← Book details Gidan Aunty Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 23

Sashe 7

Gidan Aunty Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*******
Zazzaune ko wannansu yake a falon , ko wa ka gansa cikin farin ciki da annashuwa, daga gefe daya wasu yan matane su su hudu zAune a wajan sai faman hirarsu suke , daga Dayan side din ma wasu manyan mutane ne ke tattaunawa. A hankali kamshin turaransa
Da baya boyuwa ya kara de ko ina na cikin falon, lokaci d’aya falan ya dauki shiru kowa hanyar shigowa ya zuba wa ido, a hankali yake taka kafarsa har ya shigo falon , fuskarsa kwata kwata ba alamun murmushi sai ma kara kadeta da yayi, sosai farin kayan jikinsa ya futo da tsantsan kyawunsa,motsa bakinsa yayi ciki ciki da yin sallama, a tare falon suka amsa dan ba wai sallamar sukaji ba ta motsin bakinsa suka gane. Zoyace ya taho da gudu da niyar rungumeshi, kallan da yayi matane yasata Jan burki “ana asf akhi( am sorry brother )kwalla harta fara tarar mata, lumshe idanuwansa yayi tare da bude mata hannusa guda daya , a guje ta karasa wajan sa tare da rike hannunsa” welcome back akhi , I missed you the whole day”, lumshe mata ida nuwansa yayi tare da budewa kasa kasa ya amsa mata “ me too”, direct inda mahaifinsa yake ya nufa, zazzaune ko wannansu yake cikin takaitaccen magana ya gaishesu, kowa amsa masa yayi sai faman binsa da kallo suke , abeey sai faman sakin murmushi yake . Hajiya Amina ( uwar gidan uncle musaddiq) wacce ake kira da mamy ce ta soma magana “ Kai dai king kayi wuyar gani, ba a ganinka Indai ba a part din dada ba ko na ammonia”, matar uncle Saleem ce ta Dora “ Aushe duk kanwar jace “. Murmushi ammi ta sakar musu “ Kude kawai kun fada ne”, mikewa king yayi tare da nufar wani sofa dake can gefe dasu, kallan dada zoya tayi, cikin tsokana ta kira sunan ta”dada”, harara dada ta wata a mata “kinibabbiya ba kiran Allah da annabi kikai mun ba, tunda kinga ubanki ai dole kikashen murya”,langwabar da Kai zoya tayi “Haba my dada nasan akhi na beci abinci ba , he need some coffee before eating”, tsaki dada taja “ ke kika sani kuma inma zagina kikai ba na hanaki yimun magana cikin yaran nasara ba, wani wai kamfin ( coffee)ke kika sanshi”,kowa na falon yadda dada ta kira coffee din sai da yaso basu dariya amma ba damar yi harta king maganar taso bashi dariya amma sai wani hade rai da ya kara.kallan akhi dake gefe zoya tayi, saurin daga mata hannu yayi alamun ba ruwansa ,maida kallan ta tayi kan ummey , itama dauke idanuwanta tayi daga kanta,mikewa ammi tayi nida ba a sako niba bari na bada coffee din, kulle idanuwanta zoya tayi tana dariya ,daya Daga cikin yan matan ne ta mike, kallanta ummey tayi amrah ina zuwa, cikin in ina wadda aka kira da amrah ta soma magana “dama zan taya ammi ne”jinjina mata kai ummey tayi , direct kitchen din dada ta nufa , basu dade ba suka fito daga kitchen din cikin yanga amrah ta ajje masa tray din abincin, “yaya king sannu da hutawa”, kamar wacce tayi magana da dutse yana zaune ko motsawa beyi ba ballantana tasa ran amsawa, zoya na gefensa a haka ammi ta fito da cup din coffee sai faman tiriri yake dayan kuma kayan tea ne a ciki da yaki bornviter , mika wa king coffee din tayi , lumshe mata ida nuwansa yayi , murmushi ta sakar masa kafun ta mikawa zoya tea dinta.beci abincin da aka kawo masa ba sai coffee dinsa da yake sipping a hankali yana gama sha ya mike tare da ce musu “good night “yana gama fada ya kama haryan fita . Cikin daga murya zoya ta soma magana “Laylat saeidat akhi, uhibuk( good night brother, love you)”,girgiza Kai kawai king yayi da barin part din. Sai a sannan yan matan suka tare da cigaba da hirarsu, dummy ce ta kalli amrah , Lalle amrah da raban kin kusa Shan Mari a wajan yaya king, Kinsan halinsa Sarai ba a burgeshi, cikin kasa kasa ihsan tace Garin masoya baya nisa kunsan yadda take mugun sonsa,murmushi amrah ta saki jin abinda ihsan tace “dadi na dake ihsan kin fisu fahimtar abu”ni kadai nasan yadda nake sanshi kumashidin mallakinane, dariyar mugunta firdausi ta saki , cikin kasa kasa da murya tace “mugani a kasa”, hararar ta amrah tayi dan Tasan itama san king take shiyasa basa shiri sosai , duk wannan magan ganun nasu cikin kasa kasa da murya sukai ba mejinsu, dago idanuwanta amrah tayi bata saukesu akan kowa ba sai nan auntyn ta , itama auntyn Tata daga mata hannu tayi alamun jinjina, firdausi ma maida hankalin tayi kan mahaifiyarta lokaci daya suka sakar wa juna murmushi duk wannan abun da suke ba Wanda ya lura dasu .

(Uhmmmm 🤭😟)

💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖

Duk karfin izzata (star lady)
Gidan aunty (mss Lee)
Sarki sameer( xeemat love)
Jini daya ( mss bbk)
Ya fita zakka (maman sayyid)

Comment and share

‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA

💖GIDAN AUNTY💖

( A heart touching love story)

By mss Lee

💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖

PAID BOOK

BOOK 1 📕

Free page 7 🦋

Not edited

Zaune Suke su biyu cikin wata katuwar masarauta me shegen kyau da daukan hankali, duk Wanda yazo wuce wa sai ya duka musu tare da gaishesu, TAHEER ne ya fito cikin wata kofa sanye da wasu kaya na alfarma masu tsananin kyau ba karamun kyau yayi a cikinsu ba , hannunsa dauke da wani siririn maciji fari tass dashi, Daidai inda tahee take ya nufa, zaune take cikin shigar alfarma na kayan sarauta , gefe da gefe masu yi mata fiffi tane ko wananne kawunanshi akasa, tanbarin macijin dake bayanta ya fito radau dashi, murmushi ta sakar masa ganin ya karaso inda take, shima murmushin ya sakar mata tare da Mika mata kyakkyawar farin macijin, mikewa tayi sosai tare da karban macijin, a daidai kan cinyarta ta dora macijin , shima macijin lumshe idanu yayi kamar mai jin bacci, kallan taheer tayi da mamaki dauke a fuskar ta,” kyauta ne na baki yau shekara 300 daidai da haihuwarki, zai debe miki kyewa “cewar taheer, tsananin farin cikine ya bayyana a kan fuskar tahee “ oh my god , nagode SIF” , jinjina mata kai kawai yayi , har ta bude baki zata sake magana sai wasu siraran hawaye suka zubomata”ka tuna lokacin da Nonna ta bani kyautar maciji kamar haka , amma sun kashe mun shi, sun kashe mun nonna , sun kashe mun susan”, shima girgiza mata kanshi ya shiga yi”Lola Raina yana baci duk lokacin da na turo wannan bakar ranar, kamar randa suka rabamu da nonna da susan Muma baza mu kyalesu ba,ga memaw nan ki rikeshi kamar yadda kika saba da susan, shima zaki soshi sosai”, yana gama fadar haka ya bar wajan , murmushin yake ta saki tana hadiye abunda ya tsaya mata a makogaro,kallan memaw din dake kan cin yarta tayi kafun ta kira sunan shi,”memaw”, bude idanuwansa yayi masu kalar baki tare da fara yawo a jikinta yana zagayeta , hakan ba karamin nishadi yasa taba, sai faman yawo suke , saida suka gaji dan kansu sannan suka tsaya har lokacin mucijin be dena yawo a jikinta ba.TAHEE!!TAHEE!!! A firgice ta farka daga baccin da take bakin ta dauke da adduar tashi daga bacci, kallan ta oumma tayi ganin yadda ta jike da zufa duk da kasan cewar akwai dan zafi zafin da ake ,”lapiyan ki kuwa”cewar oumma , saurin girgiza mata kai tahee tayi “ mafarki kawai nayi”, shafa kanta oumma tayi “ki kwantar da hankalinki mafarki ba gaskiya bane sannan ki dunga addua “nanma gyada mata kai kawai tayi,tunda umma ta fita a dakin kuma bata motsa ba mafarkin da tai na yi mata yawo aka“ NONNA,LOLA,SIF,SUSAN,MEMAW!? Sudin su wanene!? Maciji fa !?” Macijin da ta gani a mafarkine yashiga yawo a kwakwalwarta, amma sanin cewa mafarki ba gaskiya bane yasata share zancen tare da mikewa ganin oumma na kokarin shigowa dakin.

Bayan sallar azahar kamar yadda suka saba bayan sun kammala ayyukansu, zama sukai suna hira , lokaci zuwa lokaci tahee sai ta dako ta kalli taheer har yanxu mafarkin da tayi yana mata yawo a ka , duk lokacin da tayi tunanin mafarkin sai taji wani abu kamar ya tabata, yanxu ma dago da fuskar ta tayi tana kallan taheer, hararar ta yayi ganin tun dazu sai faman binsa da kallo take kamar wata me aljanu “na canza miki ka manni ne kike faman bina da kallo fisabilillah”,cewar taheer yana hararar ta , murmushin da yafuto da dimples dinta ta saki”gani nai ka kara kyau kamar wani balarabe “ ta karasa maganar tare da kashe masa ido daya,yanxun ma wani hararar ya mata “dadin abun bake kadai ce me kyau ba, da nice mace ma kyan da zanyi sai nasaka maza kuka”, dariya duk suka saki, oumma ta girgiza kanta “Allah ya shiryeku “.
Chapter 7 · 0% Book details