← Book details Gidan Aunty Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 23

Sashe 15

Gidan Aunty Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

************
ILORIN
babban waje ne katafaran gaske , me dauke da abubuwa mabanbanta a cikinsa , ba karamun makudan kudi aka kashe ba wajan gina falon, komai na cikin falon red colour ne tundaga kan carfet har zuwa kan labulayen dakin, hatta mutanan dake tsats tsaye ko wanne fuskarsa a rufe , matan sanye suke cikin jajayen kyalle iya gwiwa , yayinda mazan suka sanya dan karamun jan kyalle da ya bude al’aurarsu, magana suka fara cikin wani irin yare Mara dadin saturate, kasancewar falon babbane hakan yabasu daman Jan layi kowannansa dauke da glass cup ne Jan abu acikinsa, Yaren suka cigaba dayi , sunayi suna sunkiyar da kansu, wani hayakine ya cika falon , yayinda wata murya Mara dadin ji ta farara babbaka dariya, sannu a hankali ta koma ta jarirai, a haka karuwar muryar nan ta kuma karade ko ina da dariya , data gama sai kukan jarirai suma, an dau lokaci ana haka kafun hayakin ya dauke.
Wata katuwar matace ta bayyana a falon , baka kirin da ita fuskarta dauke da wasu kananan kuraje ba kyan gani, durkusawa sukai baki dayansu tare da yi mata sujjada(wa’iyazubillah), sosai suka shiga yi mata kirari”shugaba me share mana hawayen mu, kece farin cikin kowa ne halitta , kece maganin kukanmu, kamar yadda kika saba share mana hawaye “, dariya Matar nan ta fara kafun lokaci daya ta hade ranta kamar ba yanxu ta gama dariya ba, cikin kakkausan murya ta soma magana “ lokaci yayi, lokaci yayi da zaku mallaki duniya, duniya takuce , mu kuma mune abun bautawanku, saura Kiris komai yazo karshe, tabbas aikin ku ya fara zuwa gangara “, kallan daya daga cikin mutanan falon tayi, “abar kauna”shine sunan da ta kira , wacce aka kira da abin kaunace ta fito tsakiya, “tuba nake me sharemun hawaye , tuba nake shugaban dudduniya”, shafa kanta wannan bakar matar tayi , “tabbas kaso mafi yawa na aikin nan yana hannunki,dole ki tabbatar jinin da kika dade kika kiwo ya kwaranya ga dodon tsafi , muna bukatar jinin kafun nan da mako biyu”kara sun kuyar da Kai Wadda aka kira da abar kauna tayi “Godiya muke abun bautarmu tabbas babu me share mana hawaye seke”kara hade fuskarta tayi tare da bin abar Kaunar ta da mayataccen kallo,Tashi tsaye abar kauna tayi , tare da rungumar bakar matar nan, matseta sosai matar tayi ajikinta tana shinshinar wuyan ta kafun lokaci daya su bace a falon ,sun kuyar dakai ragowar mutanan falon sukayi kafun ko wannansu ya buga cinyarsa sau uku,suna gama bugawa wani bakin hayaki ya cika falon, lokaci d’aya hayakin ya dauke, sabanin dazu, yanxu ba kowa a falon.

*************
LAGOS

zaune ammi take kan daya daga cikin sofa din falo, sosai taci ado cin ash din material sai faman walwali take , ga sanyanyan kamshi dake Tashi a jikinta, iya haduwa ammi ta hadu , har yanxu fuskarta dauke da murmushi akai kamar kullum, lokaci zuwa lokaci takan duba agogon wayarta , ganin 9:00 ta kusa yasa ta mike wa , hart fara taku zata bar Wanjan, daddadan kamshin turaran king ya cika falon, jiyowa tayi tana sakar masa murmushi, shima narkakkun ida nuwansa ya zuba mata yana binta da kallo, har ya karaso wajan, hannunsa guda daya yasa tare da kamo na ammi ya zaunar da ita, har lokacin be ce komai ba , kusan mintuna daya kafun ya ce mata”kinyi kyau” sosai hakwaranta ya fito waje jin abinda yace “kaima kayi kyau son , kamar Wanda ya dawo daga zance”, dan tabile bakinsa yayi tare da kawar da zancen,”coffee ammi” har ta bude baki da niyar bashi amsa wayar hannunta ta soma ringing, tana zaunan ta daga kusan mintuna biyu kafun ta kashe ,mikewa tayi tare da nufar kitchen , a tsaye ta tarar da tahee da asabe suna aiki, kallan asabe ammi tayi a hada coffee a kaiwa son , kinsan baya san jira , tana gama fadar hakan ta bar kitchen din, hannu asabe ta dora a ka “na shiga uku na lalace”sai kuma ta shafa kumatunta, tuni jikinta ya hau rawa, ita tahee dariya ma abun ya bata daga cewa takai coffee har da yar kwalla , bata ce Mata komai ba sai binta da kallo da take,girgiza kai kawai tayi atunanin tayi coffee din ne bata iya hadawa ba shiyasa duk ta zure haka “kawo kayan na hada miki”, sosai asabe ta shiga yi mata Godiya kamar zata zugunnata mata, kayan coffee din kuwa ta dakko mata , tare da nuna mata coffee maker din, bata san yadda ake anfani dashi ba, da temakon asabe ta hada coffee din da ko a ido sai ya burgeka, neman hanya guduwa asabe , tana ganin tahee ta kammala hadawa, tace mata bari taje ta dawo, TAHEE bata gane ba sai jinjina mata kai da tayi , kusan yan mintuna ganin coffee din na kokarin jin sanyi yasa ta dauka hankali kwance tare da nufar falon, agaban idan asabe dake bayan kofa sai faman hada zufa take, da sallamarta t shigo falon, Sam ta manta coffee ne a hannunta sabida dandanan kamshin da ya cika mata hanci, kanta a kasa sai faman murmushi take, jin tana kara kusanto kamshin da takejine yasata lumshe idanuwanta,sosai yanayin falon yayi mata dadi, da bugawa kadan kadan da zuciyarta ke mata, bata ankaraba taji ta taka abu, a firgice ta bude idanuwanta, tsabar firgita bata san lokacin da kofin coffee din ya subuce mata ba ,baya baya tayi zata fadi, sosai ta rintse idanuwanta dan ta sadakar faduwa zatai….

Comment and share 😎
Daga alkalamin Mss Lee 💖

💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖

💖DUK KARFIN IZZATA (star lady)💖

💖GIDAN AUNTY( mss Lee )💖

💖YA FITA ZAKKA( maman sayyid )💖

💖JINI DAYA (mrs bbk)💖

💖SARKI SAMEER( xeenat love )💖

‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA

💖💖💖GIDAN AUNTY 💖💖💖
( a heart touching love story )

Story &written
By
Mss Lee 💖

💖💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖💖

PAID BOOK

Dedicated this page to masoyiya and the talent troupe writers, masoyiya I heart ❤️ you Lodi Lodi.

Book 1 💖

Free page 13🦋

Sosai ta rintse idanuwanta , tsawan yan sakanni jin bata fadi kasa ba kamar yadda tayi tunani, hakan ya bata damar fara bude idanuwanta a hankali cikin fargaba, akan fuskarsa dake hade sosai idanuwanta suka sauka , ta manta a yadda take sabida shagala da tayi da kallan kyawun fuskarsa, tsawar daya daka mata a lokaci daya da sakin gefen rigarta ne ya firgitata, ga kafarta dake mata zugi kadan kadan adalilin sakin ta da yayi ta fadi, a hankali ta saki wata yar karamar kara tana rike kafartata “are you mad” taji kausashshiyar muryarsa cikin dodan kunnanta, girgiza masa kai tashiga yi , sosai ta tsorata da yanayinsa ko kallansa ta kasa,ba karamin baci ransa yayi ba ganin yadda ta basa amsa “are you mute” takarajin saukar muryarsa, nan ma kai tashiga kokarin girgiza masa,wata gigitacciyar tsawar data sata mikewa ya daka mata , bata san lokacin da ta fara “kayi hakuri dan Allah “, ta karasa a hankali tana sun kuyar da kanta kasa , dan siririn tsakin da ko ita bata jisa ba yasaki tare da komawa inda ya tashi ,”clean this mess, and bring my coffee”, ya fada a takaice har ynxu fuskarsa ba a kanta yake ba, da sauri ta jinjina masa kai sai kuma tayi saurin bude baki “toh” tana gama fada ta koma kitchen, cikin kankanin lokaci ta gama hada coffee din da sai faman kamshi yake , cikin wani dan cup me shegen kyau , a hankali tayi sallama cikin rawar murya, kamar ba zai amsa ba kuma sai ya bude bakinsa a hankali”Wa’alaykumussalm “, ko ita da ke shigowa falan bana tunanin taji , cikin rawar hannu ta karasa inda yake , duk kamshin turaran sa ya cika mata kunne , so take kawai taga ta kebance, kusan mintuna daya bece komai va kuma be amsa coffee dinva, saida ta gaji dan kanta kafun tace “gashi”kamar me kokarin sakin kuka , nan din ba bai amsa ba saida ya mula dan kansa sannan ya saka fararan hannunsa ya dauka a hankali, wani sanyayyar ajiyar zuciya tahee ta sauke ganin ya karba , sai ta koma kitchen ta dakko abunda zata gyara inda ta bata , a hankali take yin komai duk da yadda zuciya da jikinta ke rawa,cikin kankanin lokaci ta gama gyara komai ta mayar kitchen . Tana shiga bata tarar da asabe ba aciki, tunani ta fara ta tafi daki ko tajira ya tafi, dan harga Allah shakkar fita take, ta dau kusan mintuna ashirin a kitchen ganin lokaci yaja atunaninta ya tafi zuwa yanxu, Daidai ta kai tsakiya falon sabida yadda tasawa ranta ya tafi sai jin muryarsa kawai tayi a fiske “coffee” daga nan be kara cewa komai ba.”Innalillahi “ shine abunda tahee ta fada cikin zuciyarta kafun a hankali ta nufi kitchen kamar wata muna fuka , wani coffee din Ta hado masa, yanxu cikin rawar murya ta bashi, kamar dazu sai da ya gaji dan kansa sannan ya karba, ta juya da niyar komawa ta kara jin saukar muryarsa “wait”,ji tai kamar ta fasa ihu a wajan, gashi tana tsoran ta tsugunna kartaje tai wani laifin , tsawan mintuna goma tana tsaye bece da ita komai ba ,cikin dan guntun tunanin da ta fada ta kara jin saukar muryarsa “coffee”, kukane kawai tahee bata saka ba a haka ta koma ta kara hada wani coffee din ta na kawo masa bata jira cewarsa ba ta arta a guje sai cikin dakinta. A hankali ya dago da kyawawan idanuwansa “ is she mad “ ya tanbayi kansa sai kuma ya tabe baki tare da jan siririn tsaki a haka yaci gaba da sipping coffee dinshi a hankali,kusan 11 na dare yana falon kafun ya nufi nashi part din.
Chapter 15 · 0% Book details