free

Inuwar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel

AuthorMoon

692 views209 downloadsEN language
React👍 Like 0 ❤️ Love 0 💡 Interesting 0 🤝 Helpful 0
BOOK INFORMATION

Details

Available
Category
Loan
Format
DOC
Access
Free
Reader
Prepared
Reading parts
9 chapters/parts
Published
Apr 29, 2026
Updated
Sep 14, 2026
BOOK IDENTITY

Author & publisher

Author
Moon
ABOUT THIS BOOK

Description

Tsit Court din da ke cike da mutane yai, ba abinda kake ji sai sautin fitar numfashi, gabadaya mutanen gun sun kurawa judge din dake zaune yana en cike cikin sa a wasu takar du ido kamar zasu cinye sa, can gefe kuma in da aka tanada don me lefi wata matashiya ce wacce bata fi shekaru 21 a duniya ba sanye prisoner’s attire, idanun ta dake a bushe ba digon hawaye ko kadan na kafe a kasa , ita kadai ta san me take ji, ita kadai tasan kalar zafin da take ji a cikin ranta, tun tana kukan tana kuma a ambatan cewa she’s not guilty har ta gaji, a halin yanxu mutuwa ko azaba sun daina bata tsoro burin ta daya shine ta samu koda mutum daya ne da ko bayan ranta xe amice da cewa ba ita tai wannan kisan kan ba, ammah da alamu haka zata bar duniya batare da ta cika wannan burin nata ba.
 
Bayan alƙali ya gyara takardun sa, ya kai hannu ya gyara sirin glasses din dake idon sa kafin cikin kakkausar muryar ya soma fadin “After carefully considering all the evidence placed before this court, the accused is found guilty of murder” “Accordingly, this court sentences YASMIN IBRAHIM life imprisonment.” yana gama fadin haka ya daki gavel din dake gaban sa. Nan take court din ya cike da maganganun mutane daban daban, gefe guda kuma sautin koke koke na tashi.
har yanxu babu ko digin hawaye a cikin idonta, se dai jikin ta ya shiga rawa ba kakkauta wa, a hanakli take motsa lips dinta tana fadin “la haula wala quwata illah billah” a karo na biyu judge ya kara buga gavel din sa ayko nan take akai Shiru Sedai sautin kukan wasu da be kare ba, gangar jikinta ne kadai ke agun ammah xuciyar ta da tunanin ta baya tatare da ita, bata dawo cikin hankalin ta ba har se da taji ana saka mata handcuff gamida dragging din ta xuwa hanyar fita daga cikin court room din, duk da koke kokon da take ji amma besa ta juya ba, suna fita bakin court din mutane da kuma en jaridu suka zagaye su, kamar kullum zagi, tsinuwa da kuma tambayar mesa kika kashe ta shine ke dira cikin kunnan ta, rintse idanun ta tai saboda hasken camera da ke barazanar dauke mata ganin ta, can kuma ta bude a hanakali tana neman sa tana kuma addu’ar Allah ya sa ta ganshi, can ta hango sa cikin attire din lawyer, en jaridu sun zagaye sa, ammah baya iya cewa komai, Idanun sa ne suka haɗu da na ta, a idon sa akwai wani abu da ya fi kuka zafi wanda shine rashin ceton ta. Bai motsa ba amma shiru ya yi magana a madadin sa, Se a lokacin taji wasu hawaye na bin kwancin ta, daidai nan aka shiga kokarin tura ta cikin motar prison, ganin hakanne ya sanya shi saurin fadin “waittt!!” Cikin karaji, ganin kamar ba zasu saurare sa bane ba ya sanya shi saurin kutsawa cikin mutanen yana ture koma wa ya gani a gaban sa, Ammah Ina kafin yaje an datse kofar motar, amma duk da hakan ya kara saka karfi gun kutsawa cikin mutanen har se daya samu damar xuwa gun wasu hudoji da yake iya hango ta tanan kafin cikin wata kalar murya ya furta “i failed you.” Girgiza masa kai ta shiga yi hawaye na bin fuskar ta kafin cikin murya marar sauti tace da shi “na-na gode” ta fadi hakan hawaye na cigaba da bin fuskar ta, kamar jira ake ta gama fadin hakan ayko motar ta shiga tafiya, se a lokacin ta maida kallon ta kan waenda ke kuka gamida kiran sunan ta, daga haka ta lumshe idanun ta gamida jingina da kanta jikin seat wasu hawayen na bin gefen face din ta a lokaci daya kuma tana tuna kalar rayuwar da tai tun bayan tasowar ta…. Kusan 3 mins da daina hango motar ammah be dauke idon sa ba be kuma motsa ba, cikin ran sa ya shiga fadin
RATINGS & REVIEWS

0.0 / 5 from 0 reviews

Sign in to rate and review this book.

No published reviews yet.
DISCUSSION

Comments

Sign in to comment.

No comments yet. Start the discussion.