← Book details Gidan Aunty Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 23

Sashe 2

Gidan Aunty Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰
GARIN LAGOS
Wasu dankara dan Karan Motocine kefaman zuga gudu akan titi, duk Wanda yazo wucewa sai ya tsaya motocinnan sun wuce tukunna sabida tanbarin da motocin ke Dauke dashi .Duk uban motocinnan basu tsaya a ko ina ba sai a NAHYAN HOSPITAL, one of the best hospital in Nigeria , ba karamun hospital bane da kallo daya zaka masa kasan ba karamun kudi aka kashewa asibitin ba , Kai tsaye wajan parking space suka nufa , cikin wani irin slow motocin suka tsaya , Wanda hakan ba karamun birge masu wucewa yayi ba . Bude motocin akai , wasu blacks American ne suka fito daga cikin motocin ko wannensu sanye da bakin suit da sunglasses,fuskarnan ba fara’a kwata kwata , yayin da hannunsu ke dauke da bindigogi. Daya daga cikinsu ,Wanda ya kasance kamar ogansu ne ya nufa wata black tinted Lamborghini sai faman sheki da daukar ido take.bude kofar motar yayi sai da aka dau kusan 40 seconds kafun ya zuro da kafarsa Guda daya , tubarkallah Masha Allah , wani irin takalmine a kafarsa kamar na sarauta, fatar kafarshi sai faman daukar ido take, wacce take fara kal cikin takalmin kafarsa, an dau kusan 2 minutes kafun mamallakin kafar fitowa. Oh my god , tubarkallah masha Allah , tabbas Allah madaukakin sarki yayi halitta anan, ba kowa bane face TAHNOON , one of the youngest billionaire kenan, daga tsohon president zayed Al_Nahyan, irin su ake kira one in thousand,dan guy din ya hadu tako ina ba Karya. Sanye yake cikin kuftan sai faman maiko da daukar ido take , wacce ta kasance blue colour , bakaramun kyau tayiwa surar jikin saba , wacce ta kasance kakkar fa, kallo daya zaka masa kasan yana motsajikin sa ,farine irin asalin fari mai shegen kyau da tsari, yana dauke da wasu irin sexy eyes fari tass dasu, kwayar idanshi ba Baka bace sannan ba brown bace ,wasu irin idanuwane dashi mai ladaftar da makaryaci, Wanda idanuwansa ba karamun tafiyar da yan mata yake ba, hancinshi dogone ba irin over dinnan ba, amma dogone da yayi matukar yiwa fuskarsa kyau , bakinshi dan madaidaicine Wanda ya kasance pink colour , yana da saje a fuskarsa wanda ya hade da gyaran fuskarsa. Kallo daya zaka masa kasan irin mutanan nanne da ake Kira half cast , ta ko ina gayen nan ya hadu, cikin taku da kasaita ya fara tafiya , Wanda da yawa mutane suke wa kallan girman kai, musamman in ya hadu da kasaitarsa da muskilanci , dan ba karamun miskili bane na bugawa a jarida, amma a hakan ba karamun tafiya yake da imanin mutane ba .
Direct cikin premises din hospital ya nufa , duk inda ya wuce sai ma’aikata da majin yata sun gaishesa , daga musu hannu Kawai yake ,yayin da wadannan kattin ke binsu a baya , Daidai wata kofa naga sun nufa wacce ta kasance ta glass , kai tsaye wannan mutumin dazun ya bude masa kofa , lifter ce a wajan , shi kadai ya shiga wajen tare da wannan mutumin , yayin da Sauran suka tsaya . A flour 4 suka tsaya inda yakasance bakowa a wajan ( abun mamaki sai na tarar da wannan kartun sunja layi kamar masu jiran karban sadaqa😂), duk inda ya wuce sai sun Sara masa . Daidai wata kofa suka tsaya , anan ma wannan mutuminne ya bude masa kofa , tafiyar muntuna 2 biyune ya kaisu wata kofar , wata koface tsararriya a wajan me shegen kyau , direct cikin kofar suka shiga , babban office ne iya tsaruwa office dinnan ya tsaru, daga gefan hagunsa wasu dan ubansun cushion chairs ne masu shegen daukan ido ash colour , medium carpet din office din ma ash colour , daga gefan damansa kuma wani gadan duba marasa lapiya ne , daga inda kake kana iya hango table dinshi sai faman daukan ido yake ( irin na yan gayun nan😂), wajan sai faman daukar kamshi da sanyin freshener yake . Samun waje yayi kan daya daga cikin cushion chairs dinnan yayi tare da crossing legs, kallan mutuminnan yayi , cikin husky voice dinsa ya fara magana ,”zaki” shine Sunan da naji ya Kira mutuminnan Wanda in ba natsuwa kayi ba bazaka taba Jin mai have ba, “yes sir “Cewar zaki , “yaushene meeting dinnan”, “sauran few minutes sir “cewar zaki, jinjina masa kai kawai king Yayi tare da Mika masa wasu files karba zaki yayi tare da Sara masa tare da ficewa daga office din , duk wannan abun da yake fuskarshi kwata kwata ba annuri a ciki , ba a dau dogon lokaci ba daya daga cikin wayoyinsa ya fara ringing , sai da ta kusan katsewa sannan ya dauki wayar dake kusa dashi akan center table din gefenshi , UKTI shine sunan da ya bayyana akan screen din wayar , ajiyar nunfashi ya sauke ganin me kiran, dauka yayi cikin kamilalliyar muryarsa, “Assalamu alaikum”Shine abunda yace , ya dau sakanni kafun ya sake cewa komai, “masa’ul khair ukti( barka da Yamma yaya)”, bansan mai akace masaba amma ganin yadda ya natsu zai tabbatar maka da magana ce me mahimmanci suke tattaunawa,ya dau kusan 10 minutes yana wayar wacce ba abunda nakeji a ciki kasancewar cikin larabci yake maganar , baka Jin sautin muryarshi sai bakinsa dake motsawa, a haka zaki yazo ya tarar dashi , sannan suka dunguma zuwa inda aka kebanceshi dan yin meeting . Sun dau kusan 1 and half hours suna tattaunawa game da asibitin da kuma tsare tsaren da za a sake , basu sukabar NAHYAN HOSPITAL ba sai wajan karfe 5 na yamma, Kai tsaye NAHYAN ESTATE dake cikin BANANA ISLAND suka nufa .

🌹GIDAN AUNTY🌹

By mss Lee💕

👑 UK WRITERS 👑

https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA

🫶 Dedicated dis page to my masoyiya ‘yar fillo ta zara’u our star lady ! I heart ❤️ you 🫶…

PAID BOOK

BOOK 1 📕
……………..بسم اللهً الرحمنً الرحيم

Free Page 2🦋

➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰
WACECE TAHEERA
TAHEERA yarinyace yar kimanin shekara 17 da dan biyunta TAHEER Wanda suke tsananin kama kasancewarsu yan biyu. Mahaifinsu Malam Mohammad nada wadatarsa kafun yasamu karayar arziki ,yarasu shekaru biyar baya , Wanda a kazo har gida akwai wa kisan gilla, kisan da haryanxu ba’a san ko suwanene ba , yana da mata guda daya me suna maryam wato oummansu taheera , haifaffiyar buzuwace fara tass da ita daga kasar Niger , anan suka hadu da mahaifin su taheera, Wanda yazo kasuwanci kasar. Mahaifiyarsu marainiyace wacce iyayenta suka rasu bata da kowa sai yayanta Wanda tun lokacin baya daya fita da daddare ba’a karajin labarinsaba .
Bakaramun wahala da gwagwarmaya suka shaba arayuwarsu , tun bayan rasuwar mahaifinsu taheera , kasancewar dangin babansu basu so ya auretaba, sun so ya auri yar dangi amma malam Muhammad ya nuna baya Santa maryam yakeso . Bakaramun wuya maryam Tasha ba a hannun dangin mijinta, babu me kaunarta sai KILISHI, wacce ta nuna mata so, ta tallafi yayanta har bayan mutuwar yayanta. Kilishi kanwace ga Malam Mohammad wacce suka hada baba dashi kasancewar shi kadai mahaifiyarsa ta haifa sai yan uwa . Ba karamun rawar gani ta taka arayuwarsu ba sabida irin yadda take temaka musu.Itace mace kwallinkwal da take fadar magana aji atake a wajan dalilin Auran wani hamshakin me kudi da take a Garin Lagos , shiyasa duk dangi akejin maganarta.Bayan shekara biyu da rasuwar Malam Mohammed, Malam bashari yanuna Yanasan auran maryam amma kememe maryam ta nuna bazata iya aure ta bar ‘ya’yanta ba , ba irin magiyar da Malam bashari beyiba har maganar tazo kunnen hajiya kilishi, sanin cewa bazata iya yiwa hajiya kilishi musu ba yasa ta Amince amma da Sharadin tafiya da yayanta. Wannan abu beyiwa Malam bashari dad’i ba amma haka yabar abun azuciyarsa. Hajiya kilishi ita ta dauki nauyin kome da kome na bikin maryam, tundaga kan kayan daki da sauransu, shiyasa ba karamun ganin girman matar takeji ba. Shiganta gidan bashari ba karamun wahala Tasha ba ita da yaranta, sabida tsangwaman da ake nuna wa ‘ya’yanta hatta abinci baya bawa ‘ya’yan maryam , ko ta tanbayeshi dalili kaitsaye ze ce mata sabida bashine ubansu ba. Wahalar dasu d’in da yake ne yasa maganar har taje kunnen kilishi Wanda takirashi tayi masa tatas harda i’kirarin zata kulleshi sannan ya saduda. Malam bashari yana da matarsa daya kafun ya auro maryam, asabe kenan wacce suke kira da mamy, mamy wata irin muguwar matace da batasan zaman lapiya , duk wani kulli kulli da tashin hankalin dake faruwa a gidan harda sa hannunta, da farko taso kullum su dunga danbe amma ganin maryam bata biye mata yasa ta canza taku take biyowa ta bayan malam bashari.yar ta d’aya Ameerah , yarinyace fitinanniya bata jin magana , ga rashin kunya a cikinta , Ameerah ta tsani y’ay’an maryam kasancewarsu farare tass kamar ka taba namansu ya fashe wani irin kyaune da su da baki baze musaltaba musamman tahee da take da asalin gashin buzaye har kugu, kasan cewar mahaifiyar su buzuwa mahaifinsu kuma bafulatani . Dalilin da yasa mamy da yarta suka dauki Karan tsana suka dora musu, dan ko ita mamin tasan maryam ta wuceta akomai amma sabida harsada da kyashi taki barinta, a haka har suka kwashe tsawan shekaru uku kafin yanxu rabuwarsu da Malam bashari.
Chapter 2 · 0% Book details