← Book details Inuwar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 6 OF 9

chapter 6:

Inuwar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 18 min read

The Man Who Healed, The Man Who Hurt
*****
Bata san sanda tace
mami ce ta bani na sayo mata kanwa
kallon irin kin rena mun sense din nan ammah ke bin ta da shi kafin tace
ni zaki renawa hankali? Kanwa a cikin wannan dankareran gidan? an gaya miki ni yarinya ce da zan yarda da karyar ki? Ko kuma an gaya miki ni sha sha ce?
Girgiza kai yasmin tai kafin tace
da gaske nake miki ammah kin san bazan miki karya ba, sirikar ta ce zata xo yau shine tace tana son cin danwake, ta tambaye ni nasan inda ake saidawa nace mata ehh shine ta bani kudin ta ce na sayo mata, in ma baki yarda ba ki kira ta ki tambaya
ta fada a tsorace don sam bata saba karya ba wannan karan ma bata san ya akai ba taji tana zuba zance haka don bata da jurar yin magana me yawa balle ma har tai karya ko musu da mutum, Shiru ammah tai tana studying face din ta kafin ta cilla mata kudin tace
duk ran da ta baki kudi karki sake ki taba ko sisi ki kawo mun su nan, in ko ba haka ba na kama ki da su wallahi se kin yi dana sanin haifar ki da akai, fice ki ban guri
da sauri ta dau kudin ta fice daga dakin jiki na rawa, ba wai ba zata iya bata kudin bane ba, kawai ta san da ta bata shikenan ta kara bude ma kanta kofar ta kura a cikin gida. Ko abba batai ma sallama ba ta fice daga gidan
Tana xuwa titi ta hango motar na jiran ta, shiga tai bakin ta dauke da sallama, amsa mata habu yai yace
sannu da fitowa preety yau an makara
looking at another direction tace
ya kuri, kuma sunana yasmin
murmushi habu yai yace
kaji wani suna irin na larabawan misra, Daman ni ina ganin ki na san cewa ke fa ba pure er nageria bace ba, ammah jin sunan ki yau ya kara tabbatar mun da haka.
Banza tai masa ya cigaba da surutun sa shi kadai. Kamar wacce aka tsikara haka kawai taji harsh words din guy din jiya na dawo mata, ita tun da take wani na miji be taba mata haka ba saboda ita bata shiga harkar kowa balle ma a zageta har haka, daman dai ammah zagin ta ya zama mata abinci da sha don haka baya daga mata hankali but surprisingly wannan se crossing mind dinta yake. Vibration din wayar ta ce ya dawo da ita daga duniyar tunanin da take, tsirawa number din ido tai na tsawon lokaci kafin daga bisani tai picking ta kara a kunnan ta, Shiru tai bata ce komai ba, daga daya bangaren taji an ce,
Alhmdllh!! Alhmdllh!! Allah na gode maka, I thought I lost you na dauka you won
t pick up my call, ammah na gode sosai am over the moon, thank you so much thank so so much for picking my call
shiru tai don sosai ya bata mamaki jin yadda yake magana with full of excitement kamar wanda akaima Albishir da gidan aljanna all in the name of tayi picking call din sa, cikin sanyin murya tace
Assalamu alaika
alaiki Salam
ya yana me Jin natsuwa a cikin ransa.
kiyi hakuri ina ta damun ki da kira and early in the morning naxo ina cika miki kunne, Im so sorry kin ji?
Ya fada a hankali, jin tayi Shiru ne ya sanya sa cewa
hello?
don ya zata ta katse wayar ne,
hello
ta bashi amsa,
I hope I
m not disturbing.
s me, hakeem the man from yesterday
ta kula duk ya daburce ya ma rasa ta ina xe fara, ganin hakanne ya sanya ta fadin
na tuna, ina kwana
lfy kalau Alhmdllh
masha Allah
daga haka tai shiru, shi yai breaking salience din da fadin
i noticed that you don
t talk that much you preferred listening that talking right?
Shiru yasmin tai tana wasa da dogayen nails din ta, kafin tace
daga daya bangaren yace
That
s fine Some people talk less but mean more. I like that about you
daga haka kuma shiru ya dan wakana kafin cikin natsuwa sosai yace
in kin ban dama ina son inyi introducing kaina, that
s in kin ban dama
cikin natsuwa tace
ba damuwa
cikin muryar sa me dadin saurara ya fara magana kamar haka
My name is Hakeem Suleiman moddibo. Ni likita ne psychotherapist. Ina aiki a Hayat Specialist Hospital, am 29yrs kuma ni asthmatic ne, I live with my parents a nasarawa, I think that
s all about me, ohh na tuna, I help people deal with emotional pain and mental stress
amma tun ranar da na ganki, it
s like my own heart found peace.
A hankali ta sauke numfashi, ta ma rasa abun fadi, ganin kamar in tai shiru bata ce komai ba yayi sounding rude ne ya sanya ta fadin cewa
ohh masha Allah
daga haka tai shiru, she didn
t mean to sound rude or something like that kawai dai bata saba bane ba this is her first time da meeting someone like him.
Now you know me a little. Tell me about you, ko sunan ki ma ban sani ba
ya fada in a calm manner, shiru tai don bama ta san me zata ce masa ba don tambayar da yai mata ya sanyata manta ita wacece ma gabadaya. Can dai ta numfasa kafin tace
sunana, yasmine, Im 20, na yi secondary school dina GGSs dorayi babba, ina da siblings guda 4 nice babba a gidan mu
daga haka tai shiru tana jiran jin me zai ce,
masha Allah, I like every single thing about your introduction
sosai tai mamakin jin abin da ya fada din coz she thought he will look down on her ammah se taga shi praising din ta yake and she could feel the sincerity in his voice,
Yasmine gaskiya zan kara nanata wa kamar yadda dai na fada miki jiya, yasmine I like you. Na san ba mu dade da haduwa ba, amma zuciyata ta kar
e ki da sauri.
Shiru tayi, zciyarta tana bugawa cikin nutsuwa, gashi ta kasa cewa komai, cigaba da magana yai cikin sanyin murya
Ki yi hakuri idan na fada hakan da wuri. Im not trying to rush anything, I just wanted to be honest.
Yana gama fadin hakan yai Shiru yana me jiran abun da zata ce, Shirun kusan 30secs tai kafin cikin sanyin murya tace
baka sanni ba, baka san daga inda na fito ba, baka san hali na ba ammah kuma?
Ta kasa karasa zancen,
I know I know yasmin but that doesn
t matter at all, naji ban sanki ba and the rest ammah Sometimes xuciya takan iya haduwa da mutum daya, sai ta ce shi ne, hakan take nima a guri na, and maybe you won
t understand now, but I
ll keep proving it and i promised you that Im not here to play with your emotions neither your heart, Im here because ina son ki zama person dina my woman and also my safe place, kuma nima in kin amince zan so na zama hakan a rayuwarki.
Yana fadin haka yai shiru. Sanyayyiyar ajiyar zuciya tai kafin tace
Im speechless
koma me ki fada amma please banda turning dina down kinji
ya fada pleadingly, murmshi mara sauti ne yai escaping daga bakin ta,
Allah ya zaba abin da yafi alkhairi
ta fada a hanakali don batai ma tsammanin yaji me tace ba, excitedly taji yace
Alhmdllh, is that a yes?
palm din ta tai amfani dashi gurin rufe eyes din ta kafin tace
se anjima
to na gode yasmin Allah yai miki albarka, Allah ya sanya mu alkhairi ne wa junan mu, se anjima
uhumm
tana fadin haka tai ending call din. Ta dade tana kallon wayar, tana jin kamar muryar sa har yanzu a cikin kunnan ta, wani irin sanyi ya sauka a zuciyar ta wanda bata san dalilin saukar ta sa ba, amma ta ji kamar wani sabon abu ya fado cikin rayuwar ta. Tana dago kai sukai ido hudu da habu that was looking at her through the mirror, shaf ta manta a cikin mota take tare da habu har ta saki baki haka tana magana irin wannan a gaban sa, da sauri ta dauke idon ta daga kan mirror din, tana tamke fuskar ta sosai,
harkin gama wayar ne?
Ya fada yana sosa keyar sa, uffan bata ce masa ba ta maida idanun ta kan window, se a time din ta lura ashe ta dade tana waya coz har sun shigo street din su mamin. Tana shiga ta tadda bahar a parlo tana en goge goge, da sauri ta karasa cikin parlon tace
aunty ina kwana
cike da kulawa bahar ta amsa mata gamida yi mata sannu da xuwa, daga haka ta amshi aykin bahar din ita kuma ta cigaba da wani aykin daban. sosai take jin ta cikin farinciki fiya da ko yaushe don yau aykin duk wanda yaga yadda take yin sa za
a san cewa tana cikin annashuwa. Mami ce ta karaso parlon time din tana saka turaren wuta a parlon kasan, har mami ta zauna kan cushion bata sani ba se da ta ce
sannu da aykk Jasmine
sannan ta jiyo ta gaida ta cikin girmamawa, mami ta amsa mata da sakin fuska sosai kafin ta ce da ita,
in kin gama saka turaren wutan ki ce ma bahar ta nuna miki yadda ake hada rize tea if ta nuna miki se ki kawo mun nan parlon sama
da labadabi yasmin ta amsa mata daga haka ta dauki burner don sakawa a sauran bangaren gidan.
Suna cikin hada tea din suka ji ana danna bell din parlon, bahar ce ta je budewa ta bar yasmin din ta kula da tea din, sosai bahar tai mamakin ganin sa don mami batai mentioning cewa xe dawo ba,
sannu da dawowa
bahar ta fada tana barin bakin kofar, kai kawai ya nodding mata sannan ya shigo cikin gidan yana me kare ma parlon gidan kallo, inda yake da tabbacin cewa ze ga mahaifiyar tasa ya nufa, yana isa parlon upstairs ya tadda ta tana waya, kamshin turaren sa datai perceiving ne ya sanyata dagowa da sauri tana kallon direction din da yake, da sauri tai sallama da kawar tata da take waya da ita. Ganin yadda mom din nasa ke kallon sa ne ya sanya shi takowa gare ta ya zauna a kasa kusa da kafafun ta kafin cikin deep voice din sa yace
sannu da hutawa mami
ya fada kamar me koyan hausa,
I thought se next week zaka dawo? Ta tambaya tana me observing din sa da kyau, shortly yace
I needed to come home
alright welcome back
mami ta basa amsa itama shortly daga haka yace
I want to take a shower
Ohk muje nai escorting dinka part dinka
ta fada still tana kallon sa, she noticed that ya rame ammah ya kara haske sosai, jimmm yai na dan seconds kafin ya mike ya nufi bayan ta. leaving room ne me girman gaske se kuma two bedrooms manyan manya a part din nasa, komai na gun fari ne kall, ko ina se sheke yake da kyali ga wasu vases wasu da plants a ciki masu kyau a cikin su, duk iyayin sa ya yaba da kyan part din nasa don kusan exactly irin na gidan su ne na instabul duk wani abun da aka san yana bukata se da aka saka masa a ciki, mami na kai shi ta juya da niyar fita,
mami nazli fah?
Ya fada looking at their family picture da aka sakala a jikin bangon,
s having Stomach cramps ammah tasha magani tana bacci ne ynx
tana fadin hakan ta fice daga dakin nasa, direct kitchen ta nufa, tun kan ta karasa take jiyo muryar bahar na bawa yasmin labari, tana shiga ta tadda sun hada duk abinda ya dace su hada, mami ta zuba ma ingredients din dake kan table din ido kafin tace
ashe kun hada?
Bahar ta bata amsa da
ehh fah ni na bude masa door, shisa ma na hado kan ingredients din dan nasan zaki bukace su da gaggawa
mami tai murmshi ba tare da ta ce kala ba, nan ta shiga preparing masa favorite din sa
Fettuccine Alfredo
da shi da mahaifin sa sune kadai suke sata shiga kitchen koda basu ce tai hakan ba, more expecially shi don dad din sa dukda shekaru sun dan tafi yana iya cin junk food ba kamar shi ba da ya fi gane abinci sosai, shisa ma dan 1week din da sukai basa tare ya rame duk dan saboda be ci girkin ammin shi ba, don is very rare ya ci abincin da ba ita ta dafa ba don ko vacation zasu tafi shi yana gida se tai masa girkin anyi deep freezing nasa duk sanda xe ci se bahar tai masa microwaving din sa, haka ma sanda yai law school a abuja time din su mamie ma biyo sa sukai baki daya kamar wani yaro karami har ya gama daman nazli time din bata shiga collage ba so Harda ita aka taho bayan sun gama suka wuto kano sukai ziyara wanda shine last time din su na xuwa nigeria banda shi da in ya bushi iska yana xuwa saboda aykin sa na law da kuma company din sa.
Mikomun tea din na sha coz har wani dizziness nake ji saboda ban sha ba
ta fada tana me dafe kanta, da sauri bahar ta mika mata kafin tace
nasan dama zaki ji haka shisa na so ki fara sha kafin ki fara girkin
se da mami ta kurbe tea din tass duk da da
a kwai zafi kafin tace
baki ga ya rame ba? kuma nasan duk dan rashin cin abincin ne ya sanya
ta fada tana cigaba da juya alferdo sauce din da kamshin sa ya gama bade kitchen din, tunawa da tai yau ba
a saka turaren wuta a part din nasa bane ba ya sanya ta umartar yasmin da ta kai bummer ta saka masa turare a part din nasa, ba bata lokaci yasmin ta fice daga kitchen din ta nufi part din nasa bayan mami ta kwatanta mata don ko dakin mami bata taba shiga ba talkless of na wanda taji ana magana akai.
Tana isa bakin door din parlon sa taji kirjin ta ya wani buga da karfi, da sauri ta rintse idanun ta tana biyo
ila ha illah anta subhanaka inni kuntu minaz zalimeen.
Se da ta daidai ta kanta sannan ta shiga katon parlon, indeed komai na gidan tsararre ne ammah wannan part din ya mugun tafiya da ita don sosai ta bata minuets tana kallon cikin parlon bayan tayi connecting burner din a jikin socket which is not her habit,
who are you? And what do you think you are doing?
Muryar sa ua dira cikin kunnan ta, he hated seeing strangers in his space, don ko nazli bata fiya shiga part din sa ba don sanin wannan halin nasa, duk da dai bata juyo ba amman yana ganin ta ya sheda cewa er ayki ce don kaff both families din su babu wanda ke dressing kamar haka, cikin firgici da tashin hankali tace
ka-ka yakuri mami ce ta sani
tana fadin haka ta juya da sauri zata fita,
keh!! Who ask you to leave?
ya fada cikin muryar sa me amo, bata san sa
addah ta dawo ta tsaya nan position din data tsaya daxu ba tana sunkuyar da kanta kasajikin ta na rawa
who is dis guy da yake mata iho daga haduwar su kamar daman ya santa a wani gun? Abun da ya ma fi tsaya mata arai shine yadda take Jin kamar she knows his voice ammah ta gaza gane a ina ne ta taba ji, a bangaran sa kuwa his eyes narrowed slowly, studying her face until recognition hit him like a slap hakan ya sanya shi fadin
you??
Da wani kalar expression a face din sa irin disgusting one din nan, Yasmin blinked confused, wanda hakan ya sanya ta dan dagowa a hankali ta dubeshi wanda dagowar ta keda wuya ta ci karo da fuskar da take zaton baza ta taba mantawa ba a rayuwar ta, nan da nan taji throat din ta ya wani bushe, xuciyar ta ta wani buga da mugun karfi, bata san sanda ta shiga karanto addu
oi ba don tafar daya ta gane cewa he
s the same man whose wallet she returned yesterday, the man who embarrassed her in his office and offered her money like she was cheap, kuma gashi yau ya bayyana a matsayin dan gidan da take aykatau a ciki
Omair suraj
tabbas bata manta sunanan sa ba, da sauri ta sauke kanta kasa tana jin kamar ta sheka da gudu, daga wani part din na ranta kuma tana tuna kalan wulakancin da yai mata jiya daga taimako kawai. Katse mata tunani yai da fadin
You found a new way to get close, didn
t you? Next time you will accidentally find my watch and bring it me right?
ya fada yana hade girar sama da na kasa, ji tai hawaye na taruwa cikin idanun ta wani abu me daci na kai komo a cikin makogaron ta, cikin rawar muryar tace
Ba haka bane, ban san kai ne dan gidan ba, kuma ni ba hali na bane bibiyar mutane ba
mockingly yace
Oh, of course. Always innocent. Always humble.
Ya fadi hakan yana me stepping closer to her, his voice low but sharp, hakanne ya sanyata yin baya da sauri, wani dan isakan kallo ta jefa mata kafin yace,
stay out of my way. I don
t like people like you the ones who pretend to be saints
Da kyar ta iya hadiya abun da ya tsaya mata a rai kafin tace
na fahimta, nima bana son mutane kalar ka
tana fadin hakan ta juya ta fice daga room din nasa, baki bude yabi ta da kallo Jin abun da ta ce, da dogon finger din sa yai pointing kansa kafin a fili yace
did she really knows who I am or she
s just clueless?
Tana fita daga dakin kawai taji hawaye na xuba daga idanun ta da sauri ta kai hannu ta share, mami ce ta karaso gun hannun ta dauke da tray babba, ganin mamin ne ya sanya ta kara dedeta natsuwar ta,
sannu da kokari jasmin kije kici abinci se ki huta
a hankali tace
toh mami
tana fadin haka ta bar gun ita kuma mami ta shiga dakin nasa. Jun an bude dakinne ya sanya shi saurin dago kai rudely dan ya dauka ita ce ta kara dawo wa, ganin mami ce ya sanya sui xura wayar sa cikin aljihun hoodie din sa sannan ya nufe ta ya amshi tray din hannun ta, mami bata bar dakin ba har ya gama cin abincin kuma bata ce masa komai ba har se da ta tabbar ya nustu sosai sannan ta dube sa tace
tun yaushe kazo nigeria?
Ta jefa masa tambayar, a tsanake yace
3days ago
shine se yau zaka xo koh? Saboda ka dauka daddy na nan shine baka xo gida ba se yau? Wai omair me yake damun ka ne? why all these saboda Allah? For how long zaka manta da duk wannan?
Ta fada looking so disturbed, Shiru yai na seconds kafin yace
mami i don
t know why? bansan me sa ba nak..
shiru yai ya kasa karasa maganar tasa, nannauyar ajiyar xuciya mami ta sauke kafin tace
Tohh Allah ya kyauta, ammah ka sani shi babanka ne and kuma shi ke sama da kai, also where
s suhaila? Mesa ka barta acan bayan da kai ya kamata ta dawo if ta gama exams din ta?
bata gama exams ba and akwai urgent work da ya taso a nan nigeria
daman I wanted to tell you something
she was speechless gabadaya coz if akwai branch din sa da yafi bama rashin mahinmma ci toh tabbas branch din sa na Nigeria ne, don shi da Nigeria sedai in something related to aykin shi na law ne wanda shima yake wulakanta aykin se case yakai case sannan yake participating, bata manta sanda ya gama karatun sa na law se da kyar ya yadda yaxo Nigeria don yin NYSC da kuma bar exam. Mami ta tattara duk natsuwar ta tana kallon sa kuma at same time tana fatan ba abunda take tunani bane ba
mami is over
looking so confused tace
me kake nufi da is over ehh omair? Nace me kake nufi
ta fada tana me kallon shi da wani kalan expression akan face din ta, he wasn
t the type to repeat himself ammah kasancewar mami ce hakan ya sanya shi cewa
mami I can
t marry her Allah ya hada ta da wani kawai
a fusace mami tace
are you out of your senses? She
s your cousin fah, me kake so mutane su ce? What about the innocent girl and su hajja da suka kwalla fa rai akan auran nan? So kake ace ni na hanaka ko me?
Calmly yace
I don
t care what the family thinks. I
m not marrying someone I don
t love
se yanxu? A
a omair u are not telling the truth, tunda baka ce haka ba se yanxu? definitely something is wrong tell me am all ears
babu komai i just realized that I will hurt myself so the girl
a zafafe mami ta ce
Se yanxu kasan you dont love her se da aski ya xo gaban goshi sannan? Yanxu kai ka kyauta ma kanka? kasan ma dad din ka baxe yarda da wannan maganar ba so kar ma ka kara wannan maganr dan Allah ya zama daga kai se ni
ganin yayi shiru ne ya sanya ta kwantar da muryar ta kafin tace
look ka zauna kaida suhaila kuyi sourting things out I promised you that zaku fahimci juna, nasan suhaila bata da damuwa amma kaima kuma if ka daina mata kallo as sister dinka kuma ka sauke duk ego dinka ka fuskaci reality komai zaka ga ya zama daidai
tai Shiru still be ce komai ba se kuma ta kara da cewa
kaifa ba yaro bane ba u are 30, 30 solid years ya kamata kasan me kake yi
i have already told her mami
shiru mami tai na kusan 1mins kafin daga nan tace
toh shikenan Allah ya sa hakan shi ya fi alkhairi, se kasan me zaka ce ma su hajja da daddy also ka samo wacce zaka aura nan kusa tunda ka ki er uwar ka
tana gama fadin haka ta mike ta fice daga dakin
NOTE: (duk yawanci maganar da mami take yi da omair da Turkish language ne saboda shi ne yaren da suka taso suna yi duk da kuma suna jin hausa, english, Arabic da kuma sauran foreign languages ammah zamu ringa yi da hausa don saukin fahimta daman kuma ni bajin Turkish language din nake ba lol)
INUWAR KADDARA (THE SHADOW OF DESTINY)
By moon
Chapter 6 · 0% Book details