← Book details Gidan Aunty Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 23

Sashe 8

Gidan Aunty Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

➰➰➰➰➰➰
A gajiye ya dawo gidan bayan mutane uku da yayi wa aiki a asibiti da kansa ,sai faman lumshe ido yake , amma a zahiri bazaka taba tunanin hakan ba , zaka dau ka yanayinsa ne haka , shaf shaf yayi wanka cikin armani white colour, sosai kayan sukai masa kyau , a maimakon gyara gashin da ya saba yan tajeshi kawai yayi ya zubo masa har bayansa, sosai yayi kyau a cikin shigarsa, wayoyinsa kawai ya dauka tare da nufar part din ammi, yau kwata kwata be sata a idanunsa ba amma a zahiri fuskarsa a hade take ba ko alamun yasan wani abu me kama da murmushi. Yana shiga part din ya tarar da su kowa da Riga da Wando sai faman rawa suke, amrah ce me koya musu yadda zasuyi step din rawar,kwata kwata basusan da shigowarsa ba , hatta kamshin turarensa da sukaji basu kawo komai a ransuba, dan kusan kullum da kamshin a cikin falon ammi. Folding din hannunsa yayi a kirji yana bin ko wannansu da kallo daya bayan daya ransa ba karamun baci yayi ba musamman irin shigarsu ko dan kwali babu, be tankamusu ba duk da yadda kan nasa ke Sara masa , sexy eyes dinsa dasuka fara canza kala daga launin fari zuwa ja ya zubamusu, ihsan ce ta fito sanye da hijab a jikinta hannunta dauke da cup sai faman tiriri yake, kallan su amrah tayi tare da girgiza kanta , “kunsan dai yaya king ya hana wannan raye rayen ko, Allah Inya dawo sai na fadamasa dan bazaku jajamun ba”, hararar ta summy tayi “ sannu kasa yanxun ma zaki iyazuwa, matsoraciyar banza kamar da gasken iya zuwa zakiyi”, girgiza kai firdausi tayi “Aah sumy Wana irin taje ta fada kinsan dai wallahi yaya king ya Kamamu ba karamun wuya zamusha ba musan man dressing dinmu, kuma kusan bama sawa sai in bayanan “, siririn tsaki amrah taja “matsalata da ku kun fiya tsoro wallahi, kafun ya dawo ba mun gama ba , ai baze san munyi ba , yanxu fa zamu gama step din rawar kafin ammi ta dawo”. Dukkansu yanajin abunda suke fadi , duk abunda suke yana ganinsu kwata kwata basu hankalta dashi ba, amrah ce ta kunna musu wata wakar, ta juya kenan a cikin salon rawar idanuwanta suka sauka a kanshi, sosai ta firgita , bakinta ne ya fara rawa kwata kwata ta rasa me zatace, kallanta summy tayi “ke kuma lapiya jikinki yake rawa”, girgiza mata kai kawai amrah take tama kasa magana ganin irin kallan tsanan da yake jifanta dashi “watan cin ubankune yayi”a zahiri kuwa yana yadda yake ko a fuskarsa bazaka gane yanayinsa ba duk da tsananin gajiyar dayayi. Ganin sai faman kallan waje taya amrah take jikinta na rasa yasa duk juyawa zuwa direction din,”Innalillahi wa’inna’ilaihi rajiun, shikenan mun kade har gay yan mu gashi ammi batanan “kowa da abunda yake sakawa a zuciyarsa , iya firgita sun firgita musamman ganin yadda launin idanunsa ya koma ,firdausi har da faduwa kasa tsabar rudewa,duk zubewa sukai akan gwiwowinsu ko waccen su sai matsar kwalla take,sosai suka rude musamman ganin irin kallan da yake bin kowannansu dashi, a hankali ya taka kafarsa tare da nufar sofa din dake left side dinsu , kwallar bakin ciki ihsan ta share dan duk su suka ja mata, ta ja musu Allah ya isa ba a dadi cikin zuciyarta, ba wacce ya kalla a cikin su sai ma wayar hannunsa da yake latsawa, cikin rawar murya me san sakin kuka ihsan tahe hannayanta “wallahi yaya zanyi bayani”, be Motsa da ga yanayin da yake ba balle su sa ran ze amsa mata, Kuka Kawai ihsan ta saki tana toshe bakinta karta kuma yin wani lefin, su amrah kuwa kowa sai faman zare ido yake fatansu Allah yasa be ji abunda suke tattaunawa. Kamar daga sama sukaji saukar maganarsa “ coffee “ da Sauri amrah ta tashi duk da acikin yanayin tsoran da take, dan iskan kallan da yayi mata ne yasa ba shiri ta koma tana zare idanu, ganin hakan yasa atsorace ihsan ta mike ganin be mata magana ba yasa ta nufar kitchen din cikin sauri, sai faman ajiyar zuciya take , duk tabi ta rikice ta rasa yadda zata hada masa coffee din , cikin sauri Sauri ta dakko wayanta dake aljihun Wandanta. Yanda ake yin coffee din tayi searching, cikin rudewa ta gama fito da abunda zata hada masa coffee din jikinta sai faman rawa yake .

Cikin dan karamin tray ta fito da coffee din kusan na uku kenan tanayi kafun tayi wannan din, ganin su amrah na frog jump ne yasa kafarta rawa idanuwanta harsun cika da kwalla, coffee din ta ajiye masa tana komarin fara frog jump din ne abazata taji saukar muryarsa “ Leave” , nannauyar ajiyar zuciya ta dauke da harshi saida yajita “ nagode yaya king, na….” Hannunsa kawai ya daga mata ,cikin sauri ta bar wajan cikin gudu gudu, tunda Allah ya kubutar da ita.

Sosai suke frog jump ko wacce fuskarta jaga jaga da majina , ga hawayen da suke yi, da zaran sunji kuka zai kwace musu zasuyi saurin toshe bakinsu gudun wani punishment’s din. Duk fadin falon ammi haka zuke zagayeshi ko wacce ta fita daga hayyacinta ba damar yin kuka a fili.

Yana zaune sai faman operating wayar hannunsa yake se yanxune ya dauki coffe din da aka hada masa” kurba daya yayi amsa ya ajjesa. “Yaya dan girman Allah da manzan sa kayi hakuri”firdausi ce tayi maganar hawaye sai bin fuskarta yake, lumshe gajiyayyun idanuwansa yayi, tariga ta hadasa da abunda baze iya musu akai ba, “God save you”yafada cikin zuciyarsa “Leave “, baki summy ta bude Baki da niyar yin magana amma ya dakatar dasu ta hanyar dafe kansa , sun gane me yake nufi hakan yasa a guje ko waccen su ta bar part din Daidai lokacin da ammi ke shigowa, da kallo tabisu ganin babu Wanda ya kula da ita kafun ta karasa shiga falon.

➰➰➰➰➰➰
Karfe uku na dare ko ina yayi shiru kasan cewar ko wana bawa yana wutawa a irin wannan lokacin, wani macijine fari tas dashi ya fito cikin wani rani tare da kwanciya bayan tahee,cikin mafarkin da take tafara lalube lalube har hannun ta ya Kai……

Manage plx🥹

💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖

DUK KARFIN IZZATA (Star lady)

GIDAN AUNTY( mss Lee)

TAFITA ZAKKA ( maman sayyid )

JINI DAYA ( mrs bbk )

SARKI SAMEER (xeenat love )
‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA

💖GIDAN AUNTY💖
( A heart touching love story)

By mss Lee 💖

💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖

PAID BOOK

BOOK 1📕

Free page 8 🦋

Karfe uku na dare ko ina yayi shiru kasan cewar ko wana bawa yana wutawa a irin wannan lokacin , wani macijine tass dashi ya fito cikin wani rami tare da kwanciya a bayan tahee ,cikin mafarkin da take ta fara lalube lalube, har hannunta ya kai kan wannan siririn macijin, jin abu me laushi da san tsi besa ta bude idanuwan ba , sai faman shafashi ,a firgice ta farka daga baccin da take “mewam “ta furta cikin firgici, juyawar da zataine idanuwanta Suka sauka kan macijin , azabure ta Kwala ihu”oumma, oumma” ta fada a tsorace ganin duk ihun da tayi oumma bata motsaba, ja da baya ta fara ganin macijin na kokarin biyotan itama ,” Innalillahi me nayi maka kake biyoni, oumma ki temakamun”, duk ta firgice ganin macijin yayi Kuri da ido yana kallanta, ga oumma da ko motsawa batayi ba,kara nufota macijin yayi ta fara girgiza kai “ Dan Allah ba danni ba kayi hakuri , ni bansan me nayi maka kake bina ba, kayi hakuri dan Allah “ ta karasa fada tana fashewa da kuka, kamar daga sama taji saukar yar muryan dan yaro” ni ba abunda zan miki , kawai inaso na zauna wajanki “, waro manyan idanuwanta tayi kamar zasu fado kasa jin maciji na magana abunda bata taba jiba a rayuwarta,mintsinin kanta tayi dan tabbatarwa”kodai mafarki nake”, ta fara tanbayar zuciyarta,”Aah ba mafarki kikeba “ta kara jin saukan muryarsa , kara fashewa da kuka tayi fuskarta duk ta hada zufar wahala “ na rokeka koma wanene kai kayi hakuri ka kyaleni, ni ban muku komai ba”, be ce mata komai saima biyota da ya fara cikin tafiyar macijar, itama baya ta faraja tana girgiza masa , wani dan kwanan da ta gani tayi saurin dauka da niyar kwala masa , kamar wacce ta tuna wani abu sai ta tsaya tana kallansa”Mewam”a hankali ta fadi sunan, cikin sauri majicin ya karasa jikinta yana zagayeta , itama sai faman dariya take , duk wannan abun ba wanda ya farka daga baccinsa duk da tsananin ihun da ta kwala.
Chapter 8 · 0% Book details