Sashe 11
Guduna Ake Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hanzarce ta fice ta barshi a tsaye cikin matsanancin mamaki. 'Anees y'ar kace. Flesh and blood' What?. Tsaban yands maganan ta dake shi ya kasa motsi sai k'ofar daya kafe da ido. Magana d'aya ce cikin ransa. But how? Bazai manta ba clear as a day ko a wancen ranan bai kusance ta ba so how is this possible? .sai a yanzu ya yi snap daga shock d'in daya Shiga a guje ya fito daga gidan amma tuni Jaleela ta fice da matsanancin gudu. Numfashi ya fesar mai zafi bazaiyi k'arya ba ya yi abubuwa da ita sosai ranan but he did not go all the way in.
Jaleela dai maimakon tayi gida sai tayi hanyar wajen Abuja kaman yanda tayi kuduri. Sosai take shek'a gudu kan titi don ta tsere masa. Tasan yanzu tunda yaji wannan bomb dole zai biyota gida, inshaAllahu ita kuma ta gama zaman Abuja. Koman dare a yau d'innan ba gobe ba zata koma Gida .zata koma wajen iyayenta.
UNKNOWN
Wani irin d'aki ne mai tsananin duhu da ko tafin hannun ka baka iya gani. Babu windo ko k'ofa a d'akin da wata iska ko haske zai shigo. Haske guda d'aya ka ke iya hangowa kaman dot. Wasu irin eerie red glowing eyes ne masu matuƙar ban tsoro da tsananin hasken su yake dan reflecting a d'akin. Blinking idon sukayi don su kad'ai ka ke iya gani saboda duhu. Direct suka kalli bango sai ga wani irin round mudubi ya nuna a jikinsa. Hasken idon ya yi reflecting mudubin a take wani irin hayaki ya fito daga cikin sa sai kuma ya koma ys rufe mirror d'in gaba d'aya. Wata irin murya mai amo da ban tsoro ta fara magana kaman mai chanting abu.
Abun mamaki saiga hoton Jaleela da Lameen tsaye jikin mudubin suna magana tsakiyar d'akin kaman mai kallon TV. Dukkanin wani abu daya faru tun daga inda Jaleela ke dariya na cewa suyi aure har zuwa sanda ta fice tana gaya masa Anees y'ar sace. Kaf ya yi playing a jikin mudubin. Wannan bakin hayakin dake zagaye da mudubin ya rikid'e lokaci guda ya yi shaping kaman mutum. Gaban wannan jan idon ya tsaya da har zuwa lokacin baka ganin mamallakinsu. Maganace ta fara fitowa daga cikin sa kaman iska
"The fairest of all ta kara dawowa shugaba. Idan mukayi sakaci zata zama mukulli da zata kawo k'arshen mu"
"A'a. "
Muryar tayi amo mai k'arfi saida d'akin ya jijjiga. Tana wani irin gurnani mai ban tsoro tace
"Wannan karon babu tantama idan ta kara shiga gonar daba tata ba zata mutu. Allahn ta da take bautawa shine yake bata kariya mun kasa samun nasara a kanta. Amma karfin ikona da magic nawa wannan karon zan samu nasara. Zamu fara da y'ar. Babu wani shamaki da zai shiga tsakanin da KING . Da nasan cewa tun wancan ranan tana d'auke da cikin sa dana hallaka shi tun baizo duniya ba. KING nawa ne ni kaɗai. A shirye nake na kashe duk wanda zai rabe shi."
WACECE JALEELA?
Shekara BAKWAI (7YRS) da suka wuce.
Seven years back.
......
Next page.
𝗚𝗨𝗗𝗨𝗡𝗔
𝗔𝗞𝗘 .
𝒜𝐬𝐡𝐚𝐧𝐭𝐲 𝐥♡︎𝐯𝐞.
A/N. Wannan page naku ne masoya littafin GUDUNA AKE. bazaiyiwu na kira suna ba don Allah kaɗai yasan yawan yaku. Ashanty tana godiya da kauna ❤.
36/40.
WACECE JALEELA?
Jaleela Mukhtar Bature ko nace ALEEYNA. Iyayenta Mukhtar Bature cikakken Kanuri ne ya yinda Ammi , Zulaikha Abdulaziz Bature sadaka yalla ce. Mutanen Niger ne sudin kuma y'an uwane. Sunyu aure ma zumunci da kuma kauna. Allah ya azurta Bature da ya'ya da jikoki. Sai ya kance suna aure tsakaninsu da wuya kaga sun auri bare. Bayan auren Mukhtar da Zulaikha suka bar cikin dangi da y'an uwa suka dawo nan Jihar ADAMAWA state Saboda aiki. Abhie yana da buri ganin ya buɗe makaranta ta yana yana koyar dasu ilimi na addini. Saboda haka suna dawo ya fara tara yara nan k'ofar gidan sa yana d'an koya musi hadithi da fikihu. Shekarar su biyu da auri Ammi ta haifi AL'MUSTAPHA. Almu dana Shekara guda cif Ammi ta fuskanci tana d'auke da wani cikin. Sosai ta shiga damuwa ga ciki ga kuma goyo. Haka tayi ta hak'uri da kukawar Abhie ta rani cikin da Almu da take shayarwa. Wata tara cif ta haifi Amnah. Almu da Amnah sun taso cikin gata da soyayya da kuma tarbiyar. Daga kansu Allah sa ikon sa Ammi bata sake ko b'ari ba. Saida Almu da Amnah suka shekara bakwai da y'an watanni saiga wani ciki. Wannan karan kam ciki mai matuƙar laulayine da saida ta kai Abhie ya aika can Niger aka turo kanwar Ammi ,Fareeda tazo tana taimaka mata. Sosai Ammi taci wuya wannan cikin kaman bazata kai ba. Yanda ta saba haihuwa wata tara cif wannan saida ya cika wata goma. Ranan da nakuda ta tashi kuwa wuni tayi tana fama. Makota da unguwar zoma sunyi k'ok'ari a kanta sosai. Cikin ikon Allah wajen asuba ta sankaco baby girl mai tsananin kyan gaske don tafi su Almu da Amnah kyau nesa ba kusa ba. A take Abhie ya yi mata hud'uba da rad'a mata sunan ALEEYNA wato ma'ana ( BEAUTY AS THE MOON). Babu wanda yakai Almu da Amnah farin cikib samun kanwa. Y'an uwa da abokan Arziƙi suna ta turuwa zuwa barka kace haihuwace ta farko. Duk wanda yazo yaga ALEEYNA saiya tanka ta. Saboda haka ne Abhie ke yawan sawa ana mata rubutu ana bata basu gaba d'aya saboda bakin mutane.
ALEEYNA ta taso cikin kauna gata da soyayyar iyaye da kuma yayye. Lokacin data shekara goma sha d'aya cif a duniya sukayi sauka gaba d'aya ita dasu Almu wajen Abhie. Ya dage sosai a kansu wajen karatu gasu yara ne masu matuƙar hazaka da kwakwala. Allah da ikon sa kuwa makarantar Abhie ta habbaka sosai almajirai ta ko ina suna tururawa wajen ganin sunzo sun samu ilimi mai kyau. Nan k'ofar gidansa Abhie yasa aka buge akayi siminti da kuma rufi na kwano. Kangon da yake jikinsa kuma ya siya aka gina masa makaranta da kuma dakuna na almajirai da suka kwana. Shekarar Almu ashirin cif lokacin ya yi sauka har bazata ta kirguga ba. A lokacin kuma ya gama secondary shida Amnah suna shirin wucewa Jami'a ta ABU dake can zaria. Aleeyna tana shekara goma sha uku. Idan kaji yanda take karanta maka hadithi da nahawu, sai ka riƙe baki. Abhie saboda ganin ta fara tasawa yasa ya sakata nan makaranta ta islamiya da take can gaba dasu. Tana fara zuwa makaranta saboda hazakar ta duk wani abu daya danganci musabaka ko taro da za'ayi itace a gaba. Wani lokacin haka zaka ganta y'ar mitsitsiya a aji tana koyarwa. Sosai Aleeyna tayi suna ga kyau ga ilimi. Qur'ani kuwa idan ta fara karatun sai kaji kaman karta daina. Tana shekara goma sha biyar kyawunta ya fara fitowa sosai da sosai. Don Aleeyna irin yarannan ce mai garin jiki saffa-saffa musamman daga kirji da kugunta. Komai nata irin na Ammi ne. Lokacin da girma ya fara zuwa zai ya kasance koda yaushe cikin hijabi take ko a gida. Kai ko barci zatayi bata cire Hijabi ,gata yarinya mai tsananin kunya da girmama mutum. Hakan ya jawo mata soyayya ta mutane lungu ta tsako. Ko baka santa ba kanajin labarinta sai ta shiga ranka.
Tana shekara goma sha shida akayi auren Aunty Amnah da Zubair. Yasha wuya sosai kafin ya sameta don Amnah da Zubair jirginsu ba d'aya ba. Zubair dan gidan attijaran mutum ne, maihaifin sa kansila ne a nan garin ADAMAWA. Acan ABU d'in ya ganta sanda yaje raka wani abokinsa. Tun daga lokacin ya haukace yana binta ita kuma sam taki bashi fuska. Saida ya had'a hannu da Almu ya shige jikinsa ya zame masa aboki na k'arfi da yaji. Cikin ikon Allah ya fara samu kan Amnah. Babu b'ata lokaci duka iyayen sukayi Na'am da batun. Lokaci kad'an akayi aure babu wata haniya sai yar walima da sukayi da y'an al'adu irin nasu na kanuri da sadaka yalla. A nan ne dan gidan wan Abhi , wato Lukman yaga Aleeyna ya rikice shifa yaga mata. Da yake ba wani zuwa Niger din take ba shi yasa dangi ba kowa ta sani ba. Saida kowa daya halacci bikin yasan Lukman na son Aleeyna. Sosai ya rikice ya zama abun dariya cikin y'an uwa. Kowa yana cikin murna da farin ciki saboda an jima ba'ayi auren zumunci ba. B'angaren Aleeyna kam sam bata son auren zumunci saboda haka tun abun Lukman baiyi nisa ba ta gaya masa ita bata sonshi. To da yake Lukman ya yi nisan da bayajin kira sam yaki haka ya yi ta bibiyar rayuwarta. Tun tana wulak'antanshi har ya fara samun kanta. Lukman ya iya soyayya da kulawa. Baya cikakken sati biyu zaizo ADAMAWA ba. Uwa uba ga kyau ga rufin asiri daidai gwargwado Family na Bature suna dashi. Don Alhaji Bature irin tsohon attajirin nan ne. Duk cikin su babu mummunan saidai ace wancan yafi wannan kyau.
Ganin yanda Lukman ke zarya Abhie ya shirya da kansa yaje can Niger ya samu wansa IBRAHIM BATURE. Bai bar Niger ba saida ya tabbatar an saka rana na Aleeyna da Lukman. Kai ranan Lukman kaman wanda aka bawa Aljanna. B'angaren Aleeyna kwana tayi taba kuka bawai bata son Lukman bane, ita tana da burine taga ta gama makarantar book tukun kafin tayi aure. Kuma tasan can Niger Lukman zai kaita tunda nan yake zaune. Ita kuma bata son abunda zai rabata da Ammi sam.
Babu yanda zatayi haka ta cigaba da zuwa makaranta boko da islamiya lokaci kuma na k'ara matsowa sosai na bikinta da Lukman.
FAITHFUL DAY.
A hanzarce ta fito sanye da Hijabi na islamiya dayazo mata har k'asa. Nikaf dake hannunta ta warware tana k'ok'arin daurawa a fuska, Ammi ta fito daga kitchen rike da kula a hannun ta.
"Har kin fita Leeyna? Bazaki bari ki karya ba?"
Da muryarta maitsananin dad'i tace
"Ammi na makara. Musabaka za'ayi kuma nice zan farayi. Tun dazu Aina'u ke kirana a waya. Idan naje bazan rasa abunda zanci ba"
Kai Ammi ta girgiza tace
"To shikenan ai Allah ya taimaka ya bada sa'a "