← Book details Guduna Ake Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 15

Sashe 12

Guduna Ake Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hanzarce tace 'Amin Ammi' ta suri jakarta ta fito daga gidan da sauri. Kaman koda yaushe Abhie na zaune baranda ya almajiransu suna karatu. Da sauri ta zagaya ta durkusa kusa dashi tana gaisheshi. Albarka ya shimata da fatan samun nasara. Tana mike motar taxi ta faka k'ofar gidan. Almu ya fito daga motar goye da jaka . A guje ya rungume shi tana dariya ya shafa kanta dajan kumatunta. Sannu tayi masa da zuwa tayi saurin wuce ta tafi makaranta.

Daga can b'angaren.

Numfashi ya sauke mai zafi ya kalli agogon hannun sa. Wani irin tsaki yaja ya d'ago manyan black eyes nashi ya watsa kan Zain dake duba wata patient. Wani tsakin ya k'ara ja. Zain ya juyo ya watsa masa harara

"Ai saida nace kar ka biyoni ka biyoni kazo ka dameni da tsaki ina aiki"

Kaman zaice wani abu sai kuma ya fasa da sauri ya miƙe ya suri coat tashi daya ajiye kan kujera. Murya a kausashe yace

"Am going out"

"Kasan garinne dazaka fita?"

"No. Babban gari ne ai. Ina buk'atar fresh air ne"

Yana gama fad'in haka bai jira abunda zaice na ya juya ya fice Zain ya bishi da ido. Kai ya girgiza yana d'an murmushi wato Lameen ya zame masa jela. Duk sanda yake son guduwa daga masarauta musamman idan yaji ana zancen aure ko hawansa kan kujerar Mulki direct gurinsa yake zuwa ya b'oye. Shida Lameen abokaine sosai da suka zama tamkar yan uwa. Tun had'uwa da sukayi suna shekara goma sha shida a makaranta ta Oxford suka d'inke. Shiya koya masa hausa sosai ya kuma kawo sa Nigeria mahaifarsa.
Tsakanin sa da Lameen soyayya ce daga Allah kawai. Zamansa da Lameen yasan abubuwa da dama da mutane basu sani ba. All this top guy da yake nunawa da bad boys duk facade ne. Inside mutum ne so soft ga tausayi .

Yana fitowa masu tsaron sa suka rufe shi. Mota suka buɗe masa ya shiga suka bar asibitin. Jingija ya yi jikin glass na motar yana kallon waje da yanda mutane ke mu'amala. Life nasu na birgeshi matuƙa. Kowa yanayin abunda yake so ne babu wani daya tsaya yana juya masu rayuwa sai yanda akace suyi. Daidai danger suka tsaya data tsaida su. Kaman ance ya d'aga kansa ya hangota tsaye bakin titi da alamun tsallakawa zatayi. Tsintar kansa ya yi ya zuba mata manyan idonsa duk da cewa baya ganin fuskatar saboda nikab data sa. But baisan abunda yasa ba idonya ya yi drawing d'insa in hakanan kawai yaji yaja son ganin fuskarta. Yana kallo ta tsallaka da sauri ta wuce mutane suka bita da kallo. Ware idonsa ya yi sosai yana kare mata kallo dason gani koda wnai inch ne na jikinta. Chak idonsa ya tsaya kan babban stain dake jikin hijabin nata wanda hakan shi ya yaja hankalin mutane sosai ta zame masu abun kallo. (Malam bahaushe kenan) .

Baisan ya akayi ba sai ganin ya yi ya fito daga cikin motar. Aikuwa yoo ido ya yi kansa kace sabon halitta aka gani. Taku d'aya biyu ya yi ya rik'o hannun Aleeyna dake neman haurawa d'aya b'arin. Da wani irin matsanancin mamaki da shock ta juyo kwayar idonsu suka sarke da juna. A take zuciyoyinsu suka harba lokaci guda. Wani irin ware manyan ido Aleeyna tayi k'irjinta ya wani matsanancin harbawa cikin matsanancin tsoro da tashin hankali tayi k'ok'arin fisge hannunta daya riƙe. Innalilllahi wa Inna'ilaihi raji'un. Wane irin tashin hankaline wannan kana tafiya katon gardi ya riƙe ka kan titi cikin mutane?. Gardin ma Arne don wannan ba bahaushe bane. Hankali a tashe ta cire hannu ta kifa masa mari.

Tsananin mamaki da shock yasa ya saki hannun nata ya zuba mata manyan idonsa yana kallonta idon nan sunyi jazur.

"Allah ya isa daka tab'a min jiki mai tsarki. D'an iska kawai. Ka d'auka nan irin k'asarce da mata ba komai bane sai riga?"

Shar hawaye suka biyi mata fuska inda ta samu sauk'i ma babu wanda zaice wacece ita. A guje ta k'arasaa tsallakawa ganin yanda suka had'a uban go slow kan titi. Kowa ya fito daga mota yana kallon wannan abu. Ga masu tsaronsa daya k'ara saka tsoro zuk'anta su sun kasa taɓuka komai. Saida ta shige wani lungu ya juya da wani irin zafin rai ya cukwukwuye rigarsa daya cire zai bata ta d'aura. A zafafe ya fad'a mota zuciyar sa na wani irin zafi dashi kansa ya rasa dalilin da yasa hakan.

"Follow her"

Ya bada command. A guje suka tashi mota suka kutsa layin da Aleeyna ta shiga don tayi yanke. Babu wasu gidaje ko mutane sosai a layin saboda yanzu yake d'an tashi. Tana tafe tana kuka tsabar bak'in ciki da sai tsini masa take koma waye . Babu zato shegun motocin sa suka fakaa gabanta. K'irjinta ya k'ara bugawa da k'arfi ta juya da bala'in gudu zata bar layin. Woof taji ya d'auke ta wulla cikin mota. Ihu da kururuwa Aleeyna ta saki na neman taimako da agaji tana dukan glass. Amma da yake glass na motar soundproof ne ga tint babu wanda yaji bare ya ganta. Tana kallo suna ta shek'a gudu kan titi duk ta haukace. Ganin babu sarki sai Allah ta juyo inda yake zauje ya kafeta da ido fuska babu emotion ta bara bashi hak'uri.

Wani irin smirk ya saki murya so husky yace

"Did you know who you just slap? Big mistake ki ka aikata you most get punish. Babu wanda ya tab'a daga hannu ya mari KING ,not know not ever. And I will show you how dirty nake"

"Wayyo Allah na shiga Uku. Ammi ,Abhie, ya Almu ku taimaka min"

Ta cigaba da kururuwa cikin motar.

Free pages na gab da zuwa karshe my people. A hanzarta a shiga sawun wanda suka fara payment nasu. Show me the love and support da nake gani.
Chat me up
👇

08140754777

𝗚𝗨𝗗𝗨𝗡𝗔
𝗔𝗞𝗘 .

𝒜𝐬𝐡𝐚𝐧𝐭𝐲 𝐥♡︎𝐯𝐞.

A/N: kuzo ku hanzarta ku shiga sawun wanda suka fara payment nasu na GUDUNA AKE. It's just 500N . Basai mun gama free pages ba da suna gabda zuwa k'arshe. Kar ku bari ayi wannan zazzafar tafiyar babu ku. A cigaba da bawa Ashanty ,love da support da ake bata. Chat me up

👇

08140754777.

41/45.

K'aramin Estate suka shiga mai kyan gaske. Bakin wani flat house suka faka motocin. Har suka isa Aleeyna na zuba ihu da kururuwa na neman taimako. Fita ya yi daga motar ya zagaya b'arin da take ya fisgota da k'arfi tana ihu da kai masa duka. Ganin zata b'ata masa lokaci ya wullata k'afad'ar sa ya yi cikin gidan da ita. Saida ya wuce can kariyar d'akin na master bedroom ya watsa ta kan gado. A guje Aleeyna ta tashi taba ihu ta haura can d'aya b'angaren. Bakin gadon ya tsaya ya zuba mata tsumammun idonsa yana k'ara accessing nata. So yake yaga fuskarta yaga wace yarinya ce ita haka har ta keda jarumta ta d'aga hannu ta mareshi saboda zai taimaka mata?. Hannu yakai a hankali ya fara cire suit d'in jikinsa lights blue. Wani irin ihu Aleeyna tayi ta kwasa a guje tayi bakin k'ofa. Da dukkanin k'arfin ta take buga k'ofar tana jijjiga abun hannunta amma k'ofa taki buɗewa don ya riga da yasa mukulli. Hucin numfashinsa dataji bayanta ta wani irin juyo da sauri daidai ya kai hannu ya fisge nikaf dake fuskantar. Saida numfashin ya tsarke sanda ya yi arba da kyakkyawar fuskarta. Manyan idanuwansa ya zuba mata kaman yanda itama ta zuba masa nata ido dake d'auke da matsanancin shock baki a buɗe. Kallo ta yake tun daga d'an k'aramin pink lips nata zuwa dogon hancinta da manyan idanuwan ta dake d'auke zararan gashin ido.
'She is so beautiful ' zuciyar sa ta furta. Kai kawai ya jinjina yana cigaba da kallonta. Da zafin rai takai hannu zata fisge nikaf d'in ya d'aga shi sama. Kuka ta k'ara saki mai k'arfi tana cewa

"Me ka ke so dani ne?. Don girman Allah kayimun rai ka kyaleni na tafi gida. Kayi hak'uri don Allah. Na taso gidan tarbiya da Addini in kana kaunar Allah da Manzon sa karka lalatamin rayuwa. Kaje can inda ka samu lalata rayuwar wasu yanda ka sab amma don Allah kyale ni."

Da gaske dai kallon d'an iska fasiki take masa?. Shi da fari duk so yake ya tsorata amma yanzu data k'ara gayama haka ransa ya k'ara zafi. OK zai fara lalata ya'yan wasun amma kanta zai fara. Wani irin zafin rai ya fisgota ya yi kan gado da ita. Matsanancin dambe suka suke da kokawa tana d'aukan dukkanin abunda taci karo dashi ta kwad'ama. Shi kanshi ya yi mamakin k'arfi da yarinya take dashi. Gata y'ar mitsitsiya amma sai k'arfin tsayi. Lokaci d'aya ya dagata ya kama kan gadon kafin tayi wani yunƙuri ya danneta da katon jikinsa. A wahalce ta saki wani irin tari idonta suka k'ara fitiwa waje don gaba d'aya ya sake mata nauyin sa. Numfashi ya fara mata wahalar fita. Hannnta ya had'a saman kanta ya riƙe da nashi guda daya. Ido ya zuba mata yana k'ara kyestima irin kyau da yarinya keda shi. Dama a Nigeria bakaken fata akwai mata masu kyau haka?. ( Nace malam Lameen. Ai babu irin matan da babu a Nigeria. 😂).
Chapter 12 · 0% Book details