Sashe 3
Hasashe Ko Buri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Na haƙura nikam, ki shiga Allah ya sa ki da ce.” daga haka ta wuce, take jikinta ya yi sanyi, sannan ta nufi ƙafan ta tura a hankali, tana sallama a cikin ranta.
Duk da tana cikin niƙaf amma sai da lafiyyan ƙamshi ya dake ta, lumshe idanunta ta yi, sannan ta kalla officer ɗin, ba laifi ya haɗu, duk da akwai abubuwa da ko ina na da ga na'urori, cameras da dai sauransu. Namiji ne ta hanga tsaye jikin glass yana kallon haraban gidan tvn, matsawa ta yi ta zauna tunda ya ji ya tashi. Tsaye yake cikin manyan kaya, hannusa riƙe da flask tea yana sha a tsaye, juyowa ya yi tare da nufo in da take tsaye sannan ya mata alama da ta zauna, a ɗan daburce ta zauna dan ya mata ƙwarjini. Guy ɗin ya haɗu ma sha Allah, dogo mai cikar kamala. Shima zama ya yi. Yana mai kallonta dan ko ƙyayar idanunta ba ya gani.
Take wayarsa ta kuma yin ringing sai ya ɗaya.
“Darling still mace ce......” take ta jiyo muryan mace ta cikin wayar tana cewa.
“Ta yi waje, na faɗa maka maza zalla.”
“Wanan matar aure ce fa.” ya faɗa yana kuma kallon yarinyar da ke zaune.
“Juya cameras kanta ya yi.” kafin ya yi magana ta katse, sannan ya yi latse-latse a System, ba'a jin ba ma wayar ta kuma yin ringing.
“Ka mata interview ɗin.”
“Okh my Darling.” daga haka ya sauke ajiyan zuciya yana mai faɗin.
“Takaddu.” da yake ta ciro sai ta miƙa mai ba tare da ta falle rubutun ba, ya amsa yana dubawa.
“Uhmmm your full name.” da sauri ta miƙa mai wani paper ya amsa ya kalla. (My name is Ameeratulkhairi. Sa'adatu Jibril) shine a rubuce sai ya ɗago da ɗan faɗa.
“Ba ki da baki ne, dan kina matar aure, ba za ki yi magana ba?.” da sauri ta kuma miƙa mai wani, kamar ba zai amsa ba sai ya amsa. (Bana magana, Bebiya ce.) Take ya ji wani abu ya tsirga a zuciyar sa. Sannan yaji tausayinta sai ya aje.
“Na fahimta, kinsan kafin na baki aiki dole kiban labarin ki, da dalilin son aikin journalist, da kuma irin gudummawar da za ki ba da sai kuma wani fanni dan na ga ba ki yi zurfi a karatu ba.” ɗaga mai kai ta yi sannna ta cori wani littafi tana miƙa mai. Ya amsa yana mai buɗe wa. ( Buri na shine zama ƴar jarida) shine ya fara cin karo da shi sannan ya ɗago ya kalleta.
“Ki je gobe ki dawo, misalin 1:30pm, in dai labarin ki ya gamsar shike nan.” godiya ta mai da hannu sannna ta yi fara tafiya, sai ya samu kansa da bin bayanta da kallo da sauri ya ɗauke kai yana cewa.
“Ki gaidamin mijinki, bangan shi ba amma ya burgeni da yake sa ki yi wannan shigar.” murmushi ta yi tana mai ɗaga kai tafice. Take ya hasaso Darling cikin shigar nan za ta yi ƙyau amma ko mutuwa zai yi ba za ta sanya ba, yara sa maike yawo a kansa ne, da zarar ya bar gida yakan ta jin wani yanayi akan ta da kuma abubuwan da baya so ta na yi, amma da ya ji muryanta ko ya koma gida shike nan sai ya mance. Kallon rubutun ya yi da ya yi mai mugun ƙyau, ita ce ta ƙarshe dan haka ya buɗe shafin gaba. (Labari na mai ɗauke da darasi da haƙuri.) Sai ya yi murmushi ganin rubutun da yawa ya sa ya miƙe sannan ya hau kan sopa ya hau karatu.............
*ABUJA*
Office ne wanda yake cike da takkadu, zaune yake kan kujera yana latsa system sannan yana kallon screen ɗin, knocking aka yi ya ba da umarnin shigowa. Take aka shigo, wani saurayi ne sa'ar shi, yana rike da laptop ya ce.
“Aboki na kammala.” sai ya kalla abokin na sa ya ce.
“Good job, yau za ka raka ni wani waje.”
“Hmmmm na san yanzu burinka kawai kake so ka cika, amma a ganina Ukasha ka sauya shawara please.” sai ya bar latsa system ɗin ya zuba ma abokin na sa idanun.
“Umar, dole na cimma wannan burin na wa, a yanzu biyu na ƙasa saura biyu, na tambayeka, burina zan fasa? ko na Hussain ɗina?.”
“Haka ne, shike nan, Allah ya cika maka burin na ka.”
“Ameen Umar, nan da watan biyu nake so na yi auren.” sai Umar ya ja numfashi yana kallon Ukasha take magana a cikin ransa.....
'Shin kunsan waye Ukasha?, Kunsan labarin rayuwarsa? Kusan ya halinsa? Kunsan ya nake haƙuri da rayuwa da shi? Kunsan ya yake ɗaukan Burinsa? Wai ma kunsan menene Burin? To Bara na baku labarin a kan Ukasha da kuma Burinsa...........✍️
> To Umar za mu haɗu next page. Still C.E.O muna jiran labarin Ameeratulkhairi. Sai jama'ata kunsan ina yin Ladies kuwa, haka su Abbas ma..........hmmmmm......akwai aiki...... PRETTYN JAJIRTATTU ce ✍️🥰🤗.
https://chat.whatsapp.com/LQFBwo1tifs84ZuT6X2xS9?mode=ac_t
*_HASASHE KO BURI_*
_SADAUKARWA_
*🌟 I proudly dedicate this platform to all the strong and creative minds of our team — JAW (Jajirtattu Writers Association).*
You are more than just writers — *you are voices, strength, and inspiration!* ✍️💪
🕊️ *May Allah keep us united, uplift us, and make our pens a means of positive change.*
Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥
*Keep shining, JAW family!* 🌺
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.
💔 *_HASASHE KO BURI_* 💔
> 📖 A powerful story filled with dreams, struggles, and destiny!
💡 *Ka shirya?* Wannan ba labari bane na wasa — *it’s a journey into the heart of dreams and reality!* 😍
🛤️ *Rayuwa tana tafiya...* _Kowa na da *burinsa*, amma ba kowa ne ke iya cimmawa ba. Some dreams are *sweet hopes*, others are silent battles_💭⚔️
Page5️⃣⏩6️⃣
*KANO*
______Bayan ta koma gida, a parlour ta iske mahaifiyarta zaune tana kallon TV, zama ta yi kusa da ita tana mai cire niƙaf ɗin. Mahaifiyar da ke zaune hancin su ne iri ɗaya, amma ba sa kama sai haske duk da hasken Ameeratulkhairi na daban ne, tana cire niƙaf ni ƙyakyawan fuskarta ta bayya. Hmmmmm haske har kashe ido yake yi, murmushi ta saki wanda fararen haƙora ta suka bayya tare da dimple ɗin ta da suka lotsa, kusa da ita ta zauna tana magana da hannu wanda mahaifiyar ta gane sannan nima na gane saboda Allah ya min baiwar hakan.
“Insha Allah komai zai yi dai-dai, ance gobe na koma, ki ta ya ni da addu'a.” shine abin da ta furta sai mahaifiyar ta ɗaga mata kai. Sun jima a nan suna kallo dan shirin da ake haskawa akwai daɗi. Su biyu suke rayuwa a gidan wanda shine kaɗai suka mallaka daga uban dukiyar mahaifinta wanda ya rasu. Kuma Alhamdulillah suna cikin godiyan ubangiji.
Ɗan ƙaramin ɗakin ta shiga in da ta ga wani littafi akan ƙaramin gadonta, ta sauri ta ƙara da tana ɗauka, take da dafe ƙirji tana fita riƙe da littafin, maihifiyar ta juyi da sauri dan jin yadda Ameeratulkhairi ta buƙa ƙofa , kai ta ɗaga mata alaman tamabaya (Lafiya). Ƙwatance ta shiga yi wa Mamar tana haɗawa da hannun tare da nuna littafin. Da sauri Maman ta waro ido tana wani irin salo da hannunta. ( Sai da na jima kafin na gane mai ta ce)
“Garin ya?.” sai naga Ameeratulkhairi ta zauna daɓas.
“Kar ki damu, insha Allah ba zai karanta wancan ba, ko kuma alhaki na ne, nai ta ki ban na karanta littafi sirrinki mai suna SIRRI ki hanani. Hmmm ai shike nan ga wani ya samu a sama.” Mahaifiyar ta buɗi baki ta koro wannan zancen da hausarta wacce ba ta wani zauna ba.
Take hawaye suka gangaro a cikin idanunta, a yau ta yi dana sanin rubuta gajeren labarinta a irin littafin SIRRI, littafin iri ɗaya ne, dan na Sirrin ya cika shine take so ga fara a sabo, sai ta rubuta gajeran labarin a shafin farko, saboda kar ya ɓaci shine ta bari idan ga je can ta falle, to gaba ɗaya hankalinta ya yi gaba. Kuma jiya duk ta yi rubutu a ciki, hasali ma a gu ɗaya suke, yanzu idan ya karanta wannan shike nan ya gama sanin komai aka ta. Ta sha ainiyin ko wanda za ta aura ba za ta so ya gani ba. Akwai abubuwa da ita kaɗai take son gani, wani ta rubuta dan nishaɗi, wani tana kuka tana rubutawa, wani kuwa duk wanda ya karanta dole ya ta ya ta kukan. Ji take kaman ta fita ta koma sai dai tasan Amma ba za ta barta ba.........
*ABUJA*
Umar ne ya lumshe idanunsa tare da fara karanto min waye Ukasha?.
*Ukash wato Hassan Muhammad, haifaffen Abuja ne, Mahaifinsa baban attajiri ne, maihifiyarsa kuwa baturiya ce, a America Alhaji Muhammad ya auro ta, bayan sun yi ɗan rayuwa a can sai suka dawo Nigeria saboda business ɗin sa. Alhamdulillah yana samun kuɗi fiye da tinin mai tunani, sannan yana da alheri sosai, a Nijer yake, haifaffen can ne, shi kaɗai ne ya yi rai a wani gobara ta ta cinye ƴan gidan su, sannna ba wani zumunci ake ba da ɗangiba dan wasu ko saninsu bai yi ba, Kasuwanci ya baro da shi daga ƙasarsa, ya gina sabuwar rayuwa a nan. Bayan ya yi kuɗi mai sunan kuɗi, shine wasu daga danginsa ke waiwayansa, ba laifi yana ƙyautata musu fiye da misali. Sun ɗau lokaci shi da Rose kafin ta samu ciki, a gun haihuwa ta mutu, dan ko musulunta ba tai ba, ya yi iya yinsa Alhaji ganin ta musulunta amma ta ƙi.