a gidan maman dadyn, sam batai gigin fadin abin da ya faru ba, toh wa ma zata fadawa? Wa ma wanda xe saurare ta. Tun da ta dawo se faman firgita take don ko motsi taji se ta firgita, haka nan dai ta gama girkin ta debar wa ammah nata shima abby haka sannan ta xuba wa en uwanta a wani tray, bata debar wa kanta ba don bata jin zata iya cin abinci yau dinan duk da dai akwai shinkafar ta ta daxu da bata ci ba. Tafi minti 10 tana kallon missed calls din
da akai mata wanda take da 100% sure cewa na wannan mutumin ne na daxu, a tsakanin fitar da tai da kuma girkin da ta tsaya yi se da ta tadda missed calls goma sha biyar, aje wayar tai can gefe sannan ta janyo cooler din abincin ta shiga ci a hankali. Se da tai wanke wanke ta wanke ma su hafsa uniform sannan ta kwanta. the next morning kamar kullum ta tashi da wuri tai gyaran gida ta daura ruwan wanka ma su hafsa sannan ita tai dana sanyi, shiryawa tai cikin army green hijab din tsohuwar islamiyyah su sannan ta fita xuwa dakin ammah, bakin ta dauke da sallama ta shiga cikin dakin,
ammah zan tafi
ta fada kan ta a kasa,
xo nan
kirjin ta ne ya wani buga jin abun da tace mata, kamar me tsoron taka kasa haka ta shiga ta kowa, ganin kamar zata bata mata time ne ya sanya ta damko ta, daman abun ka da jikin fulani se gata ta fado dukan ta kan amman, tunkuda tai kafin ta ce
tashin mun a jiki wawiya kawai
ayko da sauri ta mike tsaye xunbur jikin ta na rawa, hijabin jikin ta ta dage mata da sauri yasmin ta rike hijab din gami da sauke shi, marin da ammah ta gaura mata ne ya sanya ta sake hijab din a gigice, Allah ya xuba ma ammah zafin hannu don marin da tai mata yanxu se da ganin ta ya dauke ya dawo,
uwar me zan gani a jikin naki ehh, dan kaniyar ki? Nace me zan gani a jikin naki
ta fada tana kara kai mata mari, da sauri ta sanya hannu ta kare fuskar ta da shi,
ayyooo ta nan kuma kika bullo? Nice zan dake ki kisa hannu ki kare, wato ban isa ba kenan, toh ko zaki doke ni ne ehh marar kunya? Koda yake ma koma me kikai lefi na ne dana dauke ki na kai ki gidan daulaa yin ayki shine har kika koyo sabon sallon lalata
in banda kuka da girgiza kai ba abinda yasmin din take, har yanxu bata daina jin radadin marin da tai mata ba, laluban aljihun rigar ta ta shiga yi ayko taci karo da 1000 ragowar kudin da mami ta bata,
gidan uban wa kika samu kudi ehh?? Wato mu muna nan muna fama da kan mu ammah ke kina nan kina more rayuwar ki koh? Waye ya baki?
ta daka mata tsawan da nan take jikin ta ya dau kerma hawaye kuma suka shiga yin ambaliya akan kyakkyawar fuskar ta
Ya jama
a yasmine tayi goshi
And finally yau dai Allah yayi ta hadu da omair suraj shugaban marasa M
INUWAR KADDARA (THE SHADOW OF DESTINY)
BY moon
Chapter 5 · 0% Book details