← Book details Hasashe Ko Buri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 21

Sashe 15

Hasashe Ko Buri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Four wives?! Hmm... May God guide you. Honestly, go find someone else. I’m the jealous type — I can’t handle that. (Mata huɗu?! Hmm… Allah ya shiryar da kai. Gaskiya, ka nema wata. Ina da kishi — ba zan iya ba.)” sai ya marairaice fuska.

“Please, My Ashake, help me reconsider. (Don Allah Ashake, ki taimaka ki sake tunani).” furzar da iskan bakinta ta yi ta ce.

“Okay… I accept. But just to be clear, the other things — no hidden issues, right? (To… na amince. Amma fa dai sauran abubuwan babu wata matsala, ko?)

“No, everything is fine. A’a, komai lafiya.)"

“ Then go and speak to my uncle. Bye. (To, ka je ka yi magana da ƙanwata/uncle ɗina. Sai an jima.)" Wani nishaɗi ya ji sannan ya ce.

“Thank you so much for your time. (Na gode sosai da lokacinki.)." Hannu kawai ta ɗaga mai tana shigewa gidan nasu, saboda murna har buga jikin motarsa ya yi, yanzu mace ɗaya ta rage Bahaushiya, kuma yana fatan ya yi dace, domin kuwa watan gobe insha Allah zai auresu dukkan. Mota ya data yana mai barin layin......✍️
END.

> Ukasha Fatan nasara, saura Bahaushiya hmmm akwai bura-uba, ga dukkan alamu Asheka ƴar Yoruba akwia masifa, Fillo bafullatana akwia kunya, ita kuma Zuby Kanuri 🥺 bin Boka,hmmmm ko wacece bahaushiyar oho?.
> Haidar kai kuma haka gidan naku yake, toh Allah ya ƙyauta wasu dai akwai hassada.

> Abubakar sannunfa Darling ba ta gida ka zamu yadda kake so, amma fa Darling ba ta ƙyauta maka. Mu dai zuwa. Daga littafin *HASASHE KO BURI* by PRETTYN JAJIRTATTU 💪✍️.

🔥 *Let’s goooo!* 🔥
Hit that LIKE 👍 if you're truly *ready for the ride*!
Because *HASASHE KO BURI* isn’t just a story —
*it’s an experience.* 💭✨📚

✍️ _By PRETTYN JAJIRTATTU_ 💕

PAGE2️⃣7️⃣⏩2️⃣8️⃣

*KADUNA*

_Abbas_

Abbas da ogansu suka nufi Kano dan kai wata mota, tin asuba suka fita saboda mai motar na jira, dan Alhajin ya shigo Kaduna ne motar ta samu matsala, sun isa da wuri dan kuwa motar lafiyayya ce sosai. Da isarsu gidan Alhajin, aka umarci su jira yana zuwa, a dai-dai lokacin Haidar ya fito daga part ɗin sa cikin shigar manyan kaya ya yi ƙyau sosai, sannan ya ɗauko trolley wanda ya zuba abubuwan da zai buƙata. Har ƙasa suka gaishe da Haidar sai ya yi murmushi yana dafa su da faɗin.

“Injin miya (Haka yake kiran Ogan Abbas) ban so, ko Abbana bason wannan gaisauwar yake ba, ya Kaduna?”

“Alhamdullilah.”

“Sir good Morning." Abbas ya faɗa sai Haidar ya miƙa mai hannu suka gaisa.

“Morning, kai ma Injin miya ne koh?.” sai ya yi murmushi ya ce.

“Eh muna ta ɓa wa.”

“Allah ya ƙara jagora, bara na shiga zan fito da Abbana ɗin.” daga haka ya yi ciki, su kuma suka bishi da idanu.

“Kasan waye me wannan gidan?.” Ogan Abbas ya faɗa.

“A'a Oga.”

“Kasan H - Halal Nigeria Motors?.”

“Oga waye bai san wannan Company ba, ai yawancin daga can ake kawo mana kayan aiki.”

“Haka ne, to wanda muka zo wajensa shine mai wajen, wannan kuma da ya wuce shine babban ɗan sa, kuma ma'anar H- Haidar Halal Motors.” zaro idanunwa ya yi, yana ƙare ma gidan kallo, tabbas tin shogowanshi ya san mai gidan nan ya tara sosai, dan motocin dake gidan baya iya ƙirgawa.

“Ashe yau zanga wannan Attajirin."

“Aikuwa, shi yasa na tawo da kai, na aminta da kai sosai, kuma na yadda da kai, shi Alhajin yana neman na turo mai yaron aiki na guda 1 tak, amma bansan dalili ba, sai dai kai na za ɓa, duk da ba komai ka iya ba, amma hazaƙanka ya na min sosai.”

“Ogaaaaa na gode.” Abbas ya faɗa yana rungume Ogan sa.

“Kai sake ni, ka bari ya fito dai, tare zamu koma sai bayan wata biyu zaka dawo domin zuwa lokacin ka kammala karatun ka.”

“Haka ne, dan yanzu shirye-shiryen exam muke yi." Tare suka fito suna tafiya a tare cike da nishaɗi, yadda kasan wasu abokai, haka suka jero har wajensu.

“Ina kwana Alhaji.” suka haɗa baki wajen gaisasa, da murmushi ya amsa.

“Har kun kawo kenan, da yake wani zan ba mota kuma yau yake so, shi yasa na ta doku."

“Allah sarki, yanzu dai mota ta gyaru sosai.”

“Yauwa haka ake so, ina ɗayan maganar na mu?.”

“Alhaji gashi nan, sunnan sa Abbas."

“Haidar ga wanda na maka.” Haidar ya saki murmushi yana kallon Abbas sai ya ce.

“Masha Allah kaman kasan ina so na ƙara maka magana.”

“Ya yi maka?.”

“Eh, Abba tunda Injin miya ne ya kawosa na amince, amma sai nan da wata uku zuwa lokacin mun kammala wannan aikin har result ya fito, amma kafin nan ya fara zuwa dan sanin komai kafin na zo."

“Alhaji dama shima yana so ya kammala karatunsa gashi shirin exam suke yi ma.”

“Ma sha Allah, ai hakan ya yi, da ka kammala kawai ya zo nan.” godiya suka mai sosai.

“Abbana sai na dawo.” Haidar ya faɗa yana raba hannuwansu.

“Da kun isa ka tabbatar ka kira ni.”

“Insha Allah, Abokina zo muyi wata magana mana.” daga haka ya ja hannun Abbas, tare suka jera har gaban wata arniyar mota wanda ya shiga cikin ya ajiye abubuwan hannunsa sannan ya ce.

“Za mu yi magana, dan Allah ka riƙe amana, domin kuwa ni ba wani zama zan dinga yi ba, ina yin wasu ayyukan, amma karka damu zan ki raka, number ya yi?.” ya miƙa mai wayansa yana faɗin.

“Eh Sir, sai na jika, Na gode sosai.” murmushi Haidar ya yi yana faɗin.

“Injin miya zai baka saƙo." Daga haka ya tada motar yana fita.

Murmushi ne kwance a kan fuskarsa ya iso wajensu Alhaji.

“To muje."

“Injin miya ai ƙwayi breakfast, mu shiga ciki." Hmmmm ai ba'a magana kawai, Ogan Abbas da Abbas sai bin ko ina suke yi da kallo, dan gidan ba magana, a parlour suka zauna.

“Maman Safna, a haɗa musu breakfast, wai har kin shirya ne?.” Maman Safna da take sanye da hijab har ƙasa ta faɗaɗa murmushi tana faɗin.

“Eh Abban Haidar, muna so mu dawo da wuri ne."

“Okay, karku daɗe, kuma kuja ma Driver ku ja mai kunne ya bi da ku a hankali.”

“To Abban Haidar."

“Ku bi Flight kawai, zan miki transfer.”

“To muna godiya, daga haka ya yi part ɗin Ummin Haidar, wani harara ta dalla mai, dan kuwa duk buru-uba yau sai sun shiga tsakanin su.

Abinci masu rai da lafiya Zahra mai girki ta haɗa musu, aikam suka ja daɗi, bayan sun gama Alhaji ya basu dubu hamsin ladan aiki, sannan ya biya su kuɗin aiki. Aikam sun mai godiya sosai.

“Abbas sai mun ganka."

“Insha Allah.” a dai-dai lokacin ƴam mata biyu suka fito suna ta ranƙwaɗa, gaishe da Abban Haidar suka yi, sannan har sun ɗaga ƙafa sai Abban Haidar ya ce.

“Ni kaɗai kuka gani?.” da sauri suka gaida sauran, sai dai me da sauri Sumayya ta kuma kallon Abbas tana faɗin.

“A....A...Ab...Abbas.” ba shi kaɗai ba dukkansu suka kalleta, dan yadda ta kira sunan nasa.

“Abbas ni ce fa Sumayya Abu Haidar." (haka sunan su yake har a school, komai Abu Haidar ko Abban Haidar, shi yasa suka tsanar Haidar sosai).

“Bangane ki ba.” Abbas ya faɗa yana mamakin a in da ta sanshi.

“Yanzu school za ni, ban numberka za mu yi magana." Ganin kamar ba ta san Abban Haidar na wajen ba, yasa ya koma ciki, sam bai son ɗaga musu murya dan kanshi yana sarawa in ya yi hakan. Yana wucewa Ogan Abbas shi ya ba ta number sanann suka wuce.

“Ai da ba ka ba ta ba, sam ba ta da ɗa'a."

“A'a fa, kasan ko hakan wani alkairi ne." Suka ci gaba da hira har suka fita a babban haraban gidan.

Tana shiga mota ta rungume Safna tana faɗin.
“Finally na samu number Abbas."

“A Ina kika san shi?."

“Hmmmm a facebook, guy ɗin ya min, ke in kika bibiye page na shi ko, za ki kwasa ilimi, ɗan boko ne sosai, ina yawan ganin videos na shi yawanci friends dinsa ke daura, ke kinji speech, hmmm su 4 ne gaba ɗaya Poly na Kaduna ke ji da su.”

“Okay amma dai ba sonsa kike ba?.”

“Kina wasa ne, ai ni na haukace a soyayyar Abbas."

“Kina ruwa kinsan dai Mom ba za ta yadda ba." Ta figa motar tana wani sakin murmushi.

“Ni dai na gani kuma ya min.” girgiza kai kawai Safna ta yi dan tasan hauka kawai Sumayya ke yi............✍️

> Hmmmmm 🤐 yanzu wasan zai fara kun faji wata sabuwa Sumayya ƙanwar Haidar da son Abbas, gefe guda ga Merry ♥️, hmmm haɗin biza kenan....✍️

FREE PAGE'S ya kusa ƙare wa, ai munyi da waya, akwai point ɗin da nake so ku kai ne..... PRETTYN JAJIRTATTU ce ✍️.

💔 *_HASASHE KO BURI_* 💔

> 📖 A powerful story filled with dreams, struggles, and destiny!

PAGE 2️⃣9️⃣⏩3️⃣0️⃣

*ABUJA*

Su biyu ke tafiya a cikin mota suna hira, a hankali ta faka daga gefe dan ganin wasu mata sun tare motar, Zuby da ke driving ta sauke glass tana kallon mata biyun wanda a ƙalla za su iya haifa su. Bayan sun gaisa ɗaya ta ce.

“Dan Allah Filin Bora muke tambaya." Tana faɗin haka sai Darling ta ɗago ta kalle su.

“Ku shigo can zamu.” ba musu suka shiga cikin motan, dan kuwa ba kowa ke zuwa wajen ba, saboda hanyar babu ƙyau.

“Mama kuma wajen Mai sittin goma za ku?.”

“Ƴar nan eh.” Maman Safna ta faɗa tana jin sanyi a ranta dan yadda ake koɗa wannan malamin.

“Muma can zamu, gaskiya aikinsa ba wasa sai shi akwai tsaɗa.” cewan Zuby

“In da biyan buƙatar ai kuɗi ba matsala bane, munan daga Kano muke, flight muka biyo, to me motar da muka hau shine ya sauke a in da kuka same mu.” faɗin Maman Sumayya.

“Hala kuma an saku a gaba ne?.” Maman Safna ta tambayesu, sai da Darling ta yi murmushi sannan ta ce.

“A'a Mama, mijina zan sa a ƙara mallake min sa, sai ita ƙawata ya janyo hankalin sa wajensa.”
Chapter 15 · 0% Book details