← Book details Guduna Ake Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 15

Sashe 4

Guduna Ake Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Murmushi ne kwance kan fuskar Wazir da Abu Sufyan har Malika ta miƙe don barin fadar. Kallon Wazir tayi da Abu Sufyan da suka rungume juna bayan sunyi musa baha na taya juna murna kaman yanda Larabawa ke yi. Kai ta d'aga musu ta wuce bayin ta da fadawan ta suka rufa mata baya. Wata had'addiyar lifter dake cikin falon ta glass da aka kawata da gwal ta shiga ita kad'ai sai wata baiwa dake binta duk inda tayi. Sauran suka shiga wata dake jikin wannan. Hannu ta kai a hankali ta dafe goshinta da take ji kaman zai rabe biyu ,sosai take cikin damuwa da tunanin kaman sun k'ara tafka wani kuskuren babba. Tana fargabar abunda ya faru da sauran matan da Yareema ya aura, ya faru ga Aafiya . Duk cikin yaran dake rububin zuwa ,bata san me yasa ba Aafiya tafi kwanta mata a rai. Ko dan hakan yana da nasaba da hankali da kuma tarbiyar da take tunanin yarinya na tare da ita ne?. A hankali ta furta a fili

"Ya rabbil samawati, ya ubangijin sammai da kasai. Ya ubangijin dukkanin wata halitta. Mutum ko Aljan. Ya wanda ya halicci ruwa, ya halicci iska, ya halicci wuta da Aljanna. Ya Zuljalalu wal Ikram. Allah ka kawo mana mafita cikin wannan sark'arkiya da bamu da amsar ta. Allah ka kawo mana k'arshen wannan musiba. "

Baiwar dake kusa da ita ta amsa da Amin cike da tausayin uwar d'akin nata. Hak'ika tun tasowar ta cikin masarautar nan taga irin gwaggwarmaya da SARKI KHALELULLAH ya yi da matarsa MALIKA, ARWA . Tasan dukkanin wani kalubale da jarumta da sukayi wajen ganin sun gina wannan masarauta mai Albarka. Taga irin jarumta da Malika tayi bayan k'asa ta rufewa SARKI KHALELULLAH ido. Irin dawainiya da take da ya'yan ta da mutane wajen basu kulawa da kariya daga dukkanin wani sharri da kalubale na rayuwa. Na ciki dana waje. To amma Yareema yana tare da wani sark'arken abu da an kasa gano masa. Anyi maganin sammu, anyi na aljanu. Amma an kasa samun nasara. A yanzu kam Addu'a ce kawai ake yi da yawan sadaka Allah ya warware koma menene. Ita kanta tana tausayin Aafiya.

ABUJA.

To Jaleela dai kam an zama mutanen Abuja. Duda dama Abujan ba bakon ta bane. Sai dai zuwanta yanzu ,Kainat tayi yawo da ita sosai cikin garin Abuja musamman clubs dake ci sosai na manyan yara. Tunda suka zo take ta fad'i tashi wajen ganin ta mayar da Anees makaranta. Yarinya har sukayi kwana biyu ta kasa daina kunci ,sam taki walwala. Abun tun baya damun Jaleela har ya fara damunta. Don haka yau ta d'auke ta suka dinga yawo Park,Parks da mall don ganin tayi walwala. Ai kuwa Anees tafi kowa farin ciki. Rabon da Jaleela taga farin ciki kan fuskar yarinya kaman haka harta manta. Sannu a hankali ta fara warwarewa musamman yanzu data fara zuwa makaranta tayi kawaye sosai. Kowa yana son ganin ya zama abokinta saboda kyau da Allah ya bata ga masifar k'ok'ari.

A b'angaren Jaleela itama abun haka ne. Don yanzu dukkanin wani clubs da suke zuwa ita da Kainat tayi suna. Sunanta na clubbing shina LA REINA ,the cold Beauty. Ba ko wane namiji ne yake cire tuta a kanta ba sai ta zaba ta dirje kafin kace me,kuɗi sun fara zamarwa Jaleela tana wadaka dasu sai abunda taga dama. Nanny guda ta d'aukowa Anees dake kulawa da ita idan basa nan, duk da cewa basa fita sai ta tabbatar Anees tayi barci haka nan duk inda take, duk inda hud'u na asuba tayi zata dawo kafin Anees ta farka. Ciki kwana biyun nan ma basu cika had'uwa da Kainat ba saboda tayi busy sosai da wasu alhazawa da suka zo Nigeria.
Ita dai Jaleela nata harkan bata bada kanta. Zatayi maka dukkanin abunda ka ke so amma baza ka tab'a ba tare da kasa ko yatsa a jikin ta ba. Wannan shine sharad'in ta. Abunka da mai kyau a guje mazan ke k'arban wannan offer, sudai indai zasu huta ai basu da matsala. Can k'asan zuciyarta tana kyamar wannan abu da take. Kai su mazan ma gaba d'aya ta tsane su , don namiji shine SILAH na fad'awarta cikin wannan halaka. A ganinta wannan abu da take shine kad'ai zai bata damar da zata bawa Anees rayuwa mai kyau. Dukkanin wani abu da zatayi gani take baza ta samu ba kaman yanda take samu haka ,bare har ta gina musu rayuwa mai kyau. (To amma kin manta kuɗi irin wannan basu da Albarka tunda ba ta hanyar mai kyau aka same su ba).

Yau asabar daga ita har Kainat suna gida. Gaba d'ayan su suna falo ne. Jaleela na kwace cikin katuwar kujera sanye da riga da wando pink color. Anees na sanye cikin wata y'ar k'arama gown silver mai hoton unicorn a jiki. Kanta an rabashi biyu an kamshi gefe da gefe. Kainat kuwa n kwance kasan kafet tana mafa da waya daga ita sai y'ar doguwar riga mara nauyi. Ihu tasa ta miƙe tana zare ido a waje. A kasalance Jaleela ta kalleta ganin yanda duk ta rude riƙe da waya baki a hangame. Anees tace

"Aunty Kainat, menene? Ko kinga dodo ne a wayar?"

Dariya Kainat ta saki a hanzarce tace da Anees.

"Baby jeki d'aki ki d'aukomin laptop d'ina kinji y'ar Albarka "

A guje Anees ta ajiye Teddy da take wasa dashi tayi d'akin a guje. Da azama Kainat ta taso ta zauna kusa da Jaleela dake kallonta. Saida ta nuna mata wayar hannun ta tace

"Gaskiya ke ko, ta dabance wlh. Labarin ki kawai yaji yake nemanki ruwa a jallo. Kinsa waye yake nemanki kuwa? Yanzu nan Khairat ta turo min. Kin san waye? ZAIN"

Ta fad'i sunan da k'arfi. Tsaki mai k'arfi Jaleela ta yi tace

"Waye kuma haka?"

Ido Kainat ta waro harda d'aka mata duka

"Zain ne baki sani ba?, d'an minister babban likita dake zama a turai. Ance yazo gari yaji labarin ki shine yace yana son had'uwa dake. Ko kinsan irin sa'ar da zaki taka idan ki ka kasance dashi?. Mata da yawa suna mafarki a kansa da burin kasancewa dashi kona rana d'aya ne. To ganin sa ma wahala yakewa mutane bare ka same shi. Kaman yanda ki ke juya mutane shima haka yake dan yaga yana da kyau. Ga kuɗi, ga kyau, ga aji, ga class. Haba wlh kedai kina da sa'a, manyan yarane kawai ke binki, ko da yake kin cancanci hakan ne don duk yanda mutum zai kiyasti ki kin wuce haka"

Baki Jaleela ta tab'e cikin ko in kula tace

"Bani da lokacin sa"

Kainat ta buɗe baki zatace wani abu Anees ta fito a guje da laptop d'in datace ta d'auko mata. Dole ta taune harshe tayi shiru da maganan, amma ta kudurta a ranta dole nema ta had'asu. Itama ta yagi abunda zata yaga Jaleela baza tayi mata bak'in ciki ba.

𝗚𝗨𝗗𝗨𝗡𝗔
𝒜𝓀ℯ.

𝓐𝓼𝓱𝓪𝓷𝓽𝔂 𝓵♡︎𝓿𝓮

16/20.

Tsawan kwana biyu Kainat nayin dukkanin iya bakin k'ok'ari wajen ganin ta shawo kan Jaleela sunje club d'in da take tunanin Zain na zuwa, fafur Jaleela tak'i kwana biyu ma babu inda taje ta mak'ale a gida wajen Anees. Duk hanyar da Kainat ta biyo Jaleela zata toshe dole tayi shiru ta zuba mata, amma k'asan ranta tana had'a plan. Saida tasan yanda zatayi ta samu number Zain. Da farko tayi masa kiran duniya yak'i d'agawa saboda isa. Haushi kaman ya kashe Kainat. Batayi k'asa a gwiwaba ta tura masa sak'o cewar ita tasan yarinya da yake nema La REINA, the cold Beauty. Zata had'ashi da ita amma sai ya bata kaso mai tsoka.
Lokacin da sak'on ta ya shigo wayarsa yana kwance ne cikin tamfatsetsen d'akin sa da aka kashewa dukiya. Gajeren wando ne a jikinsa da single. Zain kyakkyawan mutum ne irin handsome black beauty d'in nan. Yana da manyan lumsheshshun idanuwa da dogon hanci ,bakin sa irin full d'innan ne dake nan jazur dashi ,kuma very oily kaman wanda ke shafa masa man leb'e. Zain yana daga cikin irin mazannan da za'a kira tsaka-tsaki a fannin tsayi. Yana da murdadden jiki burin ko wace mace. K'irjinsa kuwa cike yake da gashi yala-yala daya kwanta tsam gwanin sha'awa. Haka fuskar sa kewaye take da dan siririn gashi daya zagayo har zuwa bakinsa. Ana kiran irin wannan gyaran fuska da kwata million. Zain kan abun MashaAllah don ya gama had'ewa ta ko wanne fanni. Bak'ar fatarsa da taji hutu da kuɗi sai shek'i take irin ta aje butters. Ga fatar tasa da mugun laushi kaman mace. Bashi da gashi sosai a kansa don gashinsa irin namu ne na malam bahaushe, amma saboda gyara da mai da kan kesha gashin ya kwanta lum kansa, ya nannade kace hula ya d'ura.
Chapter 4 · 0% Book details