← Book details Ig Ajeemal Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 12

Sashe 7

Ig Ajeemal Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ajmal koda ya fito da nufin haurawa upstairs ya nufi bedroom dinsa time Heelah itama ke ta fe ta nufo downstairs sai faman mika take gamida dogon hamma because tayi jiransa harta gaji, kallo daya Ajmal yayi mata ya kauda kai kamar bai ganta ba ya ratsa gefenta ya shige abunsa , Heelah da rakiyan idanu tabi bayansa gamida tab'e baki kafin ta iya karisa takowa tadawo tsakiyar parlourn ta tsaya tana jin wani sabon haushi da takaicin Nisha da ke k'ara lullub'e zuciyarta .

Ajmal na shiga bedroom dinsa cire kayan jikinsa yayi ya fad'a bathroom wanka yayi kafin ya fito ya kimtsa jikinsa ya shirya cikin kyakykyawan jallabiyarsa kafin ya nemi saman katafaran lallausan bed dinsa ya kwanta yana mai lumshe idanu gamida saukar da ajiyar zuciya a hankai.

Turo door din da akayine yasa Ajmal waro manyan sexy eyes d'insa gamida maido da kansa da idanunsa ga door din ganin Heelah ce dauke da tray bisa hanunta sai kauda kai yayi gamida mai da idanunsa ya kuma rufewa sai wani faman had'e gira yake yana had'e fiska .

Heelah can saman table ta nufa da d'an madaidaicin tray din kafin ta dawo gefe da shi ta zauna tana kallon kyakykyawan face dinsa hanunta dauke da cup din coffee ta na fad'in

"Ga coffee kashaa nasan kanada bukata" .

" Bana bukata ".

Ajmal ya fad'i a takaice ba tare da ya bude idanunsa ya kalleta ba, cike da rashin jin dad'i Heelah ta sauke cup din coffee kasa tana fadin

"Nasani bakaji dad'in ganinaba sam bakaso na dawo na katse muku jin dad'in ku ba, ".

Heelah ta fadi cikin sanyin murya tana sunnar dakai kasa gamida matsar k'wallar bakin ciki da ta kaici kafin ta cigaba da fad'in

"Nina rasa maisa ko shaawar had'a idanu da ni bakason yi ballai ka kalleni ka tsaneni bakasona k'wata k'wata maiye laifina?" Nifa 'yar uwar kace bayan mata a gare ka kuma uwa ga d'anka Aheel".

Heelah ta kuma fadi cikin face din tausayi

"Hold down please banason damuwa da wadan surutain naki I'm tired ni ban tsaneki ba but bazan soki ba ko nan gaba".

"Daga haka Ajmal ya juya mata baya yana mai g' yara kwanciyarsa still ba tare da bud'e ya kalle ta ba

Zuciyar heelah kaman ta bashe nan da nan ta suma Sharan hawaye gamida da mikewa tanufi tray din da ta shigo da shi ta ajiye cup din coffee ciki wanda tuni ya suma hucewa ta kwashi tray tayi gaba tare da k'ud'irawa ranta cewa tunda Ajmal ya fitu kiri kiri ya fad'i mata bazai taba sonta ba to daga shi har Nisha sai tasa sunyi bakin ciki a rayuwa zuciyarsu ta k'untata kamar yanda suka k'untata mata nata ayanzu..

washe gari karfe 7: Ajmal fitowan shi daga wanka kenan sanye cikin kyakykyawan bathtub hanunsa rike da wani karamin towel yana mammatse suman kansa yana tsantsame ruwan dake suman, turo door din da akayine ana kokarin shigowa wanda a tunanisa heelah ce because ita kadai yake thetunanin zata iya ziyartarsa gamida ta kurasa a wannan lokacin but jin muryan Nisha da sallamanta sai ya kawar masa da tunaninsa.

Nisha ganin shi da tayi haka sai taji nauyin karisawa ciki ta tsaya tana zare idanu ita bata shiga ba ita bata koma ba,

"come in ".

Ajmal ya fadi gamida mamakin meya kawota da sassafen nan, Nisha hannayenta zube cikin duguwar hijab dinta jikin ba kwari tashiga jan jiki ta gamida karisawa tsakiyar dakin kafin ta durkusa saman lallausa carpet din cike da ladabi ta shiga gaishesa

"ina kwana".

"lapia ".

Ajmal ya amsa mata still idanunsa na kanta

"antashi". Nisha takuma fadi

"I'm fine".

Ajma ya kuma amsawa cikin kosawa da gaisuwan nata gamida dauke kai ya shiga kallon kansa jikin mirror ya cigaba da abunda yake

"what's your problem".

Ajmal ya tambaya ba tare da ya kallo taba, a hankali Nisha tazaro hanunta dake ta faman rawa cikin hijab tafidda kudin da ajmal ya bata bisa hanunta daga bisani ta daura masa kudin bisa table tana fadin

"Ga kudin ka bani da bukatarsu it means bansan mai zanyi dasu ba kuma dan Allah ni ka kyaleni anan bani da bukatar zuwa ko ina please..".

Nisha ba takai ga karisa maganar ba wani juyawo da ajmal yayi ya watsa mata wani kallo yasa ta hadiye sauran batun nata tashiga zare masa idanu

"Are you mad ".

Ajmal ya fadi a tsawace cikin kakkausan murya yana ta kowa inda Nisha take wanda yasa yan hanjin Nisha kadawa ta mike a zabure tana fidda idanu waje ta suma kokarin baya da nufin barin bedroom din cikin hanzari datsoro, aikuwa taku daya zuwa biyu kafin ta ankare ya fizgota cikin zafin nama yana fadin

"you are very stupid 😡 "

Ajmal ya fad'i rai a matukar b'ace ganin tsaurin ido irin na yarinyar gamida taurin kai dayi masa musu cikin lamuransa tana kokarin jayayya dashi

Hakuri Nisha ta shiga bashi cikin tsoro gamida jin zafin rikon da yayi mata yariko hannayen duka biyu ya had'e su bayanta yana jijjigata yana cigaba da magana

"kinada taurin kai bakya jin magana saina ta surutu ".

Ajmal ya fad'i time din da ya kai hannunsa jikin kunnenta ya jaa da d'an karfi wanda yasa Nisha ta saki wani kara mara sauti tana fad'in

"Dan Allah kayi hakuri na tuba ".

cikin magiya da marairai cewa da kyar ajmal ya kyaleta yaja baya Yana hararo Nisha da ta ja baya itama tana muzurai gamida fidda idanu waje

" This is the first and last da zaki karayimin musu ga duk wani batuna dan gane da ke ".

Ajmal yafi ya na kuma watsa mata wani banzan kallo, jiki na rawa ta shiga gyada masa kai alamar gamsu kafin cikin hanzari ta nufi hanyar fita , ajmal ya kuma dakamata wani uban tsawa ya dakatar da ita a tsawace yana mai umartarta data dauke masa wannan kudin ta fice masa daga bedroom dinsa aikuwa kafin ya gama rufe bakinsa daga maganar da yake Nisha ta nufi inda ta ajiye masa kudin ta fice da sauri har tana yar tuntub'e.

Guraren 7:20 Ajmal ya kimtsa ya gama shiryawa tsaf cikin kyakykyawan kananun kaya black t shirt mai dugun hanu mai mab'allai a tsakiya gamida dugun wandon jeans milk colour mai taushi da sulb'i saman kansa dauke da kyakykyawa p-cap yayi kyau har ya gaji .

phone's dinsa kawai ya dauka ya nufo downstairs, koda ya kariso sofa ya nema ya zauna gamida daura daya bisa daya ya shiga ya shiga danna phone dinsa...

Nisha ce tafito cikin kyakykyan shirinta duguwan rigar abaya ash colour mai rintsin baki baki rigan tayi matukar kyau da kayatarwa sai farin mayafi da tayi Rolling saman kanta ta fito kamar wata kyakykyawar balarabia, tayi matukar kamar asaceta a gudu.

Nisha idanunta ne ya sauka cikin na Ajmal dake zaune bisa parlourn sai da taji k'irjinta ya d'an harba , shikuwa AJmal yana daga zaune yake wurginta da kallon up and down

Ajmal
story and writing
by
Oum amreesh

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

*_ TAKUN KARSHE_*

book 3

page 1️⃣0️⃣1️⃣

______. Nisha shafo gefen wuyanta ta shigayin fiki fiki da idanu da tasan Ajmal na parlourn da ba abunda zasa ta fito yanzun because dama yunwane ya korota daga ciki ta fito neman abunda zata sanyawa cikinta saboda yau ta tashi da wuri kuma takasa komawa bacci dan haka sai taji cikinta a fafake yunwa ta tusota gaba.

Ajmal ganin Nisha tsaye can ita bata kariso ba kuma ba ta komaba yasa ajmal yimata kiranye da hannayensa alamar ta kariso wanda yasa Nisha ta daga k'afafu ta shiga karisawa tsakiyar parlour gamida samun guri gefe ta tsaya kanta kasa

"ke!"

Ajmal ya fad' i cikin cold voice mara sauti wanda yasa Nisha dago rinannun idanunta wadanda suka kumburu alamar taci kuka harta godewa Allah

Ajmal ba k'aramin tausayin yariyar ne yake d'ibansa ba but wani lokacin tauri kanta ke jawo mata wahala gunsa, sam bata jin magana tafiye tirjiya sai da ya kare mata kallo na wasu ayan mintuna kafin ya kauda kai yana fad'in

"coffee zaki kawo min ".

Aikin kenan Ajmal mayen coffee ne na gidan gaba sai yasha coffee sau biyu a yini safe da dare , ba musu Nisha ta nufi kitchen kyakykyawan coffee ta dauko ta koma dining area tashiga hado Masa zazzafan coffee kafin ta dawo ta mika masa cikin ladabi gamida kulawa shikuwa ya amsa ya rike bisa hanunsa ba tare da ya kalleta ba Nisha harta suma jan k'afa da niyar barin gurin sai tsin kayan muryan Ajmal tayi ya dakatar da ita ya na fadin

" wait! "

Nisha tsayawa tayi tana jiran taji yace wani abun but sai taji shiru yana ta faman latsa waya yana k'urb'an coffee ba tare da ya kalleta ko yace wani abinba, Ajmal sai da ya shanye coffee tas kafin ya mike tsawonsa ya tako inda take tsaye dab da ita har numfashinsu na koran najuna wanda yasa cikin Nisha tsurewa ta shiga zare masa idanu tana kallonsa sai da Ajmal ya huro mata sassanyan iskan bakinsa ya hure mata y'an idanun daga kallonsa da take tana zare masa manyan idanuta kamar wacce taga dodo sanan yace

"Dai na kallona haka ki dinga rage power idanunki yayin hada ido dani".
Chapter 7 · 0% Book details