← Book details Guduna Ake Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 15

Sashe 14

Guduna Ake Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta kasa cewa komai sai aikin kuka da take. Mai nape kam kaman wanda aka kullewa baki baice ga daga inda ya d'aukota ba yaja motar sa yabar k'ofar gidan. Sai bayan Almu ya rungume tane yaga yanda hijabinta ya b'aci. D'an murmushi ya yi ya girgiza kai ya kamata suka shige gida. Ahbie ya bisu da kallo cike da damuwa. Tsakar gida suka samu Ammi tana jin wa'azi cikin radio data kunna. Ganin yanda ya suka shigo ya rike ta d'ago da sauri tana cewa

"A'a Leeyna Lafy har kin dawo? An tashi daga musabakarne?"

Jikin Ammi tayi a guje tana kuka murya a shaƙe tace

"Ammi na manta yau watane. Naje makaranta ya batamin jiki mutane sai kallona suke"

Kai Almu ya girgiza ya juya ya fice yana murmushi. Aleeyna akwai ta kunya. Saboda wannan abu take kuka haka kaman wacce aka kashewa uwa. Murmushi Ammi tayi itama

" shine ki ke kuka haka?. To akwai wanda ya wuce hakan ya faru dashi ne? . Shi tsautsayi ai yana kan kowa. Yi shiru haka tashi keje kiyi wanka kizo kici abinci "

'A ace kunsa abunda ya sani wannan kukan da sai kunyi wanda yafi wanda nake' Aleeyna ta furta a zuci. Da kyar ta iya yin wanka ta kimtsa kanta.shige d'aki ta kwanta. Tanajin Abhie ya shigo Ammi tana masa bayani. Saida ya k'ara dubata sannan ya fice. Tana kududdune cikin bargo Almu ya shigo da leda ya ajiyr ya fice baice komai ba . Ranan wuni Aleeyna tayi tana kuka har saida ya saukar mata a zazzaɓi. Rashin zuwanta islamiya yan aji suka fara turuawa zuwa don Aleeyna abun son kowace. Haka Lukman ya wuni yana kiranta a wuya hankalin sa duk ya tashi burin ransa na kwance babu lfy.

Kallo Zain ya watsa masa yana k'ara bin k'irjinsa da kallo. Satin farce da jan da jikinsa ya yi ya bashi mamaki. Dagashi sai tawol don daga wanka ya fito.

"Wai menene ya sameka haka jikinka duk yakushi da cizo?"

Bai bashi amsa ba saida ya matsa bakin mirror da tawul rataye a wuyansa. Jik'akk'en gashin daya zubo fuskarsa ya kai hannu ya tura shi baya. Kallon kansa ya yi cikin mudubin tana tuna irin dambe da sukayi da ita. At one point harta cije shi a fegen wuya bata sani ba. Murmushi ya k'arayi ya kai hannu ya shafa gurin. Daga wani point of view na wani zaiyi tunanin ko satin soyayya ne ta bashi kaman yanda turawa suke wato HICKEY. Saida ya gaka shafe jikinsa da turaruruka masu tsananin kamshi da dad'i sannan ya juyo ya zauna gefen Zain dake kallonsa da tarin tambaya cikin idonsa.

Kaf ya kwashe komai ya gaya masa bai b'oye ba. Mamaki da shock ya kama Zain.

"What King? Kai ne ka kusa rape ta mace? , are you kidding?"

Fuska ya b'ata murya a kausashe yace masa

"When did i ever lie to you?, it's all her fault da take kirana Names. Da zace ta tsaya taji abunda yasa na riƙe ta da duk hakan bai faru ba."

"But King. Kamanta nan da DUBAI ko kasashen da kake zuwa ba d'aya bane. Akwai tarbiya da kamun kai. Ko kaine hakan ta sameka zaka bada thesame reaction. Someone you dont happens to hold in a busy road. Kasan irin suna da backlash da hakan zai haifar mata?"

Wani irin tsk sound ne ta fito daga bakin Lameen yace

"Kana nufin na barta tayi ta roaming gari haka with huge stain na period a jikinta saboda your people are cowards bazasu iya gaya mata abunda ya sameta ba?. Saidai ta zame musu abun kallo ko abun zagi?, is that what you want me to do?"

Shiru ne ya ratsa d'akin an rasa wanda zaice komai sai kafe juna da sukayi da ido. Numfashi Zain ya sauke don bashi da abun cewa. Tabbas al'umman malam bahaushe yanzu abun babu taimako ko tausayi. Saida a dinga kallo da zundenka. Kalilan ne masu taimako yanzu. This all thing ya chaja masa kyau. Muryar Lameen yaji yace

"Exactly. That's what i thought"

Baice masa komai ba sai ido daya bishi ya shige cikin kwaba. Baijima ya fito sanye cikin suit three pieces dark Ash.

"Zan koma Dubai yanzu. Urgent matter ne ya taso"

Bai jira Zain yace komai ba ya juya ya fice daga d'akin. Yana zaune ne cikin yana tunanin.

'Miss Aleeyna ' kaman yanda yaronsa ya binciko masa. Sunan ya k'ara maimaita kan leb'ensa.

'Miss Aleeyna. I'm coming back for you. Our story is just getting started.'

Wani irin smirk ya saki da zai bawa mutum chill idan yana kusa dashi.

𝗚𝗨𝗗𝗨𝗡𝗔
𝗔𝗞𝗘 .

𝒜𝐬𝐡𝐚𝐧𝐭𝐲 𝐥♡︎𝐯𝐞.

A/N: kuzo ku hanzarta ku shiga sawun wanda suka fara payment nasu na GUDUNA AKE. It's just 500N .

👇

08140754777.

Last free pages.

Not edit.

46/50.

Tsawon satin gaba d'aya Aleeyna ta k'ara zama wata so silent da ita. Ya sawa kanta damuwa zazzab'i saida ta kwana biyu tanayin. Sosai Ammi,Abhie da Ya Almu suka shiga damuwa. Harta Amnah saida tazo gidan ta kwana biyu saboda soyayya Aleeyna data game musu jini da tsoka. Ko kaɗan basa son abunda zai kwantar da ita. Ga Lukman dake ta sintiri shima babu kwanciyar hankali tattare dashi. Ita kam Aleeyna bata san me zatace ma su Ammi ba kan abunda ya sameta da damuwa da suke nunawa a kanta. Sabida haka ne tafa k'ok'arin wajen ganin ta d'an rage rashin walwala a gida ko a makaranta. Lukuta suka shude. Kwana ya koma sati, ya koma wata. Bikinta da Lukman na k'ara matsowa. Bata da wani zabi daya wuce hak'uri a wannan lokacin da fawwala Allah. Shi kuwa wannan mutum bata daina sashi cikin Addu'a ba a koda yaushe ta kafa goshinta gaban Allah. Allah ya bita hakkin ta a kansa . Sosai Ammi suke ta shiri Hajjo ,kakar Ammi ana saura sati guda ta dire Higgi da mai gyaran jiki aka. Zuwa wannan lokacin Aleeyna ta d'an warware ta ajiye komai cikin bak'in littafinta. To alhamdulillah an fara hidimar biki duk da ba wani abune za'ayi ba, y'ar walima ce sai dinner da Lukman ya dage shi sai ya yi. Ance ta rana bata k'arya saidai uwar diya taji kunya. Yau aka tashi da hidimar biki a yau rana ta alhamis. Tun safe Aleeyna ke gidan mak'otansu da y'an tsirarun kawayenta ana musu kunshi. Tayi wani irin ta k'ara fresh fatar sai shek'i take. Ga gashinnan daya sha matsanancin gyara ya k'ara sulbi da laushi. Idan ka kalleta sai ka k'ara. To a b'angaren Aleeyna tunda ta tashi yau take cikin matsanancin fad'uwar gaba da ita kanta ta rasa dalilin hakan. Koyaya ta motsa ko akayi magana kusa da ita sai gabanta ya yanke ya fad'i. Duk yanda take k'ok'arin ganin wajen ta saki ranta abun ya gagare ta. Saida Hajjo ta sata a gaba da tambaya meke damunta, amma ta kasa furta komai. Dangi dake gurin sanda Hajjo ta sata a gaba suka fara yi mata tsiya wai dan taga zatabar Ammi ne shine duk ta zama kaman mara lfy. Itadai bata iya tankawa. To a washegari juma'a aka tashi da shirin d'aurin aure da za'ayi idan an sakko daga masallaci. Abun yau yafi na kullum don har wani zazzaɓi ta tashi dashi. Tun bayan anyi sallan asuba babu wanda ya k'ara runtsawa kowa ya tashi ana ta dinima. Aleeyna tun k'arfe 8 na safe bayan sun karya Amnah suka shige da ita d'aki da mai kwalliya ana tsantsarata.

To a b'angaren ango abun ba'a cewa komai. Suma dai kaman sauran mutane ana yin sallah asuba suka d'auko hanyar ADAMAWA. Bakin Lukman ya kasa rufuwa shida manyan abokansa da guda biyu. Du da cewa kafin ya fito cikin b'acin rai yake son Mahaifiyar sa Sam bata son auren. Tana da burin ganin ta had'ashi da y'ar aminiyarta Najla ya aura, to shi kuma Lukman hankalin sa na kan Aleeyna. Ko irin d'an taron nan batayi ba ace uwa guda na Aurar da d'a. Sai daga b'angaren Mahaifiyar tashi ne da Baffan nashi sukayi taron da babu yanda ta iya.

Karfe d'aya daidai suka faka harabar masallaci da za'a d'aura aure. Burinsa yaga sanyin idaniyar sa ko zaiji sauk'in rashin ganinta da ya yi na kwana biyu. Yana k'ok'arin fita daga motar ganin ana shirin shiga masallaci. Bakinsa Sam ya kasa rufuwa, saidai yana kai hannu jikin murfin motar zsi buɗe sak'o ya shigo wayarsa. Bai buɗe ba saida ya fito daga motar ya kai hannu cikin aljihun wandon na riga ya zaro wayar daga aljihu yana murmushi. Khamis da Isma'il dake tsaye kusa dashi sai murmushi suke taya abokin nasu saboda wannan rana ta farin ciki ce a garesu baki d'aya. Ya Almu dake tsaye bakin masallaci da Zubair suna jiran isowarsu ya taho da sauri cikin manyan kaya. Sosai Almu ya yi kyau cikin babbar riga ash datash surfani. Shi kansa bakin nasa ya kasa rufuwa saboda farin ciki. Fuskar Lukman yake kallo da murmushi kan fuskar sa. Lokaci guda yaga yanayi Lukman din ya chanza wannan fara dake kwance kan fuskarsa ta chanza zuwa wani irin matsanancin b'acin rai har rawa jikinsa yake. Wani irin jiri ne ya kwashu Lukman bayan ya yi arba da mummunan abunda yasa zuciyars kusan tarwatsewa. A take ya yi luu zai kifa Isma'il dake kusa dashi ya yi hanzarin taro shi yana

"Subhanallahi, lfy?"
Chapter 14 · 0% Book details