← Book details Inuwar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 4 OF 9

Chapter 4: The price of a broken bucket

Inuwar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 25 min read

Tafi minti 10 nan tsaye bakin kofar gidan tana ta faman xubda kwalla,
uban me kike yi anan?
Tsabar firgita da jin muryar ammah se da tai taga taga zata fadi, karaf idon ammah ya sauka kan fashasshen bucket din ta, wani ashar ta mulmulo tana bin yasmin din da kallo, in ta kalli bucket din se ta kalli Yasmin din, murya na rawa yasmin tace
ammah wlh- ban-ban sani ba- wlh kus-
ay bata bari ta karasa ba ta figo ta cikin gidan, kasancewar yasmin din bata da wani kiban kirki hakan yasa gabadaya ta afka cikin gidan, reshan bishiyar dirimin dake tsakar gidan ta karyo ta shiga lafta mata a ko wani sashi na jikinta, tun tana kukan me sauti tana rokan ta akan da ta yi hakuri har muryar ta ta disashe, su twins da suka tashi daga bacci se kuka suke kamar ransu ze fita cikin gwarancin su suke fadin
ammah yaya a
ko ta kansu bata bi ba se da ita kan ta taji ta gaji da dukan nata sannan ta cillar da reshen da ya fatattake a kasa, in banda sheshekar kukan ta ba abin da kake ji,
wannan ma kadan nai miki wlh, banza kawai, ni zaki dora wa hawan jini? To wallahi kan ki doran se na kashe ki a gidan nan, zaki tashi nan gun ko sena xo na kara miki?
ta fada tana me kokarin karyo wani reshen, ganin hakanne ya sanya ta mike wa da sauri ta shige dakin su ta zauna nan kasa tana cigaba da kukan xuci. Gabadaya ko ina na jikin ta ciwo yake mata ga wani irin mugun ciwo da kanta ke mata, sosai jikin ta yai zafi kamar garwashi, ji take kamar cikin fridge aka cillata tsabar sanyin da take ji, hijab din ta tai amfani dashi gun rufe jikin ta ammah kamar bata saka komai ba don ji tai kamar ma sanyin kara mata akai don haka ta sanya hannu ta janyo wani tsohon bargonta ta yafa a jikin ta, duk da bargon ba shida wani kaurin kirki ammah ta dan ji dama dama da ta lulluba da shi, tana cikin wannan halinne taji muryar su hafsa da umar a tsakar gida, da sauri ta mike zaune gamida cillar da bargon can gefe guda, sam bata son yaran su tashi suna ganin bakin mahaifiyar su don haka bata taba nuna masu cewa mahaifiyar su is doing bad or something similar to that ba, umar ne ya fara shigowa kamar an jefo shi, yana ganin ta ya nufe ta da sauri yana fadin
yaya sannu da gida, Ashe kin dawo tun daxu
da kyarr ta iya furta
yauwaaa umar ya makaranta?
Ta tambaya tana faking smile din ta gamida kai hannun ta kan gashin kansa ta cire masa wani zare, dan rike hannunta yai da niyar yaga me ta cire, da sauri yace
kai yaya, kin ji jikin ki kuwa kamar ruwan zafi bakida lfy ne?
Ya tambaya looking so disturbed daidai nan itama hafsa ta shigo dakin tare da su twins da suke ta kuka akan se ta basu akori kishiyar da ta taho dashi daga makaranta, duk da dakin da dan duhu ba shi ya hana hafsa ganin shatin bulala kwance a gefen fuskar yasmin din ba, tsayawa tai cak tana kallon er uwar tata, ganin duk ya damu ne ya sanya ta fadin
ummm dan zazzabi nakeyi ammah yanxu ma na warke
kamar zeyi kuka yace sannu yaya bara In dauko miki maganin ciwon kai a dakin abby
ya fada yana me kokarin mikewa, da sauri yasmin tace
a ka bari in an shiga sallah magrib ka dauko yanxu dai ka je ka cire uniform din ka
toh yaya
yana fadin haka ya mike ya fara yin abun da ta saka shi yi, se a time din ta maida kallon ta kan hafsa, hada ido sukai da sauri ta ce
kukan me sukeyi ne? Ki shigo dasu ciki mana hafsa kin tsaya bakin kofa kuma magriba tayi
uffan hafsa bata ce mata ba se taso kan su twins da tai gaba suka karaso cikin dakin. Labari umar ya tsaya basu na dan wani Islamiyyah su da yaiwa malamar su rashin kunyaa aka zane shi, gabadaya hankalin yasmin baya kan labarin don ji take kamar ana sa guduma ana farfasa kashin ta tsabar ciwon da take ji a jikin ta, a hankali take saka hannu tana goge hawayen dake gangaro mata ba tare da ta bari sunyi noticing ba, a haka har aka kira sallar magriba umar ya fice domin yin alwala, hafsa ce kawai ta dawo don umar ya tafi masallaci yin sallah, zama tai nan kusa da yasmin da duk ta fara fita hanyacin ta, dafa ta tai ayko nan take ta firgita don a tsora ce take sosai, ruwa da paracetamol din da ta dauko ta aje kafin tace
sannu yaya nice, tashi misha maganin kafin ammah ta fito daga daki
jin hakan ne ya tabbatar mata da cewa sneaking tai ta dauko ruwa da magani ba tare da ammahn ta gani ba, a hankali ta amshi ruwan da maganin ta watsa a bakin ta tana yatsine fuska, ita dai hafsa se binta take da kallo kawai don sosai take matukar tausayi da kuma kaunar sistern nata. Da kyar ta samu tai sallah saboda wani jiri da take gani, Sam taki yarda ta kwanta duk dan kada ta kara jama kanta wani bala
in, gashi tun daxu take son taje gun abbyn ya shima kuma tsoro ya hanata yin hakan. kamar a mafarki tajiyo muryar ammah daga can tsakar gida tana fadin
uban wa kike jira ya daura duramen tuwan ehh
firgit ta tashi bayan ta gazgata cewa ba mafarkin take ba gaskiyane, da kyar ta samu ta daura dumamen tuwan don kanta kamar anan buga mata guduma haka take jin sa, ko da ta gama ta xuba wa kowa sannan ta kai dakin abby dake bacci, aje robar tai can gefe sannan ta fice daga dakin ta koma nasu dakin ta kwanta, Sam batai gigin dibar abincin ba don dama duk sanda ta sake ta danyi laifi to tabbas ba ita ba cin abinci a gidan nan. Duk yadda siblings din nata suka so su shiga daki su bata bincin a dabarance se da sukai ammah maman su ta hanasu. Tabbas yanxu ba iya zazzabi ke damunta ba harda yunwa da ta addaba ta, a hanakali ta kai hannunta cikin aljihunta ta laluba biscuit din da ta taho dashi dazu, hannunta har wani shaking yake tsabar yunwa, da sauri ta fara afawa a bakin ta kamar wani yace xe kwance mata, wasu hawaye ne suka fara bin gefen idanun ta, kuka take so tayi me sauti amma tsoron abunda xe biyo baya take, don haka ta saka tafin hannun ta ta rufe bakinta tana kuka marar sauti. A daddafe ta samu ta tasha maganin da taji kamar kara mata zazzabin yai, daren ranar bata samu bacci ba don daga ta kwanta se ta firgita ta bude idanun ta da sauri, se gurin 3:50 ta kwanta, 5:10 kuma kiraye kirayen sallar asuba ya tashe ta. Koda ta tashi tadanji dama dama sedai jikinta har yanxu yana ciwo kamar a time din ake dukan nata. Bata yarda ta koma baccin aa uban ba don bata manta da kashedin da ammah tai mata jiya ba gashi kuma mami tace da wuri za
a xo daukar ta don haka ta mikewa a hankali ta tattaro Kayan shimfidar ta sannan ta jona batirin wayarta jikin direct charger, ta janyo hijab dinta ta fice daga dakin. Ruwan zafi ta fara dorawa sannan tai wanke wanke, seda gari ya danyi haske sannan ta shiga share tsakar gidan, tana cikin sharar ammah ta fito daga dakin ta tana mika, da sauri yasmin ta zube kasa gamida sunkuyar da kanta tace
ina kwana
aje sharar nan ki hada kunu ki kai dakin tsohonki
tana fadin haka ta shige dakin su don taso su hafsa dake bacci don time din shida har ta dan gota. Koda ta shiga dakin baban nata kwance ta ganshi kamar kullum ya kurawa sama idanu, gaishesa tai kafin ta aje masa kunun a gefensa,
zaunar dani
ya fada yana me yun kurin mikewa zaune, da taimakon ta ya samu ya zauna, ajiyar numfashi yai kafin yace
yasmin!
A hanakali ta amsa masa tana me kallon gefe guda don bata son yaga hawayen dake makale a gefen idanun ta, cikin rarraunar murya yace
Ina me takaici da bakin cikin ganin ki a haka, tabbas kaddara ce ammah harda sakaci na, tun ina raye kenan na kasa baki kulawa yadda ya dace what if yau aka ce na fadi kasa matacce me ze faru? Sam banida maruba da babu, Innalillahi wa inna ilaihi rajiun
ya fada yana me rintse idanun sa, share hawayen da ya gangaro mata tai nan take taji wani zafi don gun ciwo yake mata sakamakon marin da ta sha a gun, Murmushi tai kawai sannan tace
kasha karya huce bara naje na gama ayki na
tana fadin haka ta mike da sauri ta bar dakin tana Jin xuciyarta na mata ciwo, a haka ta samu ta karasa aykin ta na yau da kullum Banda yiwa kannen ta wanka don yau ana sanyi sosai kuma suna mura. karfe 8:50 habu yace ta fito ya kusa karaso wa, kamar jira take nan da nan ta mike ta saka blue black din hijab dinta daya haska fatar ta, har ta xo fita daga dakin se kuma ta koma don kallon fuskar ta a mudubi, se data tsorata da ganin yadda fatarta yai jawur ga gefen fuskarta da jini ya dan kwanta, da sauri ta dauke idanta kan mudubin gamida rufe gefen fuskarta da hijab dinta, daga nan kuma ta fice daga dakin bayan taiwa kannenta sallama, a bakin kofar dakin abbanta ta tarar da ammah ta baje takardun kudin adashi tana baza lissafi, jiki ba kwari ta nufi dan nesa da ita ta tsuguna kafin tace
na tafi
a zafafe ammah ta dago tace
Ammah kedai anyi sha sha, to uban me zan miki ehhh?? Goyaki zanyi ko me? gashi saboda sakarci kin batar dani a abunda nake, zaki tashi ko se na daka ki da safen nan?
Ta fada tana me yunkurin mikewa, ay da gudu ta mike ta fice daga gidan, tafiya take tana haki don seda ta je karshen layinsu sannan ta daina gudu don tasan tsaf zata iya biyo ta harnan taci ubanta don Sam ita bata rena abun duka. Tun daga nesa ta fara hango wata kamar saddiqa a kofar gidan su, seda ta matso kusa da ita sosai sannan ta tabbatar da cewa itan ce, saddiqar ce da kanta ta karaso gun nata kafin tace da ita
tun dazu ina nan ina jiran wucewar ki, ammah Shiru, ga ajiyarki
hannu yasmin ta saka ta amsa tana yi mata godiya kafin tace da ita
har yanxu ba
ai replying email din ba koh?
Ehh fah ina ma ta duba wa ammah Shiru ko in baki wayar ne in yaso if sunyi seki wuce ki kai masu?
Saddiqa ta fada tana me mika mata wayar, da sauri yasmin ta girgiza kanta kafin tace
a ba
ayi haka ba in an yi replying kawai kya kirani sena wuce na kai
Sam saddiqa bata so hakan ba se dai tace da ita
to shikenan duk yadda kike so
ta karashe maganar tana dan tsira mata idanu, ganin hakanne ya sanya yasmin din saurin cewa
toh zan tafi se anjima
da sauri saddiqa ta riko hannun ta tace
me zan gani haka? Kinga yadda face dinki ya canza launi kuwa? Allah ya isan ki Wallahi, me kika mata tai miki haka da fuska?
Ta fada tana sauke idonta kan fararen hannun ta sukai tabon duka sakamakon using dinsa da tai as a shield, wani ashar saddiqa tai kafin tace
kina uban me kike yi tai miki kalar dukan nan baki gudu ba ehh? Saboda ke gaki damo sarkin hakuri koh? Toh Wallahi ki jirani a nan in dauko hijabi na akwai abokin masoyi dan hisba ne Wallahi gunsa zamuje mu shigar da report ay zalincin yayi yawa kuma fisabilillahi
da sauri yasmin tace
dan Allah ki bari kinsan banson tashin hankali, lefina na ne ni nai mata lefi dan Allah a bar maganar nan kin ji saddiqa? na barta da Allah kawai
baki bude saddiqa ke kallon yasmin kafin tace
kin fi son ki zauna ta kasheki koh? Toh in ta kashe ki kema kina da xunubi don baki temaki kanki ba, kuma ni wallahi bazan zauna in xuba ido ana aykata barna ban hana ba
tana fadin haka ta juya ta koma cikin gida, ita dai yasmin ta bita da kallo daga karshe ta cigaba da tafiya a hanakali don har yanxu jiri take gani sosai.
Daidai inda yai parking jiya ta hango motar, da sauri ta karasa ta bude motar ta shiga, a hankali tace
ina kwana? Na barka kana jira koh
da sauri yace
Lfy kalau emmata, a
a wlh ba komai yanxu ma na karaso
ya fada yana tada motar. Tunda suka fara tafiya take Jin kamar ana rugurguza kashin ta da guduma, hakanan tai lamo jikin kujeran gamida dan rufe fuskarta da hijab dinta, se da taji ya kashe motar sannan ta bude idon ta a hankali jiki kuma a sanyaye ta fice ba tare da tace dashi komai ba. Ko da ta isa bakin kofar shiga parlorn hannu ta kai ta danna bell din jikin kofar, ba jimawa akazo aka bude, wata mata ce wacce a shekaru zatai 40 years fara sal da ita kuma er chubby chubby da ita, kallon juna kawai suka tsaya yi kafin daga bisani ta matsa ma yasmin din ta shigo ciki, a hankali yasmin tace da ita
good morning
da sauri matar tace
morning yasmin
ta fada tana dan Murmushi, da mamaki yasmin ta kalle ta Jin ta kira sunan ta, a karo na biyu matar tace
nice bahar and I believe that kinji magana ta agun mami
sosai mamaki ya kashe yasmin Jin yaddatai hausar kamar bahaushiya, watsar da wannan tunanin tai kafin tace
ehh ta fada mun barka da isowa
daga haka ta shige ciki tabi bayan bahar data danyi gaba,
I have cleaned up everywhere, yanxu abunda zamuyi shine girki, mami tayi list din abubuwan da za
a dafa ma bakin yau and i believe that you will help me make them
with respect yasmin tace
sure
daga haka ta karasa cikin katafaren kitchen din tanajin kamar zata kife kasa don ba karamin jiri take ji ba.
Koda suka shiga kitchen din bahar ta mika mata wata piece of paper tace
these are the list of the dishes we are to make
a hankali ta sa hannu ta amsa,
zobo, dambu, fried rice with roasted chicken, kunun aya, se wasu sunayen abincin da bata ma taba Jin sunana su a duniya ba, mika ma bahar tai kafin tace
toh da wanne za
a fara?
Dan jimm bahar tai kafin daga bisani ta ce,
s start with dambu and roasting the chicken, though I have already marinated the chicken and also zobon ma anyi boiling dinsa tiger nut drink kuma was made since in the subh
ta fada tana me fito mata da vegetables, haka nan suka shiga yin girkin ba ji ba gani don she was told by bahar that guest din will arrive by 12pm don haka suke ta ayki ba tsayawa, bahar se hira take mata gamida mata tambayoyi don she was impressed by the girl
s cooking skills, haka dai sukai ta aykin se 11 suka gama, wani iko na Allah se kuma taji duk zazzabin ya barta kawai dai ciwon kai ne ke dan damunta, tunda ta xo bata hadu da mami ba se da bahar tai using telephone din kitchen din ta kira na gurin ta se gata after few minutes ta shigo kitchen din da shigar alfarma, da ladabi yasmin ta gaishe ta ta amsa mata cikin sakin fuska, harta wuce ta dawo looking at her face kamar me son gano wani abu, ganin kallon da take mata ne ya sanya yasmin din yin kasa da kanta
what happened to you Jasmin? Your face wasn
t like dis yesterday, meya faru?
Dan Shiru yasmin tai tana tunanin me zata ce mata, can tace
faduwa nai
ta fada a takaice, jimm mami tai kafin tace
sannu akwai ointment a room zan dauko miki anjima
ta fada slightly, mami bata ce mata komai ba se bude tsadaddun warmer din da ta shiga yi daya bayan daya, nan take aroma ya cika ko Ina da ko ina na kitchen din.
Mami ina kika samu great cook haka? She
s so good ni kaina se kallonta nake kawai don sosai ta birge ni
bahar ta fada tana kallon yasmin da ta sunkuyar da kanta kasa, murmushi tai kafin tace
se dai na gode Allah don da alamu nayi sa
a kam, yanxu kuje ku huta don ba abunda
ya rage kume se in sun xo ne za
ai serving dinsu
mami ta fada tana me kai glass of hibiscus drink din bakin ta, ba musu suka nufi hanyar fita daga kitchen din bayan bahar ta daukar masu nasu breakfast din don basu samu Daman yi ba saboda ayki.
tsaya yasmin
Chak ta tsaya ita kuma bahar tai gaba daya breakfast din nasu, mami ce ta karaso kusa da ita kafin tace
meya samu fuskar ki? Nayi noticing ba iya face dinki bane ba and it clearly looks like kamar dukan ki akai, fadamun gaskiya a gida ne aka dake ki haka?
Ta kare maganar a sanyaye, se da tattaro natuwarta sannan ta fara magana don ba abinda xe sa ta fada mata gaskiyar abunda ya faru
a ba a gida bane ba a islamiyyah ne aka zane duk en ajin mu
Shiru mami tai tana nazarin abunda ta fada kafin daga baya tace
ammah kuma kuna mata suke maku kalar wannan dukan? Dis is not fear at all look at you face for goodness sake, ya kamata a samu ay ma masu makarantar magana don be kamata ba, zan turo nazli ta baki ointment ki saka
taga haka mami ta fice daga kitchen din. Tana shiga dakin taga bahar takai mata abincin nata don haka ta zauna nan kasan carpet tana sauke ajiyar xuciya don yanxu kuma zafi take ji da yunwa don haka hannu a hankali ta shiga cin lafiyayyen breakfast din da bata taba cin wani abu me dadi kalarsa ba don yaji spicies da sauran Kayan girki da ita bata taba ganin irin su ba.
Guraren karfe 12:5 taji ana knocking door din da take ciki, a hanakli ta mike ta bude taga bahar ce, Murmushi ta dan sakar mata, itama bahar tace
mami tace the guest are here
a hankali ta furta
tana me fito wa daga dakin, gabadaya she
s feeling so awkward kasancewar tana ayki tare da bahar dan a haife bahar ta haife ta shisa ma bata iya kiran sunan ta ko abu take son ta tambaye ta sedai kawai tai mata magana. Tun kan su karasa parlon sama take jin kamshin perfume kala kala iri iri, kanta a kasa take tafiya harta nufi inda dining table din yake ta aje warmer din dake hannun ta, jin bahar na gaida bakin ne ya sanya ta matsa wa kadan ta durkusa har kasa ta gaida su ba tare da ta kalle su ba, su 5 ne a dakin, mata 4 da namiji 1, cikin su kadan ne suka amsa don duk ragowar hankalin su na kan smartphones din su, ganin hakanne ya sanyata mikewa a hanakali ta tashi ta bar gun, muryar wata tsohuwa ta jiyo tana cewa
ke kuma Amina ina kika samo wannan yarinyar ko itama tsintar ta kikai a turkiyan?
Tsohuwar da suke ma lakani sa suna hajja ta tambaya tana me kai fruit din da ke gabanta baki gamida bin yasmin da ido kamar zata cinye ta, Can kuma facalar mami wacce take auran kanin daddyn su nazli me suna aunty fiddou tace
Kinga mami garin kwashe kwashen nan naki wataran se kin tsinto aljanu don ita kanta wannan ni ina da ayar tambaya a kanta Jibe ta fah? Se a lokacin matashiyar macan da zatai sa
ar nazli da brother dinta wanda xeyi 28 years haka suka dago kai suka dubi yasmin da ta juya baya zata bar gun, can kan cushion daban wata mata ce ta sha shigar alfarma, a shekaru zata kai mami, suna kiran ta da hajiya karama don sunan ta daya da hajja wato safiyyah, wacce tunda ta xo take ta fama pressing phone din ta don ko cikakken gaisuwa basuyi da mamin ba, daman ita waya shine abokin hirarta don takan iya shafa hours tana danna waya ba tareda da tace wa kowa uffan ba, jin maganr da su hajja ke ne ya sanya ta dago kai gamida yamitse fuska tace
wai wata yarinya ake magana akai ne?
Aunty fiddou ta bata amsa da fadin
maid din mami ce na ganta kamar ba mutum ba
" a karo na biyu hajiya karama ta yamitse fuska tace
as in?
Tai maganar a takaice tana kallon bayan yasmin dake sauka daga stairs din, still aunty fiddou ce ta kara bata amsa da fadin
the girl is hella beautiful
bata kara cewa komai ba se maida idon ta kan mami da tai wacce was busy helping bahar gun arranging dining table din don suyi sauri, se da ta ga mamin zata juyo se ta dauke kai ta maida kan wayar ta da take dannawa,
the dining is ready
mami ta fada tana jama hajja kujerar da zata zauna. Gaba daya se yaba abincin suke ta yi banda hajiya karama dat was just playing with her spoon, ba kuma don abincin be mata dadi bane ba, kawai dai halin nata ne ya matso though she
s always moody. Seda sukai nisa gun cin abincin sannan er aunty fiddou me suna yusra fadin
mami where
s nazli? Ko ba tare kuka dawo bane ba
charaf aunty fiddou ta amshe da fadin
ayy ba zata fito ba jira take muje har daki mu gaida ta
mami dai bata tanka ba don tun dazu taje room din taji ta a toilet wai wanka take where as ita da sassafe take wanka duk don kada ta hadu da familyn baban nata shine take using din shiga wanka as an excuse, daidai hajja ta bude baki zatai magana se ga nazli nan ta shigo parlorn kana ganin yadda take frowning face din ta kasan she
s not happy to see them at all, seda ta xo dap da su sannan tace
Good afternoon everyone, sannun ku da xuwa
ta fada tana zama kan dining chair, cousin brother din ta wanda shine da daya agun hajja karama me suna hateem se binta da kallo kasa kasa yake kamar xe cinyata don rabon da su ganta anyi kusan 6years don yanxu ma se da hajja tai magana sannan suka dawo nigeria don sam in akwai inda basu son xuwa toh nigeria ne, suna hada ido da hateem ta galla masa harara don sam bata manta bakin halin sa ba da rashin M din sa don ko yaxo gidan su ma turkey bata ma shiga harkar sa saboda girman kansa da halin shariya irin na mahaifiyar sa hajiya karama daya kwaso.
kaniyarki naazli, nace kaniyarki, mu zaki gaishar a gantale kamar wasu en iska? Halan bakisan matsayin mu a gunki ba ko? Toh Wallahi ki kama kanki in ba haka ba zamu saka kafar buje daya dake cikin nigeria
ta fada tana kankance ce idanu, turo baki nazli tai kafin tace
granny daga xuwa na harkin fara mun fada daga gaisheki
ta fada kamar zatai kuka, mami ce ta daka matsa tsawa gamida hade rai tace
will you keep quiet ko se na baki dirty slap? Hajjar sa
ar kice?
Mami ta fada kamar zata doke ta,
hmmm daga baya kenan
aunty fiddou ta fada tana kai spoon din ta baki daga haka kuma ba wanda ya kara cewa komai a gun se da suka gama tasss sannan yasmin ta shigo do min dauke kwanukan, cikin natsuwa take xuba su cikin wani medium sized luxury basket, gabadaya ta kagu tai abin da ya kawota ta bar gun, dan gabadaya a takure take a gun, tunda ta fara kwashewa bata yarda ta dago idanun ta ba har ta gama ta bar gun, tana isa kitchen din ta sauke ajiyar xuciya, ta juye plates din cikin sink ta shiga washing dishes din
*******
Zaune yake kan kujera ta alfarama yana going through wasu sabon motoci cikin mackbook din sa babu wani walwala kan fuskar sa, can gefen sa kuma wani mutum ne ke kwance kan wata tsarariyar cushion 3 seater yana wasa da yo-yo hankalin sa kwance kamar wani karamun yaro, rintse idanu omair yai don gabdaya karar yo-yo din takura masa yake kuma nazir din ya san be so hasalima intentionally yake don ya saka sa magana,
would you stop that already?
Ya fada sounding so pissed up, Jin abinda ya fada ne ya sanya nazir din yin murmushi don abunda yake nema ya samu don haka ya mike zaune, daidai ya bude baki zeyi magana kawai akai knocking door da sauri nazir yace
come in
wani kallo omair ya bishi da shi Jin abun da yace, PA din sa ne ya shigo yace
good afternoon sir
be amsa gaisuwar ba se fadin
proceed
da yai hakan ya sanya PA din fadin
your schedules for today is as follows
1:00 PM Lunch meeting with potential investors regarding Dominion Auto
s expansion, 2:00 PM Inspection of newly arrived vehicle models in the showroom. 4:00 PM Strategy meeting with senior management, 5:00 PM Preparation and briefing for tomorrow
s court appearance and 6:00 PM Review and approval of pending reports and emails, that will be all for today, sir.
can kuma se yace
also
sir regarding the girl that..
daga masa hannun da omair din yai ne ya sanya shi yin shiru da bakin sa yana me jiran Jin abinda xe ce masa
Cancel the 1 PM meeting, Push the 4 PM to tomorrow and make sure I
m not interrupted
dan Shiru PA yai kafin yace
ohk sir..
ya nufi hanyar fita daga office din kamar daga sama yaji yace
call the receptionist
nan ma ya amsa masa da Ohk sir. Duk wannan abun da ake Nasir na zaune ya saki baki da hanci yana kallon ikon Allah . After a while se ga knocking din receptionist din nan, can kasa kasan makoshi ya furta
come in
nervously take tafiya dan yaune karonta na farko da ta taba shiga office din sa kuma gashi ta san ba alkhairi bane kiran da yai matan ba, after kusan 2mins da shigowar ta ya sauke medicated glasses din sa ba tare da ya dago ba ya fara magana
who came here yesterday?
Ya jefa mata tambayar, Jin ta yi Shiru ne ya sanya shi dago kyawawan idon sa yai mata wani sharp kallo daya sanya xuciyar ta buga wa, kusan a fusace a kuma gadarance yace
I asked you a question.
Murya ba rawa tace
S-sir
a girl came. She said she found your wallet but
But?
yai interrupting dinta coldly, ta hadiye wani abu daya tsaya mata a makoshi sannan ta cigaba da fadin
She didn
t have an appointment, so I told her you were unavailable.
She came all the way here
to return something that belongs to me amma you sent her away?
nan ta shiga defending kanta da fadin
sir, it
s protocol. No one sees you without
Protocol?
ya tambaya sharply kafin ya kara da cewa let me make something clear, If someone walks into my company with honesty you don
t send them away like they
re nothing.
m sorry, sir..
ta fada kamar zatai kuka Lura da nazir yai ba daina mitar abun xeyi ba ya sanya shi fadin
Kinga dismissed we will handle the situation
shi dai be kara cewa komai ba se maida hankalin sa da yai can smartphone din sa, da kamar kar ta tafi ammah da ta tuna yadda take Jin labarin kusancin nazir din da shi se ta fice don tasan tunda nazir yasa baki toh an yafe mata har gaban abada
Nazir get out of my office
banza nazir yai masa kamar beji me yace ba, ajiyar xuciya yai ya dauke idon sa daga kallon nazir din, gabadaya friend din nasa sai testing patience din sa yake more especially wanna dawowar da yai Nigeria don he
s just finding any possible excuses da xe yi amfani da shi don ganin yayi getting on his nerves, don dai shi ba biye masa yake ba amma da tuni sunyi hannun riga, shiru ne ya wanxu na kusan 5mins can dai nazir ya maida kallon sa kan abokin nasa yace
look omair saboda wallet zaka ringa acting haka? A zafafe ya juya ya kalli inda nazir ke zaune yace
keep your damn mouth quiet karka karasa batan rai pls, my concern is that my contact card, membership card and my driving license are all inside the wallet and kaima kasan how important those items are
ya fada looking so disturbed and annoyed, er dariya nazir yai kafin yace
toh dai ka yakuri, kama gode ma Allah yarinyar me gaskiya ce coz da ba haka ba da ba abinda xema saka ta taxo nan talk less of emailing you
look it doesn
t matter
ya fada yana me kallon wani direction din daban
bara zanma KB magana se a bashi address din ta yaje ya amsa, is that Ohk for you?
A takaice yace
dafe kai nazir yai yace
Wallahi omair kafi yaro dan karami damuwa, kai ba
a taba birge ka koh? Toh shikenan do what suits you
yana fadin haka ya dau belongings din sa ya fice daga office din, don daman yana nan patient suna jiran sa. Tsaki omair yaja yana jin ransa na mugun baci, saboda batan wallet dinnan nasa jiya se kwana yai a apartment din nazir gashi harta logage dinsa a cikin hotel room dinsa yake don kayan da xe sa ma da wasu kayan amfanin sa se da suka tsaya suka siya a wani supermarket even though nazir yayi insisting da yai using nasa outfits din ammah yace shi sam baze saka kayan nazir din ba duk da ko kayan sabbi ne fill a ledar su. Wayarsa ce tai kara alamun shirowar message, a hankali ya bude kyawawan idanun sa ya daura a kan screen din wayar tasa, tsaki yaja bayan ganin message din nata, daman ya san message din ta ne don tunda ya kunna wayar tasa ita da en MTN suke rige rigen masa message, batai worthing time din sa ba don haka bema bude ya karanta message din nata ba, after a while ya kara tunawa da wallet din sa that
s with a stranger hakan ya sanya ransa kara baci don haka ya kai hannu ya dau wayar direct cikin email din sa ya shiga wanda tun jiya yaga email dinda tai masa amman ya ki yin reply saboda he doesn
t feel like doing so, after a while yai replying da
Ohk, bring it yourself
yana tura email din ya dire wayar a gefe gami da mikewa tsaye ya nufi kan full body massage chair din dake office din ya zauna yana me adjusting necktie din da ke wuyan sa, sam jiya be samu damar bacci a apartment din nazir ba even though daman tun can shi he
s a night owl ga kuma surutun nazir ya cika shi da shi wanda se da akai sallar asuba sannan nazir din ya kwanta, shikuma 8 ya taho gun aykin ba tare da ya bi ta kan nazir dake ta sharar bacci ba, shine kuma by 11 ya biyo sa nan office din nasa ya cigaba da takura masa
Dan Allah wa xe raka ni muje muyi ma Yasmine duka ne? yarinyar sam bata da karsa shi
Toh dai ga me wallet ya bayyana Amman fa kamar bakin haki gare sa
Gaskiya naso ace saddiqa ta kira en hisba sunyi gaba da ita
Su hajja anxo an kwashi girki Harda takeaway amman still ana taba bakin hali
INUWAR KADDARA (THE SHADOW OF DESTINY..)
By moon
Chapter 4 · 0% Book details