← Book details Guduna Ake Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 15

Sashe 15

Guduna Ake Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

A hanzarce Almu da Zubair suka k'araso suna tambayar Lukman meke damunsa haka yanzu-yanzu. Kasancewa komai ya yi sai wasu irin hawaye masu zafi da radadi da suka biyo kuncin sa. Jiki na wani irin rawa ya d'ago zaice wani abu, Baffa ya kwala musu kira daga k'ofar masallacin suyi maza su shigo ayi sallah . Baice komai ba ya wuce da sauri yana k'ara k'ank'ame wayar dake hannun sa da yake ji kaman wuta aka bashi. Har akayi sallah Lukman baya cikin nutsuwar sa. Haka ya zauna zuru kaman mutum mutumi baya fuskantar komai. Bayan an idar anyi hud'uba, babban limami da zai d'aura auren ya juyo yana neman magabata. Abhie da Baffa suka matso kaman yanda shari'a tace. Kafin Abhie ya Baffa suyi wani yunƙuri wajen wani abu Lukman ya miƙe da wani irin sauri kaman wanda aka mintsina. Jiki na rawa ya yi maganar data girgiza mutane dake cikin masallaci suka zuba masa ido cikin matsanancin mamaki. Baffa ya b'aci sosai a zafafe yace

"Kana da hankali Lukman. Kasan me ka ke furtawa kuwa? Ko kasha wani abune?"

Shar hawaye suka wanke masa fuska murya na rawa ya girgiza kai yace

"Kayi hak'uri Baffa amma na fasa aurenta. Babu abunda nasha Allah ne kuma shedata. Ina son Aleeyna amma bazan iya aurenta yanzu ba bayan abunda na gani"

Yana gama furta hakan ya juya da sauri zai ya fice daga masallacin baima bari wani ya k'ara cewa komai ba. Wani iri shiru masallaci ya d'auka daga Abhie har Baffa matsanancin mamaki da tashin hankali ya hanasu motsi. Liman ne ya yi gyaran murya yace

"Meke faruwa ne Alhaji. Akwai wata matsala ne da ba'a sani ba? Ko kuma dama baisan auren ne?"

Da wani iri sauri Baffa ya girgiza kai zufa nan karyo masa yace

"Ko kad'an Malam. Kasan Yaran yanzu na zamani. Wlh lfy lau ya taho wajen d'aurin auren nan. Wata k'ila y'ar matsalace suka samu yake neman d'aga mana hankali. A d'aura kawai ai nini waliyin sa"

"A'a yaya. Muje dai muji meke faruwa tukun"

Abhie ya katse Baffa da sauri. Kai liman ya jinjina na gamsuwa sa maganan Abhie haka sauran mutaje dake gurin. A hanzarce suka tashi suka fito wanda Almu tuni ya rigasu yin waje. Da wani irin zafin rai ya tare Lukman dake k'ok'arin shiga mota.

"Kana da hankali. Kasan abunda ka ke yi kuwa? Dama kace zaka auri Auta ne don ka tozarta ka wulak'anta cikin mutane da dangi. Menene ribarka na aikata hakan da kayi?"

Shar hawaye suka k'ara wankewa Lukman fuska ya fara kuka kaman k'arami yaro.

"Na ranste da Allah iana son Aleeyna, har yanzu kuma ban daina santa ba, amma bazan iya aurenta ba. Niba fasikin mutum bane saboda haka bazan auri fasika...."

Kafin ya gama kai zancen Almu ya d'auke shi da wani irin b'arin makauniya. Ai a take dambe mai k'arfi ya kaure tsakanin su. Sosai gurin ya chabe da kyar aka raba Lukman da Almu. Shidai Lukman banda kuka babu abunda yake. Tsananin bak'in ciki da tsanan Aleeyna ya darsu cikin ransa da yake ji kaman ya harbeta. Duk abunda za'ayi ayi amma wlh ya fasa auren. Ran Baffa a b'ace ya kifawa Lukman d'in dake ta muzurai yan maimaita bazaiyi auren ba idan ana dole sai a sashi ya yi ,mari.

"Ni zaka tozarta? Nace ni zaka tozarta? Idan wani abune ya faru ka bari ayi cikin sirri mana. Wato na lura uwarka ta fara maka tasiri wajen ganin ka raba kan zumunci ko?"

A zafafe ya ciro wayarsa ya mikawa Abhie dake tsaye yana kallon Lukman d'in ya kasa cewa komai. Jiki babu kuzari Abhie ya mik'a hannu zai k'arbe Almu ya yi wuff ya kwace wayar. Abunda yaci karo dashi jikin wayar ya yi masifar d'aga masa hankali da jiri ya debeshi ya yi taga-taga zai fad'i. Zubair ya yi saurin tashi.

"Innalilllahi wa Inna'ilaihi raji'un. Allahumma ajirni fi musibati wa aklifni khairan min ha"

Almu ya furta da k'arfi. A yanzu kan k'irjin Abhie wani irin matsanancin bugu yake yana kalin Almu daya damke wayar da Baffa ke k'ok'arin kwacewa yaga ko Menene haka a jiki, amma Almu yaki bayarwa. Da wani iri bala'in gudu ya juya a guje ya Zubair ya bishi. Mota ya fad'a jikinsa har wani irin tsuma yake. Ganin haka Abhie da Baffa suka tabbatar lallai koma menene wannan babban abune. A hanzarce suka bi bayan sa Baffa ya saka Lukman a gaba suka shiga mota. Wani wawan fakin Al'mustapha ya yi kofar gida ko motar bai kashe ba ya fito a guje sai Zubair ne ya kashe motar
. Kaman mahaukaci ya shiga yaja kwala kiran Aleeyna. Mata duk akayi cirko-cirko ana kallon Almu daya shigo kaman mahaukaci. Amnah ta fito da sauri tana cewa

"Lfy ya Almu an d'aura auren ne?"

"Ina Auta"

"Tana d'akin Ammi"

A guje ya fad'a d'akin can kuryar gado ya sameta ta nannade cikin bargo Hajjo da wasu mata a kanta suna yi mata sannu. Wani irin fisgota ya yi ya jiki na rawa ya nuna mata fuskar wayar dake hannun sa. Yana tsuma hawaye tab cikin idonsa yace

"Menene wannan? Ki gayamin bake bace a cikin video danan Auta, ki gayamin"

Wani irin dum kanta ya Sara ta kwalao ido tana kallon kanta dake jikin video da Almun ke nuna mata. Gata nan a kwance da wani namiji yana sex da ita haihuwar uwa. Blue film ne sosai. Tsananin kidima da tashin hankali da Aleeyna ta gani ta kasa motsi. Aikuwa Almu ya d'auke da wani irin mari da a take ta sume a guri. Da ihu ya yi kanta zai rufe da duka yana cewa

"Kiyi kun magana"

Dan sam bai lura ta sumen ba. Su Abhie suka riƙe shi da sauri. D'akin duk ya kacame da ihu-ihuce. Wani irin komawa gefe Almu ya yi ya durkusa ya had'a kai da gwiwa yana kuka kaman karamin yaro. HAJJO sai bala'i take kaman zata rufeshi da dukan itama. Ammi kuwa ta kasa ceea komai tsaban mamakin wannan abu. Jikin Abhie a matuk'ar sanyaye ya kai hannu ya kwace wayar dake hannun Almu. Kallo d'aya ya yiwa wayar ya yanke jiki ya fad'i. Ai zo kaga ihu. Hankula suka k'ara dugunzuma. Sai koke-koke da d'akin ya kaure dashi. Cikin tashin hankali aka kwashe su zuwa asibiti. Lukman kuwa babu wanda yasan sanda ya sulale ya bar gurin. Taimakon gaggawa aka basu . Saida Aleeyna tayi awa biyu cur bata farfaɗo ba. Abhie kuwa tun kafin su k'arasa asibitin ya farka yana ta nanata Innalilllahi cikin ransa. Abu dai duk ya dagul an shiga cikin damuwa da tashin hankali. Duk suna zaune jugum jugum Hajjo ta d'ago ta kalli Almu dake tsaye jikin bango duk ya fice hayyacin sa tace

"Wai me yake faruwa ne? Kai Mustapha ka samu a duhu. Ka warware mana abunda yake faruwa gashi ance ba'a d'aura auren ba har yanzu. Ina ma Lukman d'in ne?"

K'irjin Abhie dake wani irin zafi ya taune harshe yana kallon k'asa saboda idan Baffa da yake ji a kansa. Kafin Almu yace wani abu likita ya fito yana cewa su biyoshi office. Abhie, Baffa da Ammi sai Hajjo ne suka shiga. Saida bayan sun zauna yace

"Sakamakon bincike da mukayi ya tabbatar mana da yarinya na d'auke da juna biyu wata d'aya da sati biyu. Ya kamata a dinga kula da Lafiyarta ita da abunda ke cikinta. Saboda early stage na pregnancy babu abunda bazai iya haddasawa ba. A daina bari tana yawan shiga damuwa saboda mun fuskanci tana cikin depression hakan kuma had'ari ne sosai a gareta dan zai iya janyo wa cikin jkinta ya zube. A dinga bata cika mai kyau saboda lfyr ta da kuma abinda ke cikinta."

Wani irin shuuu sukaji gaba d'ayan su kafin suji Tim Ammi ta zube k'asa a sume. Jikin Hajjo na wani irin rawa tace

"Likita wacece take da cikin harna wata guda da sati biyu? Badai jikita ba ko? Yarinya da ko aure batayi ba yau d'innan ne za'a daura auren sai kuma y'ar matsala ta faru. Ka k'ara dubawa da kyau dai ko kayi kuskuren wajen sunan"

Kai ya girgiza " A'a Hajiya. Ita dai wannan yarinya da aka kawo itace nake miki bayani ga file din nata ma ki duba "

Kasa motsi Abhie ya yi sai Baffa ne karb'a jikinsa na rawa. Takardun sukayi ta zubewa yana d'aukowa saida ya yi haka har sau uku sannan ya iya riƙeta a hannun ya buɗe yana karanta report d'in a fili. Innalilllahi wa Inna'ilaihi raji'un. Hak'ika wata masiba da tashin hankali ta ratso cikin family nasu kuma babu ta yanda za'ayi su iya guje mata. Wani irin gunjin kuka Hajjo take taba salati da sallami. Shi kuwa Abhie kai ya sunkuyar hawaye na diga daga idansa. Innalilllahi wa Inna'ilaihi raji'un. Firgigit Ammi ta farka ta kaman wacce aka mintsila. A guje ta fice daga d'akin tana kuka sosai mai tab'a zuciya. Kai tsaye d'akin da aka kwantar da Aleeyna ta kusa inda ta tarar da duk yan uwan da dangi a ciki saboda farkawarta. Ratsu kawai tayi daidai Amnah da Bagira K'awar Aleeyna na k'ok'arin kamata ta zauna.babu zato ta rufeta da matsanancin duka tana wani irin kuka. A guje aka rike Ammi ana bata hak'uri cewa kawai take

"Ku kyaleni na kasheta na huta da wannan bak'in ciki data jefamu. Ku kyale"

Da kyar aka janye Ammi daha jikin tana kuka sosai. Baffa ya shigo yace kowa da kowa ya fita zaiyi magana da Aleeyna. Saboda yanda Baffa keda kwarjini babu wanda ya musu duk suka fice suka barshi da ita. Wani irin kuka take ta had'a kai da gwiwa abun gwanin tausayi. Numfashi ya fesar mai zafi ya zauna kan kujera yana fuskantar ta ya kira sunanta.

"Aleeyna "

Bata iya amsawa ba sai kai data d'ago ta kalleshi da idanuwan ta da sukayi jazur .

"Ki gayamin tsakani da Allah. Waye ya yi miki ciki?, nasan tarbiyar ki Aleeyna nasan wacece ke. Tarbiyar gidanmu abun alfahari ne a garemu nasan cewa hakan kawai bazaki bari wannan tarbiyar ta lalace ba. Ki gayamin wayene ya lalata miki rayuwa ?.waye sanadin da yaja tarbiyar wannan ahali take k'ok'arin wargajewa?"

Dumdumdum. K'irjin Aleeyna ya wani iri bugawa da saida Baffa yaji. Suman zaune tayi ta kafe Baffan da ido kaman wadda ke ganin kai hud'u a tare dashi. Ita ce take da ciki? Mafarki take ko me? Taya zatayi ciki ita da bata tab'a sanin wani namiji ba? Ko wancan ranan ma tana al'ada kuma bai keta mata haddiba. Innalilllahi wa Inna'ilaihi raji'un. Luu ta koma ta k'ara zubewa a sume.

End of free page.

Chakwakwayi da gwaramar yanzu ta fara. Yar uwa kar ki sake ayi wannan tafiyar babu ke.

GUDUNA AKE it just @ 500N.
A turo payment wannan account number

👇

3078293347
Aisha sani danjuma
First Bank.

A turo shedar biya wannan number.

08140754777.

Sai na jiki masoya Ashantylove na kwarai.
Chapter 15 · 0% Book details