← Book details Guduna Ake Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 15

Sashe 2

Guduna Ake Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Wani irin kuka ne ya kwacewa Jaleela ta danne shi, hawaye masu zafi suka biyo kuncinta ta. Kai H Lami ta girgiza rai a dagule tace

"To maganan gaskiya Jaleela baza mu cigaba da d'aukan ki aiki a nan ba. Mu hisba ne da muke yak'i da mutane masu miyagun hali ,wajen ganin mun d'ora su kan turba mai kyau. Bayan haka mun samu labarin wani mummunan sana'a da ki ke aikatawa bayan wannan. Saboda haka mun yanke hukunci sallaman ki. Bazamu iya cigaba da zama dake ba. Ina so ki saka hannun a wannan takardar don mun kore ki "

Hannun Jaleela na rawa ta karb'i takardar data mik'o mata ta saka hannu hawaye na diga kan takardar. Da wani irin sanyin jiki ta miƙe tayi bakin k'ofa zata fice. Lami tace

"Amma naji mamakin wannan mummunan dabi'u da ki ke a b'oye Jaleela. Yanayin ki baiyi kama da mace mara daraja ba, mace mara sanin ciwon kanta na y'a mace. Mace data fifita duniya a kan lahirar ta. Yanzu me zaki ce da y'ar taki da ki ka haifa a titi a duk lokacin data buk'aci sanin waye uban ta?"

A guje ta buɗe k'ofar ta fice tana wani irin kuka kaman mai shirin tada asmah. Zainab da sauran ma'aikatan dake jiran fitowar ta suna ganin yanda ta fito suka kwashe da mahaukaciyar dariya harda masu tafawa. A guje ta fice tayi wajen motar ta. Jiki na rawa ta buɗe ta shiga. Had'a kai tayi da sitiyarin motar tana kuka sosai kaman babu gobe. A karo na babu adadi nan ma sun Guje ta saboda kaddarar data same ta.

𝐆𝐔𝐃𝐔 𝐍𝐀
𝒜𝓀ℯ 𝔂𝓲.

𝓐𝓼𝓱𝓪𝓷𝓽𝔂 𝓵♡︎𝓿𝓮

6/10.

Ta jima zaune cikin motar kafin tayi jarumta ta bar k'ofar office d'in. Maimakon tayi gida sai tayi inda take tunanin nan ne kad'ai zatafi samun nutsuwar zuciya. Kai tsaye tayi club dake can wajejen Suleiman crescent. Harabar gurin cike yake da motoci kace dare ne. Kowa yasan club yafi ci da daddare. Guri ta samu ta faka motar ta, bata fito ba saida ta cire abayar dake jikinta da d'ankwalin ta. Dogon gashinta dake nan har wanen hips nata ta sake shi wanda ta d'aure da ribbon . A hankali ta fito riƙe da waya da muk'ullin motarta a hannu. Rigar dake jikinta ba k'aramin kamata tayi ba wanda hakan ya bawa shape nata da k'irar ta fitowa muraran. Abun sai wanda ya gani tabarakalla Jaleela ba dai kyau. Akwai kyawu na fuska dana jiki amma babu na zuci. Daidaikun manyan Boy's dake gurin suna ganin fitowar ta suka bito da ido chaa kaman kura taga nama. Yanda take jinta a yanzu bata tunanin zata saurari wani namiji. Rai a dagule ta shige club d'in. Saida ta fara yiwa kanta order na drinks masu sanyi da y'an snack sannan ta wuce ta samu guri daga can b'angaren Vip ta lafe a bunta. Sosai tayi zurfi cikin tunanin rayuwar ta da irin kalubale da take fuskanta tun daga ranan data baro gida da gatanta, har zuwa yanzu da take iya bakin k'ok'ari wajen ganin ta bawa Anees rayuwa mai kyau. Duk wani namiji daya yunƙuro inda take zata watsa mata mugun kallo dole ya juya yana cije lebe. Yau sam bata marmarin kasancewa da wani namiji. Numfashi ta fesar ta d'aga lemonta na orange juices mai sanyi ta kora tana tunanin ,wai shin duk ina mutumin daya jefata ne cikin kangin rayuwa?. Mutumin da ya yi sanadin ta zama abun gudu da kyama?. Idan yasan cewa tana tare da y'ar sa zai k'arbe ta hannu biyu?. To wai shi d'in waye ne ma?. Menene asalin sa?. Haka tayi ta jerawa kanta tambayoyi har na tsawon wasu lokata. Hak'ika idan ta k'ara had'uwa da Mutumin nan bazata tab'a yafe masa uk'ubar daya jefata a ciki ba. Baza ta daina yi masa Allah ya isa ba da yi masa Addu'a, Allah ya gaggauta k'arban mata hakkin ta a duk inda yake a fad'in duniya. Ya hukuntashi kwatankwacin uk'ubar daya jefata a ciki.

Ba ita ta baro Club d'innan ba saida ta daidaici lokacin tashin Anees ya yi daga makaranta. Tana fakin motar k'ofar makarantar su ana tashin su. Bata jima ba Anees ta fito a guje hango Mummyn nata datayi. Suna tafe a hanya tana bata labarin abunda yau sukayi a makaranta. Duk irin damuwar da take ciki haka ta daure tayi ta biye bata ko itama zata samu salama a zuci. Ta gama yankewa gobe inshaAllahu zasu bar Kano sai kuma wani lokacin bi'iznillahi. Saida suka tsaya nan Rufaida. Suka siyi yan snacks da fura sannan suka wuce gida. K'arfe biyu ta miƙa Anees makarantar Islamiya dake can gabn layinsu nan first gate. Kafin Anees ta dawo daga makaranta tuni Jaleela ta gama had'a musu kayansu da dukkanin wani abu da zasu buk'ata. Masu gidan ta kirasu ta sanar dasu zata tashi gobe inshaAllahu. Bayan dawowar Anees daga islamiya ta iske kayansu a fake guri d'aya. Ran Anees sosai ya soso dan ta gaji da wannan yawace yawacen da suke gari-gari. Yarinya ce ita k'arama amma tana da hankali. Yanzu idan suka koma wani garin shima haka zata fara komai sabo. Makaranta, kawaye. A guje ta shige ɗakin dake kallon na Jaleela tana kuka. Da yake gidan flat ne k'arami mai d'auke da d'aki biyu sai toilet daga tsakiyar sa inda ya raba dak'unnan. Sai falo da kitchen. Daga waje gidan nada y'ar relar da aka kawata da y'an bishiyu na furanni masu kyau. Babu yanda Jaleela batayi ba don ta rarrashe ta amma fafur tak'i ko abincin dare tak'ici ,k'arshe haka ta zuba mata ido har barci ya d'auke ta. Numfashi mai k'arfi Jaleela taja ta gyara mata kwanciya ta rufe ta. Tasan akwai gajiya, amma duk abunda takeyi tana yine saboda ita. Bayan tayi sallan isha zama tayi sosai tana rera kira'a mai tsananin dad'i kace Sudais ne a mace. Ni kaina mamaki ya kamani na zuba mata ido baki a sake ina kallon yanda take karatu a nutse babu gargada. Komai tana bashi hakkin sa yanda ya dace . Ikon Allah idan kaga Jaleela a yanzu koda wasa aka ce maka itace d'azu a club baza ka tab'a yarda ba. Kai k'arshe ma sai kayi fad'a da mutum don babu abunda zai hana kayi zaton sharri ne ko kage ake mata. Yanda take rera karatun zai tabbatar maka tayi sauka ba d'aya ba, bare biyu. Wai shin wacece ne Jaleela?. Awa guda cur ta d'auka tana rera karatun Qur'anin nan mai saka zuciya da kwanji cikin nutsuwa da annashuwa. A hankali ta rufe Qur'anin ta ajiye gefenta. Hannu ta d'aga tana rera Addu'o'i masu tab'a zuciya da bargon jiki. Sosai hawaye suke bin fuskarta tana rerawa Annabi salati da kiran sunanyen Allah, kyawawa ya kawo mata sauk'i cikin wannan rayuwa data tsinci kanta a ciki.

Washegari misalin k'arfe bakwai na safe suka d'auki hanyar Abuja. Saida Jaleela tayi Addu'a sosai kafin ta shiga mota suka d'auki hanyar. Sosai Jaleela ta kware wajen tukin mota tana bin dukkanin wasu k'aidoji daya dace. Ga motar ta saki karatun Qur'ani na sheikh Sudais da Ali jabir. Bata cika tsayawa ba sai in Anees ta buk'aci yin fitsari. Wajen azahar suka isa Kaduna. Saida suka tsaya sukayi sallah ta k'ara cika musu mota da kayan abinci ,su tsire da y'an snacks da lemoka ,sannan suka d'auki hanya. K'arfe uku daidai suka shiga birnin tarayya. Kaman yanda kawarta Kainat tayi mata bayanin unguwar da take. Kai tsaye tayi Gwarunpha phase 2. Unguwar ce gwanin sha'awa ta manyan mutane harma da masu matsakicin rufin asiri. K'ofar wani k'aramin gate gida na bene tayi horn d'in motar ta. Maigadi ya buɗe ta danna kai cikin gidan. Tun kafin tayi fakin motar ta hango Kainat data fito a guje daga gidan sanye cikin riga da wando na jeans da t-shirt fara. Kannan nata yasha gashin doki har hips nata. Kainat irin black beauty d'in nan ce mai yar kiba. Bata da tsayi sam shi yasa koda yaushe cikin heels takarmi take ko a cikin gida. Kainat idon Naira kenan akwaita da san kuɗi da son jindaɗi na rayuwa.

Murmushi Jaleela tayi hango Kainat d'in da tayi. A guje ta k'araso tana ihu ta kama murfin motar ta buɗe.

"Wayyo Beauty wai kece yau a gida na da gaske?, wlh da ki ka yimin waya na d'auka wasa ki ke. Wayyo jama'a yau ga Beauty a gidana "

Y'ar dariya Jaleela tayi tana girgiza kai ta juya tana kallon Anees data fara motsin farkawa daga barcin da take saboda ihun Kainat. A hankali yarinya ta buɗe manyan Blue eye's nata ta watsa su kan Kainat dake kallonta kaman ta had'iye. Da sauri ta matsa bayan motar ta d'auko Anees dake yunƙurin zama.

"Kai gaskiya MashaAllah Jaleela. Wlh komai naki mai kyau ne. Yanzu dubi yarinya nan don Allah kaman ba mutum ba saboda kyau. MashaAllah "
Chapter 2 · 0% Book details