← Book details Ig Ajeemal Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 12

Sashe 2

Ig Ajeemal Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Allah yasa bawani babin wula kacin zai bude mata ba kasan cewar dawowar ta tsaginsa saboda a tunaninta ganin cewar ya tatare dakinsa but ba iya biyowa ta kanta ya duba ta ballai yasan mai take ciki, zare mayafin saman kanta tayi ta janyo ledar take kallah ta shiga dubawa , abubuwan da ake kawo duk wata amarya ce a ciki abubuwan ciye ciye barkate gasunan hanu ta sa ta ja goran yughourt ta bude ta kafa bakinta ba tare da wani ta raddadiba ta suma shaa because yunwa take ji sosai rabonta da abincin zata iya cewa tun safe shima cin sama sama ne.

Sai da ta sha ya kusa rabi kafin ta sauke tana ajiyar zuciya gamida komawa tayi lamo jikin sofa ta k'udundune jiki tana wulga yan idanu Nisha yanda taga rana haka ta ga dare sam ta kasa tsugul ta kasa nitsuwa ga tsoro da take ji ita kadai parlourn shiru ga kuma ta kaicin rashin k'arama wannan dare da Ajmal baiye ba yayi mata banza ko in kula kamar baisan da zaman taba ya kasa fitowa ya dubata halinda take ciki.

Haka Nisha ta dinga g'yang'yad'awa gurin tana farkawa a haka har bacci barawo ya sace ta gurin kwance, da suba k'iraye k'iraye sallah a kan kunne Ajmal ya sauka wanda ya sanya shi bude idanu gamida salatin annabi yana mika yana sauke duguwar hamma.

A kasalance Ajmal ya yaye blanket din da yake lullube ciki ya zaro santala santala kyakykyawan fararen k'afafuwansa ya zamo daga saman bed din ya nufi bathroom ya wanko bakinsa gamida yin alwala ya fito ya sanya fara jallabiyar sa yanufi hanyar fita .

Koda ya nufo downstairs ya iso tsakiyar parlourn sai Nisha ya kalla kwance saman sofa bacci yayi nisa tana sanye cikin adonta na amare ga mayafinta gefe yana lilo dan kallabin kantama ya bar saman kanta.

lumshe idanu Ajmal yayi jin wani abi da ya tsikare zuciyarsa gaba daya sai yaji ba dad'i ganinta haka shi kansa yasan bai mata adalci ba but ba yanda zayi because jiya ya tsinci kansa cikin gajiyar sosai da bai taba jin irin ta ba ta wannan ban garen .

Karisawa yayi har sofan da Nisha ke kwance yasa hanu ya sunkuce ta daga ita har mayafin nata wannan karon baccin Nisha yayi nisa don ko jin Ajmal ya daga ta ba tayi ba.

Cikin bedroom d'inta Ajmal ya mai Nisha ya nufi bed da ita ya suma k'okarin kwantar da ita but sai ji yayi tsam Nisha ta rike hanunsa bisa k'irjinta ta run gume

"Uhm please karka tafi kabarni, bana son kasake nisa dani na yi kewarka sosai". Nisha ta fad'i cikin muryan bacci tana sake shigewa jikinsa, Ajmal mamaki ya ishe sa yaushe daren ma yayi ba lallai gari yawaye ko mai take fad'i haka nan Ajmal ya sake janye jiki gamida jan hanunsa dan karfi yayi baya yana kallonta.

Ita kuwa jin yanda ya janye yasa ta dan bude idanu ta ware su bisa face d'in Ajmal wanda ke tsaye yana binta da wani kallo cikin mamaki duk da yasan ba cikin hankalinta take wannan sun batun ba sake waru idanu tayi ganin Ajmal tsaye bisa kanta yasa ta mike daga kwanciyar tana zare idanu gamida kallon d'akin da tunanin yanda tasamu kanta ciki tunda tasan dai ba anan ta kwanta ba but ganin Ajmal cikin bedroom din shi ya bata amsan tambayar ta.

Dan tura baki Nisha tayi gamida juya baya ba tare da sake kallon Ajmal wanda yake tsaye ba because haushinsa ne tab cikin zuciyarta saboda halin rashin ko in kula da ya nuna mata jiya time din da aka kawota ko lekata bai yi ba , yanzu harda dauko ta ya maido ta bedroom ko waya akesa oho Nisha sai tura baki take tana sumbatu.

Shi kuwa Ajmal ko takan yanayin da take bai bi ba sai sake kallon Nisha yayi wacce ta juya masa baya yana fadi'n

Asuba tayi ki kije kiyi alwala ki daura niyar yin sallah kafin Ajmal ya kai ga karisa maganar sai tsintar muryar Nisha yayi da cewa

"Bana yi " . yanda ta bashi amsa a fisgene ba tare da kuma ta jiyo ta kalleshi ba yasa Ajmal suma lalub'o face d'inta dan ya tabbatar da itace mai ba da amsar ko dai yar yanzu cikin yanayin baccin take .

"Mai kike nufi?". Ajmal ya tambaya yana hade gira ganin cewa cikin hankalinta take infact ma idanuta a bude suke , jin wata tambaya da ya kumayi yasa Nisha ta jiyu rigigine face d'inta na kallon celling tana fadi'n

"Eh fashi nake ina period". ta bashi amsa ba tare da takalli sun hada ido ba, Ajmal bai iya ce da ita komai ba jin yanda take bashi amsa tana wani ya mutsa gamida tura baki yasa yayi tunanin ba sense d'inta take ba shiyasa take bashi amsa gaba gid'i .

Ajmal yasa kai yayi yafi ce daga nan ya fito ya fice yanufi masallaci cikin hanzari because har yana shirin makara anshiga, ta ban garan Nisha ita kanta mamakin kanta ta karfin gwiwa wajan tsintan kanta dayi masa rashin kunya wanjan bashi amsa but Allah haushinsa ne fal cikin zuciyarta duk da tasan kad'anne daga halayensa bai kamata ta daurawa kanta damuwar hakan ba especially da tasan kallon jeka nayi ka yake wa auran.

Ajmal

Story and writing
By
Oum AmReesh

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

Book 3

Page 96

______Rintsa idanu Nisha tayi gamida mirginawa ta sakko daga saman bed d'in jiki ba kwari ta suma cire nan nauyan laces din dake jikinta wanda take jin yayi matukar ta kurawa jikinta sai da ta zame tufafin jikin nata da duk wani kyale kyalen da ke jikinta sai da ta cire because tun ba yanzu ba suka ta kurata sai yanzu ta samu daman ciresu.

Daga nan ta nemi towel ta daura bisa jikinta tare da shigewa bathroom dan tsaftace jikinta daga nan ta fito da towel bisa k'irjinta bedroom din ta bi da kallo mai fadi'n gaskiya shi kanshi bed din dake bedroom din gari guda ne ko a mafarki ba taba hasashen kasan cewa cikin wannan daular ba komai dake ciki sabone sai ta samu kanta ba kuwace ciki bedroom din tama rasa inda zata dosa daya, dugun wardrobe din tabi da kallo inda aka jira mata kyawawan trolleys d'inta maroon colour da kasa gefe kuma shima wani jerin trolleys ne dark blue reras gwanin sha'awa .

Nan tanufi jerin trolleys d'in ta janyo guda ta Suma kallon tarin kayan da ke ciki duk tarin kayan dake ciki rasa na sawa tayi domin duk yawanci manyane kuma masu nauyi kuma duk din kakune sai wanda ta zab'a but ayanzu bata da bukatan kayan da zai takura jikinta.

Gefe ta janyo wani katuwar trolley d'inta wanda ta sanya kayanta da take bukatan kasan cewa dasu ta zuge zip idanunta ya sauka kan wata duguwar rigar material mara nauyi tare da mayafinta ta janyo shi gamida mai da zip din trolley d'in ta rufe ta dauki kayan ta suma sawa ta fito d'as da ita.

Parlour ta koma ta nufi saman table din inda ta bar ledar haka ta tadda shi dan haka tashiga tattare ledar ta nufi kitchen duk wani abin ya lalace cikin ledar sai cirewa tayi daga nan ta sanya sauran abubuwan cikin fridge ta ajiye daga nan ta fito ta koma bedroom d'inta.

Saman bed din ta ta koma ta kwanta abunta domin kuwa bacci ne sosai idanunta kankace mai tuni bacci ya dauke ta, duk da baccin nata bawani tsaye yayi ba guraren 9 da wasu mintuna ta bude idanu gamida tashi ta mike daga saman bed din ta koma bathroom ta wanko face d'inta kafin ta ja jiki a hankali ta tunufi hanyar fita ta nufo parlour.

Ko da ta fito sai cin karo da Baraka tayi wacce tashigo ta ajiye musu breakfast bisa dining table wanda jin motsin fitowar Nisha ne yasa Baraka sakin murmushi gamida karisowa inda Nisha ke tsaye tana fadi'n

"Sannu yar nan an fito?".

G'yada mata kai Nisha tayi tana yar murmushin itama gamida duk'ar da kai tana fadi'n

"Ina kwana antashi lapia?."

"Lapia qalau yar nan ya kujuba kujuban biki?".

"Alhamdulillah".

Nisha ta amsa gamida dago kai tana kallon dining table din da Baraka ta jere musu breakfast domin fitowar da tayi yanzu Shirin da ta fito da shikenan na hada musu breakfast but sai ta ci karo da Baraka a parlourn time din da ta ajiye musu tray din breakfast din.

"Dama abun kari Ammi ta ce na kawo muku to nashigo ma tun dazu ina ta doka sallama na ji shiru har na ajiye zan fice sai gaki". Nisha ta tsinkayi maganar Baraka

"Ayya Ammi da bata wahalar da kanta ba shirin da na fito da shikenan".

"Lah yar nan mai ma akayi ai cewa tayi daga nan har sati biyu ma bazata so ki shiga kitchen ba sai kin huta sosai, ". Baraka ta fad'i tana washe baki.

Murmushi kawai Nisha tayi cikin jin dad'in da irin kulawar da so da Ammi take nuna mata ko ummanta iya ka so da kulawar da zata nuna mata kenan.

"Hala su Reeda sun tafi ?".

Nisha ta tambaya cikin raunin murya

"Ayya amarya fareeda sun tafi tun d'azun idan ba su isa yanzu haka ba to sun kusa isa ".

Dan jinjina kai Nisha tayi ba tare da tace k'ala ba jiki a sanyaye cikin rashin jin dad'i da kewa Allah sarki rayuwa wannan shine ba a mutuba anrabu .

Daga haka Baraka ta fice gamida yi wa Nisha sallama ta fice daga parlourn Nisha kujera ta zauna tana rintsa idanu idanunta har sun suma tsatstsafo da k'walla, jim kadan Nisha ta mike daga zaunen da take ta kai kallonta ga Upstairs Tana jiran motsin sakkowan Ajmal but shiru har dai ta gaji da tsayuwarta ta koma dining table din taja kujera ta zauna gamida kife kanta jikin table din .
Chapter 2 · 0% Book details