← Book details Guduna Ake Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 15

Sashe 6

Guduna Ake Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yanda ya kira ke d'in sai tsigar jikin ka ta tashi kaji kaman ka buga kai jikin baango tsaban creepiness. Jaleela bata san sanda ta juya da wani bala'in gudu ba har tana yarda wayarta da jakarta dake hannun ta. A guje ta fice wani irin kuka ya kwace mata. Yanda ta fito kaman mahaukaciya ya bawa mutane mamaki suka bita da kallo. A guje ta fice daga club d'in ko takan motar ta bata bi ba. Haka tayi ta shek'a gudu kan titi tana kuka kaman hauka sabon kamu. Duk wanda ya tsaya don taimakon ta idan yaga yanda duk ta firgice sai ya tsorata ya kasa mata magana. A guje zasuja motar su. Da yawa ma suna tunanin ko gamo sukayi. Gabas kawai ta saka a gaba bata tsaya ba saida ta ganta k'ofar gida.

B'angaren wannan mysterious mutum wani irin miƙewa ya yi majestically ya tako inda ta tsaya. A hankali ya sunkuya ya d'auki jakarta data yasar yana juyata cikin tafin hannun sa dake sanye da safa. Sunkuyun da ya yi lallausan gashin kansa ya zubo ya rufe masa ido. Mugun smirk ya saki murya so husky yace

"So..... finally after all those year, we meet?. Who could have thought The world is too small" ya k'arasa yana wani irin chuckling.

K'ofar banɗakin da aka buɗe yasa ya d'aga ido a kasalance ya watsawa Zain daya fito yana goge hannu da d'an k'aramin tawol. Gira ya d'aga yana kallon Zain ta gefen ido.

"What?"

Zain yace yana k'ok'arin zama. Wani irin chuckling ya yi ya miƙe rike da pose d'in ya dawo ya zauna kusa da Zain yana kallon sa.

"Your Babe. She just left"

"What?"

Zain yace yana zare ido ya yi saurin warce jakar daga hannun sa. A hanzarce ya fice daga d'akin ya bishi da manyan black eyes nashi yana mugun murmushi. Da saurin Zain ya fito har harabar gurin amma ko kurar ta bai gani ba. Baki ya cije rai a b'ace ya koma lounge nasu. Yanda ya barshi haka ya same shi zaune lazy kan kujera ya d'ura hannuwansa kan kujerar ya kafe k'ofar da sexy eyes nashi. Mugun kallo Zaid ya watsa masa

"Me kayi mata?"

Y'ar gira ya d'aga kafin ya saki y'ar deep dariya da dimples nashi suka lotsa. Oooh wannan mutum is a very sight to see. Baza kasan sanda ka ke dilalar yawu ba idon kana kallonsa. Da deep voice nashi yace da hausar da bata fita sosai

"Ni kuma? Ask her mana. Me yasa daga ganina ta tsorota ta gudu, kaman wacce taga wani mugun abu? "

Smirk d'in daya saki zaka san akwai meaning bayan maganan da ya yi. Numfashi kawai Zain ya sauke. Duk lokacin daya d'auka yana jiran wannan rana in the blink of an eye komai ya wargaje. Zama ya yi gefen sa yana kallon yanda ya koma ya kwanta ido a lumshe, har zuwa lokacin da murmushi kan fuskar sa. Tunanin abunda ya kawo shi Nigeria ma yau d'in nan yake.

2 DAYS BACK .
kwana biyu da suka wuce.

ABU DHABI.

Kaman yanda Malika tasa ayi shela, hakan ne ta kasance. Cikin d'an k'ank'anin lokaci labarin auren LK da Aafiya ya baza Abu Dhabi. Da yawa suna cikin jimami da tunanin yanda makomar Aafiya ita ma zata koma. Kaman sauran matan da Lk ke aura, itama Aafiya gagarumin biki Malika ta fara shiryawa. Dukkanin wasu dangi na b'angaren Aafiya da Lk sun hallara cikin wannan katuwar masarauta. An fara shagali bikin irin nasu na larabawa ta ko wanne fanni. To amma shi wanda ake abun domin sa yana can MALIBU baisan abunda aka be. Sai bayan an d'aura aure Malika ta tura kannan sa da suke twins. Aizak da Aryan suka je suka tisoshi a gaba. Bai san da zancen bikin ba sai da daddare ya kebe cikin d'akin sa.

Had'addiyar black suit dake jikinsa yake cirewa a hankali cike da kasala. Wani irin ingarman namiji ne majiyi karfi. Koya ya motsa jiki sai kaga damtsen nan sun motsa. Dogon gashin sa dake tufke a tsakiya kansa ya kai dogayen yatsun sa ya cire band d'in. Kaman ruwa gashin ya biyo ya kwanta wuyansa luf mai tsananin laushi da tsantsi gashi bak'i sid'ik. K'ofar d'akin sa da yaji an buɗe alamun an shigo baisa ya juyo ba saida ya kama farar rigar dake cikin suit d'in ya fara cirewa. Jin shirun ya yi yawa ya wani irin juyowa a hankali yana balle ragowar botirin rigar da ya yi saura. Numfashin Aafiya ya wani irin tsarkewa lokacin da kwayar idonta ta fad'a cikin midnight Black nashi. Kut ta had'iye yawu. Hak'ika waya da labarai basa masa adalci sam. Don yanda ta gansa haka a zahiri , Sam ba'a kwatanta irin matsanancin kyau da Allah ya bashi. Mutum kaman shi ya yi kansa. Jan wani irin numfashi tayi sanda kwayar idonta ta sauka fatar cikinsa dake uban shining ga wasu uban 8packs kace zanasu a kayi. Kut ta k'ara had'iye wani yawun. Sannu a hankali ta ke yawo da idonta dukkanin wasu sassan jikinsa kafin idonta ya sauke kan kyakkyawar fuskar dake d'auke da wani irin full lips pink masu matuƙar shek'i. Hancin nan kaman biro tsaban tsayi ya tafi da manyan idanuwan da ko ita Albarka. Tsananin bak'in kwayar idan nasa da girman idon nasa idan yana kallon ka sai kaji kaman mai kallon ruhin ka.

"Min ant?"

Taji kakkausar murya sa kaman saukar aradu. D'an firgita tayi saboda yanda tayi nisa wajen bege. Saida ta lashe leb'en ta daya bushe kamas ta buɗe baki zatayi magana , kaifin idonsa da yanda ya kafeta da manyan idanuwan sa, fuskar nan babu wani emotion yasa taji fitsari na neman kwace mata. Had'iya ta k'arayi ta k'ara buɗe baki amma ko kalma d'aya ta kasa fitowa. Gaba d'aya a firgice take da tsananin kyawun sa da kuma kwarjinin sa . Dif,dif ya nufota kaman wani bijimi. Aafiya batasan sanda ta juya da wani bala'in gudu ba tayi waje. Turus ya tsaya inda ta bari ya kafe k'ofar da ido. Wacece ne kuma wannan harta samu ikon shigo masa d'aki haka kai tsaye. Duk cikin masarautar nan ansan yanda baya son mata suna masa aiki. Why Malika zata turo masa ita don yasan bazata wuce wata Baiwar ba. To amma anya Baiwa ce? Yanda ta chaba ado haka. In har bai manta ba harda gwala-gwalai ya gani a wuyanta da hannun ta. Wacece ne wannan?. Kafin ya sake wani yunƙuri an sake buɗe had'addiyar k'ofar tasa an shigo kai tsaye. Wacce ta shigo yasa ya d'an saki ajiyar zuciya yana binta da kallo. Sanye take da alkyabba da aka Chab'awa ado da zinare. Alkyabba mai hula ce data rufe fuskatar ta ruf kaman rariya. Sannu a hankali ta maida k'ofar ta rufe saboda bayinta dake bakin k'ofar. A hankali ta juyo ta tako har inda Lk ke tsaye. Hannu ta kai ta yaye hular alkyabba data rufe mata fuska.

"RAINHA" (ma'ana Sarauniya da harshen PORTUGAL). Kyakkyawan murmushi tayi masa ta d'ago hannun ta daya sha ado da gwalgwalai ta shafa fuskar sa. Tsananin kyawun ta saiya firgita duk wanda ya ganta. Saboda haka ne take rufa fuska. MATILDA baturiyar k'asar Portugal ce. Sanadin had'uwar ta da Sarki KHALELULLAH ta musulunta har sukayi aure shekara takwas da suka wuce. Matilda ta girmi MALIKA nesa ba kusa ba don tayi shekara 50, amma zakayi mamaki idan ka ganta baza kace tayi shekara 25 da biyar ba. Kullum yarinya take k'ara zama ga wani irin shirtaccen kyau da take dashi mai firgita maza da sasu zama bayinta. Tunda ta shigo masarautar ABU DHABI ta shiga jikin LK sosai ta zame masa tamkar uwa. Kusan a yanzu yafi amfani da maganan ta akan ta Malika. Sosai sun samu sabani Saboda hakan, amma duk yacce Malika tayi LK baya tab'a daina bin umarnin Matilda.
Da yaranta na Uwa wato Portugal tayi masa magana don sosai ta koya masa yaren.

"Quem é aquela garota que acabou de sair do seu quarto?"

"Wacece naga ta fito daga d'akin ka yanzu?"

Kafin ya bata amsa suka tsinkayi muryar Malika data shigo ita da Aafiya basu kula ba.

"Matar sace"

Da azama suka juya suna kallon Malika dake takowa cikin izza da Mulki Aafiya b'oyenta. A tare suka maimaita.

"Mata?"

"Wife?"

Ran Matilda sosai ya b'aci. Wato Malika saboda taga bata nan taje garin su can Portugal wajen iyayen ta shine tayi masa aure bata sani ba?. Wato Malika bata tsoron abubuwan da suke faruwa duk lokacin da LAMEEN ya yi aure. Ido cikin ido suke kallon juna ita da Malika kafin ta maida idonta kan Aafiya. Wani irin kallo ta watsawa Aafiya da Allah kaɗai yasan abunda ke cikin ranta. Rai a b'ace ta rab'a ta gefensu ta fice daga d'akin. Lameen ji ya yi kaman ya rushe da kuka yana kallon mahaifiyar tashi dake kallonsa babu alamun wasa tattare da ita.

"Samu guri ki zauna Aafiya "

Babu musu ta zauna kan wata had'addiyar kujera . Hannun sa Malika ta kama ta zaunar dashi kusa da Aafiyan. Baki ya taune ya k'ara matse rigarsa da bai gama cirewa ba. Zama tayi kujerar dake fuskantar su tace

"Ga Aafiya matar ka dana aura maka ita yau da safe. Dukkanin wani tunani dake ranka ka ajiye sa gefe don bata amince da auren ba saida tasan kome ke faruwa. Du da haka tace tana son ka a haka zata zauna dakai. InshaAllahu zamu cigaba da Addu'a har Allah ya kawo mana sauki. Yanzu lokaci ya yi daya kamata ace ka ajiye iyali. Girma ka ke Lameen ba yaro ka ke komawa ba. Lokaci ya yi daya kamata ka hau kan kujerar mahaifin ka duk rashin sonta da ka ke"

Miƙewa tayi tsaye tana kallonsa ya sunkuyar da kai ya kasa cewa komai tsabar bak'in ciki. Wai sai yaushe Malika zata gane shifa mata ya tsanesu ne in general, saboda wata yarinya data tab'a shiga rayuwar sa wani lokuta da suka shud'e.Numfasawa tayi ta k'ara cewa
Chapter 6 · 0% Book details